Showing 69001 words to 72000 words out of 253142 words

Chapter 24 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18405

wani kuma ya tambaya wani irin taimako nake nema, na ce na wanda zai rike ni har na haihu.

"Wannan cikin ba shi da uba ne?"

"Yana da uba, ni ba ni kowa marainiyace ni, kuma mijina ya sake ni, kuma musulunta na yi ban san kowa a nan ba"

Ina rufe baki daya daga cikin dattijan dake tsaye a gurin ya rufe da fada kamar zai dake ni. Wai na tashi na bar gurin haka muke muna zuwa muna cikin shege mu zo tasha mu tare muna haifa musu yara yan iska muna bata musu tasha.

"Idan baki da kowa ki koma garinku mana, karya ce suke saboda kawai a tausaya musu, cikin shege suke yi"

Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, daman wai waye zai yarda da ni, suna da gaskiya suna bukatar tabtace tashar su. Haka na tattara na bar tashar na fito na kama hanya ina tafiya ban san inda zan je ba, can na samu guri kusa da wata mai wara na zauna na siya wara na ci saboda ban saka komai a cikina ba tun safe.

"Dan Allah ina ne? Zakka da wakafi?"

Ba tambaye ta, sai ta kwatantamin na bata kudin wararta na siye ruwan leda na sha, na tari mai achaba na hau na fada masa inda zai kaini ban tambaya nawa ba sai da muka isa yace min 500 zan bashi a lokacin 2300 ne suka rage min, na ba shi 500 na doshi gurin gabana na faduwa, domin maraicina be taba saka ni rokon kowa ba. Mai gadin gurin ya fara tambayar ina zanje na fada masa taimako nake nema a take na bayyana masa abun da ke tafe da ni da kuma taimako da nake bukata.

"Kin tabbatar cikin nan baki ba na shege ba ne? Domin suna yin bincike idan za a bada taimako"

"Wallahi gaskiya ne, ba karya nake ba"

Sai yace na jira a nan ya shiga ciki ya fito da wani mutum mutumen yayi min tambayoyi ya yi rubutu akai sannan yace min yanzu kowa ya tashi aiki saboda yamma ta yi, amman na tafi zai saka sunana a cikin mabukata na dawo wani sati, sannan ya tabbatar min kamin su bada taimako suna yin bincike saboda akwai bata gari da suke zuwa suna karya nace masa na yarda su yi duk abun da ya kamata.

"Amman yanzu idan na tafi ba ni da gurin zama ban san a inda zan zauna ba"

"Ki yi hakuri dai wani satin ki dawo da wuri kamin rana ta yi"

"tohm"

Na amsa ina kuka, sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi naira budu daya ya ba ni wai na hau abun hawa. Na karba na juya na kama hanya daman kam wa zai karbe ni a haka dole kowa zai yi zaton karya nake saboda cikin dake tare da ni ga shi kuma ina fadar ba ni da kowa kuma nace ban san kowa a garin Kaduna ba, ga ina cewa musulunta na yi wasu ma sai su dauka karyar ma ta yi yawa. Daga gurin na kama hanya ina ta tafiya a kafa ba dan na san inda zanje ba, har dare ya fara yi na siye ruwan leda na yi alwala na raba gefen wani icce dake kan hanya na yi sallah, ina addu'a ina kuka ina rokon Allah ya kawo min mafita. A gurin na yi ta zama har aka yi isha'i a nan ma na yi sallah.

Da yake akwai mai shayi nesa da inda nake zaune kadan da na yi yunwa ta matsa min sai na tafi na siya birede da ruwan lipton na koma gefe daya na sha, sai wani azababben ciwo ya taso min, da na kawo masa kofin kowa kallon wulakantacciya yake min domin mace mai daraja ba zata saya tea ta raba gefe ta sha ba, gashi na zama kamar mahaukaciya duk na firgice ga rama cikin ma yayi min nauyi haka dai nake ta fama. Da na bashi kayan sai na raba ta wata hanya dake kusa da shagon na bi na lulla da wasu kananan gidaje, a gurin na samu inda na raba. Na wahala a gurin domin ciwon ba kadan nake jinsa ba, sai da na bari sawu ya dauke na tabbatar da dare yayi sosai sannan na tashi na koma inda na fito yadda na ayyana haka na samu. Mai shayin nan ya tashi ya kwashe kayansa a gurin na kwana, washe gari tun da asuba na yi sauri na tashi na koma gurin hanyar na zauna, da haske ya fito sai na shiga wani gida dake kusa na roki ruwa dattijiwar ta ba ni na yi alwala na fito nan na yi sallah.

