Showing 108001 words to 111000 words out of 253142 words

Chapter 37 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18423

na tafi"

Ya daga mata kafadunsa alamar he don't care. Da sauri ta yi gaba da abinci ya bi bayanta har ta shiga dakin da Tasmia take, tana zaune kan gadon tana waya Emily ta shigo, shigowar Aliyu ya saka ta yanke wayar tana yana jin wani yanayi da dabam tare da mamakin ganinsa a lokaci daya.
Emily ba zata iya fadar zata je gurin aiki ba saboda kar Tasmia ta ji kamar ta fifita aikinta akan lafiyarta dan haka tace.

"Ga abinci nan ki karya, zan tafi yanzu ina da uzuri"

Ta kalli Aliyu sannna ta fice Tasmia na mata godiya murya kasa kasa.

"Ina kwana"

Tasmia ta fada bayan Emily ta fice ta bar Aliyu. Madadin ya amsa mata sai yace.

"Do you plan all this?"

Ta sake dubansa kamar da can ba kallonsa take ba.

"Ban fahimta ba"

"Kin fahimta Tasmia, don't deny it, Emily tace ba ita ta aika sakon nan ba"

"Kuma ka yarda da ita?"

"=??? percent"

Ta nuna kanta gabanta na faduwa sosai.

"To miyasa ni ka zarge ni? Me zai saka na aikata hakan? Yaushe ma na dauki wayar Emily?"

Ya saka hannayensa duka biyu aljihunsa.

"Ban sani ba tukuna, abun da na sani a yanzu shi ne Emily ta yarda dake, ban sani ba ko ta fada miki labarinta, ta sha wahala sosai kamin ta hadu da mu, ta hadu sa musulmai masu gurbatattaccen tunani da son zuciya sun bar mata tabon da take kallon kowane musulmi ma haka yake, sai dai haduwata da ita da kuma ke ya fara sauya tunaninta, toh be kamata ta same mu da wani nakasu ba, ko da musulma ce be kamata mu ci amanar junanmu ba, kuma mu watsar da yardar mutanen da suka minta da mu"

Yana kaiwa nan be tsaya jiran abun da zata fada ba ya fice ba tare da ya bata hakurin zubar hawayen da take ba. Sai da ya fice sannan ta share hawayenta.

"Shi namiji na gari nemansa ake ba sai ya kawo kansa ba, yadda Kameela tana walawa a gidanka tana watayawa abun so ne a gurin kowace mace, ko da ace baka da kyakkyawar sura kulawarce kawai, dole zata burge duk wata mace mai son auren namiji irinka, ballantaba kuma ka hada duka biyun ko uku ma, ga kyau ga kudi ga bada rayuwa irin wanda mace take so, ku kanku maza wata rana ba kusan wanda ya dace da ku ba, Aliyu kana bukatar mace mai hankali mai wayo ba irin Kameela ba"

Ta sauka daga kan gadon

"Kowa da kalar kaddararsa wata kila ni tawa a haka ta zo, son mijin kawata ko ba komai matarka ta kira ni da marar tarbiya kuma ta yi min gorin aure, toh sai na nuna mata rashin tarbiyan, kuma sai na koya mata darasin da ace kewa mace bata yi ma yar'uwarta mace gori"

Ta zauna a kujera ta bude abinci.

"Sai kace ni na fi kowa bakin jini daga fara plan har ya gano ni, wai ni haka rayuwata zata kare ne? Kalar mazan da nake son aure basa zuwa su ce suna so na sai yan wadanda basa cikin tsarina kamar ni na fi kowa bakin jini, gaskiya ba zan bari Aliyu ya subuce min ba, daman tun ganin da na yi masa da farko ya burge ni"

Tana cin abincin tana magana da kanta kamar wata tabbabiya.


KAMEELA POV.


"Ai dama ya samu shiyasa kuma kin ji hausawa sun ce kowa ya ga rana yayi shanya, da bata karya farashinta ba tun farko ta zubar da kimarta Wallahi Aliyu ko marin uwarsa kike yi be isa yace ki dawo gida sai ya neme ki ba? Me yake takama da shi?"

Cewar Hajiya Asma'u Anty taba ya tsina fuska.

" Wallahi kuwa nan kika watsa mana kasa a ido kika tsaya kai da fata babu mai son auren nan kika ce sai Aliyu, gashi nan tun ba aje da nisa ba ya koraki ya nuna wata banza ta fiki muhimmanci ina alkawarin da yayi miki toh?"

