Showing 195001 words to 198000 words out of 253142 words

Chapter 66 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18398

muka tashi komawa Abuja ma dake zan tattara mu tafi, idan ma kin zabi sake buguwa ki fada sai na hada kayana mu tafi kin ga neman zai fi dadi"

Aliyu yayi murmushi Emily ma ta yi murmushi tana kallon Ummi.

"Ba zan sake guduwa ba"

"Zamu gani dai, amman ni dai ba zan sake bari ki gudu ba"

Ummi ta tabe baki tana yi ma Aliyu kallon zolaya. Emily ta kalli Aliyu suka sakar ma junansu murmushi mai laushi da sanyaya zuciya sannan ta sauke kanta kasa, Aliyu kuma suna hada ido da Ummi ya ga irin kallon da take masa sai ya girgiza mata kai alamar ba abun da take tunani ba ne domin ya san hasashenta, ya mike tsaye yana murmushi mai sauti.

"Bari naje na yi sallah"

Ya fice daga falon, Ummi ta kalli Mama Barakat.

"Ki shigo dakin kasa sai ki yi sallah ko"

"Dare yayi Hajiya zan tafi gida dai, gobe sai na dawo"

"Toh ba matsala direba yana waje sai ya sauke ki gida"

Mama Barakat ta mike tsaye.

"Mu kwana lafiya Hajiya na gode"

Bayan Ummi ta amsa mata ta juya ta fara tafiya kamar daga sama ta ji muryar Emily.

"Sai da safe"

Ta juyo jiki a sanyaye ta kalli Emily.

"Na yi tunanin ba zaki amsa ni ba ne, shiyasa ban miki sallama ba, ki gafarce ni"

"Zuciyata ta saba da karbar ko wane kalar sako na bakinciki, kaddara ta sunnanta min haka, shiyasa na fahimci rayuwar da nake ciki, ni ce nake son mutane ba wai mutane ne suke so na ba, kuma na yarda zan cigaba da rayuwa a haka"

Mama Barakat ta fashe da kuka.

"Wallahi ba haka ba ne, karki yi zaton bana kaunarki, ina sonki fiye da tunaninki"

Ummi ta kwantar da Emily dake kuka a fadarta sai ta yi ma Mama Barakat alama ta tafi da hannu. Mama Barakat ta fice tana kuka.

"Toh miye amfanin kuka? Abun da ya wuce ai ya wuce, ni uwa ce a gareki Emily, kuma ki daina wannan tunanin na cewa babu mai sonki, da kin san tashin hankalin da muka shiga ni da Aliyu da mai gidana na rashinki sai kin tausaya mana"

Ummi ta dagata daga kan kafadarta.

"Muje ciki ki yi wanka ki ci abinci ki huta na baki labarin yadda aka yi muka gano ki, ko Aliyu ya fada miki?"

Ta girgiza yau.

"Yauwa aikuwa ni zan baki wannan labarin, daman duk ya bi ya ishe ni komai ya tattare baya barin ma wani ya shiga balle ya kyautata miki, shiyasa ma ya fara ba ni haushi sai ka ce shi kadai yake da ke"

Cikin yanayin rarrashi da son faranta rai Ummi take maganar da Emily kamar mai magana da yar yarinya karama sa'ar Fatima. Ummi ta rika ta ta kwantaa fadarta ta rike hannayenta suka fara haurawa sama.

"Kudi ya zuba can gurin Office din kamfanin sadarwa, bayan mahaifinsa ya saka baki aka duba wayoyin da kika kira, aka ga layina da na Aliyu da kuma na wannan likitan, aka ce wunin ranar da su kawai kika yi waya, Aliyu na jin haka ya ce duk yadda aka yi kina gurin Dr, ya fara bibiyar layin, amman da yake likitan nan baya son mu da alheri da Aliyu ya tura masa sako be ba shi amsa ba, muka rika sama da kasa sai da muka hada da Hajiya Baraka ta sama mana Information din mahaifiyarsa Aliyu ya dage, amman ni nake taya shi da addu'a fa dan kar ki yi zaton kamar ban yi komai ba, ke daga karshe sai da mahaifinsa ya shiga kuma ita ma Hajiya Barakat ta yi magana da roko da komai aka samu ta amsa mana tace su zo wannan satin Aliyu ya saka date suka tafi, kamar a mafarki sai na ga sun dawo min da ke, na ma yi zaton za ku tsaya ku kwana Abuja, ashe ya damu da halin da nake ciki sai ga shi be tsaya kwana ba ya dawo"

Emily tana kwance kafadar Ummi tana bata labarin har suka shiga dakin.