Rayuwa ta zama min haka, da dare sai na kwana a shagon mai shayi da rana kuma na shiga gari Bara da neman taimako. Ta inda Allah ya taimake ni babu wanda ya taba cewa me nake a gurin ko ya kure ni, ko da yake bana dawowa gurin sai dare yayi, idan kuma sawu ya dauke sai na kwana a shagon mai shayin da be san ina yi ba. Ranar da na kwana uku a gurin ciwon ya matsa min sosai har na tafi yawon bara na dawo na shiga gidan matar dake bani sadakar ruwa ina ta gumi na roki ta ara min wayarta na kira wata nu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????mber. Har tace min bata da waya na juya sai kuma ta kira ni ta ba ni amman tace na zauna a kusa da ita na yi wayar bata yarda na fita ba kuma ta saka wayar a speaker saboda bata yarda da ni ba.
Na warware zanena na dauko number Maman Luratu na saka a number na kirata, babu jimawa tana ringing ta daga wayar da sallama

 Maman Luratu nice Aisha ce"

"Aisha Allahu akbar sannu Aisha ya kike ina kike yanzu"

"Ina wani guri, maman luratu dan Allah ko kin san abun da zan yi na daina jin ciwon cikin da baya? Wallahi ciwon nan ya tsananta min yanzu sosai yau ma kamar bana iya tafiya"

Ina fada ina kuka.

"Toh ko haihuwarce? Amman cikin ai be isa haihuwa ba ko?"

"Eh wata bakwai ne, amman ina jin wahala sosai"

"Ko nakuda kike yi? Oh Allah gashi bana kusa, amman dai ki daina yawo nesa"

"Idan haihuwar ce me zan yi?"

"Kina tare da wa ne?"

"Babu kowa ni kadai ce"

"Ki nemi reza ki aje kusa saboda yanke ciki, kuma idan da hali ki tafi asibiti Aisha kin san baki da lafiya tun a nan ma"

"Tohm"

Na amsa sannan na kashe wayar na mikawa matar ina godiya, sai matar ta tambaye daga ina nake.

"Labarin mai tsayi ne ko na fada miki ba zaki yarda ba, na gode"

Na fice daga gidan ina ta sharar kwallah. A rabar ne zuciyata ta debeni na yanke shawarar ziyartar coci ba dan komai ba sai dan na samu kudin da zan tafi asibiti kuma na samu kulawa. Dan canjin da ya rage min na hau abun hawa bayan na tambaye shi wace coci ce a kusa na fada min, da muka isa na bashi kudinsa na doshi gurin gabana na faduwa a zuciyata ina jin kamar hakan ba daidai ba ne amman ya zan yi? Dole ce ta saka. Na isa gurin na yi magana da mai gadin coci na fada masa damuwata da abun da ke tafe da ni, sai yace na jira a gurin ya shigo ciki ya fito da wata Sister tace ba shigo ciki na shiga nayi mata bayanin damuwata sai ta kira wani pastor shi ma ya kira wani muka shiga wani office na sake karanta musu damuwata, da na yi hakan ne saboda kawai su taimaka min.

Sai dayan yace za su taimaka min da gurin zama da abinci amman sai idan zan yarda na koma gidan jiya, ma'ana na zama christen kamar baya, har ita macen take ce min ko da ace ban taba yin addinin a baya ba zan shiga a yanzu su kuma za su bani duk abun da nake bukata kuma za su shirya ni da mai rikona ma dake Lagos."


***. ****. *****.

Ta daga kanta sama, Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zaro tissue ya mika mata, ta karba ta share hawayen da suka ki tsaya mata. Ta kalleshi da fuskarta da ta yi ja tsabar kukan da take.

"Ni na sani a yanzu ba akan shiriya nake ba, na sani ba akan daidai nake ba, na san addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, a wacan lokacin ban yarda da tayinsu ba duk kuwa da kasancewar ina cikin tsananin bukatar taimako a lokacin, amman akwai wani abu da Allah yake sakawa a zuciyar wanda ya so da shirya, na musulumta saboda Khaleefa da aurensa ban san cewar ina son addinin ba sai a lokacin, sai kawai na ji raina ya bace akan me za su ce na koma addinin da bana samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali irin na ruhu sai da na bar shi, ni dai a lokacin na san ina son musulunci dan haka sai na ki yarda, na fada musu ni taimako kawai nake nema ba wai ina nufin barin addinin ba ne, su kuma suka ce ba za su taimaka min ba haka na taso na fito"

