Showing 6001 words to 9000 words out of 253142 words

Chapter 3 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18421

dace

Har Ammy ta yi shiru sai kuma ta kalleshi.

 Eh ina zuwa

Ta mike tsaye ta nufi hanyar da zata sadata da dakinta, wani sanyi ya ji ya sauka a zuciya jin cewar kamar ya kusan samun hanyar da zata sadashi da Aisha. Babu jimawa Ammy ta sauko tana kallonsa idauwanta a kankance irin bacin rai, sai da ta zauna sannan ta mika masa takardar dake hannunta.

 A lokacin da ta shigo ta dauki danta ba tare da na sani ba, ta bar min wannan akwai address dinta a ciki

Turhan ya karba da sauri ya warware takardar da kana ganinta kasan ta jima a ajeye.

_Kin ce danki ya sha babban da sauran, wata kila dai baki fahimci danki ba ne, wata kila kin hada aurena da shi ne saboda kina neman mafitar yadda zai dawo gareki, amman duk halinsu daya, shi ma be san daraja ta ba, na fada miki musulmai ba su da kirki kika karyata ni, akan abun da yake zahirinsa, musulmai basa kaunar tubabben basa son kowa sai wanda ya tashi dan asalin dan?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? musulmi, ba su da mu'alama mai kyau, basu san darajar kowa ba sai junansu, abun da kuke aikatawa dabam karantarwarku dabam, shi ma an da kike cika baki da shi ya wulakanta ni kamar wancan, duk akan me? Addininku? To na bar muku, zan koma a gurin da nake da daraja

Tun gabani ya gama karanta wasikar zuciyarsa ta tsinke hawaye suka taru a idanuwansa har suka sauko a fuskarsa.

 Saboda kai Aisha ta ji cewar bata da gata a gurin Musulmi, ka karyata duk wani abu da na yi amfani da shi na karfafa guiwar yarinyar nan, kuma ka saka ta ji cewar na yaudareta, ba ni da wani addireshinta bayan wannan

Turhan ya daga kansa ya kalli Ammy, ganin hawaye a fuskarta, ya saka shi cikin tashi.

 Zan nemo ta Ammy, zan nemo ta ko da hakan yana nufin na yawace duniyar nan, zan samo ta ko da hakan yana nufin rasa rayuwata ne, zan kawo miki Ammy wannan alkawarina ne

Ya mike tsaye ya share nasa hawayen ya fice daga dakin rike da takardar.




_________________________

Wai me Turhan ya aikatawa Aisha ne? Me yasa Ammy ta gagara shiryawa da shi?

Anya kuna ganin Emily zata jure aiki a karkashin Amal kuwa? Bayan kuma Amal bata son kafirai, Emily kuma bata kaunar musulmai?

[4/20, 9:57/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*


3??

Teburin dake office din ta nufa ta dora file din da Amal ta bata, tana karewa karamin office din da be karasa girman na amal ba kallo. Sannan ta nufi windows ta bude tana kallon kasa, iska mai dadi na shigowa office din. Ta dade tsaye a haka sannan ta matsa baya ta rufe, ta nufi gurin da durowar office din take ta fara budewa tana dubawa, kusurwar farko an rabata biyu ne da wani katako tsakiya, daga sama an dor Kur'ane daga kasan kuma Bible, doka ce ta sabon CEO na yanzu, aje Qur'ane mai fassarar turancin, da Bible a kowane office a kokarinsa na son tallata addininsa, ta dayan bangaren kuma gudun complain ya saka yake aje Bible din domin baya kowa hakkinsa, sai idan baka bujata sai ka yi magana a dauke.
Risinawa ta yi ta rage tsawonta ta taba Bible din da hannunta na dama. Wani bangare na maganar da Momy ta yi mata ya dawo mata sabo a yanzu.

_Emily karki bari yaron nan ya yaudareki, kar kyaunsa ya ja ki ga halaka, domin bayan kyaun ban ga wani abu da yake da shi ba, mun fi shi arziki a gidan nan, zaki samu miji mai kudi mai komai ba, zan inganta rayuwarki ni da mijina, please karki kunyata mu, abun kunya ne ace kina gidan Pastor kin bar mu kin bi musulmi, karki lalata rayuwarki da kananan shekarunki please Emily, ki rike wannan Bible din ki yi karatu bana son na sake jin maganar yaron nan, kin ji my beautiful Diamond Girl_

Ta dauke hannunta da sauri tana hawaye, ta rufe durowar ta juya ta zauna a gurin ta jingina da ita sai kuma ta fashe da kuka, jikinta na karma kamar wanda ta firgita.

