Showing 51001 words to 54000 words out of 253142 words

Chapter 18 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18399

yawu na sauko masa, ta cire tissue ta goge masa bakin.

 Amman Chidimma tana son London sosai bata masa fada, Sir Vito ma yana son London amman Momy bata son London"

Ta matsar da kujerar ta kusa da tashi ta rumfume shi tana murmushi tare da shafa bayansa alamar rarrashi. Sai da Emily ta ga wucewar motar da aka dauki Fatima zuwa makaranta sannan ta fara tafiya da sassafar, tafiya ta yi mai nisa har ta fita daga unguwar daga daya, daman manufar fitar ba domin motsa jikin ba ne kawai. Unguwar dake kusa da ta su ta shiga tana kallon shagunan da suka gurin wanda ta ga alamar babban shago ne ko super market sai ta dauki hoton gurin saboda kar ta manta. Kusan duk inda ta bi kallonta ake saboda yanayinta, kusan kowa kallon baturiya yake mata saboda yanayin shigarta idonta da kuma gashin kanta dake bude.
Taxi ta hau a lokacin da zata dawo gida saboda gajiya da ta yi, cikin gidan ta shiga ta dauko masa kudinsa ta ba shi sannan ta koma ciki ta yi wanka ta karya ta haura sama domin bawa gado hakkinsa.


KAMEELA POV.

"Na jidadi sosai ko da na iso na tarar an kawo min komai na gode Honey"

"You deserve it, Allah ya kara miki lafiya"

"Ameen, yaushe zaka zo?"

"Soon dear"

"Ka kula min da kanka"

"I will"

Ta sauke wayar tana kallon kanwarta dake tabe baki, Anty Shafa data doro alwala ta tana yarfar da ruwa ta ce.

 Kina godiya akan abun da kin fi karfinsa, dole ne daman yayi miki hidima tun da haihuwa kika yi kuma dansa kika haifa ba dan wani ba"

"Hmmm Anty Kameela da yanzu ke matar Governor ce, da yanzu ke ce first lady, amman kika ki yarda kika watsa mana kasa a ido kika zabi dan makiyinmu"

Ta sauke numfashi.

 Siyasa ce fa, saboda Baba ya rasa kujerar Senator mahaifinsa ya samu ba wani abun ba ne, kowa rabonsa yake ci, kuma zamansu yar jam'iyar hamayya wannan siyace, daman ta gaji haka, ni ba zan iya zaman kishi da sa'anin mahaifiyata ba akan zama first Lady, kuma yadda nake da kishin nan ba zan iya raba kwana da wata mace ba, kuma ba zan iya auren dan siyasa, dan haka ku bar ki na zauna da mijina muna son junanmu"

"Ga ki gashi ai idan namiji ne, har da wani yarda da alkawarin da yayi miki saboda baki da tunani, mahaifiyarsa har magana ta fada min wai ban yi aure ba"

Cewar Anty Shafa again tana kokarin saka hijab.

"Aliyu ya san ni ya san halina kuma ya san suwaye iyayena ba zai taba yarda ya karya alkawarin da ya daukar min ba, domin ya san yadda zan hana shi zaman lafiya"

Anty Shafa ta tabe baki ta kabbatar sallah, Farida kuma ta yi dan tsaki.

 Har abada dai Wallahi bana son Aliyu bana son iyayensa, domin shi ne silar bakincikin mahaifinmu"

"Sai ki kashe shi idan baki son shi"

Kameela na rufe baki aka turo kofar dakin, Mama Barakat ce ta shigo dakin da far'arta.

 Maa Shaa Allah, Kameela jiki yayi kyau"

Kameela ta wani hade rai ta juyar da fuska kamar ba ita ake yi ma maganar ba. Farida ta amsa.

 Eh jiki yayi kyau sosai Mama Barakat"

"Sannu Kameela ashe kuma dan be zo da rai Allah ya baki lafiya ya bada na aikawa yace shi din kuma mai ceto ne"

"Ameen"

Ta amsa daker kamar an mata dole.

