Showing 144001 words to 147000 words out of 253142 words

Chapter 49 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18393

yi shiru.

"Na gwada kiran wayarki bata shiga kuma na miki text baki maido min da amsa ba, lafiya?"

"Lafiya ?alau, hankalina ne ya tashi da kace min ka tafi da Fatima na kasa natsuwa kuma na kira wayarka ban same ka ba..."

Magana take a shagwabe tana yi tana yankewa.

"Na zo da ita ne saboda na san kina bukatar space, kuma zuwa da ita ba wani abu zai haifar ba In Shaa Allahu lafiya kalau zan dawo da ita, gobe ma zan dawo, I'm so sorry na tafi da ita ba tare da neman izininki ba"

"Aliyu ina Kaduna fa..."

"What? Wasa kike yi?"

Ta girgiza kai.

"No da gaske ina Kaduna ina Airport ma yanzu haka, hankalina ya tashi ne please ka fahimce ni ina son yata ba zan taba samun natsuwa idan bata kusa da ni ba"

Mamaki ya hana shi kara tambayarta wani abu.

"Kina ina a airport din"

Ta fada masa sai ya kashe wayar, guri ta samu ta zauna tana ya kallon mutanen dake kai da kawo feeling so guilty kamar wanda ta aikata wani laifi. Tana zaune a gurin har sai da ya sake kiranta ya fada mata inda ya faka ta daga kai tana kallo har ta hango shi tsaye jikin motar sanye da manyan kaya da hula.

"Na ganka gani nan zuwa"

Ya rike wayar yana ta kalle kalle har ya hangota tafe sanye da riga da wando sai kuma jacket din dake daure a kugunta, gashin kanta ya rabo gida biyu sai bin iska yake tana tarewa. Idan yace Emily bata da kyau yayi karya ta ko'ina ta kai mace duk wani abu da namiji zai kalla a jikin mace ya sota Emily tana da shi, a kokarinsa na haramtawa kansa kallonta gudun wuce gona da iri ya saka shi kawarda idonsa sai ya lura mutanen dake tsaye kusa shi ma kallonta suke, na nesa da ita ma kallonta suke domin ta ko'ina mace ce mai jan hankali, ko ba dan jikinta da kyauta ba dole a kalleta domin gashinta da idonta da kuma hasken fatarta. Hakan ya saka shi jin babu dadi domin a musulunci mace mai kima ce suturta ake.

"Hi"

Ta fada tana kallo????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  nsa a yayinda take tsaye a gabansa, ya kalleta karab idonsa suka fada cikin nata idanuwan masu matukar daukar hankali, sai ta sakar masa murmushinta mai sanyi da kyau, duk wani bacin rai da damuwa dake tare da shi sai ya ji yayi kasa kamar an jefa dutsen kankara a rijiyar dake cike da ruwa take fitar da kara tit tit tit haka zuciyarsa ke bugawa a hankali ba bugawar tsoro ko fargaba ba.

"Wane irin dress ne haka? Kin sake komawa Emily dinki kenan nan?"

Ta kalli jikinta sai a lokacin ta saka hannunta kwance jacket din Dr A-B dake daure a jikinta.

"Haka na zo, Dr Adam Bello ne ya daura min wannan jacket din tasa"

Ta yi zaton yadda ta dauro jacket din ne be masa dadi ba.

"Waye Dr Adam kuma?"

Ta fada masa shi ne likitan da suka hadu asibiti da Tasmia ta kwanta kuma ta fada masa irin hidimar da yayi mata a yanzu har ta samu sauka a airport din. Aliyu ya dan ji babu dadi kadan ko ba komai uwar yar abokinsa ce be kamata ace tana mu'amala da maza anyhow ba, ya san ta dana kyau karamin aikin yan'uwansa maza ne su kawo mata hari da alheri ko da sheri.

"I thought i warning you about this, ko ba komai ke fa mace ce kuma uwa, idan ma baki duba duk wannan ba why not ki girmamani kamar yadda kike yi a wacan karon ki saka tufafi masu kima? And baki fada min matsayin wannan Likitan a gurinki ba har kika karasa labarinki"

"Ba shi da wani muhimmanci a gurina wannan ne haduwata da shi ta uku"

"Me ya same ki a fuska"

Bata amsa masa ba ta ce.

