Showing 57001 words to 60000 words out of 253142 words

Chapter 20 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18425

mai nade da sarkar cross sai aka fara yayyafi, kowa ya fara gudu an fakewa a wani gurin domin ruwan ya sauka da karfi, ni kam tafiyata na ke da dai daya ina daga kaina sama ruwan yana saukarka min a fuska da kai. Hango bakin shagon wani mutume dake road din mu babu kowa a gurin yasa naje gurin a guje na aje ledar hannuna na fito tsakiyar titi da babu motoci na tsaya ina waka da ruwan saman ina juyawa ina rawata domin babu abunda ya dame ni.
Shakaf ka jike a guri a gurin idan na hango mota tafe sai na koma gurin shagon a guje na fake ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dugun kar a min daukar mahaukaciya sai motar ta wuce sannan na fito na cigaba haka nai ta yi har aka gama ruwan a kaina. Sannan naje na zauna bakin teburin mutumen na saka hannuna a aljihu na ciro yar karamar wukar da babu wanda yasan ina yawo da ita na dauki lemu daya na yanka na sha.
Sai da naji na koshi da kayan marmarin sannan na faki idon mutane na maida wukar ajihuna, na dauki ragowar kayan marmarin na kamo hanyar gidan marayu wanda zan iya kiransa da gidanmu ko kuma na ce gidana. Kamar dai dazun yanzu ma sai da muka gaisa da mai gadin gurin har yake min sannu da jikewar da yai sannan na wuce sashenmu wato block C. Rossy na ganina ta rugo da gudu ta tare ni, daman ta saba min haka ita ba ma ita kadai ba har da sauran an block din, domin ni mutuniyar kowa ce komai nawa na kowa ne, idan na samu bana iya ci nidai ko da basu san da shi ba.

"Ku aab? pada. arabinrin mi"

Ta min sannu da zuwa da yaren yarbancin tana kokarin karbar ledar hannuna. Sakar mata ledar nai ina murmushi na ce.

"Kije ku raba tare da du Elina"

"Wow wato oga shakur yayi miki sallama ta kwarai kenan nan yau"

Da yaren yarbancin muka yi maganar ni dai murmushi kawai nai na kama hanyar dakinmu, daman na san kowa zai dauka cewar kyautar oga Abdulshakur ce, domin ya saba min irin wannan sallamar idan rana tai hi kyau. Oga Abdulshakur wani oganane a gurin aikin gyara mota, shi yake da gurin a gurinsa nake zuwa ina koya duk kuwa da kasancewarsa musulmi, na fara aikin ne a lokacin dana kare makarantan kuma ban samu damar shiga babba ba, an rubuta takarda zuwa ga gabnatin Lagos domin daukar nauyin karatun mu zuwa mataki na gaba mu yan wannan shakarar da muka gama, amman har yanzu babu wani abu da ya fito daga can, wata kila dan aikin har yanzu be kai ba, ko kuma ta manta da sha'aninmu ne.
Ni kuma bana son zaman banza ba aiki, bayan kuma shugaban gidan marayu ya bawa kowa damar mai son aiki ko sana'a yayi domin tallafawa kansa.
Ko da na shiga dakinmu babu kowa sai Nine ackor ita kadai a gafenta tana bachi, dakinmu babban daki ne mai daukar mutum takwas kamar sauran dakunan, an kawata dakin da kananan gadaje na kwanan mutum daya da yar karamar waduruf ta saka tufafi. Gadona kusa da window yake hakan kuma na min dadi duk kuwa da kasancewar wani lokacin ina jin tsoro. Tufafin jikina na fara cirewa na canja zuwa wata yar karamar gown, sannan na dauki wukata na saka a cikin jakata inda na saba ajeta, gado na hau na kwanta fuskata da murmushi mutum dazun ne har yanzu na kasa daina ganinsa a idona, yana da kyau sosai kamar wani aljani gashi fari ni kuma ina son fararen mutune duk kuwa da kasancewata fara.