"Alkawarin banza, dadin baki ne irin na maza kuma ni daman na san ba da zuciya daya ya aureta ba, ya aureta ne kawai saboda ubanaa ya karbi mukamin ubanki a yanzu, ke kuma ya aure ki ya wulakanta mu, kuma yayi nasara tun da kin ba shi hadin kai"

Hajiya ta fada, sai Anty Shafa ta sake karba mata

"Ai kara ma auren ya kare kowa ya huta, idan abun be tsaya iya nan ba gaba ba a san ya zai kasance ba, kuma dan Allah Hajiya ki hana D
Alhaji kiransa dan jin ba'asi ko kiran iyayensa"

Hajiya ta daga hannu.

"Ai Alhaji ma ya fini daukar zafi shi da kansa yace tun da ya turo masa ya gida sai ya san yarsa tana da gata"

Ganin ba za su barta da damuwar abun da ya isheta ba ya saka ta tashi ta bar musu bangaren gaba daya ta koma part din Mama Barakat ba dan ranta ya so ba, kan kujera ta zauna tana rushe da sabon kuka bayan wanda ta sha har ya kumbura mata ido ya hana ta cin abinci tun da ta dawo gida.
Mama Barakat ta aje abincin dake hannunta ta taso da sauri ta dawo kusa da Kameela dake zaune kasa ta zauna kan kujera.

"Subhanallahi Kameela lafiya? Yaushe kika zo?"

"Aliyu ne yace na tafi gida sai ya neme ni"

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un Me kika masa?"

"Ban masa komai ba, saboda wannan bakar kafirar ne, ba ma ita kadai ba har kawata yake bibiya"

"Abun be yi dadi ba, amman kin yi bincike? Kar ya zama kin masa mumminar fahimta ne, ko kuma kim yanke hukunci cikin fushi"

"Mama Baraka har test fa Emily ta turo min tana fada min magana son ranta"

Mama Baraka ta yi shiru na mintuna tana shafa Kameela alamar rarrashi sannan tace.

"Kina da hoton Emilyn ne Kameela?"

"Ba ni da hotonta"

Mama Baraka ta sauke ajiyar zuciya domin tun a fadansu na farko take son ganin hoton Emily saboda yadda Kameela ta siffanta ta.

"Ki yi hakuri idan mahaifinki ya dawo zamu yi magana da shi"

"Aa ni na hakura ba zan koma ba, kar ma ki masa magana ko Aliyu ne autan maza ni ba zan koma gidansa ba"

"Ba'ayi ma aure haka, tun har kuna son junanku baki san abun da Allah ya tsaro a tsakaninku ba, hakuri zaki yi"

Kameela ta kara fashewa da kuka tana fadar ita ba zata koma ba ta hakura da Aliyu.





_______________________

Sannu  yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe Winki da kaya masu kyau, masu ?ima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau?in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taSawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet Winmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau?i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ?ayatarwa duk a farashi mai sau?i.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sau?in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ?ima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki WanWani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haWuwa.
[6/11, 11:51/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing




*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 3?? 4??


Barka da Sallah, Allah ya maimaita mana.

EMILY POV.

Daga Asibiti kai tsaye gurin aikin ta wuce saboda gargadin da Aliyu yayi mata, duk wanda ya ganta ya san zuwan kawai ta yi ba dan ta shirya ba, domin gashin kanta a yamutse yake tufafin jikinta ma regular one ne irin da wanda ta saba sakawa a gida kafafuwanta sanye da talkamin da ta saba sakawa a gida.

A yau din ma data shigo office sai ta rasa me zata yi saboda bata shiryama zuwan ba, dan haka ta zauna a kujerarta taba ta kallo kofa kamar ta san Aliyu zai shigo, after like 30 min ya turo kofar ya shigo fuska ya yabo ba fallasa.

"Ai na dauka ba za ki ji magana ta ba"

Yana maganar wayar dake hannunsa ta yi ringing da ya duba sai ya ga sunan Abokinsa Turhan kuma direct kira irin wanda ba kadafai yake masa ba, ba ma ta whatsapp ba, Aliyu ya kalli Emily dake cizon akaifa ya kalli kiran what a coincidence.

"Sallamu Alaikum"

Ya amsar wayar idonsa na kan Emily.

"Hello Aliyu, ya kake?"

"Ina lafiya ya kwana biyu"

"Alhamdulillah"

Daga haka Turhan be sake cewa komai ba yayi shiru kamar yana jiran Aliyu ya fara magana, Aliyu ma ya kasa cewa komai feeling so guilty.

"Ya Ammy"

"Bata jindadi, ina shirye shiryen shigowa na ganta, Aliyu har yanzu babu wani labari ta bangarenka?"

Aliyu ya dauke idonsa daga kallon Emily ya juya baya yana shafa kansa.

