Showing 189001 words to 192000 words out of 253142 words

Chapter 64 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18403

tun da gashi ina da Fatima, ni ne na kawo duk wata matsala da muke ciki yanzu, tunani ne sai na rasa wane zan yi, kullum da fargaba nake farkawa a guntun bachin da yake daukata a karshen dare, fargabar tambayar Fatima, ga shi ta dauki damuwa ta saka a ranta yanzu ta daina sakewa da kowa ta daina walwala, kuma ita kanta Aisha yanzu ba mu san wane hali take ciki ba, kuma ina fargabar kar ace ta fada wani hali saboda rashin Fatima idan har haka ya faru laifin a kaina zai sake komawa"

Ta kalleshi cike da tausayi.

"Ka yi iya kokarinka kuma na baya ba, ka nemeta a lokacin da baka san tana tare da yarka ba, a yanzu kuma da ban saka ka ba, ka saka kanka ka je har garin da ta zauna baka sameta ba, a garin nan bana tunanin akwai inda kafarka be taka ba gurin nemanta, nan ma baka dace ba, tun da ka baro Sudan baka koma ba saboda Aisha, a haka ma ka biya Turhan kuma ina alfahari da kai, jikina yana raya min kamar tana wani guri kusa ta boya ne kawai saboda ta fitine mu, tun da gashi yanzu Fatima kullum sai ta daga mana hankali saboda neman mahaifiyarta"

"Amman me yasa bata dawo ba?"

"Saboda ta azabtar mu mana, saboda idan ta waige mu sai mu mika mata Fatima jiki na rawa"

"Da ma dai ban sake ta ba, zata iya zuwa fa ta dawo da auren wani akanta"

"Zuciyar yarinyar nan bata da kyau, duk wata uwar kirki ba zata iya tafiya mai tsayi haka ta bar yarta ba, saboda kawai ubanta yayi mata ba daida ba, ni miyasa ban kyale ka ba? Bayan duk abun da ubanka yayi min? Wani lokacin idan na tsaya ina tunani sai na rika ganin kamar ba Aisha bace ban yi zaton zata iya aikata haka ba"

"Na fi tunanin kamar bata lafiya, ko kuma wani abun ya same ta, wata kila da yanzu ta dawo, domin yadda nake jin Fatima ni kam ba zan ma iya sati ban saka ta a ido ba"

"To ya sani tun da ta zabarwa kanta guduwa? Wani abun ba kaddara ba ce har da hali"

"Kuma ni sai nake ganin kamar Aliyu ya san inda take, kawai dai yana wasa da hankalina ne ko kuma yana jiran na nemi taimakonsa ne wanda abun ne da ba zai taba faruwa ba har abada, gashi ba wani tufafin kirki take sakawa ba yanzu"

Yana maganar cike da zafin kishi marar misaltuwa.

"Idan har abun da kake zargi ya tabbata to ni ina baka shawarar ka hakura da yarinyar Turhan, shi kuma sai mu ga idan dan halak ne"

"Ai be san kunya ba Ammy ina cire kafa tasa zai saka ya taka, da ace ya san kunya ba zai aikata abun da ya aikata min ba, domin no matter what ya fi kusanci da ni fiye da Aisha, amman ya zabi ya ci amanata, na san ban kyautata ba amman dai ai ni abokinsa ne Aisha kuma be da alakar komai da ita"

"A wani mutum makiyinka ne Turhan a cikin yan'uwa ma akwai su kuma munafikin mutum yana da wahalar zama da ganewa, amman ba zaka taba sanin sai wani abun ya faru, wani zaka samu yana maka hassada ne domin idan babu wannan ban da dalilin da zai saka mutum ya zabi bare sama da wanda ya sani ba, kuma har ya nuna maka kirkiri ai kiyayya ta kai kiyayya, sai dai ka yi taka tsantsan"

Turhan yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya mike tsaye ya fice daga dakin gaba daya kansa ya kulle ta ina zai samu Aisha? Ina ta shiga? Tana raye ko kuma tana cikin wani hali? Miyasa zata masa irin wannan horon mai azabtarwa haka? Tsanar da take masa ta kai har can? Amman ta saba guduwa halinta ne. Wani bangare na zuciyarsa ya raya masa, sai dai be gamsu da hakan ba domin yana ganin ga rayuwarta a nan wato Fatima.
Ya jingina jikin mota yana kallon tausarin da suka yi sararin samaniya ido, ya tsada idonsa gurin wata tauraruwa wacce ta fi sauran haske a dare.

