Showing 204001 words to 207000 words out of 253142 words

Chapter 69 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18444

miyasa idonki ya rufe har haka ne? Mu fa iyaline be kamata kina haka ba, ki yi hakuri da duk abubuwan da suka faru na san ban kyauta ba ina neman afuwarki ki yafe min dan Allah, Wallahi na yi nadama, kuma na yi bakinciki abubuwa na da na yi miki, ina neman afuwa, kuma na miki alkawari hakan ba zai sake faruwa ba"

Ya bata fuska sosai kamar zai mata kuka.

"Na yafe Turhan, that's okay zaka iya tafiya ka yi rayuwarka"

Ya kalleta da sauri domin be yi tsammanin zata yafe masa haka da sauri ba.

"Kin yafe min Emily? Zaki koma zama da ni kenan?"

"I forgive, never forget ba za mu sake zaman aure ba Turhan, na kasa manta abubuwan da ka yi min, ka fada min ba zaka taba kaunata ba wannan ya zauna a kaina"

"Baki yafe min ba kenan, indai kin yafe min to zaki yarda ki zauna da ni ne Aisha, Fatima ma zata yi farinciki, idan har baki yarda kin aureni ba zan shiga mummuna hali Aisha, Wallahi ba ina fada miki haka saboda kan karya ba ne, har cikin raina ina kaunarki Aisha, kuma ina son zama da ke, idan kika guje min ban san iya halin da zan shiga ba, Wallahi ba dan ke ba, ba zan taba tako kafata a cikin gidan nan ba, ni yanzu damuwata ki amince da ni ban damu ko kina so na ko baki so na ba! Zan iya zama da ke a kowane hali, Aisha karki ba ni kunya a gaban makiya dan Allah, don't break my heart please"

"You broke me first.... Shin baka yi tunanin ya abun yake da zafi ba? Ni ma a yanzu ban damu da duk wani zafi da zaka ji ba, ka tafi ni dai na yafe maka amman zama a tsakaninmu ya kare"

Ya lumshe ido ya rasa ina zai saka kansa ya zai yi Emily ta fahimceshi. Emily ta wuce shi ta fice daga gurin, tana shiga falon ta samu Ammy zaune ita kadai a falon Fatima na saman jikinta, kallo daya Ammy ta yi mata ta san Wanta be samu nasara ba.

"Momy nace dady ya dawo nan mu zauna tare gaba daya, ya fi dadi kina nan Ammy ma ta zo ga Uncle Aliyu ga Dady ko?"

Emily ta girgiza mata kai.

"Aa Dady zai zauna gurin Ammy, idan kina so zaki je ki gan shi"

Sannan ta kalli Ammy ta ce.

"Ammy na gode da ziyara, zan haura sama"

Ta nufi stairs, Ammy ta bita da kallo har ta haura sannan ta sauke fatima a jikinta ta kama hannunta.

"Fatima muje ko?"

"Aa ki tafi sai gobe zan zo"

"Baki son gurin Daddynki?"

"Ina so gobe zan zo tare da Momy"

Ammy ta saki hannunta ta fice rai a bace.


[8/6, 11:10/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *


*?? Khadeeja Candy*



Page 6?? 4??


Ammy ta same shi zaune a motar cikin wani yanayi marar dadi. Bata ce masa uffan ba shi ma be furta komai ba yaja motar suka kama hanya sai da suka isa gida ta bude motar ta fita sai ya ji shi ya kasa fita, yana mamakin yadda Aliyu ya shige masa hanci, haka zai zura ido wani katon banza yana kallon masa mata? Yana jindadin yayi nasara akansa? Miyasa wai tun farko be yarda girmama zabin mahaifiyarsa da yanzu duk be samu wannan matsalar ba. Ya dade a zaune a cikin motar sannan ya fita ya shiga falon ya zauna, Ammy ta kalleshi cikin tausayi da kuma bacin rai ta ce.