"Ayi ma Aliyu gaisuwa"

"In shaa Allahu zai ji Mama Barakat an gode"

Farida ce kawai take amsa mata Kameela kam ko gafen da da take bata kalla ba kai kace ba ita ta shigo ta yi ma sannu ba, Mama Barakat na fita Kameela ta ja tsaki.

"Ni ban san abun da Abbah ya gani a jikin matar ba ya aurota, gashi nan ta zo ta tsika mana zuri'a da yarbawa, sai bakin munafurci da iyayi, Wallahi na tsaneta kamar mutuwa"

"Saboda me?

Farida ta tambaya. Kameela ta watsa mata harara.

 Ke har sai an fada miki? Wake son kishiya sai kin yi aure zaki gane kan gari, duk wani abu mai alaka da kishi ko kishiya ni bana ciki, gashi nan ta zo ta tsirka mana da nata jinin a gida"

Anty Shafa da ta sallame sallah ta jefa nata baki.

"Ai ba laifinta ba ne Wallahi laifin Abbah ne duk matan duniyar nan ya rasa wa zai aura sai bayarabiya"

"Wallahi na rantse da nice Hajiyarmu ba zan yarda mijina ya kara aure ba, bayan duk wahalar da aka Sha an samu kudi yanzu sai kawai ya karo aure, tab ai sai dai a mutu"

Kameela ta fada. Farida ta kallesu da mamaki.

"Yanzu fa ana maganar shekara goma sha biyar da auren nan, toh miye amfanin yin maganar yanzu, tun da har yara ta haifa da ai sai hakuri"

"Ke dalla gafara can baki san ma duniya ba"

Anty shafa ta karasa tare da jan taja tsaki ta fice daga dakin.


EMILY POV.

Bata farka ba sai karfe biyu da rabi na rana wani wanka ta sake yi ta yi kwalliya cikin wata shigar ta kananan kaya ta canjan sarkar cross din dake wuyanta zuwa dabam wanda ita ta siya da kanta ba wanda Vito ya siya mata ba, even though da kudinsa ta siya but not t like wanda ya bata da hannunsa, jakarta ta nufa ya dauko agogon mutumen nan ta saka a hannunta sai dai yayi mata yawa yana zubo mata a hannu.
Ta zabi haka ne domin ta shiryawa amsawa Vito ko wace kalar tambaya da zai mata a duk lokacin da yayi arba da sarkar wuyanta ko kuma agogon mutumen da baya fatan ta hadu da shi yanzu ko nan gaba.

Ta saka turare sosai sannan ta fito daga dakinta tana sanye da fararen flat shoes. Babu karya duk wanda ya kalleta zai san ta yi kyau domin red dress din yayi mata kyau ya karbi farin fatarta, ga gashinta data sako a gaba ta kulle sauran a bayan kanta. Chidimma ma da take mace kallonta take ta ko'ina Emily ta hadu kuma ta kai mace, wata kila shiyasa Vito yake sonta baya sauraren ko wace mata sai ita, sam baya kallon yaranta data haifa ma da kuma yadda yarta take yarfashi a gaban kowa, haka ma yake ta wahala da danta marar lafiya amman ita ma bata gani, idan ba shi ba wake wannan wahalar yanzu...

"Are you okay"

Emily ta tambaye ganin yadda take kallonta har ta sauko bata san ta iso kusa da ita. Da sauri Chidimma ta sauke kai kasa jikinta ya dan yi rawa.

 Ina tunani ne"

"Kina cikin wata matsala ne?"

"Aa babu komai Ma'am karki damu"

Emily ta daga kafadunta ta duba agogon da yayi mata yawo.