"Na zabtu Aisha, na azabtu fiye da yadda kike tunani, na shiga damuwa na rashin sanin halin da kike ciki, fargabar irin tarbar da zan samu a gareki ya hana ni walwala, ban taba sanin muhimmancin wani abu na kimanta shi ba kamar yadda nake jinki a yanzu, na yi iya yadda zan iya na san wane hali kike ciki amman hakan ya gagara, yaushe zaki dawo gareni? Idan kin dawo zaki saurere ni kuma dai yafiyar ba yanzu ba ce? Kin ce baki taba so na ba, kin yi komai saboda mahaifiyata, yanzu miyasa ba zaki yi saboda yarki ba? Ina son ki Aisha ina son kasancewa da ke"

A hankali yake lumshe ido yana budewa zuciyarsa cike da kuna, ya hade yawu.

"Ni mai tarin laifuna a gurinki na sani, amman ki ba ni damar da zan gyara mana, kina ina Aisha? Na ji fiye da yadda kika ji a lokacin da na barki, saboda ni a yanzu kin tafi ki bar ni da azababben Ciwon Sonki da tsananin kishinki, kin bar ni da tunaninki, ga fargabar abun da zai same ki da yadda zaki karbe ni, a yanzu ke baki jin komai saboda bana kusa da ke, amman ni ina jin duk wata azaba ta duniya saboda rashinki"

Ya juya baya.

"Ban san dacin rashi ba da kewa ba sai da na rasa ki, amman zan nemo ki, zan jure duk wata tsana ko tsangwama daga gareki har sai kin yarda ni ABOKIN RAYUWARKI ne, a inda na wulakanta zan daukaka darajarki wannan alkawarina ne, ki yafe min Aisha, dan Allah karki bar ni, ina da bukatarki a kusa da ni, ko da ke baki ra'ayi na na san ba zaki so ni ba, amman ni ina Sonki haka ma ya wadatar, abun nan ba shi da sauki ko kadan, ya wuce duk yadda kike tunani"

Ta lumshe ido ya cije lebensa na kasa cike da kukan zuci wanda ya fi na hawaye daci. Sai a yanzu yake ta kara dorawa kansa laifin abubuwan da suka faru, yake nadamar abun da yayi mata kuma yake ganin rashin dacewa a hakan, babu komai a tare da shi a yanzu sai tsantsanar kaunar Aisha da kewarta da kuma nadamar da bata da amfani.



EMILY POV.

Ya aje mata tsarabar da yayi mata a gafen gado sannan ya kai hannunsa ya taba jikinta sai ya jishi da zafi kamar kullum. Taba ta da yayi ya saka ta bude ido daman idonta biyu ba bacchi take ba, ta kalleshi da idanuwanta da bata iya budewa sosai.

"Babu ranar da zaki ji sauki idan ba zaki daina tunani ni ba, tunanin nan shi yake haifar miki da damuwa, ita kuma damuwa bata barin kwakwalwa ta huta, kwakwalwa kuma bata mikawa kowa matsalarta sai zuciya da jiki"

"Am so fighting for peace, ina ta yin kokarin abun da zan iya, da kowane numfashi ina tunanin yata da rayuwata, na yi marmarin kurciyarta a lokacin da ban san tashin hankali ko bacin rai ba, ban san muhimmanci iyaye ko yan'uwa ba"