 Hamza ka cuce ni... Ka cuce ni... Ka raba ni da matar da ta rike a matsayin ?a, kasa na butulcewa macen da suka rike ni da amana

Ta girgiza kai.. Ta dayan bangaren ba laifinsa take gani ba, laifin zuciyarta ne data? barta ta fada soyayya da mutumen da be san darajar addininsa ba balle ita. Wani irin duka ta kai kirjinta tana jin kamar ace zata iya ganin zuciyarta a fili ta yi mata duka. Tuna cewar ba a gida take ba ya saka ta natsu ta sassauta kukan da be gama fita ba, ta hade kanta da guiwa.
Ta dauki lokaci tana rarrashin kanta sannan ta mike tsaye ta dauki file din ba tare da sake taba komai ba ta fice daga office din ta rufe kofar da key ta nufi hanyar da zata sadata da elevator.?

Babu abun da take a cikin elevator sai tunanin yadda rayuwa tayi da ita. Har ta isa first floor bata hankara ba sai da kofar ta rabe biyu, ta fita ba tare da ta lura da mutanen da suke tsaye suna kokarin shiga elevator ba. Daya daga cikinsu ya biyo bayanta a sirance har sai da ta yi rabin gate din dake da tsayi sosai.

 Excuse me Miss

Ta juyo ta yi sai ta yi arba sa wani bakin mutum bayanta yana sanye da yellow t-shirt da black jean.

 Can i help you?

 Yes

Ya matsa kusa da ita.

 Kin shigo neman wani abu ne? Ko kina daya daga cikin team din Resrezor?

 No na fara aiki a nan ne

 Yaushe?

 Yau

 A ina? Wane guri office dinki yake?

 Four floor hannun hagu office na biyu

 Nice to meet you, I'm William, ina 5 floor office na hudu

Ta mika masa hannunta kamar yadda ya mika mata nasa.

 Emily

 Nice to meet you Emily, kin samu aboki yanzu

Ta yi murmushi tana kallon sarkar Cross din dake wuyansa hakan sai ya saka ta ji dadi ganin kirista ne dan'uwanta.

 Har kin tashi ne?

 Eh

 Okay Bye

Ta yi murmushi ta juya ta cigaba da tafiyarta. Shi kuma ya tsaya a gurin yana kallon yadda wandon jikinta ya dame jikinta yayi mata kyau.

 Wow...

Ya shafa kansa sannan ya juya ya cigaba da tafiyarsa. Ta isa gida da wuri saboda ta samu abun hawa da wuri, sai da ta sallame shi sannan ta kwankwasa kofar gate din. Mai gadin ya bude mata ta shiga tana amsa gaisuwarsa. Tura kofar falon ta yi ta shiga sannan ta rufe ta cire talkamin kafarta ta saka na falon sannan ta karasa ciki. Ganin kwalbar giya aje a tsakiyar center Table din dake falon ya karantar da ita V ya bar gidan cikin bacin rai, domin abu ne da ta sani, idan ransa ya bace giya yake sha ko marijuana.

Da sauri ta jefar da Jakarta da file din hannunta ta nufi dakin da London yake ta bude gabanta na faduwa, ta duba dakin har bandakin baya ciki, hakan ya saka hankalinta ya kwanta domin shan abun maye ko drugs abu ne da bata son yana yi a gaban yaranta, wannan yana daya daga cikin dalilin da ya saka ta zabi raba gida da shi, ta zabi rayuwa ita kadai sai yaranta.
Fitowa ta yi ta dawo falon ta dauke kwalbar ta shiga Kitchen ta tsiyaye ragowar barasar dake ciki ta fasa kwalba ta zuba a dustbin sannan ta wanke hannunta ta fito.

A gurin da ta jefar da jakarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, tare da daga kanta tana kallon rufin falon zuwa gurin da katon plasma ta yake. Ta sani ahalin yanzu bata rasa komai ba sai kwanciyar hankali, Vito ya jika da kudin da bata jin akwai wata mace mai tarin dukiya irinta, ita kanta bata san adadin abun da ke account dinta ba, domin kowane sati sai ya saka mata kudi ita da yaranta London da Fadima duk kuwa da kasancewar karamar yarsa Fadima bata son shi, amman be taba kula haka ba saboda yana matukar kaunar mahaufiyarta.

A cikin gidan da take rayuwa gidane da ko wucewa kawai ka yi a gaban gate din sai hankalinka ya tashi saboda kyaunsa, shi kansa nasa gidan be kai nata kyau ba, ya zuba mata kayan more rayuwa daga sutura har abubuwan ado na kawata falo ko daki, ga mayan motoci da ya zuba mata a cikin gidan, ga Nannyn da ya dauka mata mai kula da yaronta, ya saka yarta a makarantar kudi ta yayan manya, London kuma da ya kasance Autism ya biya ake karantar da shi a gida. Bayan kudin da ya biya aka yi mata aiki, ya kaita waje ta yi karatu.
Amman duk da haka tana jin ta rasa wani abu a tare da ita, she felt something is missing inside her.
Ji take bata cika ba har yanzu, tana jin akwai abun da ta rasa kuma bata san miye wannan ba, sai dai ta san dalili daya da ya saka take son tsayawa sa kafafuwanta, wannan sirri ne da ba zata iya budewa kowa shi ba.

