Showing 12001 words to 15000 words out of 253142 words

Chapter 5 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18441

kuma kallonta kadai da jindadin yadda take cin abincinsa ya wadatar da shi, farincikin fada masa abincinsa yayi dadi da ta yi ya kosar da duk wata yunwa da zai ji a wunin ranar.

Ya daga mata kai yana murmushi kadan, yana jin kamar ace su daure a haka, su yi zama irin na masoya ko ma'aurata, sai dai ya san samun haka a gurin Emily a yanzu ba abu ne mai sauki ba. Kallon agogon falon da ta yi ya saka ta yi hanzarin karasa cin abincin ta mike tsaye.

 Bana son na yi latti, karfe 6:30am zan tafi aiki

 Wane irin aiki ne za'a tafi karfe 6am? Me yasa kike son takurawa kanki a yanzu Emily kina da komai a nan

Bata ce masa komai ba, ta cire jacket dinsa ta aje a jikin dayar kujerar, ta kwashe kayan da ta bata ta kai kitchen sannan ta wuce ta haura sama. Mikewa yayi tsaye ya nufi jacket din ya dauka yana kallon stairs din kamar mai jiran fitowarta.







TURHAN POV.

 Baka amsa ni ba

Ta maimaita da yaren da ita da shi suka fi fahimta, wato Larabci. Lemun dake gefen Laptop din ya dauka ya sha ya aje sannan ya kalleta ta cikin Systems din dake gabansa.

 Ba yanzu ba, akwai wani aiki da ya taso min, ina son sai na karasa shi tukuna?

 E' 7(J9) 9EDC J' -J'*J
 Wane irin aiki ne Hayatie?

Ya kawar da fuska kaminnya juyo ya kalleta yana shafa kansa, bata jira amsarsa ba ta sake aika masa da wani zancen.

 D' #3*7J9 *-ED :J'(C 9FJ.

 Ba zan iya jure rashinka a kusa da ni ba

 Abu mai muhimmanci baki bukatar sani, idan na kammala zan dawo

 Ka canja min a yanzu

Ya shafa kansa yana jin wani sabon fushi na kokarin rufe shi.

 Saboda bana haihuwa ne, ko kuma dai ka gaji da zama da ni ne?

 Zaki iya ba ni a? Zaki iya haifa min jinina Jalila?

Ta yi shiru tana kallonsa kamar yadda shi ma yake kallonta, kamin ya kai hannu ya rufe Laptop din ya kwanta jikin kujerar yana maida numfashi, me yasa ya fada mata haka? Al'adunsu da dokokin sa ake cilasta masa bi ba daga ita ba ne daga masarautarsu ne da kuma mahaifinsa.
Ya tashi zaune yana jin fushinsa yana karuwa tunawa da yayi da yadda Ammy ta yi fushi da shi, saboda yarinyar da bata da ala komai da ita.
Gaba daya an hada masa zafi ta ko'ina, babu wani daki daya da zai laba yaji sanyi. Wayarsa ya dauka ya kira abokinsa har lokacin be sauka daga fushi da bacin rai da yake ji ba.




ALIYU POV.

Yana zaune a kan gado, matarsa na kwance kanta na cinyarsa, ita da shi sun sakarwa plasma dake dakin idonsu, gadon da suke kai kuma ya karbi amanarsu, domin kana kallonsu zaka san hankalinsu a kwance yake basu da wata damuwa ko kadan.
Wayarsa dake can kan karamin tebur ajeye ce ta yi ringing, a take ya ja tsaki domin ya ji dadin zaman baya son motsawa.
Gashi be saba zama kusa da wayarsa ko yawo da ita idan yana tare da matarsa ba.
Abu ne da ya sabawa kansa da shi aje wayarsa a nesa da matarsa a duk lokacin da yake tare da ita, doka ce ya sakawa kansa matukar yana gida tare da iyalinsa to lokacinsa na matarsa zai bata kulawa iyak???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ar kokarinsa.
Gwanar na jin haka sai ta tashi zaune tana kallonsa.

 Na dauko maka ka ba ni dubu biyu?

A take murmushi ya subuce masa.

 Wai ke ina zaki kai kudi da son kudin nan?

Ta saka dariya.

 Zaka biya na dauko?

 Aa ni ma fa na san zafin kudi Hajiya, zan dauko kayata

Sai ta maida kanta a cinyarsa.

 Ni gaskiya na jidadin kwanciyar nan ba zaka tashi ba

 Okay saboda ni zan dauko ko?

 Idan ni zan dauko zaka biya, idan ba haka ba gaskiya ba zan daga a cinyar nan ba, ai kasan idan kana gida kai nawa ne ni kadai

 Ko ma bana gida ni naki ne har abada, yanzu daga ni na dauko sai na biya 2k din, kin ga wannan tsohon cikin naki ba zan so kina wahala ba

Ta daga masa saboda ta ji yace zai bata kudin kuma zai dauko wayar da kansa.