Ya zauna gefen gadon sai ta tashi zaune ya kalleta gaba daya ta bi ta fita hayyacinta saboda tunani da damuwa, kusan tun da ta zo gidan ta gagara sakewa da kowa abinci sai dai a kawo mata a daki, sai idan yana gidan yake cilasta mata fitowa dinning ta ci abinci tare da kowa, ga ciwo kullum lafiya ta ki sama mata salama. Dr A-B yayi iya kokarinsa gurin dauke mata hankali da wasu abubuwa amman hakan be samu ba, ko Tv aka kukuna mata madadin damuwa ta ragu sai ta karu, idan ta ga yara, idan kuma wani bangare ne da ake kuka haka zata yi ta kuka kamar gaske. Idan ta auna yadda take ji a yanzu da ta san Fatima tana hannu da guri mai kyau, sai ta yi mamakin yadda mahaifiyarta ta iya jefar da ita kuma ta jure rashinta, a nan ta fahimci wasu mutanen an yi su ne kawai saboda su kaunaci mutane ba dan su samu kaunar daga gurin kowa ba.

"Da nace zan saka a dauko Fatima ko? Kika ce aa kuma saboda ita kullum kike damuwa?"

"Bana son kowa ya san inda nake, ina jin aminci da natsuwa a nan, kawai dai na gafara sabo wa da kowa ne, kuma ina ta guje ni bayan tsawon shekarun da muka dauka a tare, idan har zan kusance ta sai ta bukace ni, ina son na saba da rashin komai kamar yadda kaddara take koya min"

Ya kai hannu ya shafa kanta cike da tausayin hawayen da take zubarwa.

"Kina horar da kanki ne kawai, Fatima karamar yarinya ce bata iya gane daidai ko kuskure yara suna bin son zuciyarsu ne kawai"

"Haka ne, ni ma son zuciyar na bi ya kai ni ya baro"

"Wannan tunanin yake haifar miki da damuwa, Momy ta fada min tun da na tafi baki fito ba, da zarar tafiya ta kama ni zuwa wani guri baki sake fitowa, kuma zuwa yanzu ya kamata ace kin sake jiki da kowa Emily"

"Ka yi hakuri zan saba, amman ba lokaci daya ba, abun ba shi da sauki ko kadan"

"Na sani, yanzu taso muje mu ci abinci a upstairs"

Ya share mata hawayenta, ta san duk yadda zata musa masa ba zai taba barinta ta zauna a dakin ta ci abincin ba, dan haka ta sauko da kafafuwanta sai ya yaye mata bargon dake jikinta ya rika hannunta ya nufi kofa ya bude ya rike mata ta fito ta yi rama sosai kurmin idonta har ya fada, kana ganinta ka ga mace mai damuwa. A falon Momynsa yake cin abinci dan haka ya nufi upstairs watching her steps har suka haura ya shiga falon yana rike da hannunta.

Tun da suka shigo akan hannunta da Dr A-B ya rike Aliyu ya sauke idonsa, kamin ya isa gurin fuskarta, for the first time ya ji kamar yaje ya da gudu ya rumgumeta ya fada mata komai zai wuce, saboda yadda yayi marmarinta da kuma damuwar da ya gani a tare da ita ga wata rama da ta yi abun tausayi. Tsayawa ta yi cak, Dr A-B ya kalli kafarta kamin ya kalli fuskarta zuwa abun da take kallo, sai ya ga mutanen da ba bakin fuska ba ne a gurinsa musamman Mama Barakat. Ya kalli mahaifiyarsa dake zaune zai yi magana ta riga shi.

"Ka same ni Waki zamu yi magana"

Ya saki hannunta.

"Je dakinki"

Ta juya tana jin abun some how, taya suka san tana nan? Ko dai shi ya fada musu? Ta sauka kasa tana tafiya hawaye na sauko mata har ta isa kofar dakin ta murda ta shiga ba tare da ta juyo ba balle ta rufe.

"Har yaushe zaki yi ta gudu ne ke kam Emily?"

Ta juyo ta kalleshi har ga Allah bayan yarta shi ne mutum na biyu da ta yi marmarin gani.

"Taya ka gano ni?"

Ta taka ya shiga cikin dakin.