 Good Afternoon Ma

Cewar Chidimma bayan ta shigo falon. Emily ta kalleta da irin fuskar nan na wanda tunani be gama sakin kansa ba.

 Chidimma, a gaban London V ya sha alcohol dazun?

 Aa bayan na shiga dakin Landon ne na canja masa tufafi saboda za su fita tare

Ta sauke numfashi a hankali.

 Okay please duk yadda za'ayi karki bari yarana su ga lokacin da Vito yake shan giya, balle har hannunta ya kai gurin

 Okay Ma zan kiyaye

 Ki shirya musu wani abu ni zan yi bachi

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta dauki jakarta da file din ta haura sama ta shiga dakinta ta aje jakar da file din a kusa da gadonta ta kwanta, tunani ya fara kawo mata ziyara kamin bachi yayi gaba da ita.





ALIYU POV.


Dagowa yayi a hankali ya kalli kofar office din da aka turo. Mutumen ya karaso gaban teburin cike da girmamawa ya bude masa daya daga cikin files din da suke hannunsa.

 Nan zaka saka hannu

Sai da Aliyu ya gama abun da yake a computersa sannan ya kalli file din ya saka hannu.

 Ranka ya dade cikin sabin ma'aikatan da aka dauka har da turawa?

Cewar mutumen dake tsaye gabansa, shi dai be ce komai ba, har sai da ya gama saka hannu a duka files din.

 Na ganta zata fita dazun

Aliyu ya sake dubansa ba dan ya fahimci inda zancensa ya dosa ba.

 Baka ga sabin ma'aikatan na mu ba

 Ba ni nake da hakkin ganinsu ba, ban san suwaye aka dauka ba

 Wata baturiya ce fara kyakkyawa har ta fika haske ga blue eyes

Aliyu ya dan yi jimmm alamar nazari can kuma sai yayi murmushin da ya kara masa kyau.

 Ka ganta kenan?

 William, na ganta and what?

 Tana da kyau, ga fari duk yadda aka yi wannan yarinyar baturiya ce ko half cast, na gode da ka dauketa, and finally kirista ce yar'uwata

 Ka godewa Amal aikinta ne not mine, ni ban san su waye aka dauka aiki ba ma

Ya aje zaren zancen a daidai lokacin da wayarsa ta ringing. Kallon wayar yayi yana murmushi.

 Shiyasa ake daudararku koda yaushe kyaun kuke bi ba hali ba

Ya amsa kiran ya kara wayar a kunnensa, at the same time da William yake fadar.

 Ka rantse da Allah ka na musulunci cewar ka taba ganin yarinyar da ta fita kyau? Ni fa rudewa na yi na kasa rike kaina sai da na yi mata magana

Da sauri Aliyu yayi saurin yi masa alama da hannu na yayi shiru ya yi tafiyarsa. William zip up his mouth yayi ta tafiyarsa.

 Hello yar kyakkyawata

 Na'am ya aikin?

 Alhamdullahi ya cikin?

 Ban sani ba

Ya saka dariya daman da neman magana ya saka shi tambayarta.

 Miye laifina dan na tambaya?

 Ni dai ban sani ba, kawai dai na kira na fada maka Gwaggo ta kira tace Anty Sa'ade ta haihu

 Maa shaa Allahu, me muka samu?

 Irina ce aka samu

 Ki ce irinki marar jin magana ko?

Ya fada yana wani abu da ido kamar tana gabansa.

 Ba zaka daina ba ko?

 Na daina yar shawalwalar yarinyar yar dirarar yar black beauty na kyakkyawata

Ta yi dariya.

 Bye sai ka dawo

 Okay mai ciki

Yana fada ya kashe wayar da sauri yana dariya, sannan ya aje wayar ya maida hankalinsa gurin aikinsa.


TURHAN POV.

Ya aje mug din tea dake hannunsa.

 Yadda kasan yarinyar nan ta yi ma Ammy magani haka ta juya min baya, gaba daya na kasa gane kan mahaifiyata

Mannir dake kallonsa ya ce

 Amman dai ka san abun da ka yi mata baka kyauta ba? Baka ji haka ba?

