Showing 120001 words to 123000 words out of 253142 words

Chapter 41 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18383

yana girkin, duk abun da ya zuba sai ya daga ta ta gani da ya gaji sai ya goyata a bayansa ta leko kanta ta saman wuyansa tana kallon yadda yake girki, idan yayi abun da bata saba gani ba sai tace masa ba a haka ake yi ba, shi dai dariya kawai yake ya cigaba, da ya gama hada komai sai ya koma tare da ita falon suka zauna sai da ya nuna sannan ya koma ya zubo musu a plate daya shi da ita.

"Kai kadai zaka ci?"

"Aa ni da ke"

"A plate daya"

"eh ko baki cin abinci a plate daya da wani?"

Ta yi dariyar jindadi

"A gida raba mana ake kowa plate dinsa dabam, amman ina so"

Ya zauna ya sake komawa ya dauko ruwa da lemu, sannan yace ta zo su ci, madadin ta zauna a gefensa ko gabansa sai ta tsallake abinci ta zauna a kan ciyarsa, yana ganin haka sai ya aje Spoon daya ya dauki dayan yana ciyar da ita da shi shi ma sai ya ci, ko loma nawa yayi sai ta kirga tun be hankara ba har ya fara dariya, ita da shi suka ci abinci cikin nishadi, har wayarsa ya dauko yayi mata hoto yayi mata video, kusan a lokacin ne ya ji yana matukar kaunar samun nasa yaran, Fatima kuma ta yi enjoying moment din tana jinsa kamar mahaifinta.

Bayan sun gama ya bude quran app din wayarsa ya tana karanta dan abun da ta iya yana mata gyara, har bachi ya dauke ta, daukar ta yayi ya haura da ita sama ya kwantar da ita kan gadonsa ya lullubeta ya zauna gafen gadon ya karanta mata addu'a ya tofa mata sai ta bude ido ta kalleshi.

"Meyasa kake watsa min yawu"

"Addu'a ce ta tsari idan aka karanta ma yara ko suka karanta babu abun da zai same su har safe, Momy ki bata miki idan zaki kwanga bachi?"

"Aa"

"Toh ki koya ki rika yi ma kanki kin ji?"

Ta taso daga kwance da take ta rumgume shi.

"Da nan nake zaune tare da momy da mun rika jindadi, kowa yana son ace yana da ba Baba, momy ta maka girma amman zamu iya zama yayanka mu duka biyu"

Yayi murmushi ya shafa bayanta a haka ta sake yin bachi sai ya kwantar da ita ya fito falon, ya dauki wayarsa ya kira Mama Baraka, sai dai bata daga kiran nasa ba har ya yanke, aje wayar yayi a tunaninsa ta yi bachi domin tara da rabi har ta gota, yana dauke hannunsa daga mazaunin wayar sai ga kiranta ya biyo baya, sai ya sake dauka ya amsa, tare da sallama ta amsa masa suka gaisa sannan ta tambaye shi.

"Aliyu me yake faruwa tsakaninka da matarka?"

"Mama Me ta fada muku"

"Bata fada mana komai ba, an yi anyi da ita ta ki ta yi magana ba, sai kuka da damuwa abinci ma bata iya ci, gaba daya ta fita hayyacinta"

Yayi shiru na dan lokaci tare da tunanin alfanu da kuma rashin sa da zai haifar idan har ya fadi dalilin da ya saka ya turata gida, ba dan Ummynsa ba da babu abun da zai hana ya fadawa kowa abun da ta yi masa ko dan ta shiga taitaiyinta ta hankalta.

"Babu komai Mama"

"Aa mu fa iyayene, babu komai zaka turo ta gida ko sakinta ka yi?"

"Aa"

"Toh me ke faruwa tsakaninku? Aliyu ita rayuwar aure sai da hakuri na san ka yi ne, amman ka kara, na san idan ba kai ba ne ba zaka iya zama da Kameela ba, sai dai bana son kana duba sherinta ka rika duba alherinta ko dan ku bawa marasa da kunya, kaga yanzu dawowar da ta yi nan iyayen sun nuna babu ruwansu da ita yan'uwa kuma sai dariya suke mata, dan Allah ina rokon alfarma Aliyu ba dan na isa ba, sai dan na san ka da biyayya da kawar da ido da kuma hakuri da tunani, dan Allah ka yi hakuri ka zo ko kuma ka aiko daukar maka matarka ka bata hakuri ka bawa iyayenta, ku shirya tsakaninku"

Ya sauke ajiyar zuciya.