"Ta yadda mutuwa take neman rai, duk inda kika shiga zan nemo ki Emily, duk inda kika tafi zan biyo sawunki"

Hawaye ya sauko mata

"I don't need to do this, ban cancanci wannan sadaukarwa ba"

"You just don't know what you mean to me, tabbas ban cancanci sadaukarwa daga gareki ba, alfarma nake nema, Emily ina son na maida ke gida"

Ta yi baya baya ta zauna tana rumgume da hannayenta tana wasu hawaye masu zafi. Ya karasa cikin dakin yana kallonta cike da tausayi. Ya zauna nesa da ita tana kallonta shiru yatsasu na tsawon lokaci, kamin ya yanke shirun da fada mata abun da ta fi bukatar ji a yanzu.

"Fatima tana lafiya, amman ta yi marmarinki sosai"

Ta lumshe ido, bata da tabbaci abun da Aliyu ya fada amman dai ta ji sanyi a zuciyarta.

"Why are you here?"

Ta tambaya ido a lumshe, muryar a dakishe, Aliyu ya amsa mata kamar mai rada.

"To take you home"

Ta girgiza kai tana maida numfashi sai dai bata ce komai ba, ita a tunaninta rayuwarta ta zo karshe mutuwa kawai ya rage mata. Aliyu ya cigaba da kallonta cike da tsantsar tausayinta dake ta dawainiya da shi.

"Duk lokacin da kika ji ba zaki iya ba, ina nan kusa da ke, hankalina zai fi kwanciya ace duk lokacin da kika farka, zan kasance kusa, na ga nauyin da kike Wauka ke kaWai
ya?in da kike yi, tabon da kika nuna"

Ya hade bacin ran daya tsaya masa a wuya.

"Ba sai kin Soye shi ba yanzu
zan zama ?arfinki, kuma na yaki ba?in cikinki, idan dare ya yi miki sanyi kuma duniya ta zama maras tausayi a gareki, ki bar ni in zama lafiya da kike nema"

Yayi shiru na dan lokaci.

"Zan Waga darajarki, zan share hawayenki
zan tsaya tare da ke cikin kowane hali, farinciki bakinciki ko kuma duka, idan kina bu?atar hannun da zai rika ki ya tsamo ki daga rijiyar da kika fada, zan mi?a nawa, idan kina bu?atar yin ihu, ki yi zan ji kukanki na saurareki Emily"

Yayi shiru yana kallom hawayenta, hawaye take sosai har wani kololon kuka ke mata yawo a zuciya.

"Duk abin da zan Wauka don ki samu nutsuwa dauka, zan tsaya tare da ke, hakan zai samu idan kin zauna a kusa, ki bar ni in kiyaye ki lafiyarki cikin guguwar rayuwa, zan zama mafakarki zan Wauki zuciyarki idan bazaki iya da ita ba, tare zamuyi ?arfi, za mu fuskanci duhu, ke ce duniyata a yanzu, wata da
tauraruwa da ke jagoranta ta"

Ta bude ido ta kalleshi, kalamansa na ratsata da tsuma zuciyarta, ashe dai ita ma tana da muhimmamci, a yau Aliyu ya karanta mata abun da ta dade tana musunsa a zuciyarta.

"Kowane hawaye da kika zubar, kowa rauni da kika bayyana zan kasance a tare da ke, abun da ke tsakaninmu a yanzu ya wuce tausayi kawai, wata katangar karfe ce da bata rusuwa, wani kololon nauyi ne wanda ni da ke muke dauka da baya zai taba yiyuwa mu aje ba, every time you fall I'm breaking too, amman ina kokarin na ga na tashi saboda ke, so I'm here to take you home karki ce min A A"
[8/1, 1:58/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL?mode=ac_t



*

*? Khadeeja Candy*



Page 6?? 0??


Dr A-B ya bi bayan Momy ya shiga bedroom dinta, ya zauna cikin rashin natsuwa da kuma bacin rai.

"Ya aka yi suka san nan? Kuma suka san Emily tana nan?"