 Na san ban kyauta ba Manir kuma na ji babu dadi, ina kan jin babu dadin ma a duk lokacin da na tuna, amman yadda Ammy ta hau karamin abu ta maida shi babba shi ke daga min hankali kuma ya ba ni mamaki

 Iyaye sai hakuri, kuma kasan Ammy ta dora hope sosai akanka game da yarinyar nan, sai kuma gashi ka bata kunya, waya sani ma da ace ita kake aure har yanzu wata kila da yanzu kun haihu, gashi nan wannan yarinyar da ka fifita akanta har yanzu baka baka a ko ya ba

A take yanayin Turhan ya canja duk kuwa da ya san gaskiya aminin nasa yake fada, kuma samu a ko ya wani abu da yake fata kuma ya dade yana mafarki.

 Mace bata bawa kanta haihu, duk wanda ka ga ya samu haihuwa hukuncin Allah ba yin kansa ba

 Haka ne, sai dai kuma wata kila yana cikin dalilin Ammy na yin fushi da kai, kuma yarinyar nan fa abar tausayi ce

 Na sani, amman Manir ana samun sabani sosai akan abubuwa kuma sai ka samu iyaye sun yafe sun duba dansu, amman ni Ammy ta kawar da idonta a kaina gaba daya

Manir ya sauke ajiyar zuciya.

 Yanzu ka aje duk wani hange hange da tunanin banza, ta ina zamu fara?

 Nemanta, zan shirya duk abun da zan yi a yau, gobe zan sauka Lagos zan fara nemanta

 Wane tabbaci kake da shi cewar tana Lagos?

 A can aka haife, acan ta taso kuma bata san kowa a nan arewa ba, kamin ta bar nan Ammy ta fada ta ganta a coci, bana tunanin zata iya zama garin nan ma gaba daya, idan har zata zabi zama cikin kista yan'uwanta ba ta da wani gida da ya wuce Lagos, matsalar kawai a Lagos din ban san wane gida take ba

 Shi ne Matsalar, kuma Ammy bata ffada maka wane gidan Marayu ta zauna ba?

 Bata fada min ba, amman dai zan yi ta bincike har na gane

 Baka san kowa a Lagos ba, nemanta ba zai maka sauki ba, gaskiya Ammy ta dauki abun nan da zafi

Turhan ya busar da iskar bakinsa.

 Zan tuntubi Aliyu yayi zama Lagos kamin ya koma Port Harcourt, maybe zai iya hada ni da wani da zai iya taimaka min mu yi neman tare

 Oh na manta ma da shi Wallahi, ka yi masa magana mu ji ba zai rasa wanda zai taimaka maka gurin nemanta ba, ni kuma zan yi ta lallaba Ammy a nan ko zamu samu wani abu daga gurinta

Turhan ya sake daukar Mug din ya sha tea.

 Ta fa yafe min, kawai dai ita wai yadda muke a da ne, ta ki ta dawo min a haka

 Irin wannan ai sai ya saka ka ji ka tsani yarinyar, ko da yake..

Manir yayi shiru ba tare da ya karasa ba. Turhan ma be sake ce masa komai ba ya maida dubansa wani gurin sai tunani yake.




EMILY POV.

Jin an taba fuskarta ya saka ta bude blue eyes dinta a hankali tana kallon Vito dake zaune gefen gadon kusa da ita. Tashi ta yi zaune tana kallonsa, kallonta yake shi ma irin kallon nan mai cike da kauna, sai dai girman kai da jin isa ya hana shi sakin fuska balle har ta ga murmushinsa.

 Ina London?

 Yana dakinsa, me yasa baki fita da mota ba?

 Bana son kowa ya san wani abu akaina, na fada maka wata sabuwar rayuwa nake son yi

Ta yaye blanket din dake jikinta ta matsa ta saka kan gadon ta dayan gefen, sai yayi hanzarin rikota ya juyo da ita da karfi.

 Fita mota zai hana wani abu daga canjin rayuwar da kike so ne? Mi kike shiryawa ne Emily?

 Me kake tunanin ina shiryawa? Na sha fada maka ina son na yi rayuwa kamar kowa, ina son rayuwata ta zama daidai, dole ne sai na shiga mota? Bana ra'ayin haka? Me yasa kake cilasta ni yin abubuwan da bana ra'ayi? Why?

Ya matsa kusa da ita sosai yana kallon cikin idonta.

 Saboda ni kadai na isa na cilasta ki, kuma idan tunaninki ko shirinki na rabuwa da ni ne, to kina shiryawa kanki wani rame ne na halaka, domin ban gane duk wannan abun da kike ba? Me ye ban aje miki ba? Amman tunaninki yana wani gurin dabam, ke tawa ce har abada ba zaki iya guje min ba ki saka wannan a ranki, you're forever mine

Ta fara kokarin kwacewa daga rikon da yayi mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login