Showing 63001 words to 66000 words out of 253142 words

Chapter 22 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18388

a kauye yake zaune ba, su kan shigo gani na wasu wasu kuma idan na fita tsakar gidan nake ganinsu ko su gan ni.

Akwana a tashi dan abun da Khaleepa yake da shi ya kare domin ciki muke ci, ga mahaifiyarsa ko gishiri ya siyo min sai ta karba ta raba biyu ta bani rabi, taliya ma idan daya ce to rabi zamu aje mu bata rabi.
Da kudinsa suka kare sai ya rika karbo mana abincin da suke, da safe kunu ko dumame, da rana kuma sai dai ayi kwado ko kuma asiyo abunci na siyarwa a ciki da dare kuma tuwon gero.

Bana iya cin tuwon kunun ma kadan nake sha domin babu suga, da rana kuma sai na wuni da yunwa, na ga alamar yunwa zata halaka ni idan aka ba ni tuwon geron sai na dukula na hada da ruwa na rika hadewa ba sai na saka miya ba. Washe garin ranar Inna da kanta ta sallama min na fito ta ba ni tabarya wai ai da ni ake cin abinci yanzu, ta saka ni turfe ban iya ba amman haka na rika yi ba, daker na samu yayi na kwashe mata, na dawo daki ina duba hannayena da suka yi kwancin jini suna ciwo. Sai yace

"Da sannu zaki saba, mu a nan garin yawanci duk gidan da ake cin tuwon gari a gidan ake surfe, Inna ma bata yi, amman da kin lura dayan bangaren ai har na siyarwa suna yi"

Ban ce masa komai ba, gudun kar na yi wata maganar ya fusata. Wasa wasa matar nan ta fara sani surfen siyarwa idan aka kawo kudin kuma sai ta karba tace za a hada a kudin cefane. Gashi haka nan nake wuni da rana babu komai a ciki, domin Khaleefa be da kudin siya min abinci yanzu, sai can wata rana idan an yi kwado ta aiko min idan na ci cikina yayi ta ciwo, da dare kuma abinci kadan nake ci haka da safe.
Kan kace me na rame na lalace ba kadan ba, idanuwana suka cicciko suka fito fuskar ta koma karama, kassana suka bayyana.
A lokacin ne Khaleefa ya dauki katifar dakin ya siyar mahaifiyarsa ta hada masa da wasu kudi yayi kudin mota ya tafi Nijar gurin nema, ya bar ni babu komai sai damuwa, kullum da fargabar daka nake kwana nake tashi, ga abinci bana iya cin na kirki. Sai aka fara rade r???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aden wai ina da kanjamau shiyasa na yarda na biyo shi.
Wata rana ina cikin surfe matar da muke zaune da ita gida daya wadda take kamar matar kawunsa ce ta dube ni tace.

"Aisha amman kamin Khaleefa kina da wasu samari ko?"

Na yi murmushi ina gyara rigar atamfar da ta yi min yawa, daman tufafina gaba daya kala shida ne a gidan.

"AA ban taba yin saurayi ba sai Khaleefa"

"Ban yarda ba gaskiya yadda kike da kyaun nan haka ai sai maza sun yi ta kawo miki hari, ko da yake ance ku baku dauki wannan komai ba, ance dan miji ya yayi mu'alama da ku ba komai ba ni shiyasa sai an gwada mace ake aurenta"

"Ba kowa ba, wasu dai suke yin haka"

"Toh Allah yasa wannan rama taki dai ta yi yawa"

Ban fahimci inda ta dosa ba dan haka ban maida hankali akan zancenta ba, na gama surfen na dauka na wanke na kawo na aje na nufi dakina. Na shimda tabarma na dora zane na kwanta, nan da nan sai bachi yayi gaba da ni, can cikin bachin na ji ana tashina kanwarsa ce wai na tashi na yi sallah, na tashi ina jin kamar na yi kuka, domin sallah na daga cikin abubuwan da suke wahalar da ni a lokacin saboda rashin sabo haka dai nake daurewa na yi.
? Bayan ta fice na dauki buta na zagaya bandakin, kamar ance saurara ki ji sai na ji muryar mahaifiyarsa kasancewar bandakin yana like da dakinta ne ta gafe.

"Badan halin Hamza na son karya, shi gaba daya rayuwarsa ta karya ce ta son burge mutanen, ka tsallake garinku jiharku ka tsallaka har kudu kudun ma Lagos ka dauko mata, Allah kadai ya san dalilinta na biyosa, wannan ramar da take yanzu na fara tsorata da ita"

Na kai hannu ma dafe zuciyata idona ya cika da hawaye, can na ji wata kanwarsa mai da da zo ta karba mata.