"Tafiyar ta gaggawa ce shiyasa ban yi tunanin saka wani kayan ba, ma tsorata ne na yi tunanin... I'm sorry ka fahimce ni please, ka san halin da na shiga ba wai ina nufin ban yarda da kai ba amman hankali zai fi kwanciya idan Fatima tana kusa da ni, na zo na dauke ta ne sai mu koma gobe dan Allah karka min rashin fahimta"

Ya motsa bakinsa a hankali har wani iri yake ji saboda yadda ta marairaice murya da fuska tana masa magana sai ya dorawa kansa laifin tayar mata da hankali na tafiya da yarta ba tare da amincewarta ba.

"Ma fahimta, shiga mota mu tafi"

Ya bude bangaren da yake tsaye ta zagaya ta shiga baya ta zauna gudun kar ayi masa mummunar fahimta domin ta fahimci shi din mutum ne mai mutunci kuma kai addinin. Be ce me yasa kika zauna a baya ba yaja motar suka fara tafiya be yi nisa ba ya samu kansa ta saita madubin gaban motar zuwa saitin da Emily take zaune a baya ba dan komai ba sai dan yana son karantar yanayin da take ciki, jikinsa na bashi wannan kwancin jinin dake fuskarta dukanta Vito yayi ko kuma wani abu ya faru tsakaninta da Dr A-B din ne, waya sani ma ko Vito ne ya cilasta mata zuwa ta tafi da Fatima, sai tausayinta ya kara kamashi, mutanen da babu zumuntar nesa ko ta kusa suna ta juyata yadda suke so saboda rashin dangi da wanda zai tsaya mata.

"Shi likitan yayi kokarin taba mutuncinki ne?"

"Aa"

Ta amsa tana kallon titi.

"Ba zaki fada min abun da ya sami fuskarki ba?"

"Duka ne"

Tun da ta amsa da duka ne ya fahimci wanda yayi mata dukan ba sai ta fada ba.

"Saboda na taho da Fatima ne?"

"Ba yau ba ne tun wacan ranar ne da na saka Abaya"

"Shiyasa kika hana na ganki? Karya Tasmia ta min kenan?"

Ta yi shiru idonta na cika da hawaye ta share, be sake cewa komai ba ya cigaba da tukin har ya iso gida yayi horn mai gadin ya bude masa ya shiga ya faka motar harabar gidan ya fito, Emily kuma ta zauna domin bata san su waye a gidan ba kuma be ce ta fito ba. Zagayawa yayi bangaren da take ya bude kofar bayan ya bar kofar a bude ba tare da yace mata komai ba. Tana ganin haka sai ta sako kafafuwanta kasa ta fito tana rike da jacket din.

"Na taho?"

Ta tambaya kamar mai jin tsoro, Aliyu ya juyo ya kalleta ya girgiza mata kai.

"Bari na daukota"

Ya shiga ciki ita kuma ta tsaya a gurin ta rumgume hannayenta, ba a dauki lokaci ba ta ga ya fito da sauri ya nufi gurin mai gadi.

"Malam Tahir ka ga wata karamar yarinya ta fito nan waje?"

"Eh sun fita ita da Hajiya, ba su ma wani jima sosai ba Hajiya ta zo da mota ta dauke ta suka fita"

"Hajiya? Wace Hajiya?

" Hajiya ta gidan nan"

"Kameela"

"Eh ranka ya dade"

"Me ya faru"

Emily ta tambaya tana karasowa inda suke tsaye. Aliyu be ce mata komai ba yayi hanzarin ciro wayarsa aljihu ya kira Kameela kusan 3 missed call bata daga ko daya ba.

"Ina Fatima? Ni fa ban gane ba"

Ta tambaya hankali a tashe
"Kameela ta dauke ta"

"Kamar ya Aliyu karka min haka idan ma wasa kake dan Allah ka daina ba haka muka yi da kai ba ina yata take?"

