Showing 48001 words to 51000 words out of 253142 words

Chapter 17 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18442

ba su son tafiya gidansa ne shiyasa suka ce ya hado mata kayan, madadin ita yayarta ta tafi ta hado mata kayan, shiyasa Hajiya take son da am sallameta ta wuce da ita daga nan ba tare da sun tafi gidan ba.
Shi kuma be shirya wulakanta kansa ba, ko neman rigima da su ba shiyasa, be musa musu ba ko ya nuna musu damuwarsa akan yunkurinsu. Da kansa ya hada nata wani tea mai kauri ya bude naman da ya zo mata da shi har tiriri yake yana saka mata a baki.

 Yanzu ya aka yi da Emily din? Kuma taya aka yi ma ka gane ta?

Anya zai iya fada mata a gurin da yake aiki take aiki? No.. Ya tambayi kansa sai kuma ya bawa kansa amsa.

 Hotonta ai ya bada yanayi da kamaninta, kuma kana ganin yarta zaka san yar Turhan ce domin fuskarsa ce

 Meyasa ba zaka fada masa ba, bayan kasan yadda yake ta nemanta

Ya kai mata tea a baki.

"Ita ta bukaci kar na yi haka

 Saboda me?

 Wata kila tana da dalinlinta

 Dan Allah ka fita sabgarta ka cire kanka a tsakaninsu, ba a shiga tsakanin mata da miji ni dama ace be saketa ba abun zai fi min sauki"

"Saboda ke zaki hada aurensu? Dan Allah masoyiyata ki bari mu rabu tafiya, karki saka kanki a wata damuwa dan Allah, ke kin san wanene, kuma yaushe na ce miki ya sake ta."

"Au be sake ta ba? Au to da sauki ai"

Yayi murmushi yana kara jinjina lamarin Kameela, shi dai ya fadi haka ne saboda hankalinta ya kwanta. A asibitin ya kwana tare da matarsa ya kwantar mata da hankali kuma ya lalabata akam tafiyar da Hajiya za ta yi da ita.



EMILY POV.


Driving kawai yake tana kalle kalle bata shirya komawa gida, kuma bata san gurin da zata je ba, haka ta yi ta yawo kamar zata zagaye garin kamin ta faka motarta kusa da wasu dakuna da suke kamar quarters. Bude gambun motar tayi ta fito daga cikin motar ta nufi wani katon dutse da yake gurin ta zauna. Kallo daya zaka yi mata ka fahimci bata cikin farinciki, domin fuskarta a fili take nuna damuwar dake zuciyarta.
Rabo ido take amman zuciyarta da hankalinta suna wani gurin na dabam.

 Me kike a nan?

Maganar ta ji ne daga gefenta ya saka ta juyo gaba daya sai ta yi arba da matar da ya kusan kade Fatima, kuma ita dai matar da ta gani asibiti ta yi mata magana.

 idan kina son na tashi na baki guri, zaki iya cewa na tashi na bar unguwar ko gurin, ba sai kin tambayi mai nake ba, ai zaune kike same ni, zama nake yi

Ta dan yi murmushi ta zauna kusa da Emily.

 Baki yi kama da masu zafin rai ba, daga ganin yanayinki na san ranki ne a bace, na hango ki tun daga dakina, karki manta jiya ne ko shekaran jiya ke kika min magana kamin na miki

 Da na yi miki magana yi kika yi kamar baki san ni ba

 Ni ma ranar raina yana bace ne ki yi hakuri, Sunana Tasmia"

Ta mika mata hannu, Emily ta kalleta kamin ta mika mata nata hannun.

 Aysha Emily

"Nice to meet you Aysha, me kika zo yi unguwar mu?"

 A nan kika"

"huh"

Emily ta daga kafadunta.

 Kawai dai ina yawo ne ban san inda zan je ba"

"Zaki iya shigowa ciki ki sha ruwa?"

Emily ta kalleta for few seconds...

"Be kamata na yarda da kowa ba"

"Haka aka fada miki?"