"Kin ji yadda aka yi, amman fa mum shiga tashin hankali sosai, ba dan ni ba dan Allah Emily karki sake guduwa ko minene kamata yayi ace kin tsaya kin fuskance shi ba wai ki gudu ba"

"Na rasa ya zan yi ne, abubuwan suka hade min ko'ina ba dadi"

"Har da gidana? Ko kadan ni fa ban bi bayan Hajiya Barakat ba dama ta ba ni labarin abubuwan da suka faru ke na fi tausayawa, to kin ga ni miye nawa da zaki dora min laifi?"

Emily ta dago da sauri.

"Ban dora miki laifi ba, ko kadan baki min komai ba"

"To miye na duguwa ki bar gidan? Na yi tunanin ko ba zaki iya zama ko'ina ba zaki zauna a gurina, har tambayar kaina nake wai ko dai na miki ba daidai ba?"

"Baki min komai ba, kuma ba zan sake guduwa ba"

"Alhamdulillah Allah yasa haka"

Ummi ta rumgume har ga Allah Ummi tana jin tausayin Emily sosai. Bayan Emily ta yi wanka ta canja tufafi sai ta dauki abaya ta dora saman kananan kayan da suke jikinta domin suturta jikinta, na ci abinci ta kwanta kan gado, babu jimawa Nafeesa ta shigo kiranta wai Ummi ta ce ta sauko kasa idan ba bachi take ba.
Babu musu ta fito a dakin na Ummi ta sauko kasa tana jin kamar ta samu gata a yanzu ko da yake bata san me gobe zata haifar ba, amman dukanin wani kulawa da uwa zata nunawa yarta Ummi ta nuna mata a yanzu.
Ta sauko a hankali ta karaso ganin kowa yana zaune kasa sai ta zauna ita ma, kusa da Aliyu sosai a gurinta ita ba komai ba ne dan jikinta ya taba na wani wanda ba Muharraminta ba, a addinin data samu kanta ciki hakan ba laifi ba ne, kuma ta saba.
A kokarin Aliyu na bin umarni Allah sai ya matsa kadan dan kar jikinsa na taba nata, domin ya san ita din ba halalinsa ba ce.

"Muna ta fira muna shan tsamiyar dila baki kusa na ce a kira ki sauka mana cikin dangi, amman na fada mata idan bachi kike ta barki ki huta"

"Ba bachi nake ba"

"To ga abun da muke ci idan zaki iya ci, saka hannunki ki dauka sai an balle ake ci"

Ummi ta fada, kamin ta saka hannunta sai Aliyu ya dauki karamin plate ya aje gabata ya zuba mata wanda ya banbanra.

"Sha ki ji ko zaki iya ci"

Ta dauka ta kai baki sai ta ji abun wani iri domin bata taba ci amman dan tsami tsamin da ta ji ya karbi bakinta dan haka ta cigaba da sha. Kwankwasa kofar falon aka yi kadan kadan kamar bugun yaro, Emily ta kalli kofar da sauri zuciyarta na bugawa da gudu kuma tana raya mata Fatima ce. Aliyu ya mike tsaye ya nufi kofar ya rufe sai ga Fatima ta shigo da gudu.

"Uncle..."

Har ta rike shi zata rumgume shi sai kuma ta sake shi ta nufo gurin Emily da gudu, Emily ma kasa rike kanta ta yi sai ta zabura da sauri ta rumgume yarta ta fashe da kuka, zata iya yafe komai da kowa amman ban da yarta, ko kadan bata son Fatima ta dandana rashinta domin ta san yadda ta rayu saboda uwarta bata kusa da ita, cikin kuka Fatima ta ce.