"Yawanci fa yan kudun nan ance idan suna da hiv suke bin yan arewa saboda su lika musu, gashi nan a gari sai rade rade ake wai Ya Khaleefa ya dauko mai ciwo, wasu har da cewa wai ciki yayi mata aka korosu"

"Ai yaje dai ya dawo, aure zan saka ya kara yaushe zai zauna da zabiya kalli idonta ma kamar matsafiya, ance a can fa kowa da kalar tsafinsu na gado, kuma nan gaba idan suka haihu ai zata iya kwashe yaranta ta koma can"

Kasa fitsarin na yi na fito na dawo dakina na zauna na ci kuka na har na koshi. Sannan na fito na yi sallah, kalaman da na ji ya saka na ja jikina daga mutanen gidan domin idan wani abu ya faru za su iya cewa ni ce. A lokacin damuwa ta kara yi min yawa gashi tun da ya tafi be taba kiran waya yace a ba ni mu gaisa ba sai dai ya yi waya da mahaifiyarsa. A haka ya shafe shekara daya be waiwaye mu ba, sai dai yayi mana aike idan kuma ya aiko komai yana hannun mahaifiyarsa babu wani canji. Yanayin yadda ya turo kudi aka siya masa fili a kusa da gidan aka fara masa gina na fahimci ko wane kalar kasuwanci ko aiki yake can toh ya karbe shi, ina ta jindadin ina murna mijina zai gina gida mu koma a can mu tare, ashe ba ni yake yi ma ginin ba.

Ranar da na yi ma mahaifiyarsa maganar ina son ta rika ba ni kudin surfen da nake na rika siyen abinci ranar ta yi min tatas wai duk abun da take min bana gani, ba zata sake min komai ba daman hakkin ciyarwarta ba a hannunta yake ba, har tana fadar musuluntar kawai na yi amman zuciyar kafirarce a kirjina. Da mutanen gidan suka taso madadin su shiga tsakani su bawa mai gaskiya gaskiyarsa sai duk suka goya mata baya, wasu suka dauki gaba da ni ciki har da kanwarsa da nake shiri da ita.
Tun daga ranar ba a sake bani abinci ba, sai dai idan na yi surfe dan abun da na samu sai na siya abinci da shi, bayan surfe sai na rika hadawa da wanki domin na samu kudin su min auki, wahala sai ta taru ta yi min yawa har wasu kujera suka fito min kamar na sauyin ruwa kamar na wahala. Idan na samu matsala kadan da mutanen garin sai min gori akan kudin surfe na ko wanki, ko aika ko kuma wani abun dabam, sai min gori, wasu su zage ni ni da iyayen da ban san a ina suke ba, wasu suce min zuciyar kafirar ce tana cikin kirjina, wasu suce min tsintacciyar mage.

Gashi idan ina son abu sai dai na fita na yi da kaina, babu mai bari na aiki danta, idan na fita mutanen su yi ta kallona. Ana sauran wata uku ya dawo wata rana ya kira waya sai aka kawo min na karba da murna ina kai masa gaisuwa sai ya rufe ni da fada. Wai an fada masa na yi fada da mahaifiyarsa na ci mata mutunci, kuma ina fita yawon gantali a cikin unguwa, shi ba zai dauki wannan ba.

"Ba zan iya daukar wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar kafiran lagos ba, yadda kike tubababiya dole ki dauki halinmu da al'adarmu wannan kiristancin da bakin hali ki aje shi a gafe, ba ni da kamar mahaifiyarsa"

"Baka saurara ka ji bangarena ba, yadda kake da addini Khaleefa be kamata ka yanke hukunci ba tare da jin dayan bangaren ba"

"Bana son jin bangarenki marar kunya, rashin tarbiyace zaki nuna min ko? Da an yi magana kice baki da kowa sai ni baki da kowa amman baki kokarin rike mahaifiyata? An fada min kuma gaba kika da kowa a gidan, ki gyara halinki Wallahi kamin na dawo Aisha"

Ban iya cewa komai ba na fashe da kuka domin shi dai ba zai saurareni ba yan'uwansa kuma ba za su fada masa gaskiya ba. Madadin ya rarrashe ni sai ya kashe wayarsa na mikawa kanwarsa wayar ina kuka.