Cewar Tasmia tana murmushi.

"Haka duniya ta koya min"

"Da alama duniya ta rike ki a makarantarta ta yi ta zuba miki darussa a ajinta"

"Haka ne, na zuba min ilmi kuma na karantu, yanzu yayewarta kawai nake jira

Emily ta karasa zance idonta na cika da hawaye.

 Matsalar miji ce? Ko ta yaya? Ko ta family?

 Ya kamata na yi wata maganar dake?

Emily ta yi maganar a siga tambayar.

 Zaki iya yarda da ni, baki ga yadda kaddara take ta hada mu ba? Wata kila tana nufin mu zama kawaye, ko kuma abokan shawara ta wani bangaren, karki damu da banbanci addininmu ba, ko launin fatarmu dukanmu mata ne, da suke dauke da matsala in one way or the other

"Zan fada miki damuwata ne kawai saboda ina bukatar fashe kurjin dake min ciwo, kamar yadda na so na yi a wacan ranar da na yi miki magana, saboda bani da kawar da zan tattauna damuwata da ita, ba ni da uwar da zata ba ni shawara, bani da dan'uwa da zai share hawaye, ba ni da kowa sai ni kadai

Tasmia ta zauna a kusa da ita tana kallonta cike da tausayin ganin yadda hawaye suke kwaranya a idonta.

 Kin rasa iyayenki ne?

"Kin rasa iyayenki ne?

 Ni ma dai ban sani ba, mutuwa suka yi aka rasa inda za a aje ni sai gidan marayu? Ko kuma dai haihuwata aka yi ta gurbatacciyar hanya aka jefar da ni, su waye iyayena miyasa suka bar ni? Shi ya fi tsaya min a rai, ki kalli fatar jikina haskena yayi yawa, ina da blue eyes, gashin kaina ja, waya biyo mahaifina ko mahaifiyata, ban sani ba

 A ina kika samu kanki bayan kin girma? Su wa suka rike ki?"

"Mutanen da ban sani ba, labari ne mai tsawo

"Toh yanzu wa kike aure? Baki jin dadin zaman gidan mijin ne ko me da har kika tunawa da baya tunatar da ba zata miki amfani ba

Ta share hawayen da suka ki tsaya mata.

 Wasu sun yi dacen rayuwa Tasmia, sun san su waye iyayensu, wasu sun yi rayuwa da su, wasu sun san a ina familynsu suke, wasu suna da kawaye, suna da masu kula da su, ni ba ni da kowa yarana ma basa bukata ta a yanzu"

Jimmm Tasmia ta yi kamin ta ce.

 Yaranki suna bukatar tsawatarwa, gaskiya na lura da tarbiyar yarki sai a hankali, me zai saka ba za ku tattauna da mahaifinta...

Bata karasa ba Emily ta tari numfashinta.

 Bana tare da mahaifinta, a yanzu ina zama a karkashin kulawa da ikon wani ne, da baya bari ma rabi kowa, baya barin na yi kawa, banbancin rayuwar baya da ta yanzu kadan ne, har yanzu a cikin kangi nake"

Tasmia ta dafa ta.

"Miyasa ba zaki yi nesa da shi ba?

"Ba zai bari ba, saboda shi yake ciyar da mu shi yake mana komai ko da kuma na yi kokarin gina kaina ba zai bari ba"

Tasmia ta juyo da ita suka fuskanci juna.