Bata tsaya jiran amsarsa ba ta nufi kofar falon ta shiga da gudu. Aliyu kuma ya bude motar sa a fusace ya shiga yana jan numfashi da karfi ya dauki hanyar gidansu Kameela.
Emily ta duba duk inda zata iya na falon domin ba wani sanin gidan ta yi ba, ta kalawa Fatima kira shiru ta shiga har dakunan data gani ta duba bata ta ga Fatima ba ta sauko tana kiranta bata ji ta ba. Da wayar dake hannunta ta yi amfani ta kira layin Aliyu na farkon wanda ta kira da shi dazun har Fatima ta daga. Kiran ya shiga yana bugawa tare da bugun zuciyarta.

"Hello Fatima my baby girl where are you?"

Shiru ba'ace komai ba.

"Hello Baby Girl talk to me, ina kike?"

Shiru ba'ace komai ba. Ta yi zaton Kameela ce dan haka ta fara magana cikin kaushin halshe.

"If you hurt my baby Kameela, sai na kashe ki Wallahi sai na halaka ki"

"Your Baby is in safe hands..... Aisha... Emily..."

Ta ji an fada cikin wani sauti mai kamar rada kamar rarrashi, da wata murya da bata fatan sake jin irinta, dip bugun zuciyarta ta tsaya wayar ta subuce tsakanin hannunta da kunnenta ta fadi kasa...











_________________
Na biya bashin jiya kuma na yi long page
Kar inji wani yace Pim.... =??
[7/4, 5:08/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=KhadeejaCandy





*? Khadeeja Candy*



Page 4?? 6??




KAMEELA POV.

Tun da ta fara tukin bata tsaya ko'ina ba sai bakin gate din gidanta, ta yi horn mai gadin ya leko ya ga ita ce ya koma ciki ya bude ta shiga ta faka rai a bace bata ko tsaya kashe motar ba ta fita ta banki kofar falon da karfi ta murda ta shiga, Fatima dake zaune kan kujera ta zabura ta mike tsaye tana kallon Kameela. Kameela ta harari Fatima kasa da sama ta tabe baki.

"Eh lallai ashe da gaske ne, amman Wallahi Aliyu ya gama cin mutumci na, kuma ya nunawa yarinyar shegiyar matar nan ba ni daraja a gurinsa"

Ta yi kwafa ta shiga kitchen din ta duba abincin da suka ci suka rage, ta fito tana tambayar Fatima da turanci.

"Ina Emily take?"

"Tana can ba da ita muka zo ba"

"Ke ma da ganinki zaki yi munarfuci, waya sani ko daukota yayi har uwar suka zo"

Ta fada da hausa sannan ta kama hannun Fatima ta karbe wayar hannunta.

"Ai yau za'ayi ta ta kare, sai na datse duk wata alaka dake tsakanin matsiyarcin uwarki kwartuwa mai bin mazajen mutane"

CONTACT list dinsa ta shiga ta nemo number Ammy ta kirata da layin Aliyu, Ammy ta daga tare da sallama, Kameela ta amsa tana fadar ba Aliyu ba ne.

"Ni ce Ammy matarsa Kameela"

"Maa Shaa Allahu Kameela kina lafiya ya gidan?"

"Ammy ba lokacin gaisuwa kwatancen gidanki zaki min faka faka"

"Lafiya?"

"idan na zo zaki ji Ammy fada min kawai"

Ammy ta kwatanta mata Kameela ta sauke wayar ta kama hannun Fatima sai Fatima ta ficike hannunta.

"My Momy warn me not to talk to strangers"

"Aliyu ne ya ce na zo na tafi da ke yana can wani gida zai siya miki ice din yace ma kawo ki"

Fatima na jin haka sai ta yarda Kameela ta kama hannunta suka fita ta bude mota ta saka ta ta shiga taja motar mai gadin ya sake bude mata ta fita, tana tukin tana bala'i Fatima sai kallonta take domin bata jin yaren da take.