"Shikenan zan yi tunani Mama"

"Aa ba tunani nake son ka yi ba, idan ka tsaya tunani ai sai shedan ya samu damar baka wata gugurwar shawara, domin shi kullum burinsa ya lalata rayuwar aure, dan Allah ya shirya cikin weekend din nan ka zo ka dauki matarka, gobe friday zuwa assabar ko lahadi sai ka shigo ka koma, ka turo min number Mahaifiyarka na kira ita ma na bata hakuri"

"Aa ba sai kin kira ba, bata ma san abun da ya faru tsakaninmu ba"

"Tohm ai haka ake so, ana son ma'aurata su zama masu sirri, Allah ya hada kanku ya baka hakuri da wuyan dauka, kuma maganar nan ta tsaya daga ni sai kai dan Allah, domin Kameela da iyayenta ba su san na kira ba, ni ce kawai na damu da halin data shiga shiyasa na kiraka mu yi magana, number ka ma a boye nasa yara suka dauko min, ba tare da sanin Kameela ko iyayenta ba"

"Na gode Mama"

"Toh Allah ya maka albarka, kuma ka kara hakuri domin matarka tana kaunarka sosai"

"In Shaa Allahu"

"Na gode"

Ya sauke wayar, ya amsa mata ne kawai saboda yana jin nauyin ce mata aa ba zai iya ba, haka kuma yana tsoron matsalar da fadin gaskiyar abun da Kameela ta yi masa zai janyo, ita yake tausayi ba kansa ba, domin ya san tana son shi, kuma ya san irin gwagwarmayar da suka sha kamin aure, kana ya san idan har aka ji abun da ta yi abu ne mai wahala wani namiji ya sake aurenta, shi kansa ya san auren Kameela jarabawa ne a gurinsa ba dan baya kaunarta ba sai dan zafin kishinta da kuma halin da take kokarin jefashi kuma ta jefa kanta.

EMILY POV.

Bata farka ba sai karfe takwas na safe, saboda tunani da kuma dukan da Vito yayi mata be barta ta sami bachi da wuri ba, daker ta iya saukowa daga kan gado saboda tsamin da jikinta yayi ko'ina ciwo yake mata. Bathroom ta fara shiga ta wanke bakinta ta yi wanka da ruwa mai zafi sosai saboda ta gasa jikin sannan ta fito daure da tawul, rass gabanta ya yanke ya fadi ganin Vito tsaye a dakin yana jiran fitowarta. Tsayawa ta yi cak a jikin kofar bata karasa fita ba kuma bata koma ciki ba sai kallonsa take.

"Good Morning"

Ya tako zuwa inda take sai ta yi baya baya zata koma ciki, ta bata fuska sosai alamar zata yi kuka.

"Tsorona kike ji? I'm so sorry i didn't mean to hurt you ke kika janyo, jiya ban yi bachi ba saboda tunanin abun da na yi miki"

Ya karasa ya rikota ya fito da ita sai ya rumgume ta a kirjinsa.

"I'm sorry"

Sun dade a haka kamin ta dago daga jikinsa ta nufi kujera ta zauna.

"Jikinki da zafi zan kira Likita ya zo ya duba ki"

"Bana bukata"

"I'm sorry Emily am sorry"

Ya karasa kusa da ita sai ya zauna a kasa ya kama hannunta ya rike.

"I'm really sorry, zuciya ce ta rufe ni"

"Wannan ba shi ne karon farko ba"

"Na sani, kuma ba zai zama karon karshe ba matukar baki daina kula wasu mazan ba, kuma baki cire ranki akan addinin nan ba"

Ta fisge hannunta daga rikon da yayi mata ta mika tsaye, short gown ta dauko ta saka ta daure kanta da ribbon tana kokarin juyowa ta ji shi bayanta tsaye.

"I'm sorry Emily I'm sorry, i didn't mean to hurt you"

Ya juyo da ita yana kallon fuskarta dake zubar da hawaye.

"But you already hurt me, baka da banbanci da Khaleefa shi ma dukana yake, Turhan ma ya dukene, kowanenku yana juyani ne son ransa, idan kuka gaji da ni sai ku watsar, ina ta fadawa hannun mutanenda babu komai a gabansu sai son zuciya, na tabbatar da ace ni kanwarka ce, ba zaka yarda wani yayi mata wannan dukan ba, jiya ban iya bachi da wuri ba saboda radadin dukan da ka yi min, takamarka kawai saboda ina karkashinka ne, saboda kana ganin ba ni da kowa, da ace ina da gata ba zaka min wannan dukan ba Vito"

Ta wuce shi ta fice daga dakin, zaunawa yayi a kujerar data tashi dazun ya dafe kansa, babu abun da ya tsana kamar ganin hawayen Emily, a yau da ace wani ne yayi mata abun da yayi ba zai kwana duniya ba, but still yana jin babu dadi meyasa ba shi da hakuri why yake da saurin hannu? Yana son Emily yana mutuwar sonta yana kishinta wannan ne abun ne ya ci shi da yaki ya gagara fin karfin zuciyarsa har gobe...