Ina jin kamar shi kadai ne wani hukunci da na taba yankewa kuma ban yi nadama ba, da kafa na dawo saboda ba ni da kudin da zan hau abun hawa na dawo, sai kuma na sha wahala a hanya saboda ni ba har gari bace hanya da mai achaba ya bi da ni na bi ina tafiya, idan na rikice sai na tambaya mutane da sannu har na kawo kaina unguwar da nake zaune. Na iso ban isha'i sai na samu guri na zauna ina ta jin ciwon cikin da ban gane nakuda ce ba, daker na iya roko ruwa na yi rama sallolin da ban samu yi ba, na kwanta a gurin azabar ciwo cikin bata karu ba sai da dare ya raba.
Na koma gurin da nake kwana na kwanta da ji abun ba zai daina ba na taso na fito na dawo gidan matar nan na kwankwasa mata gida sai jikanta ya bude yana haska ni da fitila.

"Dan Allah matar gidan nan nake nema"

"Lafiya wacece"

"Ni ce"

Na leka sai ta ga fuskata.

"Dan Allah ki taimaka min da ruwa na sha, kuma idan kina sa wani magani dan Allah ki taimaka min na sha, kar na mutu ciwon ciki nake da na mara"

"Ba ni da magani amman dai zan baki ruwa ki sha"

Ta shiga ta dauko min ruwa na karba da hannu biyu na sha na juya na koma shagon na zauna ina ta kuka domin ciwon ya matsa min ga kuma abu ina ji a kasana kamar zai fito, ban san lokacin da na fara ihu ina rike teburin mai shayin dake gurin ba, sai matse kafa nake ina juyawa, tsabar bala'i da azabar da ciwo har wani juri nake ji ina jin kamar ba a duniya nake ba, ashe haihuwa tana da zafi ban sani ba sai a ranar, gashi babu kowa a kusa da ni, duk zafin nan na haihuwa a haka iyayena suka wofintar da ni? Ina cikin tsananin nakudar dana na farko dan wata bakwai matar da ta taimaka min da ruwa ta iso gurin ta dafa ni, ta haska ni da fitila ina jin jikanta na fadar Gwaggo kika sani ko jikin shege ne. Sai tace.

"Ko cikin shege ne ai ba za a kyaleta ba Kabiru rayuwa ce"

Ta bude kadata ta haska sai ta saka salati.

"Haihuwa ce zaki yi kuma kafa nake gani ba kai ba subhanallahi"

Ta rika ni, da taimakon danta suka kai ni gidanta, ita tayi ta fada min yadda zan yi tana taimaka min tana danna min ciki har na haihu, amman na ji azabar da ban taba ji ba, har na ji kamar babu kasana gaba daya a lokacin. Da zanenta ta lullube dana ta yanke min cibi na sake wata nakudar sannan wani abu ya fado wai shi uwa, ta saka a leda ta kulle. Ta dauko wani zane ta lullube ni ta dora min dana a kusa da ni, ni dai ina kwance a gurin bana bachi bana farin ciki haka kuma bana kishiyarsa, hawayena kawai masu zafi suke sulalowa a idona, har ta yi zaton ko na mutu ta girgiza ni sai na kalleta.

"Sannu"

Na daga mata kai, da safe sai jikina yayi tsami sosai, ta taimaka min da tsumma na tare jini ta gyara dakinta tace na wanke kayan jinina haka na daure da ciwon jiki na da kasa na wanke kayana da kaina na zauna ina jin kamar fata ce kawai ta rage min a jiki, ta kawo min dumame na ci na sha ruwa sannan ta tambayi labari. Na fada mata komai sai ta tausaya min amman ta fada min ba zata iya ba ni gurin zama ba saboda zargi. Kuma ban ga laifinta ba tana da gaskiya ba kowa zai iya rike ni ba, dawainiyar ma ai sai ta yi masa yawa.
Ta fada min idan mace ta haihu a musulunci akan yanka mata rago idan yayi kwana bakwai, kuma uba yana yi ma dansa huduba a kunne, amman ni daya be samu ko daya ba, hakan ya saka ni kuka sosai. A lokacin na saka masa suna Ibraheem ba dan na san ma'anar sunan ba, kawai dai na saka masa haka ne.