"Ban san iya hidimar da yake miki ba, amman da alama akwai tsoro da fargaba a zuciyarki, irin tsoron da fargabar da yake samu kowane dan'adan mai rauni har yayi nasarar sauya tunaninsa ya saka shi a cikin wani kogo ya hana shi walwala, daga lokacin da tunaninki yake hango miki rauni a tafiyarki, zuciyarki take raya miki ba zaki iya ba, to ba zaki iya ba ne har abada, a yadda na fahimce ki kin sha wahalar rayuwa kamin yau, idan kuwa haka ne be kamata ace wani ne yake fada miki yadda zaki tafiyar da ita ba, ai babu wanda ya san kalar talkamin da suka dace da kafarki, ina nufin babu wanda yayi tafiyar da kika yi a hanyar rayuwar ki saboda kaddarar kowa dabam, idan babu mai sonki shin ke ba zaki so kanki ba? Kar tsoron sherin wani ya hana ki gina rayuwarki, ki tsaya da kafarki irin tsayin da ba za a iya kallon idonki a fada miki wata maganar ba, ki sakawa ranki zaki iya, ki yarda da kanki Emily, idan baki da kowa to ke ki zamewa kanki kowa mana, ki gina labarinki, ki yi taki duniyar ki cikata da zuri'arki"

Tasmia ta karfafa mata guiwa ta zuba mata kalaman da wani be taba tsaya ya tsara mata su a cikin kanta ba, hakan ya tsayar da zubar hawayenta a yanzu tunaninta ya karkata ta inda bata yi zato ba. Karar shigowar sako ne ya sauka a wayarta sai ta sauke kanta kasa tana duba wayar.

 Kina ina?

Ta karanta sakon na Vito. Kamin ta dago ta kalli Tasmia dake zuba mata kalamai.

 Ki fara mafarkinki daga yanzu, kar kowa ya sake baki tsoro, karki yarda zuciyarki ta fada miki ba zaki iya ba, tsoron cutarwa wasu ta hana ki cika burinki, ita rayuwar duniya ciki take da kalubale babu mai kaiwa karshenta sai wanda ya barta, ke kadai kika girma babu kowa a kusa da ke! To taya zaki bari wani ya milke ke a yanzu? Wani be kamata ya rubuta labarinki ba, ke ya kamata ki aje alkamin da kanki... Ki rufe tawadar sai ki bada damar a karanta...

Ta karasa tana share mata hawayenta tare da yi mata murmushin karfafa guiwa. Emily ta yi murmushi still hawaye a idonta.

 Ke ce mutum ta biyu da na gani musulma mai zuciya mai kyau, daga wacan mutumen da ya taimaka min lokacin da zan haifi Fatima sai kuma ke, amman duk sauran daga masu gorin addini sai masu cin amana

 Haka muke mu musulmai cikin akwai na gari akwai bata gari, kamar dai kowane addini, idan kina son zaman lafiya da kowa da kuma fahimtar rayuwa, ki kalli addinin da mutane suke yi, da kuma abun da ya koyar, ba wai rayuwarsu ba"

"Haka ne"

Ta amsa tana share hawayenta.

"Toh yanzu zaki iya shigowa ki sha ruwa?"

Emily ta yi murmushi.

 Wata kila wani lokacin"

"Shikenan tun da haka kika zaba, amman yanzu zaki saka min number ki zan saka miki tawa, ni da ke mun zama yan'uwa daman ni bani da kawa a nan kawata daya ce kuma sarkin kishi ce saboda mijinta bana son zuwa gidanta, ina zaune a gurin wata yayata, ke kuma daman na taba sauke ki a gidanki, amman asali ni yar Kaduna ce"

"Amman ke me ya kawo ki nan"

"Bautar kasa"

Emily ta daga mata kai alamar gamsuwa, sannan ta saka mata numberta ta karbi nata number. Ta mike tsaye

 Zan tafi wata kila yarana suna bukatar gani izuwa yanzu"

"Hakan yana da kyau, muje na rakaki"

Tamia ta rakata har gurin motarta sannan ta yi mata sallama tana daga mata hannu har ta yi nisa.
[4/26, 5:40/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??:

*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 6??

Yadda ta bar gidan haka ta same shi domin kusan lokaci daya Emily ta shigo gidan tare da Chidimma da London.

"Ina kokarin gyara falon ne da gidan ne yanzu sai na dora abinci"

Ta fada ganin yadda Emily take kallonta.

"Ina London"

"Tare muka dawo an sallame shi"

Har Emily ta juya sai kuma ta juyo ta kalli Chidimma.