Tana fita dakin ta nufi downstairs, sai kuma ta fasa sauka ta dawo saman ta nufi dakin London ta shiga, saboda tana bukatar gurin da zata kebe ta tausayawa kanta.
Sai dai kuma shiga dakin ya dawo mata da tunanin danta da kewarsa, dakin yana nan yadda ya bar shi babu abun da aka cire ko aka sauya, sai datti da yayi domin Chidimma ta daina share dakin. Kwalliyar dakin ta fara kallo sannan ta sauke idonta gurin hotonsa ta karasa gurin gadon ta zauna a kasa ta dora kanta akan gadon tana hawaye.

Can kuma ta dago tana kallon study table dinsa dake gefe daya, ta tashi ta koma kan teburin ta zauna saman kujera tana duba takardun da yake zane da su da rubutu, wani gurin ya zana ta ya zana kansa da Vito da Fatima da Chidimma ya rubuta sunan kowa, ta kai hannu tana shafa zanen, ta bude wasu takardu ta dauko tana dubawa, wani gurin ya rubuta, na yi fushi wani gurin ya rubuta i hate Momy, wani gurin ya rubuta I'm sick har ta kai gurin da ya rubuta.

"Chidimma tace Momy bata so na, bata so na bata so na bata so na, tana son Fatima Fatima bata son London, Chidimma tace Momy bata son London, Momy bata son London Momy ta tsani London"

Tana karantawa hawaye na sauko mata kamar ruwa, ta girgiza kai da sauri.

"Ina son ka dana, ka fi soyuwa a raina fiye da Fatima, baka fahimce ni ba ne"

Ta kwala wani uban ihu cikin kuka, ta mike tsaye da fito dakin da gudu kamin ta sauka kasa Vito ya fito dakinta ya biyo bayanta Chidimma dake mopping ma ta tsaya tana kallon Emily dake saukowa tana kuka rike da takardun.

"Meyasa kika saka dana ya tsane ne? Me na miki? Me yasa kika tsane ni? Me na miki? Kin sa Wana ya mutu da tunanin bana son shi, baki kalli lalurar da take tare da shi me yasa kika cusa wannan a kwakwalwarshi? Yanzu ta ina zan fada masa ina kaunarsa? Ta ina zan nuna masa kaunar da nake masa? Why Chidimma why? Shiyasa ya daina son na rabe shi na baya yarda da ni sai ke? Why Chidimma why?"

Kalaman Emily ba su daga mata hankali ba kamar kallon da Vito yake mata.

" Ki amsa me yasa kika yi?"

Ta girgiza kai jikinta na rawa numfashinta na gargada.

"Ba haka ba ne, wata kila be fahimta ba shiyasa yake rubuta wannan, amman ban fada masa cewar baki kaunarsa ba, ba gaskiya ba ne"

"Meyasa Matata tsone miki ido? Na sha fada miki ki daina fada min idan Emily ta yi wani abu, kamar jiya, ke kika fada min ta shirya ta shirya Fatima cikin abaya sun fita, kika sa na zo na mata duka da ya tsaya min a rai yanzu yana ci na, kuma na gargade ki ba tun yau ba akan ki cire idonki akan Emily, the more kika fada min laifinta the more zan tsane ki, me yasa kika shiga tsakaninta da London why? Answer me....!!!

Da farko cikin natsuwa ya fara magana da mugun kallo, daga karshe kuma ya karasa da tsawar da ta saka Chidimma sakin fitsari...








Hmmmmmm, masu karatu wai ba ku ganin Aliyu yana wuce gona da iri ne?
Ina Team Vito? Ni fa iya wuya muna tare>?p?>?z? wanda ya so ka taimaka a lokacin da baka da komai ai shi ne naka.


_______________________

Sannu  yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe Winki da kaya masu kyau, masu ?ima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau?in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taSawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet Winmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau?i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ?ayatarwa duk a farashi mai sau?i.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sau?in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ?ima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki WanWani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haWuwa.
[6/22, 6:33/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


*

*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?



FOLLOW ME ON =?G?
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08



Page 3?? 8??