'Musulmi ne fa!'

Zuciyata ta fada min, miyasa zan yi tunanin musulmi bayan a coci ana yawan fada mana cewar musulmi yan ta'adda ne kuma basa son kistoti irina, a take gabana ya fadi sai na ji kamar nayi wani sabo, take nai saurin praising Jesus na roki gafarsa, nai saurin tasowa na baro dakin gudun kar tunanin ya sake dawo min na samu zunubi.

Haka muka raya yammacin ranar da laraba tare da yan'uwana marayu, sai da dare yai sai na nufi gurin dana saba zama na zauna karkashin wata bushiyar lemu na jingina jikina ina kallon sama, yadda taurarin suka jera abun ya burgeni sosai, sun yi ma sama ado sai sheki suke, kirgasu na fara yi da yatsana duk kuwa da kasancewar na san ba zan taba iya kirgesu su duka ba, wata maganar taurari ce dake cikin Bible ta fada min a rai.

"Sa'an nan sarki Yosiya ya umarci Hilkiya, babban firist, da firistoci masu daraja ta biyu, da masu tsaron ?ofa, su fitar da tasoshin da aka yi wa Ba'al, da Ashtoret, da dukan taurarin sama, daga cikin Haikalin Ubangiji. Sai ya ?one su a bayan Urushalima a saurar Kidron, sa'an nan ya kwashe tokarsu zuwa Betel"

Murmushi nai ina mamakin yadda wani zai iya kona taurarin nan na samaniya har ya kwashe tokarsu. Wani lokacin bana son zufafa bincike akan addini na amman ina ganin kamar akwai gyara a litattafin bible domin kuwa wasu kalaman ko nace surorin da suke ciki sai kaji kamar abun ba zai yiyu ba wani abun ma nakanji kamar labari ne irin na shaci fadi.

"Kina nan kina aikin kallon taurari ko?"

Maganar marry ce tasa na dawo da dubana izuwa gareta, kokarin zama take kusa da ni.

"Wata rana za ki zauna tare da mijinki ku kirga taurari"

Na kalleta

"Marry kina da ban dariya"

"Miyasa na ke baki dariya idan nai maganar miji? Baki taba daukar hakan da gaske ba"

Shiru nai kamin na ce mata.

"Ina ganin wani abun kamar ba zai faru ba, akwai wadanda suka girmemu a nan gidan kuma suna nan basu yi aure ba balle kuma ni da ke, balle ma ba zamu auri mutumen da zai ga girman mu saboda ba mu da iyaye"

"Wata kila ke din kina da iyaye Emily, ina ji a raina kamar muna da iyaye yawancin mu da muke gidan marayu muna rayuwa kawai a matsayin marayu, amman wasu iyayensu sun yi cikinsu ne sun jefar da su"

"Indai har haka iyayena suka min bana kaunar ganinsu, domin sune silar shigata wannan hali"

"Idan kuma iyayenki suna tsoron ki wahala ne suka kawo ki nan fa? Ko kuma wani ne ya sace ki ya kawo ki nan?"

"Zan iya yafe musu idan wani ne ya kawo ni nan, zan yafe musu amman talauci ba hujja bace komai talaucinsu kara su yi hakuri da ni a haka mu zauna a haka, tun da suka kasa hakurin zama da ni ba zan yafe musu ba"

Na fada idanuwa na cika da kwalla, sai ta saka hannunta ta lakamoni.

"Zaki yafe mata Emily, lokacin da mijinki zai risina a gabanki ya roka mata yafiyarki ba kisan lokacin da za ki yafe ba"

"Ba zan iya yafewa ba marry, i just can't"

Dariya tai jin yadda nai maganar ina son yin kuka. Mun dade zaune a gurin sannan muka tashi muka shiga block din mu ta nufi dakinta ni ma na nufi namu. Babu wuta a dakin amman an kunna hitila kamar yadda aka saba idan ba wutar, ban kula kowa ba dukuwa da irin wasan da abokina na dakin ke jana da ita, ganin bana cikin yanayin wasan yasa suka kyaleni na hau gado na kwanta wata kofar tunanin ta bude min.