 Hmmm ku dai maza idan kuna tare da mu ku namu ne idan kun fita kuma na wasu dai

Ya mike tsaye ya isa ya dauko wayar yana murmushi already kiran ya yanke.

 Ke dai kishi zai miki illa, me ya kawo wannan maganar kuma?

 Ai na san halin maza

 Bayan wa kika aura? Da zaki ce kin san halin maza?

 Kai kadai na aura amman ai ana fadar halinku

 Ni dai na banbanta da sauran, yanzu wanda yake da mace yar dumaduma irinki har wata zata burge shi?

Ya fada bayana bin bayan kiran da aka masa.

 Hello Allah ya taimaki Yarima

Daga dayan gefen Turhan yayi murmushin karfin hali.

 Tsokanar ta tashi kenan, ya gida?

 Lafiya kalau

 Sorry na kira late na san kana tare da Madan ko?

Aliyu ya kalli uwargidansa yana murmushi

 Kamar ka sani kuwa, daker ta bar ni na amsa wayar ma

 To a bata hakuri, wani uzurin ne ya taso min...

Turhan ya shimfida masa kudurinsa sannan ya bijiro masa da bukatarsa.

Aliyu ya dan sosa kansa.

 Akwai wandanda zan hada ka da su ba ma daya ba, amman Turhan kana ganin nemanta abu ne mai sauki? Ni ma fa na saka anbincika maka lokacin da na yi zama a Lagos din nan amman ba a dace ba

 Wannan karon ina son na bi gidajen marayun da yake cikin garin Lagos ne, na bincika ko zan dace

 Eh toh kuma ka kawo shawara, amman duk da haka ina ganin zai yi wahala saboda an kwana biyu, kuma ka fada min tun tana karama aka yi rikonta a can, kuma ba lallai ne ka sami ma'aikatan gurin na da ace su ne har yanzu?

 Yeah amman ina zaton indai sun santa sosai da sosai za su gane ta idan na bada misalinta wata kila za a dace

 Dama dai kana da hotonta abun zai fi sauki

 Haka din ma zan gwada wata kila a dace, ina tunanin duk wanda na fadawa sifofinta blue eyes red hair, fara mai kiba sosai zai gane ta matukar ya santa

 Allah yasa a dace, zan yi magana da wani yarona da yake can da safe sai na hada ku

 Okay thank you

Ya aje wayar ya sake zaunawa kusa da matarsa, wannan karon sai ta tashi zaune tana kallonsa.

 Kyakkyawana

 Hmmm

Ya amsata yana wani tunanin na dabam, har idonsa suna motsawa, sai kuma ya tabe baki zuciyarsa na raya masa abun da be isa ya fada a gaban matarsa mai tsananin kishi ba.

 Kana ji na

Ya aje wayar ya mika mata hankalinsa gaba daya.

 Ina jinki Sarauniyata

 So nake ka yi min wani alkawari

 Na me?

Ta yi shiru na wani lokaci kamar mai nauyi fada sai kallonsa take tana nokewa kamar marar gaskiya.

 Na miki alkawari cewar ba zan kara aure ba bayan ke?

Ta daga masa kai tana mamakin yadda yayi saurin lagonta.

 Eh ya aka yi ka gane me nake son fada?

 Na sanki da kishi ne ai, zuciyarki zata raya miki idan na fita waje mata nake kulawa ko?

 Na san ba halinka ba ne, ba zaka kula mata ba, amman su matan za su iya kawo maka hari kuma zuciya bata da kashi, kuma ni gaskiya ba zan iya sharing dinka da kowa ba

Yayi murmushi ya shafa fuskarta.

 Saka ranki a inuwa, Aliyu na ki ne ke kadai daga ke babu kari babu wanda zata kawo hari na rufe kofa, na miki alkawari ba zan taba miki kishiya ba

Ta bude ido tana mamakin yadda yayi hanzarin bata hadin kai da wuri haka, ko da yake ta san waye mijinta ba mutum ne mai son mata ba, kuma ya sha fada mata tun kamin ya aureta cewar shi ba shi da ra'ayin aure mace sama da daya.



______________
Anya Aliyu zai rike alkawarin nan kuwa?

Turhan zai samu ganin Aisha kuwa?

Wane irin so Vito yake yi ma Emily?

Meyasa Emily ta dage sai ta yi aiki? Bayan duk gatan da ta samu a gurin Vito?
[4/20, 9:58/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*


Barka da warhaka mutanen arziki=?
?

Shim kun san cewa Khadeeja Candy komai da komai? Amman banda Wan mutum da mutum=??