"Turhan ka hakura da yarinyar nan, tun da ba mata suka kare duniya ba, ka nemi yafiyarta kuma ka kwatanta kyautata mata Alhamdulillah, a haka ma Allah ya maka albarka, kana da mata ka rike aurenka ka koma a can ka cigaba da harkokinka idan kana bukatar ganin Fatima ka dawo ka ganta"

Turhan yayi shiru na lokaci kamin ya ce.

"Ammy kin cire rai da dawowar Aisha ne?"

"Babu amfanin mu yi ta bibiyarta tana wulakanta mu, sai kace kanta farau wulakancin Wa namiji na ga mazan da suka fika wulakanta matansu kuma matan ne ma suke neman mazan su zauna da su balle kai da har ka gane kuskurenka kuma ka nemi yafiya? Wai yau ni Aisha zata kalli kwayar idona ta fada min bata sonka. Sai binta muka tana da juya mana baya kamar autar mata"

"Aisha fa bata da laifi, laifin Aliyu ne, saboda shi ya fara ganin ta kuma ya shirya mata abun da ba gaskiya ba ya dorata a kai, gashi kuma yanzu tana gidansu su suke kitsa mata komai"

"Idan da su har da ita, ai ba jaririya bace balle ace saka mata magana ake a bakinta"

"Wallahi Ammy Aisha bata da laifi, laifin duk na shegen katon banzan nan ne Aliyu, kuma da yarda Allah sai na ba shi mamaki"

Ammy ta sauke dogon numfashi.

"Da zaka hakura da ita da zai fi, tun farko rashin daukar shawara ne ya jefaka a cikin halin da kake ciki ai, da na aura maka ita miyasa baka rike ta ba ka bi son zuciyarka? Da duk haka bata faru ba kuma da yanzu Allah kadai yasan yara nawa ta haifa maka, yanzu kuma idonta ya bushe bata ganin kowa kai kuma ka dage sai ka zauna da ita, ko zaman kuka yi auren ba zai muku dadi ba saboda bata ganin mutuncinka yanzu bata ganin girmanka"

"Ni ne mai laifin ai na sani, shiyasa yanzu nake kokarin ganin na gyara laifina, ko na yi kamar zan hakura idan na tuna da Aliyu ba zan iya hakura ba Ammy, hankali ba zai kwanta ba sai idan na ga ta yi aure kuma ba shi ta aura ba, shi ma kuma idan ba zata dawo min ba"

"Ai Aliyun ma da wuya ya aureta, kawai dai kai suke son gasawa aya, shi da yake da matarsa ma, dole shiryawa za su yi, idan ka yi hakuri kana nan Aisha zata nemeka, ni na san Ummi ba zata yarda Aliyu ya auri wannan yarinyar ba, ita hauka ce take dibanta"

"Ammy saboda kina mace ne, ba zaki gane ba, Aisha ta kai duk inda mace ta kai babu wanda zai ganta be ji yana sonta ba"

"Tohm sai ka gwada naka kokari, ni dai daga bakin nan na cire hannuna"

Turhan ya ji babu dadi.

"Wani abu Aisha ta fada miki ne Ammy? Kamata yayi ki goya min baya, duba yadda Ummi tana bin bayan danta duk kuwa da cin amanar da yayi, na tabbatar da ni ce ba zaki yarda na dauko Kameela matar Aliyu na aje a nan ba"

"To me zai saka ka yi haka? Ka nemi wata ka aura idan har kana son auren ne"

"Aa Aisha dai, idan ba ita ba..."

Yayi shiru takaici ya saka Ammy tashi ta bar masa falon.

"Aifa sai dai a mutu, amman ba zan taba yarda Aliyu yayi min wannan cin kashin ba, bayan ya gama da ni ya rabi matata Allah kadai ya san abun da ya faru kuma yanzu yace wai zai aureta saboda kawai bakar kiyayya ba tare da na masa komai ba"

Ta juya fuska.