"Yanzu na san Fatima tana kusan da dawowa, idan zata je makaranta islamiya fine idan kuma ba zata je ba, kar a barta taje ko'ina, zan fita maybe sai dare zan dawo, ki shafa min kan London kuma ki fada masa ina kaunarsa"

"Tohm ranki ya dade"

Ta amsa Emily ta kalli dinning ta dauke idonta ta nufi kofar fita falon ta fice. Gudun abun da zai je ya dawo ya hanata fita da motarta sai ta zabi tafiya a kafa, haka ta bi shagunan da ta gani dazun da safe ta gabatar musu da kanta ta kuma tallata kanta a matsayin ma'aikaciya idan suna bukata, sai dai ta manta bata dauko cv dinta ba sai a waya take nuna musu ko ta karbi number mai gurin ta tura masa.
Kusan kowane shago kallonta ake domin bata yi kama da wanda zata iya aikin siyar abu a duka shaguna nan ba, dan haka wasu a take suke fada mata basa bukata, wasu kuma su yi tunani ko dai an turo ta ne, ko kuma an shirya yi musu wani zagon kasa ne, kadan ne suke bata tabbaci za su tuntube ta idan bukatar hakan ta taso.
Ita kam a bakin gaskiyarta take neman gurin da zata iya tallafawa kanta, domin samun aiki na gobnati ko kamfani ba karamin abu ba ne ta san irin gwagwarmayar da ta yi kamin ta samu aikin da Amal ta yi mata sanadin barinsa yanzu kuma Aliyu yake son ta dawo saboda ya mulketa.

Wani babban shago siyar da talkamin maza dake cikin quarters din dake kusa da unguwarsu ta shiga, sai suka yi mata maraba bayan security ya bude mata kofar shop din, kai tsaye ta tambaye manajan gurin sai da ta basu tabbacin babu wata matsala kawai tana son ganinsa ne sannan aka nuna mata shi. Ta doshi gurin da yake zaune tare da wani.

"Ssnnu kai ne manaja a nan?"

Ta tambaya mutumen ya kalleta Aliyu ma dake zaune ana sanya masa talkami a kafa ya juyo ya kalleta daga sama har kasa.

"Eh sannu da zuwa fatan dai babu wata matsala ko?"

Arba da ta yi da Aliyu ya saka duk wani hanzari da confidence nata yankewa, wani abu mai kamar fargaba kamar tsoro ya lullubeta, har take ji da ace ta san shi ne yake zaune a gurin ba zata karaso ba, gashi ta kasa sake hada ido ta shi kuma ta kasa cewa komai, ta jimke agogon hannunta dake kokarin zubewa dayan hannunta kuma ta rike jakarta.

"Lafiya dai?"

Mutumen ya tambaya, Aliyu ya sake juyowa a kallo na biyu sai dai wannan karon ya sauke idonsa ne akan agogon dake hannunta, fuska ba yabo ba fallasa ya mike tsaye.

"Kala hudu nan sun isa for now"

Ya saka talkamin da ya zo da su, ya ciro katinsa ya aje akan babban table din dake gabansa.

"A kai min a wannan addireshin"

Manajan ya kalleshi da mamaki domin be taba siye abu yace a kai masa gida ba sai dai a saka masa mota ya tafi da shi.

"Okay ranka ya dade"

Ya nufi gurin biyan kudi ya biya da amt dinsa har kudin kaiwar sannan ya nufi kofar fita, sai a lokaci Emily ta jiya juyawa tana kallon bayansa har ya fice. Sai kuma ta ji haushi kanta meyasa be mata magana ba ko ya nuna ya santa, and why ita ta kasa yin magana a gabansa.

"Akwai abun da zan iya taimaka miki da shi"

Ta karkarto hankalinta gurin manajan.

"Eh, ina neman aiki ne a nan idan da hali"

Manajan ya kalleta saka da sama domin bata yi masa kama da mai neman aiki ba. Ta gabatar masa da kanta kamar yadda take a sauran guraren ta karbi number wayarsa ta tura masa cv ta sannan ta fita jikinta na raya mata abu ne mai wahala ta samu aiki a gurin duba da wanda ta tarar da kuma irin kallon da mutumen yake mata kamar be yarda da ita ba.
[4/27, 4:43/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01



*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 7??