"Baki san dadin yan'uwan ba, saboda baki tashi da kowa ba, kuma baki samu zuciyar kwarai ba shiyasa kike son idan ya dawo ya bata da kowa saboda gaki yar gwal ko?"

Ban rama kalma daya daga maganarta ba domin a lokacin ban iya maida marta ni ba, kallonta kawai har ta fita. Haka na cigaba da rayuwa ta bakin ciki a gidan suka gade min kai bana jindadin zama da kowa, idan suna surfe su ta yi min haibaici tun bana fahimtar habaicin na su har abun ya fara damuna. Ina kofar dakina ina wanki mahaifiyarsa na madafa tana girka shimkafa da miya, sai gashi ya shigo dauke da kaya yayi burun burun gashi duk ya tarar masa kai yayi jiki sosai sai dai kuma yayi duhu a lokacin. Da gudu na je na rumgume shi ina murna, a take mahaifiyarsa ta daka min tsawa.

"Ke ba mu san wannan rashin kunyar da rashin tarbiyar ta mutanen Lagos ba karki bata mana tarbiyar gida"

Na sake shi ina murmushin karfin hali, domin idan na ce ban ji zafin maganarta ba na yi karya, ta taso ta sauri ta karbe kayan da ya zo da su ta kai dakinta kanwarsa ta kai masa ruwa yayi wanka, ya shiga dakin mahaifiyarsa ya canja kaya ya gaisa da mahaifinsa da yake kamar fanko a gidan, sannan ya shigo dakina ina ganin haka na tattara wankin na aje na bi bayansa wai ni mai miji. Abun da ban sani ba ashe shigarsa dakin ta shirya masa karya da gaskiyar abun da ban yi ba, sai ganin na yi yana ta hade min fuska.

"Sannu da zuwa tun da ka tafi ko waya babu Khaleefa"

"Tafiyata ai ta miki rana domin gashi nan kin samu sana'a kina yi, kin fallasani a gari kowa ya san bana iyar da ke"

"Ko kawa ba ni da a garin nan balle na fada sirrina, ban taba fadawa kowa baka ciyar da ni ba, ban taba ba khaleefa"

"wannan wanki da kike ai da shi da fadar duk daya ne"

"ina yi saboda na samu abun da zan ci"

"Matsalar auren yare kenan baku da tarbiya baku da rufin asiri ga rashin yarda da kaddara"

Na nuna kaina ina kallonsa zuciyata na raya min kamar na Khaleefa da na sani ba ne.

"Khaleefa ni kake fadawa wadannan maganganun? Ka chanja min ba, yanzu duk ka manta irin sadaukarwa da na yi? Ka yi tafiya shekara daya da wata uku amman daga dawowarka sai ka rufe ni da fada kana ta bani rashin gaskiya?"

"Okay mahaifiyata zan bawa rashin gaskiya ke kuma na baki gaskiya kenan? Da kika zancen sadaukarwa sadaukarwar me kika yi? Ai ni na sadaukarwa ni da na dauko ki na kawo ki cikin yan'uwana, na musulumtar da ke, ba dan haka ba ai da yanxu ko mutuwa kika yi wuta zaki tafi"

Kalleshi kawai na sauke kaina kasa kuka, daman idan ba kukan ba to me zan yi.

"Tun da kin zabi haka, ki ta zaman wankewa jama'ar ga tufafi, sai ki ciyar da kanki"

Ya fada, ashe kuma zai iya, sai gashi babu abun da ya sauya bayan dawowarsa, sai ya zama kamar yana kyamata saboda kurajen dake jikina na sauyin ruwa da kuma wahala, mu'amalar aure ma dan kawai ta zame masa kamar dole ne da ko kallona ba zai yi ba. Idan yana son abinci mai kyau zai fita waje ya siya ya ci ko ya siyo mahaifiyarsa ta girka masa...
Wata rana na kebe kaina a daki ni kadai ina ta kuka, da nadamar da somin tabi ne a lokacin."


***. ***. ***

Emily ta mike tsaye hawaye shar a fuskarta ta nufi dayar kujerar dake office din ta zauna jiki ba kwari ta kalli Aliyu dake kallonta cike da tausayi marar misaltuwa ta ce.

"Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da baya sonka, ba ka son shi...!
Yawancin irin waWannan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi.
Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?'
Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman k'aya da k'usoshi tawa soyayyar tai min shimfidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa haWari a duniya, ruwan da kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...'