"Ita ma dai wani lokacin da matsalarta da gaskiyar Ammy, ni ban ce ta raga min ba, amman ta daina sake jiki mana da wannan katon kwarton, ji yadda ta kyau dan Allah haka zai sakata gaba yayi ta kallo, macuci"

Ya hade yawu da karfi, ya saka hannunsa yana karawa rigar wuyansa fadi kokarin yagata take, yana jin kamar numfashinsa na danne, bani irin kishin Emily yake ji har na bala'i




EMILY POV.

Misalin karfe 9pm tana zaune falo Ummi na kara mata wasu darussan na rayuwa, Aliyu ya sauko Fatima na janye da hannunsa. Da suka kawo kasa sai Fatima ta sake shi ta nufi Emily ta kama gashinta tana yaryadawa a bayanata.

"Momy Dady yace in dinga rufe miki jiki"

Emily ta juyo ta kalleta, Ummi ta yi murmushi bata ce komai ba, Aliyu kuma ya kalli Emily kadan ya dauke kai.

"Uncle Aliyu yace zai koma gidansa gobe, Momy zaki je? Zamu koma can ne kuma? Miyasa ba zamu zauna gidan Dady ba, Ammy tana sonki da Dady sai mu koma can har Uncle Aliyu ko?"

Ummi ta kalli Aliyu dake gefenta.

"Ina zaka koma"

"Gidana dake nan Ummi, zan fi jindadi, kuma yana da kyau mu kiyaye dokokin ubangiji"

"Hankalina zai fi kwanciya ka zauna a nan, kwantarka ake ne zaka koma can? Ina jin nan da sati biyu ma za mu koma Abuja gaba daya"

"Aa Ummi indai kika ce zaki sama min masu tsoro zan yarda shi ma saboda ki zamu kwanciyar hankali ne, amman Addu'a ta ashe ni, zan koma can In Shaa Allahu"

Emily ma ta kalleshi tana jin babu dadi ganin take kamar idan baya cikin gidan ba zata sake sosai ba, yanayin ya sauya har ta kasa boyewa ta cire gashinta dake hannun Fatima ta mike tsaye ta bar falon.



ONE WEEK...


Ba banza aka bar Aliyu ba, daman fa yarbawa sun iya mugun abu, idan ba haka ba taya Aliyu zai sake ta, daga kawai ta kai yarinya gurin Babanta, gashi har ya fadawa Ummi ta saka guba a abinci, ko Ummi bata nuna mata bata son zuwanta gidan ba ta san ba zata sake aminta da ita ba, gashi yanzu ko zuwa gidan bata son ta yi.

"Kai gaskiya ba banza ba, kalli ko Bakar Barakar nan dan ba zan ce Mama ba ni bata haife ni ba, kamata yayi abbah ya koreta gaba daya daga gidan nan kamar kare, amman be yi ba sai saki daya yayi mata har da cewa wani wai baya son kowa ya fitar da maganar ta yi zaman yayanta, yana nufin zai maida ita kenan, shiyasa take ta shige min tana kiran Aliyu tana wani bani shawarar munafukai, ashe ta san Emily yarta ce shi take hangowa"

Magana take da kanta tana ta safa da marwa tana dora hannu a kai tana saukewa, ita a yanzu babu tashin hankalinta kamar yadda Aliyu ya juya mata baya, sakonta be reply ya bi yayi blocking din number ta ma, Ummi ma bata amsa mata idan ta kira kuma bata maida mata da amsar sako, gashi yanzu Aliyu gida daya suke rayuwa da Emily.

"Wai to shi wannan Turhan din in ban da sakarai ne shi haka zai zuba ido wani ya karbe masa mata? Ayi mutum kamar dusa, wannan bakin ciki ina zan kai shi? Wallahi Aliyu be ma dace da yarinyar nan ba, ga kafirci ga shi bata hanyar aure aka aureta ba"

Ta fashe da kuka ta sauke hannu ta sake dorawa, haka take kowace rana ta saka wannan ta kwance waccan ita kadai domin yan'uwanta babu mai tayata gaba daya ma basa son zancen Aliyu, su sun ji dadin haka daman ba sa son aurenta da Aliyu gashi yanzu an rabu kuma sanadin haka Abbah ta saki Mama Baraka, Hajiya sai shiga da ita take na balmar baka tana son mijinta ya kori Mama Baraka daga gidan gaba daya.