Ina masu neman kayan Kitchen masu kyau masu inganci, Luxury Warmers manya da kanana, ina masu neman Bedsheet kings and Queens manya da kanana, ina masu neman Akwaitunan lefe da na tafiya. Khadeeja Candy na da Boxes kala kala, ina masu neman tufafi, kama daga Atamfa, Laces, Shadda Lace, Veils, shoes and Bags, Materials. Akwai freezer, Gas cooker and water dispenser.

Duka zaku samu a gurin Khadeeja Candy Store, Khadeeja Candy dai taku ta makaranta, da fatan za ku yi patronizing Wina.

Za ku iya join group dina domin bawa idanuwanku abinci https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

Kuma zaku iya saka order ta wannan number 08036126660 WhatsApp.

KHADEEJA CANDY STORE expect more, and pay less...=?
?



Page 5??

Bata sauko ba sai da ta tabbatar ya fice daga gidan, sannan ta sauko ta sakawa Fatima lunch dinta a lunch box ta shirya mata komai kamar yadda ta saba, Londom kuma da ake masa darasi a gida sai ta zuba masa a nasa na nasa kayan cin abincin, sannan ta haura saman ta shiryawa cikin shiga ta riga da wando ta saka turare ta maida sarkar Cross dinta a gaban rigarta yadda zata fito da kyau.

Red hair dinta ma ya faku da kyau ta yi kyau ta fito tsab, kana ganinta ka ga kyakkyawar mace mai aji, da matukar daukar hankali. Id card dinta na aikin ta fara dauka ta saka sannan ta dauki jacket ta saka saboda yanayin garin akwai sanyin sai dai ba sosai ba. File din jiya ta dauka tare da jakarta ta wayarta ta fice daga dakin, sai da ta shiga dakin Londom ta duba shi ta sunbance shi sannan ta fito ta leka dakin Fatima, sai ta same ta zaune da alama farkawarta daga bachi kenan. Da murmushi Emily ta karasa kusa da ita ta aje kayan dake hannunta ta shafa kanta.

 Good Morning Princess

Fatima ta kalleta ba tare da tace komai ba.

 Okay jiya na san mun yi fada kamin ki kwanta kin kwanta da fushina I'm sorry

Ta bata fuska.

 I just hate Vito Mom, ke kuma kullum kina shigar masa baki ganin laifinsa

 Princess V be mana komai na ganin laifi ba, yana kula da ku yana kula da ni, gidan nan da duk abun da yake ciki nasa ne, be taba mana komai ba

 I just hate him, bana son ki aure shi Momy

Ta fada cikin kuka, Emily ta juyo ta fuskance da kyau damuwar ganin hawayen yarta na bayyana a fuskarta.

 Ba aurensa zan yi ba, ni na gama aure a rayuwata, amman baki da dalilin tsanarsa, shi yake kula da mu, shi kadai ne mutumen da ya rike ni ba tare da kyama ba, shi kadai ne ya kaunace ni a yadda nake yake kokarin kyautata min, shi ya maida ni yadda nake a yanzu

 Ya fada min aurenki zai yi ko da bana so, yace min na fara kaunarsa tun a yanzu saboda shi zai zama step father dina

 No no... Princess ba zan auri kowa ba, ba zan aure shi ba, ba zai zama stepfather dinki ba, but ya kamata ki girmamashi

 No... To mu bar masa gidansa Momy

Emily ta shafa fuskarta.

 Shi ne kudirina, amman ba zan iya haka ba sai na tsaya da kafafuwana, shiyasa na dage nake son fara aikin nan, zan rika saving kudi idan na tara zan koma wani gurin za mu bar masa gidansa da komai nasa, na miki wannan alkawari Fatima

Fatima na jin haka sai ta rumgume ta da sauri tana murna.

 Promise Mom

 I promise

Ta fada yana shafa bayan yarta, Fatima ta dago daga jikinta ta rike fuskarta.

 Momy a ina kika samu aiki

 Wani babban kamfani ne dake hakar ma'adanai da bincike akan albarkatun kasa, babba guri mai girma kuma mai hawa har biyar

 Ke a hawa na nawa kike?

 Na hudu, ina aikin da wata mace mai mumman hali, sunanta Amal kin san musulmai ba su da kirki ko? Ita ma bata da kirki ko kadan

Fatima ta wara ido kamar ba ita ce ta gama fushi dazun ba.

 But I'm Muslim Mom you know

Emily ta ja kumatunta.

"You're different because you were raised by a Christian mother"

Ta yi dariya ta sauka daga kan gadon, Emily ta bita da kallo tana jin kaunarta sosai, haka take son yaranta fiye da kanta, tana son farincikinki yaranta fiye da nata, bana son su rasa komai domin ta san yadda ake ji idan ka rasa wani abu, domin ta tashi ita kadai ba tare da yan'uwa ko iyaye ba.

