Showing 27001 words to 30000 words out of 253142 words

Chapter 10 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18432

saka ihu tana son fisge hannunta a na mahaifiyarta.

 Ki kyale ni Momy ki sake min hannu, akwai ciwo ina son na tafi gida yanzu

Matashiyar ta dan zaro ido tana kallon Fatima da mamaki, ganinta karamar yarinya amman da take yi ma mahaifiyarta ihu.

 Ya sunanta?

 Fatima

Emily ta amsa mata idonta na cika da kwalla. Matashiyar ta rage tsayinta tana kallon Fatima.

 Sunana Tasmia, please Fatima ki daina yi ma mahaifiyarki rashin kunya da tsawa kin ji babu kyau, ba ayi ma iyaye tsawa da uwa da uba dukansu abun girmamawa ne

A madadin Fatima ta amsa mata da OK sai ta fada mata abun da ba kowa ya kamata ya sani ba.

 Ni ba ni da uba haka nan aka haife ni babu uba, can you imagine?

Matahsiyar ta kalli Emily sannan ta mike tsaye ta yi mata sallama.

 Allah ya tsare gaba bye

Ta juya ta fara tafiya Emily ma ta fara takawa tana kokarin ganin hawayen dake idonta basu zubo ba.

 Can you take us home?

Cewar Fatima tana kallon Tasmia da already ta bude motarta zata shiga.

 Yes darling ku shigo sai na sauke ku

 No mun gode zamu hau okada

 Ni ba zan hau okada ba ni mota nake son ta kai ni gida

Ta fada a tsawa.

 Is okay Fatima ba sai kin yi tsawa ba, zan sauke ku, please ki shigo ko dan masalahar yarki

Tasmia ta karasa tana kallon Emily, Emily bata da sauran tace bayan abun da yarta ta take so kuma ta zartar, dan haka ta nufi motar ta bude gidan baya suka shiga ita da Fatima, Tasmia ta shiga mazaunin direba ta ja motar.

 Ina zan sauke ku?

Fatima ta fada mata unguwar da Number gidan, Emily kuma ta maida fuskarta gefen titi tana kallon ababen hawa, sai dai a badini, zuciyarta zafi take mata tunanin rayuwarta na baya ya dawo mata, damuwa ta baibaiye mata zuciya. Har suka isa unguwar Emily bata ce komai ba haka ma Tasmia Fatima ce kawai ke nuna inda za'a bi har suka isa kofar gidan. Bata jira komai ba ta bude motar ta fita ta rufe gambun da karfe ta doshi gate din gidan ta fara kwankwasawa.
Emily ta bude dayan gefen ta sauke kafafuwanta.

 Mun gode, ki yi hakuri da abun da ta yi miki, haka take bata jin magana, yaran yanzu sai a hankali

 Haka ne amman yana da kyau mu rika tsawatar musu, idan har bata tsoronki ko ki hada da wanda take tsoro yayi mata hukunci ko yayi mata fada, kamar yayanki ko kanenki ko mijinki ko saurayinki, su yara wani lokacin sai da mai tsawatawa, amman fa ki yi hakuri na shiga abun da babu ruwana

Tun da Tasmia take magana Emily ke jin wani abu na mata yawo a zuciya, har ya saka ta kasa rike hawayenta sai da suka zubo.

 Wata kila ke kina da duk abubuwan da kika lissafa saboda haka ba zaki gane komai ba, na gode sai anjima

Ta share hawayen sannan ta karasa fita ta rufe mata motar a hankali. Tasmia bata wuce ba sai da Emily ta shiga gidan, sannan ta ja motarta. Emily na shiga falon ta jefar da jakarta a saman kujera ta zauna ta dafe kanta sai hawaye.

 Duk abun da nake kokarin yi a yanzu, ina yi ne saboda ku da kuma rayuwarku ta gaba, kin ce baki son zama a gidan nan baki son Vito, ina ta kokarin ganin na tsaya da kafafuwana saboda ku, yau kina kallon yadda aka koremu gurin aikin nan kuma mun kama hanyar gida kina min tsawa kina neman ki daga min hankali, dole sai kin fadawa kowa baki da uba?

Fatima dake zaune a kujera rumgume da hannayenta ta kalleta tana turo baki gaba irin na fitsararun yara.

 Toh ai bani da uba, ba karya na yi ba

Emily ta dago ta kalleta cikin bacin rai ta daka mata tsawa.

 Kar bakinki ya sake furta haka ga kowa, baki san zafina ba ne shiyasa kike fadar hakan, lokacin da nake kamar ke da ace na samu wata macen a matsayin uwa ko yaya take zan rike ta

 Toh miyasa baki da uwa? Ni ina ruwana da hakan?