'Suwaye iyayena? Yarbawa ne, igbo ne ko ibra ko hausawa? Ban sani ba, wane addini suke? Miyasa suka jefar da ni? Basa sona ko wani dalilin ne na dabam?'

Da wannan tunanin nai bachi kuma har gari ya waye ban samu amsar tambayoyina ba. Ban farka da wuri ba kasancewar ban yi bachi da wuri ba, shiga nai bandakin mu dake can kusa da kofar shigowa dakin nai fitsari ba tare da tsarki ba na wanke bakina kuma nai wanka sannan na fito. Mai kawai na shafa, ni ma ina da kyau kamar mutumen jiya duk kuwa da kasancewarsa namiji.
Karamin wandon jean na saka wanda iyakar tsayinsa guiwa na saka wata t-shirt black na dauko kofina na jika gari na sha domin an san by this time an gama raba abincin safe kuma wanda be je ya karbo ba ba za a aje masa ba indai ba wani ne ya karbo masa ba. Bayan na gama sha na rufe waduruf din na saka wukata a aljihu tare da makullin lokar na dauki jacket dita na daura a kwankwaso na sannan na fito zuwa gurin gyaran mota wato gurin aikina.
Nayi ta sauri a hanya ganin na yi latti ba kasafai nake son oga na rigana zuwa gurin ba, naje latti sai dai duk da haka oga Abdulshakur be fito ba wata kila wani abun ya tsayar da shi a gida ko wani gurin, rigar aikin na dauka na dora saman tufafina na soma gyara gurin sannan fito da kayan aikin a waje, na kusan awa biyu a gurin sannan ya iso. Cikin girmamawa na gaishe shi ya amsa min da far'a kamar kullum, sannan ya shiga aikin gyara motocin da ke gurin a lokacin ne mutane suka fara zuwa ciki kuwa har da yaran da muke aikin tare da su yan gareji. Ni nake tsaye kusa da shi ina aikin miko masa abubuwan bukata kamin ya bani list din abubuwan da zan je na siyo a kasuwar da ake siyar da jarafuna a unguwar Orile Iganmu a nan lagos. Zuwa nai dakin dake garejen na cire rigar aikin na dawo ya bani kudi na saka a aljihu sannan na kama hanya. Ba mu da nisa sosai da unguwar dan tafiyar bata wuce ta awa daya da rabi ba, so i decided naje a kafa na rike kudin babur din ko wani abu zan iya siya da su. Na tafiyar minti arba'in kamin na kama hanyar da ke kusa da kasuwar, hanyar kamar unguwarmu take babu mutane sosai duk kuwa da kasancewar da rana ne. Gungun wasu mutane na hango za su kai mutum hudu zuwa biyar a tsaye gefen titin, ban ji tsoron ganin mutanen masu kama da yan ta'adda ba domin na saba ganin irinsu da ma wadanda suk fisu a lagos. Ban lura da abunda suke da niyar aikatawa ba har sai da na isa kusa da su, mutumem jiya ne suke kokarin karbewa mashin suna masa barazana da katuwar wukar da ke hannunsa.

"Bamu makulli"

Dayan ya fada da yaren turanci ni kuma na katsa masa tsawa da yaren yarbancin ganin zagen fuskarsa da yana nuna cewar shi bayarabe ne.

"Ba zai bayar ba, ku kananen yan iskane da kuke yawo da wuka, kuma duk wanda ya kuskura ya taba shi ai cikinku sai nasa an kasheshi ba kune yan apapa ba?"

Duk tsayawa sukai cirkocirko suna kallona yadda nai musu barazanar yasa sun dan tsorota, ban san su ban san yan ina ba ne amman yawacin yan iskan lagos apapa suke, sun dauka a yadda nai musu kamar na sansu ne ko kuma ina da wani mai tsaya min ne.