"Ki bani wayar zan cigaba da kallona"

Kameela ta mika mata wayar ko kira zata yi ai ba shi da amfani yanzu tun da ta riga ta san gidan Ammy, daman sau daya ta taba zuwa shi ma kuma Aliyu ne ya kaita.

"Dan ubanki gurin uwar ubankin zan kaiki, ayi ta ta kare, na huta da wannan bibiyar da uwarki take ma mijina, sai kace shi yake nemanta, ga mai nemanta ga wanda take likewa, ina na taba ganin haka dan kawai neman a dora min hawan jini"

Bata sha wahala gurin gane gidan ba kasancewar unguwar ba a boye take ba, kuma gidan babban gida ne a layin, tana isa bakin gate din gidan ta gane lallai gidan dai da suka taba zuwa da Aliyu sau daya. Ta yi horn mai gadin ya bude mata ya shiga ciki ta faka ta zagayo ta budewa Fatima ta riko hannunta ta fito da ita.

"Ina yake?"

"Yana ciki sai mun shiga"

Fatima ta bita babu wani rigima suka shiga cikin falon, tsabar neman fitina da tsoron abun da zata aikata da kuma bakin kishi da suka hade mata guri daya Kameela har numfashi take sama sama kamar wanda ta dauko katon dutse. Da sallama ta shiga falon Yan matan nan biyu da Ammy take riko suka amsa mata, Ammy na zaune kan kujera nurse na kusa da ita tana hauna bp dinta, daman ta fi yawan zaman falon gudun wahalar da mazu zuwa ganinta ba sun haura sama inda take ba.

"Ina yake?"

Fatima ta tambaya da karfi tana fisge hannunta daga rikon da Kameela ta yi mata. A take Kameela ta daka mata tsawa ta watsa mata harara.

"Ki zauna"

"Ba zan zauna ba, ina Uncle Aliyu? Kina kokarin sace ni ne? Su waye wadannan mutanen mama na tace kar na yi magana da wanda ban sani ba"

Ta saka ihu mai karfi babu saurara ahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh ta cika musu kunne. Ammy ta kalli Kameela tana tambayar tafiya, Kameela ta rasa ta ita zata fara bayani ga Fatima na mata ihu gashi bata san yadda zata fara warware zaren zancen ba.
Ihun Fatima ne ya saka Turhan dake dakinsa cikin damuwa ya saukowa kasa domin duba abun da ke faruwa. Saukowa da Turhan yake ne a hankali ya saka Ammy daga kai ta kalleshi daga kansa ta sauke idonta akan Fatima dake ta ihu, sai gata a tsaye kamar ba marar lafiya ba. Ta ko'ina Fatima kama take da Turhan kamar an tsaga kara kamar har ta bace har gashin kanta baki ne kamar na mahaifinta sai ka rantse tsumata aka yi a cikin jikin Turhan aka ciro bata rage komai nasa ba, banbancin kawai ita mace ce shi namiji kuma ita tana karama shi kuma babba.

"La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu, La'ilaha illallahu"

Kawai Ammy take maimaitawa jikinta na rawa hawaye na sauko mata.

"Yauwa kin gane kenan"

Kameela ta fada kamin ta juya ta kalli Turhan daya tsaya be karaso ba, bata san yana garin ba sai a lokacin.

"Alhamdulillah faduwa ta zo daidai da zama"

Ta fada tana kallon Turhan da gabansa ke dukan uku uku ba kuma tare da fahimtar komai ba, shi dai ya san ba lafiya ba, ganin yadda Ammy take ta ambaton Allah ta mike tsaye ga kuma yarinyar dake ihu ga kuma Matar Aliyu.

"Ka karaso mana Turhan wannan yarka ce"

Turhan ya kalleta ya kalli Ammy.