"Baki kira ni na daukoku ba?

"Na ga kin fita a cikin fushi ne, shi ma kuma fushi yake da ke, ina gudun bacin ransa ne, shiyasa sai na kira Sir Vito ya kawo mu gida"

Emily ta juya ba tare da ya sake cewa komai ba.

 Ki yi hakuri da abun da London yake miki, kin san yana dauke ta lalura ne, amman a hankali zai fahimta ya daina kamar yadda yake yi abaya"

Har ta ci ta cinye Emily bata sake juyowa ba haka kuma bata sake cewa komai ba ta haura sama ta shiga dakinta sai ta samu Vito zaune a ciki yana kallon kofar data shigo.

"Ina kika je?"

"Inda nake ra'ayin tafiya"

Ta amsa masa rudely, kallonta kawai yake har ta nufi closet dinta ta cire talkamin kafarta. Ta saba fada masa bakar magana but like ya tambaye ta wani abu ta amsa masa da wata maganar dabam. Wayar dake aljihunta ta yi ringing ta ciro wayar ta amsa ba tare da fargabar komai ba.

"Kin isa gida lafiya?"

"Lafiya kalau, na gode da kulawa"

Ta aje wayar a gefen closet din bayan ta amsa.

 Da wa kike waya?"

"Will you excuse me? Ina son na huta ne"

Ya sake dubanta a tsanake kamin ya mike tsaye ya fice daga dakin. Yana fita ta sauke numfashi da karfi ta lumshe ido tana sauraren yadda zuciyarta take bugawa da karfi.
Vito ya sauko yana kallon Fatima dake gabansa kadan tana saukowa, juyowa ta yi tana kallonsa har ya kawo daidai inda take tsaye.

 Vito... Kasan waye babana"

"Emily bata fada miki baki da mahaifi ba?"

"Meyasa ni kadai ce a makarantar mu ba ni da Baba? Kowa a duniyar nan yana da Baba amman ban da ni why? Meyasa sunana yake Fatima Aysha Emily?"

Ya rage tsawo ya risina daidai ita.

 Saboda ke kadai aka haife ki, you're special girl with bad attitudes"

Ya barta a gurin tana binsa da kallo cike da tsana, fasa sauka ta yi ta koma sama ta shiga dakin dan'uwanta. Wanka Emily ta yi ta fito ta shirya cikin short gown ta atamfa ta zauna gaban madubi tana kallon kanta. Maganganun Tasmia suna ta yi mata yawo akai, sai ta ji ina ma ace wani ya fada mata haka tun a baya, ko da yake a yanzu din ma lokaci be kure ba. Ta yi murmushi.

"Ina fatan yadda kalamanki da fuskarki suke, haka zuciyarki ma take"

Ta fada sai ta bude aljihun madubin dake gabanta ta dauko wani karamin box ta ciro agogon mutumen da ta kasa manta yadda ya taimaki rayuwarta har ta rayu. Ta shafa agogon tana rausayar da kanta.

"Ku biyu ne kawai musulmai masu halin kirki, kai ka bar min shigo Tasmia kuma ta bar min kalamai"

Ta karasa tana murmushi, sai kuma ta mike tsaye ta nufi jakarta ta saka agogon ciki ta nufi wayarta da sako ya shigo ta duba.

"Zaki iya zuwa office a duk lokacin da kika shirya, Office dinki yana nan yana jiranki"

"Why? Saboda kai ma ka yi amfani da wannan damar ka shimfida min dokoki ka mulke ni a yadda kake so?"

Ta yi jira har ta gaji be dawo mata da amsa ko wani sakon ba. Aje wayar ta yi ta fice daga dakin zuwa dakin da danta yake, wasa ta samu yana yi da Fatima har da dariya sai dai shigowarta ya saka dukansu su biyu yanayinsu ya sauya, Fatima ta dan hade rai, shi kuma ya juya mata baya gaba daya irin yadda yake idan yana fushi baya son kallon fuskar mutane. Ta zauna akan gadon ta kai hannu ta shafa bayansa.