Da dare yayi matar bata bari na kwana a nan ba saboda kukan da London yake ba ji rarrashi ga shi kuma nono na babu komai a ciki, na kwana a ashagon mai shayi kamin lokacin tashina yayi sai ga mutane na gani har hudu ciki har da mai shagon da abun dukansu, suka ce an fada musu a nan nake kwana kar na sake kwana a gurin su yanka ni, dayan ya so ya mare ni wai dan na raina musu wayo wato har haihuwa na yi a gurin. A daren suka kore ni na goya daya da zanen matar na kama hanya ina ta tafiya har gari ya fara haske gashi ko'ina na bi sai an kalleni saboda kukan da London yake domin ba lafiyayyen ana na haifa ba, gashi dan tsito ba shi da girma, ni kaina tafiyar ma daker nake yi ina ta raba kafa saboda zabar da nake ji a kasana.
A haka na rika raba manyan gidaje ina yin Bara wani gidan masu gadi basa bari na karasa ba suke korata wasu kuma basa ma bude gate din. Har na fada gidan wata mata mai farar zuciya mai tausayi mai jinkai, da alama da saba taimakon domin na tarar da gate din gidan a bude kuma da na fadawa mai gadin taimako nake nema sai yace min na wuce ciki.

Na shiga sai na zauna daga bakin kofar falon ina jiran fitowarta, na dade a gurin sannan aka bude kofar falon, wata matashiyar yarinya ce ta bude kofar ganina kamar tana mamaki ta tambaye ni lafiya. Nace mata taimako nake nema sai ta tambaye ni wane iri na furta abinci domin shi na fi bukata a lokaci, yarinyar ta juya ta shiga ciki bata jima ba ta fito da plate din shimkafa irin wanda aka ci aka rage tace ba a gama shirya mana abun karyawa ba amman ga ragowar shimkafar jiya idan zaki iya ce. Na karba jiki na rawa na fara ci hannu baka hannu kwarya kamin na kwance dana dake ta ihu ga wani zafi da jikinsa yayi na rumgume shi na gyara zama na fara saka masa shimkafar a baki tana kaiwa makoshinsa sai ya dauke numfashi...



***. ***. ***. ***.

Ta aje zaren zancen tana neman nata numfashin dake kokarin daukewa saboda kuka na tuna rayuwar da ta dade da rufe shafinta. Aliyu ya matsa baya yana kallonta cikin tashin hankali, a lokacin ne ta fara zaga office din tana neman numfashinta kamar zata mutu, da sauri ya fita Office din ya fadawa Nick ya nema masa wata mace da take kusa ya dawo ya nufi fridge dinsa ta dauko ruwa ya nufeta hankali a tashe, wata mace ce ta shigo dakin tana sanye da suit.

"Rikata dan Allah zaunar da ita ki rumgume ta"

Ya nuna mata Emily a take ta nufi Emily ta aikata abun da ya fada sai ya miko mata ruwa yace ta bata. Matar ta karba ta kai mata ruwan a baki Emily na shan ruwan ta fara amai babu kakkautawa bata tsaya ba sai da ta amayar da komai na cikinta, matar na rike da ita har ta fara dawowa hayyacinta sai dai kuma jiki babu kwari.

"Shiga da ita ciki ki wanke mata baki"

"Okay Sir"

Matar ta rika Emily suka shiga bathroom dinsa dake office din ta taimaka mata ta wanke baki da fuskarta sannan suka fito, Aliyu ya mikawa Emily Tissue da hannunsa.

"I'm sorry"

Ta karba kawai tana kallonsa da idonta da suka kumbura fuskarta da hancinta suka yi ja.

"Anna ki rikota ku fito ku same ni gurin mota"

Ya fice yana fadawa Nick ya sa a gyara masa office dinsa. Anna din ta taimaka mata suka sauka kasa suka isa har gurin motar da Aliyu take ya bude backseat Anna ta shigar da Emily ta rufe sannan ya shiga gaba yaja motar suka fice. Madubin gaban motar ya saita saitin da Emily take jingine da motar tana hawaye kana ganinta kasan tana cikin bakin ciki da rashin kuzari.

"Kina da likitan da yake dubaku?"

Bata amsa masa ba tana ta kallon gefen titi ta yi samo kamar ba ita ba. Shi kuma be fasa kallonta ba har ya isa bakin gate din gidan yayi horn mai gadin ya leko ya kalleshi... Sai ya sauke gilashin ta gefen da Emily take.

"Ba sai ka shiga ciki ba"

Ta bude motar ta fito da kafafuwanta ta yi tsaye kamar zata fadi, Aliyu ma ya bude ya fito ya zagayo inda take. Tasmia dake zaune a can gefe cikin mota ta bude motar ta fito da mamakinta tana kallonsu, tun kamin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login