Ta fada tare da mike tsaye ta dauki remote dake gefenta ta jefar a kasa sannan ta nufi upstairs tana tafiya da karfi kamar wata babbar mace. Emily ta bita da kallo hawaye na sauko mata zuciyata na zafi sosai, ko da damba ne kake wahala da shi kake kokarin ganin ka faranta masa, idan ka fahimci ba kai ne a gabansa ba dole hakan zai maka zafi, balle kuma ace mutum ne, mutum ma yarka jininka. Ta girgiza kai ta share hawayenta ta mike tsaye nufi dakinta, keys din mota ta dauko ta sauko ta sake daukar jakarta ta fice daga falon.

Tafi minti goma a motar zaune tana sauke ajiyar zuciya sannan ta murza key ta yi warming dinta ta juyar da ita mai gadin ya bude mata ta fice, restaurant din dake kusa da su ta fara biyawa ta yi takeaway sannan ta karasa asibitin da danta yake, dukanin abun da take tana kokarin ganin ta boye damuwarta ne, so take ta zama jajirtacciya, wannan dalilin ne ya saka take tare hawayenta a duk lokacin da suka so zuba. Ta shiga dakin da danta yake tana murmushi kamar babu damuwa a zuciyarta, Chidimma ta gaisheta ta amsa tana kallon danta daya dauke fuska alamar baya son ganinta.

 My Boy how are you

Ya sake juyar da fuskar dayan gafen, bata damu ba ta aje takeaway dake hannunta ta juya gefen da fuskarsa take ta zauna tana masa murmushi sai ya sake juyar da fuska ya matsa gefe.

 Tun da ya tashi yake kiran sunanki

Chidimma ta fada mata.

 Baki fada masa ina gurin aiki ba?

 Na fada masa, maybe yana son ganinki ne a lokacin be samu damar hakan ba, saboda baki kusa

Emily ta sauke dogon numfashi sannan ta dawo gabansa ta tsuguna ta rike kunnuwanta, tana neman yafiyarsa kamar yadda ta saba yi idan ta bata masa rai.

 Okay I'm sorry, Momy ta bata maka rai ka yafe min I'm sorry

 No i hate you

A take yanayinta da fuskarta suka sauya, ta kalli Chidimma ta sake kallonsa, sai dai wannan karon bata sake cewa komai ba ta mike tsaye tana jin zuciyarta kamar zata rufe, domin be taba furta mata kalmar i hate you ba sai a yau, ta fice daga dakin ta sake komawa cikin motarta ta zauna tana ta hade wani abu da ya tsaya mata a zuciya.
Bata yarda ta yi kuka ba sai shafa fuskarta take tana kokarin kwantar ma da kanta hankali. Ta sake yi ma motar key ta fice daga asibitin tana tukin motar zuciyarta na kara yin nauyi har ta iso gida, ta faka motar a gun da ta dauke ta, sannan ta bude ta fito tana rike da jakarta har ta isa balcony din kofar falonta ta zauna a gurin ta sauko da kafafuwanta kan interlock tana kallon harabar gidan kamar wata bakuwa.

A lokacin da wayarta ta fara ringing sai ta saka hannunta a jakar dake bude ta dauko wayar ta duba, V ne rubuce a jikin screen din. Ta amsa wayar ta kara a kunnenta ba tare da tace komai ba.

 How are you?

Kamar jira take sai kawai ta fasa masa da kuka, kuka sosai mai dauke da ihu kai kace yayi mata bushara da mutuwa ne, har sai da mai gadin da mai sharan harabar gidan suka mike tsaye suna kallonta. Be sake furta komai ba ya kashe wayar, ita kuma ta cigaba da kuka da karfi har numfashinta na rawa tana shafa sarkar Cross din dake wuyanta. Da sauri Mai gadin ya karaso kusa da ita yana tambayar lafiya, bata amsa masa ba ta mike tsaye ta shige falonta a kan kujerar falon ta jefar da wayarta da jakar ta haura sama ta shiga dakinta ta kwanta saman gado tare da jan filo ta rumgume tana cigaba da kuka sai dai wannan karon babu kururuwa...



VITO POV.

Ya aje bottle din Hennessy XO dake hannunsa that's Worth 430k, ya gayen dake kusa da shi.

 A siya min ticket din tafiya ina Port Harcourt yanzu nan

 Okay Sir

Ya jingina da kujerar da yake zaune gaba daya ransa ya bace jin kukan Emily da yayi, after like 10m gayen ya dawo ya sanar masa babu flight din da zai tashi daga Lagos to Port Harcourt yanzu sai gobe. Ya dago ya kalleshi.