Na yi zaton idan na samu matsala da Khaleefa mutanen garin ko na gidan za su rike ni kamar dai yarsu ko yar uwa domin sun san ba ni da kowa, ban sani ba ashe ni shashasha ce, idan na samu matsala da Khaleefa har ta kai ga duka Wallahi babu mai raba mu sai mazan garin idan suna cikin gida, ta zama na yayi masa dadi sai ta kai ko numfashi na yi da karfi sai ya rufe ni da duka, idan na yi magana yace na kai karar duk inda zan iya, ko yace na fadawa duk wanda nake ganin zai zame min gata, wai takamarsa kawai a lokacin ba ni da kowa kuma ba ni da gurin zuwa.

Tun kamin ya dawo ake gina, zuwansa karasa kawai yayi, aka yi fanti aka saka wuta, sati daya da gyaran na ga ana ta hada hadar biki a gidan, ashe aure Khaleefa zai kara aure be fada min ba sai ranar da aka daura masa aure, ina zaune a dakina na ga an shigo da katifa sabuwa ya siyo min, na karba na yi godiya na shimfida zanen gado sai ya jefo min turmin atamfa guda daya, a nan na san hausawa suna da wata al'ada wai idan namiji zai kara aure yana yi ma matarsa ta gida kayan fadar kishiya. Na karbi atamfar na masa godiya sai yace.

"An daura aurena yau, wannan atamfar fadar kishiya ce, a kuma ga katifa nan na siyo miki a al'adar garin nan ko kuma mu arewa idan aka yi aure ana kawo yarinya da komai, ke kuma na ga ba wasu kayan kike da su ba, dan haka ki zauna a nan tare da su Inna, anjima za a kawo amarya a sabon gidan da na gina, bana son tashin hankali kun zauna lafiya, ki bita sau da kafa kin ga dai baki da kowa a garin nan ita kuma yar gari ce"

Ina daga zaune na daga kai na kalleshi.

"Ba zaki ce komai ba"

Bance masa komai ba bayan kallonsa da nake har ya gaji ya kada kai ya fice. A lokacin na sauko daga kan katifar na ji ba zan iya kwanciya akanta ba, na fara yi ma kaina wadansu tambayiyin da ba ni da amsarsu.

"To wai ni mi na yi ma iyayena suka jefar da ni? Miyasa na gujewa matar data rike ni kamar yarta? A wane dalili na tsallake shawararta da dokokinta? Na yi sadaukarwa ga wanda be san darajata ba, na bar ki na zabi iyalin da ba su san kimata ba"

Na kwanta a gurin ina wani irin kuka mai karfi ina jin kamar zuciyata zata fashe...



Don't forget to follow my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

Kuma karku manta ku yi sharing
[5/4, 6:26/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08




*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 2?? 1??


Ban san a addinin musulunci idan namiji yayi aure yana sati a gurin amaryarsa ba idan budurwa ce, idan kuma bazawara ce kwana uku, dan haka da aka kwana biyu ban ga mijina ya shigo dakina ba sai na sami wata makociyarmu da nake siyen kayan girki gurinta wato Malika ita ma dai yarinya ce sai dai ba kamar ni ba domin tana da yara har uku.
Na fada mata cewar ina son ta rakani gurin mai gari saboda ina son na kai karar Khaleefa, ita kam bata yarda taje ba wai gudun kar ace ita take zuga ni nake abun da nake, amman ta kwatanta min gidan kuma ta dorani akan tsarin yadda zan yi magana da shi idan na tafi.

Ina fita gidanta ban zame ko'ina ba sai kofar gidan mai gari na aika a sallamo min shi sai iyalinsa suka ce na shigo ciki, na shiga na yi musu sallama suka amsa muka gaisa na gabatar musu da kaina sai dayar tace.

"Oh ke ce wadda aka ce an musuluntar ko?"

"Eh"

Na amsa ina maida kaina kasa, babu jimawa Mai garin ya fito muka gaisa na gabatar masa da korafina cewar Khaleefa ya aje ni a daki daya ita kuma matarsa ya kaita gidansa kuma ya siya mata abinci mai kyau ni kuma ya daina ba ni, gashi kuma kusan kwana biyu be shigo dakina ba, ko da ya shigo gaishe da iyayensa babu ruwansa da dakina, ga kuma duka da yake yawan yi min.
A take Mai garin ya aika aka kirashi tare da iyayensa na zayya abun da na fada da farko, sai ya tambayi ba'asi, Khaleefa yace karya nake yana bani abinci kuma baya shigo bangarena ne saboda ai kwana bakwai ake idan aka aure budurwa, ban san mace na zuwa da abinci ba idan aka aureta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login