Momy ta dube shi.

"Samu sakon neman yarinyar nan ta email, waya daga wannan yaron Aliyu, kullum da kalar magiyar da yake min da rokon na ba shi dama ya zo yayi magana da ita, ya fada min Madam Barakat ce mahaifiyarta, ita kanta ta same ni da maganar kuma na fahimce ta na karanci damuwa a tare da ita sosai saboda ni ma uwa ce, and kai kanka mafita kake nemawa yarinyar ai kuma yanzu yan'uwanta sun bayyana me zai saka mu cigaba da boyeta?"

"You just don't like her Momy haka ne?"

"Me zai saka na tsane ta? Me ta min? Labarinta abun tausayi kamar rayuwarta, amman ba mu da wata hujja na cigaba da rike ta, kasan mahaifiyarta tana da damar ta saka kara ma akan boye mata yarinya? Balle kuma Madam Barakat ta yi min komai? Ba zai yiyu na gagara cireta daga matsala ba"

Dr A-B ya mike tsaye ya taka ya juyo.

"Amman baki shawarce ni ba, ni na kawo ta gidan nan akalla ta kamata ace ina da labarin abubuwan da suke tafiya akanta"

"Ba lallai ita ko kai ku aminta ba, shiyasa ban fada maka ba, kuma ai ba tafiya suka ce za su yi da ita ba, magana kawai za su yi, ni kaina na dauki tsawon lokaci kamin na amince da yaron ma, daga baya Mahaifin yaron ya tuntubi mjjina akan yarinya and i can't said NO"

Ya sauke ajiyar zuciya mahaifiyarsa ce ba zai iya daga mata murya ba, sai dai sam abun da ta yi masa be masa dadu ba ko kadan. Ya fito daga dakin yana kokarin boye bacin ransa ya kalli Madam Barakat da bakuwarsa ba.

"Barka da zuwa Madam ya hanya?"

"Alhamdulillah"

Ta amsa tana kallonsa kamin ta kalli Aliyu dake kofar shigowa falon tana takowa a nutse. Dr A-B ya kalleshi shi ma ya kalli Dr A-B kamar ba za su yi magana da juna ba, sai kuma Aliyu ya mika masa hannu. Dr A-B ma ya mika masa hannu suka gaisa, sannan ya nunawa Aliyu kujera shi ma ya zauna.

"Yaya Emily take a yanzu?"

Aliyu ya tambaya, Dr A-B ya fada masu yanayinta da kuma abunuwan da yake kokarin ganin ya cin ma a game da lafiyarta.

"Maa Shaa Allah haka ake so, ka yi kokari mun gode sosai"

Mama Barakat ta fada. Dr A-B be ce komai ba ya kalli agogon hannunsa.

"Momy tace kun zo nan ku ganta ne, bari na yi magana da ita sai ku shiga ku ganta"

"Already na yi magana da ita, kuma mun zo nan ba dan magana da ita kawai ba, maganar gaskiya mun zo nan ne saboda mu tafi da ita gida"

Aliyu ya amsa masa, Dr A-B ya kalli Aliyu.

"Bana tunanin tana bukatar tafiya wani guri yanzu, domin abun da Emily take bukata a yanzu shi ne kulawa da kwanciyar hankali"

"Zamu bata fiye da abun da kake tunani Dr already mun yi booking flight in the next 40 to 1h zamu juya In Shaa Allahu"

Dr A-B yayi kokarin mikewa tsaye sai ga Momy ta fito dakin ta dawo falon tana zaunawa Emily ma ta shigo falon tana tafiya a hankali.




EMILY POV

Mikewa yayi tsaye.

"Jirgin da za mu bi zai tashi nan da awa daya, ban sani ba ko rayuwa zata ba ni aron lokaci na dawo gareki, wata kila kuma sa'a ce zata rabe ni ta saki ki bi ni, duk wannan ba ni da ilimi akai, sai abun da zuciyarki ta gamsu da shi"

Ya juya ya fice daga dakin. Emily ta bishi da kallo har ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login