"Momy ina kika je? Kin dade baki zo ba"

"Saboda kin ce baki so na"

Sai ta kara rumgume Emily.

"Ina sonki ke da daddy ina sonki,. Karki sake tafiya ki bar ni bana son ki tafi"

Emily ta rumgume.

"Idan baki son na tafi ki daina zabar Mahaifinki kina barina, ko gobe kika ce shi kike so to zan tafi na kyale ki"

Sai Fatima ta kara fashewa da kuka.

"Amman ina son shi Momy, yana so na"

"Who do you love the most? Ni ko Dady?"

"You"

"Good"

Emily ta rumgume ta sosai a kirjinta kamar zata maida ita ciki. Fatima na shiga cikin falon Aliyu ya kalli Turhan dake tsaye bakin balcony din be tako ba, sai ma dukawa da yayi yaje masa wayarsa a kasa. Ya saka hannayensa duka biyu aljihu. Aliyu na ganin hakan ya fita ya karasa gurin da wayar take ya duka zai dauka.

"Ka ji kunya Aliyu, ka ci amanata"

"Ban ji kunya ba, kuma ban ci amanarka ba, akwai tsarin da na yi sai dai Allah be ba ni ikon cika wannan burin ba har Kameela ta yi abun da ta yi"

"Ai baka da bakin kare kanka"

"Ba kokarin kare kai nake ba, kuma ba so nake ka fahimta ba, ina fada maka abun da yake gaskiyarsa ne"

"Har abada... Ba zan taba barin yata ta kira wani katon banza da sunan Baba ba, yata ba zata yi agolanci ba yana da kyau ka san wannan"

"Kai yanzu baka ji kunyar fadar hakan ba? Kai yanzu abun da ya dame ka wa Emily zata aura? Ko wa take so? Baka damu ka san lafiyarta ko samun farincikinta ba? Kana da son kanka Turhan... Kuma har gobe ban yi nadamar taimakin Emily ko kuma boye mata kai ba, saboda ta fada kai ne wanda bata son ganin kuma zaka karbe mata yarta ga shi ka aikata, kai yanzu iyakar burinka Emily ta dawo gareka, idan ta dawo zata dawo ta yi farinciki ko aa ba shi ne a gabanka ba, kaico da zuciyar dake take kirjinka"

"Kai kuma Tirrrr da aboki irinki mai fuska biyu, zan baka mamaki Aliyu, kuma ina gargadinka da shiga tsabgar matata da yata, baka da alaka da dukkansu"

Aliyu yayi murmushi kawai ya juya ya shiga ciki, Turhan ya tofar da yawu yana jin zuciyarsa tana kuna. Aliyu na shiga falon Fatima ta juya ta kalleshi.

"Ka ce Dady ya tafi sai gobe zan koma tare da Momy"

"Already ya tafi ai, ni ba zaki min oyoyo ba?"

Ya ware hannayensa, sai ta taso tana dariya ta nufe shi da gudu ta rumgume shi ya daga ta sama ya jefa ya chabe yana dariya ita ma sai datiya take tana farinciki domin ta yi marmarinsa da Momynta. Emily tana ta kallonsu tana murmushi.

" Kin yi missing din Momy?"

"Sosai"

Ta fada tana kallon Emily, sai Aliyu ya dauke ta haura sama da ita suna tafe yana mata hira. A ranar Emily ta yi bachin farinciki irin wanda ta kwana biyu bata yi irinsa ba, ta kwanata rumgume da yarta a dayan dakin da Ummi ta bata saboda ta ki yarda ta hau gadon Ummi ta kwanta sai dai kasa, Ummi kuma ba zata iya jurar kallon ta kwana a kasa ba, dan haka ta bata wani dakin ita da yarta. Kamin Fatima ta yi bachi sai da ta yi ta bata labarin abubuwan da Ammy take mata da kuma Dadyta.
Washe gari Emily na cikin bachi ta ji an taba ta sai ta bude ido, ta yi zaton Fatima na dakin sai ta yi arba da Mama Barakat ga kayan abinci an jere a gurin kamar dai wacan karon.