 Ka fadawa manager Happy Home Hotel ya siya min ticket din tafiya Port Harcourt, a siye tickets din duka ina son tafiya yanzu nan

 Okay Sir

Ya sake komawa ya kwanta jikin kujerar da tunani biyu, mutumen da ya gani dazun da kuma kukan da Emily take, kokarin hada biyun yake yaga yadda za su zame masa daya ko zai samu amsar kukanta, sai dai zuciyarsa bata natsu da hakan ba. Yadda ya bukata haka maganer hotel din ya aiwatar aka daukar masa shatar jirgi private jet shi kadai daga Lagos to Port harcourt, tun kamin ya bar Lagos ya turawa direbansa dake port Harcourt sakon lokacin da zai sauka, so that ya zama cikin shiri. In less then awa biyu ya sauka Lagos daman daga Lagos to Port Harcourt 1hr 10m ne to nonstop flight. Yana sauka direbansa ya dauke shi a cikin 2022 -BMW X3 baka mai bakin gilashi.

Be sauka ko'ina ba sai gidan Emily, yana fitowa motar be tsaya rufewa ba ya nufi kofar shiga falonta da saurinsa irin saurin dake ake hadawa da guda, a falo ya fara cin karo da Fatima tana zaune a dinning tana shan cornflakes, kallonta kawai yayi ya dauke kai ya kalli wayar Emily dake aje kan kujera da jakarta, be taba komai ba ya haura sama ya tura kofar dakinta a hankali ya shiga. Talkaminsa ya fara cirewa sannan ya taka ya karasa bakin gadon yana kallon fuskarta a take zuciyarsa ta fara rawa ganin yadda fuskarta ta yi ja ta kumbura saboda kukan da ta yi, idanuwanta a lumshe tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take irin na yaran da suka gaji da kuka suka yi bachi.

Zaunawa ya fara yi a hankali sannan ya kai hannunsa ya dagota ya kwanto da ita a jikinsa a hankali ya kai hannunsa yana shafa fuskarta, jira kawai yake ta farka ta fada masa wanda ya saka kyakkyawar sarauniyarsa kuka. Jin ana shafa fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali ta sauke su akan fuskar mutunen da murmushi ba shi da muhalli a gurin. Ta tashi zaune tana kallonsa sai na juya ta kalli gadon ta kalli agogo ta ga karfe biyar na yamma ta sake kallonsa.

 Yaushe ka zo?

Ya ki ya amsa sai kallonta yake.

 Kace min zaka tafi Lagos? I thought kana can

Nan ma be ce mata komai ba sai kallonta yake.

 Why are you here?

Ya saka yatsansa ya shafe mata gefen bakinta.

 Waya taba ki?

Kallon fuskarsa take zuwa kirjinsa da boturan rigar suke bude, sannan ta sake kallon fuskarsa sai ta fashe da wani sabon kuka.

 Kowa baya so na, babu mai bukatata a kusa da shi, Fatima tana bata min rai yau sauran kadan mota ta bugeta saboda ta bata min rai, na tafi asibiti London yace baya so na ya tsane ni

Ya matsa kusa da ita ya rumgumeta tare da dora chin dinsa saman kanta.

 Sai kuma wa?

So yake ta ambata masa sunan wani dabam ba yayanta ba tace su suka bata mata rai, domin ya san ba zai iya taba yayanta ba, amman zai iya taba kowa bayan jininta. Ita kuma bata yarda sunan kowa ya fito daga bakinta domin ta san waye Vito ta san abun da zai iya, kuma ta san yadda yake sonta. Ya dago ta daga jikinsa ya rike fuskarta da hannunsa biyu yana kallon kyakkyawan idanuwanta.

 Akwai wanda ya taba ki bayan Fatima da London? Akwai wanda ya fada miki wata magana?

Ta girgiza kai alamar aa, ya mutsa bakinsa kamar zai yi magana sai kuma ya saketa ya mike tsaye, kasa ya sauka ya shiga kitchen ya dauko mata ruwa ya fito har ya nufi stairs ya fara takawa sai kuma ya juyo ya dawo gurin da fatima take zaune a dinning ya kalleta.

 Idan kika sake batawa mahaifiyarki rai har ta yi kuka idonta ya kumbura kamar yau, sai na miki danyen hukunci

Ya fada fuskarsa babu alamar wasa sai ma kara hade mata rai da yayi.

 I hate you, kuma Momy ba zata aureka ba

Ta fada masa cikin tsiwa tana murguda baki. Wani mugun kallo ya watsa mata sannan ya dauke kai ya haura sama. Tana ganin haka ta mike tsaye ta nufi wayar mahaifiyarta ta dauka ta haura sama da gudu ta shiga dakinta, jakar makarantarta ta bude ta dauko kati da Aliyu ya bata ta zauna bakin gado tana cire password din wayar.



ALIYU POV.