Kuka Kameela ta ci sosai ta rasa ina zata saka kanta, ko ba Emily ba ba zata so Aliyu ya so wata ba balle kuma Emily, mace da ita kadai ce ta hana ta walwala ta kuma rabata da mijinta, kuma sanadinta ta sakawa mijinta guba gashi yanzu shi ne silar komai, ba dan haka ba da duk abubuwan da suka faru ta san Aliyu zai iya yafe mata su zauna domin tana son mijinta, amman yadda Ummi ta dauki zafi ta san zata sha wahala kamin ta samu kanta. Balle kuma Emily tana gidan ta dauke masa hankali da kyaunta ta san ba zai tsaya tunaninta ba, daman tun farko kyaun ne ya dauki hankalinsa ba komai ba.

"Ni ban san ma san miyasa wannan Mama Baraka ta hadu da bature ba har aka haifo wannan yarinyar, kuma abu ya zo ya zama kamar na gida ni na shiga uku, shiyasa na ki ya rabu da ita, ashe ita wannan Mama Barkatar tana nan tana shirya masa soyayyar Emily ni aka maida mahaukaci"

Ta kwanta ta tashi ta rasa ma wane irin tunani zata yi, kuma ta san idan ta yi sake bata hankara ba zata ji an daura musu aure domin ba a banza aka bar mijinta ba, kamar yadda aka yi ma Babansu.
Ta zauna tana ta cizon baki, babu wanda ta fado mata a rai a yanzu kamar Tasmia zuciyarta ta raya mata babu inda zata samu mafita sai a gurinta. Ta janyo wayarta ta duba sai ta tuna bata da number Tasmia ta goge tun a wacan lokacin da suka samu matsala. Sai dai abu mai sauki ta can gidansu, bata da tabbacin zata iya samunta a gidan amman saboda neman mafita ta dauki key din sabuwar motar da Momynta ta siya mata ya fita ba tare da sanin kowa ba ta dauki kafa zuwa gidansu Tasmia.

Ta isa gidan tana ta sake sake kuma tana dan jin kunya da nauyin Tasmia na abun da ya faru tsakaninsu, be ma kamata ace ta je neman taimakon Tasmia ba amman saboda bata da wata mafita sai wannan ya saka ta aje komai a gefe ta faka harabar gidan na masu rufin asibiti bayan mai gadi ya bude mata gate.
Ta rufe motarta ta nufi cikin gidan tana rike da key ta a hannu da green din hijab dinta idan ka ganta ba saka yi zaton zata yi fitina ba.

Ta shiga da sallama a tsakar gidansu Tasmia jikokin da suka nan suka amsa mata suna wasa da ruwa. Su ta tambaya ko tasmiya na ciki suka ce mata tana cik sai ta nufi kofar falon ta shiga da sallama. Suka amsa mata da mamaki domin Tasmia ta fada musu sun samu matsala da Kameela sai dai bata labarta musu gaskiya maganar ba kawai ta ce saboda Kameela tana da zafin kishi ne. Mamasu ta amsa mata da far'a kanen kam sai kallonta suke.

Ta kai har kasa ta gaishe da mamansu sannan ta tambaya Tasmia ko tana ciki, maman ta tambaya ko lafiya ta amsa da babu komai tana dariya. Sai aka nuna mata dakin da Tasmia take, ta nufi dakin ta shiga da sallama tana yaye labule. Ita kanta Tasmia ta yi mamakin ganinta har tana tsoro domin bata san da me ta zo mata ba.

"Yan bautar kasa wato kun gama babu ko labari babu ziyara?"

"Ke da wacce kika zo? Ni da ke fa kai ta san kar ne"

Tasmia ta fada sannan ta tashi zaune da kyau kar a shammace ta. Kameela ta tabe baki.