"Ciwon Ammy yana da alaka da hakan ne?"

Turhan ya sauke ajiyar zuciya.

"No Aliyu i want to make things right, mahaifiyata ta yi going through abubuwa marasa dadi a zamanta da mahaifina, and ni kadai ta haifa ni ne kawai last hope dinta and i failed her, idan na zauna na yi tunanin wasu abubuwan ina jin babu dadi kuma ina son na kyautata mata, ina bukatar Emily a yanzu saboda mahaifiyata if i can turn back the clock, zan gyara abubuwa saboda mahaifiyata, I'm losing my sleep bana cikin kwanciyar hankali a yanzu, Aliyu na shiga na fita na yi iya yadda zan iya just to fix what i broken, amman na gagara samun yarinyar nan, kuma mahaifiyata ta ki ta fahimce ni, rayuwa tana ta tafiya ina tsoron kar ni na mutu ko na rasa mahaifiyata ta tafi da wannan kuncin a ranta"

"Hakan yana nufin ka bata abubuwa da yawa Turhan? Akwai abun da baka fada ba?"

Emily na jin sunan Turhan sai ta mike tsaye da sauri ta zagayo gaban Aliyu ta tsaya cikin tashin hankali tana girgiza masa kai.

"Babu amfanin fada, zamantakewa ce ta aure ka auri wanda ba type dinka ba, ba ka sonta dole za a samu wannan, balantana lokacin tunani be tsaya kamar yanzu ba, and Aliyu you will never know what is arranged marriage saboda kai da Kameela auren soyayya kuka yi, komai zan fada maka ba zaka fahimta ba, yanzu dai Maneer ya ba ni shawarar cewar na saka kudi da tsohon hotonta akan duk wanda ya ganta zan ba shi wannan kudin, ya kake ganin abun?"

Aliyu ya ji gabansa ya fadi gumi ya keto masa, be taba aikata wani abu ya ji kansa mai laifi ba irin boyewa Turhan Emily da yayi, anya zai iya bari Abokinsa ya bata kudi akan abun da zai iya masa kai tsaye.

"Hello.."

Turhan ya fada a dayan bangaren, Aliyu ya amsa a rikice yana dawowa daga duniyar tunanin da yake.

"Ehm Hello, Turhan yanzu ina Office bari idan na samu natsuwa na koma gida sai na yi tunanin abun da ya kamata mu yi"

"Okay"

Ya yanke wayar ya kalli Emily.

"Ban san me kuke tattauna ba, amman dai ba zaka fada masa ina nan ba, i trust you"

Ta fada idonta tab da hawaye.

"Turhan Trust me, ke kin yarda da ni to yardar? wa zan karya? Kun saka ni a tsakiya I'm feeling guilty, wadanda ban sani ba ma suna magana da ke like likitan nan na yau? Shi kuma a ina kika san shi? Kina zaune a tare da shi har kina masa dariya bayan abokina yana can cikin damuwa saboda nemanki? Anya na yi adalci"

"Ka riga ka karya nasa tun da har ka kasa fada masa inda nake duk tsawon lokacin ne, hakan yana nufin nawa ya fi karfi a gurinka dan Allah karka karya, idan ya sani ba zai bar ni da yata ba ita kadai ta rage min, kuma baka san iya abun da mutumen yayi min ba i don't need him"

Damuwa karara a fuskar Aliyu, ya nufi kujera ya zauna ya dafe kansa.

"There is something about you Emily, kin saka na yi abubuwa da ba halina ba, like boyewa abokina gaskiya, kamar saka mahaifina ya saka NDLEA su bincike gidan Vito kai tsaye daga Abuja, so that idan an same shi da laifi a dauke shi ki samu yanci, amman kika ci mutunci akan haka, and na kyale haka be bata min rai ba, like sitting here in your office talking to you?"

Ya dago ya kalli Office din sannan ya kalleta. Hawaye ya sauko mata.

"I understand, na yi fada da kai ne akan Vito saboda idan wani abu ya same shi ba ni da mai kula da ni, kuma idan ya gane kai ne ba zai kyale ka ba, ba zan so wani abu ya sake ka saboda ni ba. About Turhan kuma idan kana son fada masa gaskiya amman ka sani cikin rai biyu za a rasa daya ne, nawa ko nasa, domin zan yi duk yadda zan iya na saka Vito ya hana shi raba ni da Fatima, idan kuma har yayi nasarar raba ni da ita, to ni tawa rayuwar bata da sauran amfani, babu abun da zan tsaya yi, ko kuma so kake na dauketa mu yi ta gudu muna boya?"

Tana maganar tana hawaye sosai.