Misalin karfe 3pm ya faka motarsa harabar gidan ya bude ya fito yana kallon bakuwar motar dake fake kusa da balcony. Bayan ya rufe motarsa ya nufi entrance din ya fara takawa har ya isa bakin kofar falon ya tura ya shiga. Matarsa ya tarar a tsaye tare da wata bakuwar fuska dake rataye rike da karamin mayafi a hannu dayan hannunta kuma rike da jaka.
Aisha na ganin shigowarsa sai hankalinta ya tashi, ta juya ta gefen da bakuwar take tana tarewa dan kar Aliyu ya kalleta da kyau, domin atamfar dake jikinta da matse ta sai dai ba sosai ba, amman ta karbe ta yi mata kyau. Ta inda ta yi sa'a mijinta baya daga cikin irin mazan nan da suke son kallon mata balle kuma ya san halin matarsa da kishi ko a tv ya kurawa mace ido sai ta yi masifa balle kuma a zahiri, tun kallon farko da yayi ma bakuwar a farkon shigowarsa be sake kallonta ba.

 Sannu da zuwa

 Sannu Babyna ya gidan?

 Lafiya Kalau

Yayi kamar be san da bakuwar ba ya shafa fuskar matarsa zai wuce sai ta gabatar masa da kawarta tana dan kareta.

 Tasmia ce ta zo mana

 Maa Shaa Allah, ina mata barka da zuwa

Ganin alamar be gane ta ba ya saka ta ce.

 Tare muka yi Secondary School

 Nice

Ya fada ba tare da ya kalleta sannan ya wuce zuwa dakinsa, tun da ya bada baya Aisha take kallon Tasmia ta ga ko ta kalli mijinta and yes ta kalleshi da kyau har ya shige ciki, Aisha ta dan canja mata fuska tare da jefa mata zagi cikin wasa sai dai har a zuciyarta ta ji zafin kallon da ta yi ma Aliyu.

 Yar iska me kike kallo? Da wani billenki a nan

Tasmia ta kalleta ta yi murmushi.

 Masu ciki fa zuciyarsu a kusa take, daman gaki ba tsaye kin san ance short people suna da saurin fushi, wai su da fushi 5&6, ni kin ga tafiyata

Ta nufi kofa, Aisha ta tsaya a gurin bakinciki ya hanata raka kawar da suka shafe shekaru ba su ga juna ba, sai ma binta da ta yi da harara. Aliyu na shiga dakinsa wayarsa ya fara cirowa ya aikawa Turhan da sako bayan ya gama karanta wanda ya turo masa.

 Yau gidan marayu hudu muka je ba mu dace ba, ko'ina cewa suke ba su santa ba

 Baka amsa ni ba, Turhan me ya rabaka da yarinyar nan? Me yasa ka sake ta?

Ya aika masa sannan ya aje wayar ya fara cire tufafinsa.
[4/20, 9:59/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/FdvabUKwybz6ogMKtgx02w

*

*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?

Page 1?? 0??


EMILY POV.

Tana shan ruwan tana shan ruwan tana ajiyar zuciya kai kace yar yarinya ce aka saka kuka, hannu ya kai yana shafa saman kanta har ta shanye ruwan, sai ya karbi kofin ya aje.

 Ba Fatima ce kawai ta saka ki a cikin damuwa ba, waya taba ki?

 Ita ce kawai

Ya kalleta ba dan ya gamsu ba, ba zai cilasta mata ta fada masa abun da ya haifar mata da damuwa a yanzu ba, amman da sannu zai sani domin ya san yadda take sauyawa idan ta shiga damuwa. Mikewa yayi tsaye rike da cup sai ta rike hannunsa na hagu ta dago tana kallonsa da idanuwanta dake bayyana damuwa sosai. Komawa yayi ya zauna sai ta dora kanta a cinyarsa ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali, ta sani bata da sauran kima a idon kowa sai Vito a yanzu, ita din ba abar tausayin kowa bace sai mutumen da ya ganta a rana ya saka a inuwa kuma ya lullube ta da kulawa da kauna, yake gudun bacin ranta yake kaunarta fiye da kansa, tana jin kamar shi kadai ya rage mata a yanzu.

 Mommy ta fada min zata zo satin nan, idan ta sauka a nan na san zata rage miki kewa, ko ba komai zaki samu uwa zata kula dake kamin ta tafi, amman idan baki ra'ayi zata sauka gidana sai idan kin bukaci ganinta

Ya fada yana shafa fuskarta a hankali kaunarta na kara zafafa a zuciyarsa. Bude idon ta yi ta tashi zaune tana kallon wani gafen, ta yi marmarin kasantuwa kusa da wasu iyalin, sai dai kudurin da take da shi ba zai barta ta sake kusantar iyalin Vito ba a yanzu. Ta mike tsaye ta cire ribbons din dake kanta jan gashinta ya sauko har bayanta, sai ta tsaya gaban madubi tana cire dankunenta, shi ma tsayen yayi ya matsa kusa da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta ta madubi, baya bukatar ta bashi amsar tambayarsa, ya zauna da ita na tsawon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login