Ta sani ta rasa farinciki, sai dai ta daukarwa kanta alkawarin ba zata yarda yaranta su rasa farinciki ko su shiga makamanciyar kazantacciyar rayuwar da ta shiga ba. Tana zaune gurin har Fatima ta fito daga bandaki ta shimfida karamin sallayarta ta dauki hijab, kallonta kawai take cike da burgewa tana jin dadi tana jin farinciki a duk lokacin da ta ga yarta tana ibadar da ta zabarwa kanta, bata son tauye mata hakki ko kadan hakan ya saka ta barinta ta aiwatar da addinin da ta dorata akanshi da farko kamin ta yi kokarin canja mata ra'ayi hakan kuma ya gagara saboda abun da shiga zuciyar Fatima sosai. Even though ba ko da yaushe take sallah ba, amman duk inda zata shiga ko a tambaye zata fadi cewar ita musulma ce, hakan kuma ya kan bawa duk wanda ya san mahaifiyarta mamaki, domin mutanen da suka san Emily a yanzu sun santa a Christian, kamar yadda sarkar Cross din dake wuyanta take nunawa a kullum.

 Okay Princess zan tafi aiki, na san yanzu Chidimma zata shigo ta shirya miki zaki tafi makaranta, i love you

Ta fada sannan ta mike tsaye ta dauki kayanta ta fice daga dakin. Ta yi tafiya sosai kamin ta samu abun hawa kasancewar safiya ce ba kasafai ake samun ababen hawa a unguwar da safe irin lokacin da ta fita ba, gashi bana da ra'ayin amfani da motar da V ya siya mata tana son nesanta kanta da wasu abubuwan ne tun a yanzu.

Karfe bakwai daidai mai texi din ya shiga da ita cikin kamfanin, sai da ta sallame shi sannan ta fita tana kallon yadda a yanzu ake bude wasu bangaren ma, masu shara da mopping na yi. Tsirararun mutane ne kawai suke shigowa a kamfanin. Kai tsaye ta shiga ciki ta hau Elevator zuwa 4 floor din da take, a nan din ma ta samu masu mopping suna gyara floor din. Da Keys din hannuna ta yi amfani ta bude kofar Office dinta ta shiga sai ta shiga ga mamakinta sai ta samu an goge ko'ina. Da mamaki ta aje file da jakar hannunta ta fito ta tambaye wani namijin dake mopping a gurin.

 Dan Allah ka ga wanda ya shiga office din nan?

 Gaskiya bayan ni babu wanda ya shiga

 Kai ka gyara office din?

 Eh ni na gyara ni nake gyara ko'ina ai

 Kana da key din dakunan kenan?

 Eh ni nake kula da ni ni aka hannatawa komai

 Okay sannu da kokari

Ta koma ciki, har ta zauna sai ta tuna da Office din Amal a take ta yi hanzarin tashi ta fito ta nufi office din ta bude sai ta juyo ta kalleshi.

 Me yasa baka gyara nan ba?

 Tace ke zaki rika gyara mata

 Okay...

Ta furta with little bit of confused, why her? Bayan ya fada mata shi yake gyara ko'ina, ko da yake Amal din ta fada mata da kanta tun a ranar farko.

 Idan ka gama ka ara min mopper zan gyara gurin

A madadin ya bata sai yayi mata jagoranci zuwa gurin da ake aje moppers din ta dauko daya da tsintsiya ta gyara office din tsab sannan ta mayar ta aje. Komawa ta yi office dinta ta zauna bata san me zata yi ba dan haka ta bude data ta ta shiga social media sai misalin tara ma'aikatan kamfanin suka fara shigowa. Misalin 9:15am telephone dinta ta yi ringing, a gurinta abu ne sabo a kirata da telephone in her own office, sai da ta yi murmushi sannan ta amsa kiran

 Hello

 Ki same ni a office

 Oka...

Kamin ta karasa wayarta furta okay din Amal ta aje telphone din. Emily ta mike tsaye ta fice daga office din zuwa office din Boss dinta. Tsayawa ta yi tana knocking domin bata manta gargadin da tayi mata ba a jiya.

 Yes

Ta mata izinin shiga bayan ta bata lokaci tsaye a gurin.

 Good Morning Maa

 Na fada miki sunana Amal ki daina kirana Maa kamar wata tsohuwar

 I'm sorry

 Waya gyara dakin nan yau?

 Ni na gyara

 Good, sauraka kasa ki samo min snacks zan yi breakfast da ki siyo min bubble tea

Ta jafa mata Atm dinta, tana duba wasu takardu.

 Ina file din da na baki jiya

Emily ta kalli Atm din dake kasa, me yasa ba zata iya bata da hannunta ba ko ta dora a tebur ta dauka? Me yasa take son wulakantata? Ko da yake ba abun mamaki ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login