" Daga kai sai Tasmia sai Vito ne abokan rayuwar da nake sa ran idan ina cikin wata damuwa za ku taimaka min"

"Ki cire Tasmia, kuma ki aje Vito a gefe"

Ya amsa mata yana kallonta ita ma kallonsa take kamin ta nufi kofa zata bude.

"Emily dawo ki zauna"

Ta tsaya a gurin na tsawon minti uku sannan ta koma ta zauna kamar yadda ya bukata.

"Fada min irin zamantakewar da kuka yi da Turhan, wata kila hakan zai kara min kwarin guiwar kara boyeki a gurinsa, i trust you ba zan so wani abu marar kyau ya shafe ki ta dalilina ba"

Ya cire agogon hannunsa ya mika mata.

"You can keep this"

Ba zallar agogon yake bata ba, yana tuna mata da rayuwar baya ne, dan gutun lokacin da yayi sanadiyar agogon ya zauna hannunta, what he need is ta fada masa gaskiya kuma ta tuna yadda ya taimake ta kar ta boye masa komai. Ta tara hannunta ya zuba mata agogon ta jimke...!



KAMEELA POV.

Mama Baraka ta dafa ta.

"Kameela ba ni na haife ki ba abu ne da kika sani na sani, na san kuna kallona a matsayin kishiyar uwa wacce bata son ku alhalin ba haka ba ne, yadda ba zan so wani abu ya samu Aleeya ba haka ba zan so wani abu ya same ki ba, da na kowa ne ba mu san inda na mu yayan za su samu kansu ba, dan haka nake rike yayan wasu da amana"

Kameela ta kalleta.

"Me ya kawo wannan maganar yanzu?"

"Ina son zan baki shawara ne a matsayin na uwa, ina son ki kalle wannan ta fuskar uwa ba kishiyar uwa ko matar uba ba"

Kameela ta dan share hawayenta ta natsu.

"Da farko na so na ga hoton yadda yarinyar take, na ga shim me ta fiki da shi da har kike tunanin ta dauke hankalin Aliyu akanki, wata kila ke kika ganin haka amman bata fiki komai ba, kin san wani lokacin mu mata mu muke bada kofar da wasu suke gani har su samu damar juya mu, tsakaninki da mijinki kin fi kowa sanin waye shi me ya fi so me ya fi tsana sai ki kiyaye ita kuma wanda ta dauke masa hankali sai ki duba ki ga dame ta dauke hankalin nasa yawan kyalliya ko kalamai, ko biyayya duk yadda take da shi na san kin fita kusanci da mijinki, kuma ke da kanki ke kika kawo Aliyu kika ce kina so, babu wanda ya muku dole, kuma a yadda na fahimta idan har zan fadi tsakani da Allah Kameela na san ke ce mai laifi duk da ban san abun da ya shiga tsakaninku ba, iya wannan ne ko akwai wani, amman a yadda na fahimta Aliyu mutum ne mai hakuri mai juriya"

Kameela ta yi shiru tana sauraren maganar hankali da mahaifiyarta bata zaunar da ita ta lurar da ita ba.

"Shi zaman aure dan hakuri ne, kuma kowa da kalar jarrabawarsa, wani a gidan mijin ne da wasu abokan zama wasu kuma iyayen miji, wasu mazan ne ba na kwarai ba, wasu iyayensu ne fitina wasu yara, wasu ma shiga gidan miji ko samun mijin aure ya gagara, kaddara rayuwa gata nan birjik an raba an bawa kowa tasa, amman ke baki samu muguwar suruka ba, kuma mijinki yana sonki, toh me zai saka ba zaki yi hakuri da dan abun da aka jarrabe ke da shi ba? Kaddara ma Aliyu neman matan yake ai be yi ba sai da baki kusa ko?"

Ta daga kai.

"Kin gani, wata kila rashin ki ya saka shi aikata hakan, a yanzu kuma da kika dawo madadin ki gyara sai kika kara lalata lamarin, kin ga kin bude masa kofa kenan kuma ita wacan kin bata galaba, ita na kawarki da kike zance kar yi mamaki ace son take ta cire ki a gidan ta saka kanta ma gaba daya, na san baki rasa komai a gidan nan ba, mahaifina yana da kudi zai iya miki komai, amman karki duba wannan shi aure Rahama ne daraja ce kwanciyar hankali, ki yi hakuri ki jure ki danna komai ki koma dakin mijinki, iya mai turo miki sakon tana yi ne saboda tana son ki bar gidan ita ta shiga"

"Mama Baraka shi da kansa fa yace na dawo"

"Eh wata kila akwai abun da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login