Cikin karfi hali da kashe murya ta fara magana tana kuka.

"Shekara cikin ta shida nake a gidan nan, idan ina nufin cutar da Emily ko yaranta zan yi tun kamin a kawo yanzu, a janye maganar London tun da shi ba shi da lafiya, amman Fatima tana da wayo tana da fitina, da a ce ina musu wani abun cutarwa da yanzu ta fada, ko kuma ta ki ni, bata kila London be fahimce ni ba ne, shiyasa ya rubuta abun da ya rubuta, amman ni miye ribata idan na rabaki da dank? Idan baki gode min a tsawon shekarun nan ba, toh be kamata ki tuhume ni da wani abun ba"

Ta juya gurin Vito.

"Ka gafarce ni, ina saka kaina aikin da ba nawa ba, amman ni ina tayaka yaki ne kawai, tun da ka kawo ni a gidan matsayin yar aiki, ma lura kuma duk wanda ya kalli yadda kake nunawa Emily gata ya san kana sonta, hakan yana min dadi, ina sha'awar mace ta samu kulawa a gurin wanda take so kamar uba ko miji ko dan'uwa, domin ni nawa uban be dauke ni a matsayin ya ba, na kan fada maka Emily ta kula wani ne saboda taya ka yakin da baka san ranar cin nasararsa ba, na kan zauna na yi tunani yadda ka yi ma Emily gata ita da yaranta ka nuna mata so da kauna fiye da kowa a duniyar nan, amman ko na rana daya bata taba duba wannan ba, har takan bawa wasu mazan damarda za su iya sonta, bayan kuma kai ka cancanci zama a zuciyarta, na kan fada maka ne saboda ayi ma tukkar hanci, amman son da kake yi ma Emily ya hanaka fahimtata, a yanzu kuma kuna zargina da abun da ban aikata ba, kar idonka ya rufe, ka tsaya ka yi tunani gudun yanke hukunci a ciki fushi domin komai daren dadewa sai ka fahimci dalili kuma ka yi nadamar abun da zaka yi min a yanzu, London ba shi da lafiya ba mamaki lokacin da ya rubuta hakan ba a cikin hayyacinsw yake ba"

Duk wani yanayi da muryar da Chidimma ta san zata iya amfani da ita ta siye zuciyar Vito daga yi mata hukunci a cikin fushi sai da ta yi, kuma ta yi nasara domin kuzarinsa na son yanke mata hukunci mai tsauri ya karaya, maganganunta suka shige shi. Emily ta turata ta karfi.

"Are you saying all this saboda kina son Vito? Ko kuma saboda ki kawar da laifin da kika aikata?"

"Ban aikata ba, idan ma na aikata har kake kokarin kawar da laifin shim bancanci ki taya ni ba? Tsawon shekara biyar da na yi ina kula da yaranki ban cancanci godiya ba? Ko kuma dai ke haka halinki yake? Butulu ce ke? Shiyasa shi kansa Oga Vito kika duba halaccinsa ki kaunace shi ko da na kwana daya ne? Ya so ki kamar zai mutu, ya so yayanki kamar nasa, ko matar governor ba zata nuna miki gata ba, amman duk baki gani ba, ni kuma na bauta miki babu dare ba rana, ni nake kula da yaranki, ni nake girka musu abinci na gyara gidan, na karanta musu storybook ko wane dare, idan ba su da Lafiya ni da ke muke jinyarsu, ki kaddara ma na aikata abun da London ya rubuta shin ban cancanci yafiya ba?"

Cikin daga muryar da ya fi kama da tsawa take maganar tana nuna kanta sai kuka take sosai. Emily ta kai hannu zata mareta Vito yayi karaf ya rike, Emily ta kalleshi da sauri tana mamaki.

"She's right, shekara biyar ba kwana biyar ba ne, ta bauta miki, ni kuma na so ki fiye da komai da kowa a duniyar nan, ita baki gode mata ba, ni kuma baki ba ni abun da nake so ba, akanki na kusa haukacewa, akanki bana ji bana gani na kyautata miki iyakar kyautatawa, na baki gatan da babu wanda ya taba baki, a tsawon lokacin nan bana son bacin ranki, ban taba cilasta miki kwanciya guri daya dake ba jira nake har sai kin amince da kanki, fada min bayan ni ba zai iya miki? Babu mahaifiyata bata fada min ba akanki amman ban saurareta ba, babu iya cin fuskar da yarki Lisa bata min amman na daure saboda ina sonki, na kashe kudi mai yawa akan maganin danki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login