"Wacece ke?"

Dayan ya tambaya da yaren yarbancin kamar yadda nai masa magana dazu.

"Idan kun taba ni zaku san ko wacece ni"

Na fada ina zaro wukar dake cikin aljihuna na nuna musu ina yatsine fuska kamar yar ta'addar gaske.

"Ku wuce daga nan"

Kamar umarnina suke jira suka kama hanya suka kyaleshi suna ta waigena. Sai da suka wuce sannan ya kalleshi na ce

"Kai sakarene zaka tsaya haka a kwace maka babur?"

"Kamar ke ce yarinyar da kika taimake ni jiya"

Ya fada cike da mamaki yana nuna ni.

"Yes kuma yau ma na taimakeka ba, dan ka zama dolo"

Murmushi yai.

"No ina tsorone amman kin san su ne?"

"Ai a lagos ba dole sai ka san kowa ba, as long as kasan sana'ar mutun barazana kawai zaka masa, idan har kace kyalewa zaka yi kowa zai cuce ka ne, shiyasa na ke yawo da wukata"

Na fada ina maida wukar aljihuna sannan na kama hanya tafiya kasuwa ta ba tare da na jira abunda zai ce min ba.

"Na gode Emily"

Ya fada sai na juyo na kalleshi ina murmushi.

"Baka manta sunana ba?"

"Taya zan manta sunan Jaruma"

Ya fada da dariya nima dariyar nai na cigaba da tafiyata.



_________________________

Want more?
*Comment*

*Share*

*Follow* my channel https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01
[4/29, 6:17/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??:

*? Khadeeja Candy*


SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 9??


Tun daga wacan ranar ban saka ganinsa ba, amman ban manta sunanansa ba, ban manta kyaun fuskarta domin Khaleefa yana da kyau sosai kwatankwacin yadda mutane suke baya kyauna. Kusan zan iya cewa kyaun ne abun da ya ja hankalina izuwa gareshi.
Na cigaba da rayuwata ta yau da kullum kamar yadda na saba a gidanmu na marayu, da safe zan tafi makaranta da yamma kuma na leka gurin aikina na gyaran mota wato garejen oga Shakur, idan aka samu aiki yayi kyau ko kuma muka samu customers da yawa a ranar yana min alheri kamar yadda ya saba.

Kasancewar yau assabar na tafi aikin tun safe ban tashi ba sai yamma, da zai sallame ni yayi min sallama mai kyau, ba karamin faranta min rai yayi ba hakan ya kara min karfin guiwar tafiya gida, na yi wanka na shirya na fito domin kashe kudin da aka bani, domin abu ne da kowa ya shaideni da shi alheri hali na, idan na samu kudin na kan sawo abubuwan dadi na kawo, kowa ya saka hannu ya ci, ban san na ci ni kadai ba. Na isa gurin na gaisa da shi da yaren igbo na ba shi kudi nace ya hada min kayan marmari, a nan yake fadan min domin da na taimakawa yayi siyayya ranar nan kullum sai ya zo nemana. Da mamaki na tambaye shi.

"Nema na? Me zan masa?"

Yayi murmushi ya koma cikin karamin shagonsa ya dauko farar takardar ya miko min.

"Number ce ya rubuta yace idan kika zo a baki, duk da haka kuma yana zuwa kullum da zaki iya jiran shi anjima kadan zaki ga ya zo"

"Amman yace na yi masa laifi?"

"Alamu be nuna hakan ba"

Ya miko min ladar na karba, har zan tafi sai kuma wata zuciyar ta ba ni shawarar na tsaya na jira shi mana idan ma wani abun ne ai zan ji. Haka kuwa na aikata na zauna a gurin muna ta hira da Mutumen sai ga shi ya iso da babur dinsa kamar wacan karon.
Tun kan ya sauko daga kan babur din fuskarsa ta washe da murmushi, ya karaso kusa da inda muke zaune yayi min sallama, na amsa masa kamar musulmai, sai ya washe hakora.