"Ban fahimta ba"

"Yarka ce sunanta Fatima, Emily ta haife ta muma jininka ce Aliyu ma da kansa ya fada, tana boye maka ita ne tana boye maka kanta, ni na gaji shiyasa nake son ayi ta ta kare shiyasa na kawo ta, na gaji dan Allah idan ka ga Emily ka rike ta na huta, na samu kwanciyar hankali da mijina, ta kyale min mijina dan Allah duk wani boye boye da ake ban gane kanshi ba, matar nan ta hana ni zaman gidana cikin kwanciyar hankali abun ya wuce PH ya biyo har nan Kaduna na gaji, Aliyu be san na kawo ta nan amman na san dole Emily zata zo"

A cikin kalamanta babu wanda Turhan ya ji kuma ya fahimta?sai kalmar ?ARKA CE... kalma ta maimaita kanta a kunensa ya fi sau saba'in tun da ya dora idonsa akan Fatima be kyabta ba, sigar jikinsa kawai ke tashi zuciyarsa ta karaya bugun zuciyarsa ya karu fiye da kima, sai a yanzu ya fahimci Ammy na ambatar Allah ba tare da an bata mata ba, kamaninsa ne sak a fuskar Fatima.

"Ke dalla dufewa mutane baki kin ga ubanki can"

Kameela ta fada ma Fatima da turanci tana nuna mata Turhan. Sai Fatima ta lake kafada ta fara magana cike da tsiwa da iyayi.

"Noooo Momy ta fada min ni bani da Baba ni kadai aka haifa haka, kowa yana da Baba amman Momy tace ni ba ni da Baba baki kiji sunana ba Fatima Emily Aisha"

Turhan ya zube kasan guiwowinsa ya daga kansa sama ya bude baki yana numfashi da karfi kamar wanda zai mutu. Fatima ta fashe da wani irin kuka mai karfi na gaske domin bata fahimci me suke ba, gashi bata san kowa ba a cikinsu yanzu kam ta fara tsorata.

"Take me back to uncle Aliyu or Momy"

Kameela ta buge hannu. Ammy ta karasa ta dafa Fatima tana kuka ta kama fuska tana kallo, ta zube a gurin tana ta taba taba jikin Fatima

"Allah na gode maka, Allah Aisha kawai nake nema amman ka hado min har da yarta, jikata Allah na gode, Allah ya miki albarka Kameela"

Kameela dai bata ce komai ba ta juya ta fice da sauri.

"I want my momy"

Ammy ta dorata a cinyarta tana kuka ta rumgumeta. Turhan ya ka dagowa daga inda ya fadi durkushe ya kara karasa gurin da Fatima take jikinsa da zuciyarsa sai rawa suke abun ya zo masa kamar mafarki, ya rasa ta yi zai yi ya yarda wannan abun ba mafarki ba ne, shi dai Emily kawai yake nema shi ma kuma saboda Ammy. Da rarrafe ya karasa gurin tana kallon Fatima ya kai hannunsa zai taba ta sai ya kasa ya maida hannu, ya shafe hannunsa jikin rigarsa gaba da baya kamar mai kokarin cire kazanta ya sake mika hannunsa zai taba ba a nan ma ya kasa jikinsa sai rawa yake.

"Yarka ce Turhan, jinin ya fi ruwa kauri, jini be karya, yarka ce"

Ammy ta kama hannun Turhan ta kai a jikin Fatima, sai ya ji wani abu kamar shokin Fatima kuma ta zabura da karfi, a take ya tuna da abun da ya faru a airport lokacin da suka hadu da Aliyu ya taba babyn da yake dauke da ita tana bachi amman sai da ta zabura. Turhan ya fisge Fatima a jikin Ammy ya rumgumeta da karfi jikinsa ya mike tsaye yana kuka kamar wani karamin yaro, a take kukan Fatima ya yanke ta yi shiru kamar ba ita ba, ita m ta ji wani abu na dabam gashi ta ji yana kuka bata san dalilin ba, daga tsayen kukan ya kasa rike shi ya zube kasa yana rumgume da ita, kusan kowa a falon kuka yake har Nurse din da bata san hawa da sauka ba. Ammy ta daga hannunta tana magana.

"Haka na yi nufi, ku zauna tare ku yi zuri'a ta dalilina, Alhamdulillah ko a yau na mutu burina ya cika, na ga jininka Turhan, ashe ba a banza na ke jin bukatar ganin yarinyar nan ba, ashe akwai abun da Allah ya shirya min da ban sani ba Allah na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login