Yadda ta tafi a kafa haka ta dawo a haka feeling so lonely and hopeless. Ta kwankwasa gate din aka bude mata ta shiga, ganin bakuwar mota ya saka ta juyo ta kalli mai gadinta kamar zata tambaya waye sai kuma ta fasa, ta nufi main door din da sauri zuciyarta na raya mata wata kila Aliyu ne ya rigata iso gidan, sai dai hango direban Vito da ta yi a gaban motar ya sauya tunani, ta tura kofar falon ta shiga, sai ta samu babu kowa a falon sai wata bakuwar fuska da ta yi arba da ita a zahiri, a badini kuma mace ce da ta sha ganin hotonta a wayar Vito da kuma gidansa.

"Da alama ke ce Emily"

Matar dake tsaye a dinning din falon ta fada tana kallon Emily da murmushi a fuskarta.

"Barka da sauka Mrs Gloria"

Cewar Emily tana kallomta fuska babu yabo ba fallasa.

"Vito ya fada miki wacece ni a gurinsa kenan"

"Na sha ganin hotunanki a wayarsa da gidansa"

"Kamar yadda ya cika ni da labarinki"

Tana maganar tana nufo gurin da Emily take tsaye, ta kama hannunta suka zauna.

"Fatan na same ki lafiya, ya yaranki"

"Duk muna lafiya"

Ta kai hannu ta rike fuskar Emily.

"Ke kyakkyawa ce, kina da aji amman ba irin kyaun da za'a ce babu wata macen bayan ke ba, ana yana kaunarki sosai kin jama lu'u-lu'u a zuciyarsa, a duniyarsa kuma kin zama numfashinsa wanda yake jin kamar idan ya rasa ki ya rasa rayuwarsa gaba daya"

Ta shafa fuskar Emily.

"Kin canja rayuwar ana, a da babu ruwansa da mace ko wace kala ce, be taba min zancen budurwa ba, ban taba ganinsa da wata ba, idan ma na yi masa ransa baci yake, be taba soyayya sai akanki, ada baya tsoron aikata kowane kalar aiki ko jefe kansa a hatsari, amman sanadin ki a yanzu yana tsoron shiga matsala, ya kan ce min idan wani abu ya faru da shi ya zaki yi? Wa zai kula da ke da yayanki?"

Emily ta sauke kanta kasa tana hade yawu.

"Amman kin san danki yana siyar da kwayoyi? Drugs"

Mrs Gloria ta yi murmushi.

"Na sani, wannan sana'ace da ya gada tun daga gurin mahaifinsa, kamin a kashe shi, kar hakan ya dame ki, amman ki yi taka tsantsan da zuciyarsa, ba saboda ke ba saboda wadanda suke tare da ke"

Ta mike tsaye.

"Be san na zo nan ba, karki sanar masa. Na barki lafiya"

Emily ta bita da kallo har ta fice, ta sauke ajiyar zuciya ta jingina da kujerar, ta daga hannunta tana kallon agogon dake hannunta ta lumshe ido ta bude ta maida dubanta gurin Jakarta da wayarta dake ciki ke sanar da ita isowar sako. Ta ciro wayar ta duba sakon da shigo daga number Aliyu even though bata yi saving number ba, amman ta gane number shi ce domin sakon yana a saman wacan sakon da ya turo mata a ranar da suka hadu asibiti.

"Mahaifina dan siyasa ne, sau hudu yana tsaya takarar dan sanata amman be taba yin nasarar ba sai bana"

Ta karanta sakon ta sake karanta sai ta aika masa da quation marks, like why are you telling me this?
Ta tashi ta nufi dakin da danta yake tana ta mamakin dalikinsa na bata tarihim mahaifinsa ba ma nata ba, tana tura kofar dakin sai ta same shi tare da Fatima da Chidimma suna ta wasan doki cikin far'a da sakewa, sai da ta fara kawata fuskarta da murmushi sannan ta karasa cikin dakin ta shafa kan London a take ya hade rai ya matsa gefe, bata damu ba ta shafa na Fatima sannan ta karasa kusa da shi ta zauna a kasa.