"Ki yi hakuri na tashe ki kina bachi"

Emily ta murza ido ta tashi zaune tana duba gadon har tana kokarin sauka sai ga Aliyu ya kwankwasa kofar dakin, sannan ya turo ya shigo yana dauke da Fatima.

"Mama Ummi tace min kin shigo yanzu"

Ya fada yana kallon Mama Barakat.

"Eh ku yi hakuri na yi muku sammako, bana son Emily ta karya da komai ne sai abun da na dafa"

"Wacece wannan?"

Fatima ta tambaya tana nuna Mama Barakat.

"Kakarki ce, ita ce ta haifi Emily"

Fatima ta wara ido kamar wata babba tana mamaki.

"Muna da kowa a nan ina farinciki da zama a nan ba za mu koma can ba ko Momy? Ashe ke ma kina da Momy"

Emily ta daga mata kai. Aliyu yayi murmushi.

"Karki yi zaton ko na shigo na same ki a yanayi marar kyau ne, ita ce ta farka da kanta ta fito tana bin daki har ta same ni, wai ta yi zaton ko na tafi ne"

"Momy mun yi sallah mun yi sallah da shi kina bachi"

Emily ta yi murmushi tana kallonsu.

"Aci dadi lafiya ni zan sauka, Emily idan kin gama da wannan sai ki sauko na mu breakfast din yana jiranki, Ummi ma sai fada take wai Mama Baraka ta dako sakko baki farka ba kuma ta san zata shirya miki abun karyawa"

Mama Barakat ta yi murmushi.

"Ka bata hakuri, na tashi tun karfe uku na fara shirya komai saboda kar na makara, zan yi farinciki idan ta ci"

"Zata ci, ai Emily bata da matsala ko kadan kamar ruwa haka take, kifi ce musulmi nama"

Ta fada sannan ya juya ya fita yana dauke da Fatima dake tambayarsa miyasa Emily bata kama da Mama Barakat? Bayan ita tana kama da Turhan. Emily ta shiga bandaki ta wanke bakinta da sabon brush da ta gani ta yi fitsari ta fito ta zauna bakin gado, sai Mama Barakat ta sauka kasa ta bude abincin gaba daya tana tambayar wane zata ci.

"Ina son na kira ki da Aisha ban san ko kina son haka ba, Ummi ta fada min ana kira Aisha amman Emily ya fi karfi, amman sunan da na saka miki Aisha ne ba Emily ba, musulma na haife ki ba kirista ba"

Emily ta dube ta.

"Kina so na haka kika bar ni? Har yanzu na gagara gane wane laifi na aikata miki, na wahala an wulakanta saboda ba ni da kowa, anyi min gori, abubuwa na suka banbanta da na sauran masu iyaye, ban san gata ba ban iya komai sai guduwa daga wannan gurin zuwa wani, fada da kika yi cewar da saninki kika jefar da ni kuma baki taba tunanin ki waiwaye ni ba ya tsaya min a rai, mu ma yaya muna da hakki akan iyaye, baki yi adalci tsakanina da sauran yayanki ba, su kika zabi haifarsu da aure kuma kika zauna tare da su, ni kuma kika watsar da ni, baki yi tunanin waca kalar rayuwa zan yi ba, wane kalubale zan fuskanta ba, kin yi komai saboda gujewa kunyar duniya, shin ba na ji ku musulmai kuna cewa lahira akwai hisabi ba? Saboda kin haife ni ba da aure ba ni miye laifina? Ba shawara aka yi da ni kamin a haife ni ba, ya kamata ki yi tunanin idan kika jefar da ni wace kalar rayuwa zan yi? Zan rayu ko kuma zan mutu ne? Baki tunanin ni ma ina da hakki akanki? Taya kika iya kwantawa ki yi bachi alhalin kin san kina da ya a wani gurin da baki san wane hali take ciki ba? Wace irin uwa ce ke? Taya zaka sha wahalar ciki wata tara da nakuda kuma ka jefar da yaron? Shi ma fa rai ne? Uwa tausayi aka sani da ita ke da iyayen da suke haka ba ku kyauta ba, miye laifin wanda aka haife? Wai illar kawai saboda ba shi da uba, kuma ba da aure aka haife shi ba, miyasa baki yi tunani ba kamin ki haife? Wallahi na Wahala na wahala na wahala, ni kadai na san yadda na yi na Wahala na wahala na wahala na wahala na wahala........... Ahk ahk ahk..."

Ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya da ?o?on rai. Mama Baraka ta bar inda take ta dawo kusa da Emily ta zauna ta rumgume ta tana kuka.

"Ki gafarce ni, ki yafe ni na yi kuskure na sani, ki yi hakuri Emily ki yafe min..."

Emily kuka Mama Baraka kuka babu mai iya rarrashin wani...




______________________

Ga iyayen da suke haifar yara ba da aure ba su jefar, shin kun san kuna daukarwa kanku hakki ne? Hakkin zina hakkin haihuwa ba da aure ba hakkin jefar da yaro, ba ku san wane hali zai fada ba wace rayuwa zai yi a wane hali zai girma ko ya samu kansa ya rayuwa zata kasance, wasu yaran ba za su taba haduwa da iyayensu ba sai Alkiyama.

Allah ya tsaremu, ka tsarkake zuciyarmu.>?2?
[8/4, 9:55/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t



*

*? Khadeeja Candy*



Page 6?? 2??


Na tashi a wani ?aramin gida a Beere, cikin unguwar da ruwa ke ta faman gudu daga bututun da babu mai kulawa da shi, cikin amo da hayaniyar kasuwa, da ?amshin ewedu da ata rodo na mahaifiyata.
Baraka suke kirana Wiya ga wani tsohon malamin addinin.
A cikin al'adun Yarbawa, mata suna da 'yancin yin kasuwanci, sana'a ko aiki tun da dadewa. Wannan ya bambanta da wasu al'ummomi da ke takaita mata ga aikin gida kawai. A yawancin biranen Yarbawa, musamman kamar Legas, Ibadan, da Abeokuta, za ki ga mata masu kasuwanci ko aiki a hukumomi.
Iyayen Yarbawa suna koyar da 'ya'yansu mace da wuri cewa ta rike kanta

Yana daga dabi'unsu su karantar da 'ya mace ta nemi ilimi ko sana'a domin ta rike kanta, ba tare da dogaro da namiji ba. Wannan ya sa da yawa daga cikin matan su ke da ?warin gwiwa wajen kokarin ciyar da kansu ko tallafa wa iyalansu.
Na koyi juriya daga rayuwa, ba daga littafi ba. Na girma ina kallon mahaifiyata tana dafa abinci a kan itace, tana kula da gida kusan nauyin mu da na mahaifina a wuyanta yake, mahaifina ba shi da wani karfi kuma be damu da nema ba, ta kan ce min:

 Baraka, mace na da ?afa biyu? Waya tana goyon gida, Waya tana neman arziki.



Na shiga cikin harkar girki wato siyar da abinci, tun ina 15yrs mahaifiyata kuma tana fita shago siyar da kayan masarufi, a lokacin ban fara karatu a kolege ba, na iya hada tuwo da hannu, da kwasar romon miyar ogbono cikin harba guda. Na kammala karatu a wata college Ibadan, amma bayan na gama sai na gane cewa takarda ba ta nufin abinci a kwano.
Domin bayan gamawa, ba aikin da ya biyo ba. Na zama kamar mutumin da ya haWiye ?ashi, ba zai hade wuce ba, kuma ba zai iya fitarwa ba. Na tattara kayan da ba su wuce buhu biyu ba, na tafi Lagos, wurin kanwar mamata, saboda gurin da nake siyar da abinci a da gonati ta kwace, mahaifiyata ta kuma shagonta yayi kasa, ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login