"Ni da alheri na zo miki, ba sheri ba"

"Koma da wacce kika zo ni daidai nake da ke"

Kameela ta zauna ba tare da an mata tayin zaman ba.

"Ke dan Allah ki bar abin da ya wuce ya wuce mana, ni ma yanzu ina cikin tawa matsalar mafita nake nema shiyasa na rugo a guje na zo gurinki"

Tasmia dai kallonta kawai take.

"Dan Allah ki ba ni aron hankalinki kuma ki natsu sannan kuma ki fahimce ne"

"Ina jinki"

Kameela ta yi shiru na lokaci can kuma sai ta ce.

"Emily ce matsalar, amman ba zan fada miki komai ba sai idan zaki taimaki kanki ki taimake ni"

"Zan taimake ki ba tare da sanin me ya kawo ki? Hajiya ki fada min damuwarki kawai ba wani noke noke"

Kameela ta rage murya ta marairaice ta fara karanta mata damuwarta sannan ta koro da labarin Emily. Tasmia dai sai saurarenta take har ta kai aya. Kameela ta juya makullin motar dake hannunta tana kallon Tasmiya bayan ta gama bata duk labarin Emily da kuma abun da ya faru.

"Tohm yanzu ni miye nawa a ciki? Har kike ba ni wannan labarin?"

"Tasmiya aurena fa ya mutu?"

"Na san aurenki ya mutu mana, abun duniya ai baya boyuwa na ji tun kamin na dawo garin nan kuma yanzu gashi kin kara fada min, dalilin da zai kawo ni cikin matsalar ne ban sani ba"

"So nake ki taimaka min, ni biyanki ne ma zan yi Wallahi, na san da can kina son Aliyu ai ki yi duk yadda zaki iya ki dauke hankalinsa daga gurin kafirar nan, ni da ta aure shi Wallahi gara ke ki aure shi"

Tasmia ta yi dariya

"Wato Kameela kin dauke ni marar hankali marar wayo ko? Ke ce mai wayo? Bayan duk abubuwan da suka faru yanzu ni kike son na zame miki tsanin hawa? Miyasa ke ba zaki yi yakin da kanki ba?"

"ba zaki gane ba ne, gaba daya baya saurare ni yanzu ya juya min baya kamar ba Aliyuna ba, daukar yarinyar da na yi na kaita gurin Turhan har Aliyu ya sake ni ni sai nake ganin kamar ba banza aka bar ni ba, Wallahi idan Aliyu ya auri kafirar nan an gama da ni gaba daya, uwarta ta yi kishi da uwata ni kuma na yi kishi da ita? Da dai ita ta aure shi kara ke"

Tasmia ta tabe baki.

"Ni yanzu ina da wanda zan aura masa Kameela, kuma mijinki mai wuyar sha'ani da shegen wayon tsiya"

"Ai mataki zamu dauka ko ta halin yaya, idan kika ba ni hadin kai ma har acit sai mu watsa mata fuskar ta lalace daman ai kyau ne yake jansa"

Tasmia ta yi murmushi a nan ta gane Kameela so take ta jefata a matsala.

"Ki yi kishi da ita taya? Ai ke ba Aliyu kike aure ba, kuma tun da kika ga ya sake ki saboda ita ya nuna ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????miki ta fiki muhimmanci kenan, haka ya buga min warning lokacin da muke can fa saboda ita, kin san mijinki dan duniya ne duk inda aka juya sai ya gane mutum, dama kin hakura domin yadda kika cika idda abu ne mai wahala ya maida ke, balle kuma kin ce har mahaifiyarsa bata sonki a yanzu, yo daman Kameela uban waye zai so ki? Kin ga yanzu ni dake ai mun zama daya, wai ke uwar gori kin ce ban da aure ko? To yanzu ni da ke waye shegen? Ni Wallahi Emily ma tausayi ta ba ni da kika ba ni labarinta, daman tun da na ganta ganin farko na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login