"Garkiwata kamar dai kin fini iya hausa"

Na yi murmushi zuciyata na bugawa da wani irin karfi, irin bugun da bata saba yi ba.

"Kana ta nemana aka ce, amman dai ba laifi na yi ba ko?"

"Laifi kika yi babba kuwa"

Ya fada yana dagawa igbon hannu tare da mika masa 2k.

"Laifin me"

"Kin san kin taimake ni a nan haduwar farko, haduwa ta biyu kuma kin ceto rayuwata kin ceto abun hawana kuma abun sanata, tun daga lokacin zuciyata bata barni na zauna laifi ba, na yi bata hakuri har na gaji amman bata bar ni ba, wata kila saboda ba ni da kowa a garin lagos ne, wata kila kuma saboda taimakon da kika yi min ne, ko kuma dai saboda kina marainiya ne amman dai kin tsaya min a rai kuma kin ba ni tausayi sosai"

"Baka da kowa a nan"

Na tambaya da mamaki fuskarsa na cika ni da kwarjini, ba dai kyaun ba kam Khaleepa akwai kyau kamar dan indiawa.

"Ba ni da kowa, kawai na biyo abokina ne da yake achaba a Lagos saboda ance yafi arewa samun kudi, sai na zo ni ma nake yin achaba, ban san kowa ba sai ke sai abokin nan nawa, sai kuma mutumen igbo"

"Interesting"

Na furta not knowing what to say next, yayi tagumi yana kallona.

"Ashe dai zan sake ganinki, na ji kamar na yi hauka, kullum sai na zo nan neman kyakkyawar fuskar nan"

"Amman ya kan yi ka iya magana da igbo nan bayan baka jin yarensa"

"Wani na samu yake rubuta min duk abun da nake so na tambaye shi idan na zo, sai shi ma ya rubuta min idan na tafi gurin wacan sai a fassara min"

Na yi murmushi ina yaba karfin halinsa, amman fa ya burge ni, neman ganina kawai zai saka shi wannan hidimar.

"Ni zan tafi"

"Haba ban gama kallonki ba fa, kuma kin san yaushe nake bata lokaci ina zuwa nan nemanki"

"Idan na dade ban dawo ba kawaye za su neme ni, kuma ba a son muna fita muna dadewa a waje ba tare da wani dalili ba"

"Shikenan muje na rakanki, akwai abubuwa da yawa da nake son sani akanki, kamar yadda aka yi kike jin hausa, kuma kike da kirki da kulawa, kuma gashi kina da kamun kai, dan na yi mamakin yadda na baki kudi baki karba ba, kuma gaki kyakkyawa"

Duk yadda na so na tafi ni kadai be yarda ba sai da ya goyani da babur dinsa ya kai ni kusa da gidanmu na marayu, a boye na sauka domin bana son kowa ya gan ni, idan aka gani ma za'ayi min fada. Ya sake rubuta number shi ya ba ni ya bani kudi a nan din ma ban karba ba, be tafi ba sai da na masa alkawarin zan kira shi mu gaisa da wata wayar.
A ranar kasa cin abincin dare na yi, na gagara cin kayan marmarin da na siyo sai tunaninsa nake, a wacan lokacin akwai kurciya sosai a tare da ni, domin ina da shekara goma sha biyar ne, a lokacin ina sss1, gashi kuma wani be taba nuna min kulawa kamar yadda shi ya nuna min ba, ina da kyau wannan abu ne da ni kaina na sani, amman kyaun nawa be taba sakawa wani be taba nuna min kulawa mai kama da soyayya kamar shi ba, sai dai mutane su na haba haba da ni, wata kila suna gani ko tunanin ni na yi karama ne.
Abu kamar wasa muka fara shakuwa da juna, da wayar mai dafa mana abinci a gidan nake amfani ina kiransa mu gaisa, wani lokacin har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login