"My babu, har yanzu fushi kake da Momy? Why saboda Momy ta jima bata zo ba? Me Momy ta yi ne London har kaka juya mata baya? Momy da take kaunarka? Taka siya maka abun dadi...? Ina kake son mu tafi? Kana son mu yi wasan ruwa?"

Duk rarrashin da ta yi masa da kalamai be juyo ba kuma be sauka daga fushin ba, da ta yi kokarin juyo da shi ma sai ya saka mata ihu ya ruda dakin har sai da Chidimma ta bar abun da take ta shigo ta rumgume shi. Tashi ta yi ta fice daga dakin ta sake komawa dakinta, ta kwana da tunani kala kala a ranta ta kulla wannan ta kwance wacan, daga karshe ta bi tsarin da zuciyarta ta dorata ta hau ta hakikance cewar ba zata koma aiki ba, amman zata nemi wani aikin domin cika burin da take da shi.

Washe gari ita da kanta ta shiryawa yaranta abun karyawa, ta zubawa Fatima nata a lunch box na London kuma ta bawa Chidimma ta ba shi, ita kuma ta koma ciki ta saka kanana kaya da sneakers ta fito ta shiga kitchen ta dauki water bottle ta zuba swan water sannan ta fito.

 Zaki tafi wani gurin ne Ma'am?

"Yes zan je motsa jiki ne"

Chidimma ta dan tabe baki kadan domin ba abun da Emily ta saba yi ba, Emily ta nufi London da Chidimma ke feeding dinsa ta sumbance shi ta shafa kansa sannan ta fice tana fadawa Fatima ta yi hanzari direban dake kaita school yana jiranta.

"Yau ba zan je School ba"

"Saboda me?"

"Saboda kowa yana tsokana ta a makaranta, idan aka kira sunana"

Ta fada tana huci, Emily ta aje gorar ruwan dakin hannunta ta nufi Fatima ta kama hannunta nufi sama da ita. Ta zaunar da ita kan gado.

 Cikin masu miki dariya akwai wanda ta fiki gata? Ko ta fiki kashe kudin da kike kashewa?"

Ta girgiza kai kamar zata yi kuka.

 Toh karki sake bata ranki idan sun fada miki haka, ai su iyaye maza suke da, ke kuma kina da uwa mace jajirttaciyya mai kokarin sama miki rayuwa mai kyau, mai son abun da kika so, ba kin ce kina son mu bar gidan nan ba.?

Ta daga mata kai.

 Duk abun da nake kokarin aikatawa a yanzu na yadda zan bar gidan nan ne, ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa da abun da suke fada miki, kuma ki daina fadawa kowa labarin ki Fatima ke ma kina da surutu, idan suka miki dariya kice haka kike so, kuma ke baya damunki, ki min alkawari ba zaki sake damuwa da maganaer su ba, ni kuma zan miki alkawarin barin gidan nan cikin kankanen lokaci kuma na siya miki duk abun da kike so, tashin hankalinki tashin hankalina ne Fatima, karki sake min magana makamanciyar wannan

Ta daga mata kai sannan ta kai mata yatsa.

 I promise"

"Good yanzu shiga ki wanke fuskarki idan kika yi haka kin wanke bakin ciki babu sauran damuwa sai ki fito da murmushi muje na rakaki mota"

Ta tashi da saurinta ta shiga bandaki ta wanke fuskar ta fito da murmushi Emily ta kama hannunta suka fita tana far'a kamar na ita ba. Chidimma na kallonsu har Emily ta dauki lunch Box dinsu suka fice, sannan ta kalli London da fuskar tausayi tace

 Ka gani Momy bata son London sai fatima, idan London yayi fushi Momy bata tsayawa ta rarrashe???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?shi amman tana tsayawa ta rarrashi Fatima

Ya bata fuska sosai yana ta yawo da idonta ta saki baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login