"My handsome Man"

Kamar jira yake ta rufe baki sai ya saka mata ihu da sauri ta tashi daga gurin ta matsa.

"Baya bukatar ganinki ne a yanzu, da dai zaki yi hakuri ki fita saboda muna wasa a yanzu kar a bata masa rai, mu wuni a damuwa"

Ta daga ma Chidimma kai cikin rashin jindadi ta fice daga dakin, ta shiga nata dakin ta aje jakarta da duk wani abu da yake hannunta ban da wayarta da yake karanta sakon Aliyu da ya shigo mata yanzu.

"Wata rana a Kaduna ranar 20 ga watan march 2020 aka ina tare da friends dina a inda muka saba haduwa mu yi shawara ko wani abu mai amfani, a ranar muna kallon tv ne a lokacin ake sanar da sakamakon zabe wanda mahaifina ya tsaya a karo na hudun kuma karo na karshe a rashin nasararsa, aka sanar cewar ya fadi kamar kowace shekara abokin hamayyarsa yayi nasara a karo na hudu, daman shi ya saba yi nasara a duk zabe"

"Miye alakata da zaben mahaifinka?"

Ta aika masa da tambayar domin har yanzu bata fahimci inda ya dosa ba, ya aiko mata da murmushi sai kuma wani sakon.

"Na ji babu dadi sosai, abokaina suka karfafa min guiwa, muna haka sai ga mahaifiyata ta kira ni cewar mahaifina yana ciki wani hali na damuwa saboda faduwa zaben da yayi, na yi hanzarin barin abokaina na shiga motata domin tafiya karfafawa mahaifina guiwa kasancewata namiji daya tilo da ya haifa a cikin yayansa mata, a hanyata ya tafiya aka fara ruwa daman hadari ya gama rufe garin kaduna a wacan lokacin... A hanyata ta tafiya na hango wata mata tare da danta sun fake a wata kazantaciyar tumfa, yana daya daga cikin halina taimakon mai rauni a duk lokacin da na samu hali, and it does not matter if musulmi ne ko ahalul kibat, a nan na gagara wucewa na matsa kusa da inda matar take na faka motata na fita sai na same ta tana ihu da dukannin karfinta, ashe nakuda take a gurin tana dauke da tsohon ciki ne, ga kuma danta da ya kasance marar lafiya,

"Sannu miya same ki? Ko haihuwa ce? Me kike yi a nan? Wacece ke?"

Haka na jera mata tambaya ina leken fuskarta, sai ta kalleni amman bata iya magana ba sai dai ta kalleni a lokacin ta mika hannayenta ta riko hannuna.

"Subhanallahi... Christen ce ke?"

Na tambaya domin na lura da sarkar cross din dake wuyanta, sai na yi cire hannuna hannayenta, a kokarin yin haka agogon hannuna silver color ya zame ya tsaya a hannunta, sai ta jimke agogon tana cizon baki tana nishi mai karfi alamar tana jin zafin ciwo, hakan ya saka ban yi yunkurin karbarsa ba.

"Am... Akwai wanda kika sani nan kusa?"

Na sake tambayarta sai ta girgiza min kai alamar aa,

"Okay zan kai ki asibiti yanzu nan... Danki ne wacan..."

Na tambaye ta, kamin na dagata na sakata a motata ina istigifari.

"Allah ka yafe min wannan ba da niya na aikata ba"

Na saka danta na tuka motar ina tafe ina mata sannu har muka isa asibiti, na bada damar ayi mata komai a cikin aljihun familynsu domin asibitin da na kaita kamar ta gidanmu ce, a nan na barta na tafi gurin mahaifina, bayan na dawo sai a aka samu bata dakin da aka aje ta ta gudu ita da yar da ta haifa da danta kamar yadda suka fada min, tun daga ranar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login