Showing 180001 words to 183000 words out of 253142 words

Chapter 61 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18371

ya yayi masa ya jiki Aliyu ya amsa masa da kai, bayan ya fice Ummi ta zauna tana murmushi.

"Maa Shaa Allah, jiki dai Alhamdulillah alamar sauki yana ta bayyana"

Aliyu yayi murmushi ya yi addu'a yayin da ya kai karshen aya ya fita daga app din.

"Ummi barka da rana"

"Barka dai ya jikin?"

"Alhamdulillah"

"Haka ake so, wayar nan taka zan karbe ta gaskiya na aje har sai ka samu sauki tukuna"

"saboda me?"

"Saboda bana son ta dauke maka hankali, zan kawo Kur'ane sai ka rika karatu da shi"

Ummi ta bude abinci zata fara zuba masa.

"Saboda Emily ne?"

Ta kalleshi.

"Kamar ya? Ka yi magana da ita ne?"

"Na yi magana da ita, ta fada min Turhan ya sake ta, kuma Fatima ta zabi ubanta tace ba zata bita ba, and lastly ta fada min wai wata mata ta bayyana a matsayin mahaifiyarta, kumq ta fada min zata shiga duniya"

Ummi ta maida plate din ta aje.

"Taya ka samu magana da ita? Mun yi ta kiranta bata daga ba, daga baya kuma muka ji wayar a kashe har yanzu wayar a kashe take"

Yanayin fuskarsa ya sauya sosai.

"Kamin ta kashe layin na kirata mun yi magana, Ummi me yasa kuka bari ta fita gidan?"

"Babu wanda yasanta fita, satar kafa ta yi bayan dawowa daga gidansu Turhan ta gudu saboda ta ji muna magana da Hajiya Barakat, kai ma kasan da sanina dai ba zan bari ta gudu ba, ko dan ma gudun tashin hankalinka, amman ya zan yi tun da haka ta zaba ma kanta?"

"Haka dai rayuwa ta zaba mata, ba zata tana zama guri daya ba, sai ranar da wani ya gina gida mai cike da burinkanta da mafarkan da ta dade tana yi, tana guduwa ne saboda tun tashinta bata san wani gida da zata rike a matsayin nata ba, ta kasa aminta da kowa ne saboda duk wanda ta raba sai ya cuceta, ko da kuwa ya taimake ta da farko, shiyasa take kallon kowa haka yake a yanzu, bata da wasu yan'uwa da idan wani ya nunata da yatsa zata juya taje garesu, ita kadai take rayuwarta fadi ta shi duk ita kadai take abun ta, Emily fa ko kawa bata da a yanzu, ni da ke ba za mu gane ba, saboda mun tashi da yan'uwa da iyaye, amman a idon wanda ba shi da kowa yana kallon duniya colorless ne"

"Amman yanzu ai ta samu uwa, sai ka ga yadda Hajiya Barakat take ta kuka gwanin ban tausayi"

"Daman ta fada min wata daga dangin Kameela ce take ikirarin ta haife ta, amman da gaske ita ce mahaifiyarta?"

"A yadda ta fada min dai, ita ta haife ta, amman a zahiri kam ba hadi domin Emily bata kama da ita"

Sai a lokacin Aliyu ya cika da mamakin jin cewar Mama Barakat ce mahaifiyar Emily, dazun tunanin tafiyar Emily be bar shi ya sararara ba balle yayi wani tunanin, sai a yanzu ya tuna labarin da ta ba shi cewar matar da ta zo da ita daga Kaduna sunanta Mama Barakat kuma ta tafi da ita gidanta amman bata tsaya ba ta gudu.

"Amman da gaske bata hanyar aure aka haifeta ba? Kuma da gaske jefar da ita ta yi?"

Ummi ta daga mishin kai cikin yanayin damuwa. Aliyu ya jingina ya rufe ido yana fadin.

"Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un"

"Wallahi, ni ma ta ba ni tausayi, wasu iyayen basa da tunani ne kawai, taya zaka jefar da abun da ka haifa bayan duk wahalar daukar ciki da nakuda, saboda kawai ba ta aure aka samu yaro ba sai ka jefar? Ko a ina suke aje tausayi da kaunar da uwa take da shi ga yayanta lokacin da suke aikata haka? Kuma baka san wane hali yaronka zai tashi ba, baka san ya rayuwa zata kasance masa ba, kalli dai wannan yarinyar, yanzu ai ta daukarwa kanta hakkin yarta, wannan kiwon da Allah yake cewa ya bawa iyaye na yayansu ka ga matan da suke jefar da yayansu ba su sauke wannan nauyi ba, kuma sun jefa kansu da yayan a ciki bala'i da bakinciki, Allah dai ya shirya mana zuri'a"

Aliyu ya bude ido yana kara jin tausayin Emily ya kama shi.

"Amman ta hanyar banza ta same ta ko kuma dai kuskure aka samu?"

"Shi ne ban tambaye ta ba"

"To miye amfanin bayyana akanta a yanzu? Kuma a irin wannan lokacin da take cikin matsala? Kawai sun kunno mata wuta ta rasa ma ina zata saka kanta? Ban tashi tare da ita ba, amman dan zaman da muka yi ina jin tana yawan maganar iyayenta amman ban yi tunanin haka abun zai zo ba"

"Allah dai ya saka idan ta huce ta dawo, idan kuma ta zabi tafiyar ne Allah yasa ta fada hannun kwarai"

"Ameen"

Ummi ta bude abincin zata fara zuba masa ya dakatar da ita.

"Ummi karki zuba abincin nan, ba zan iya cinsa a yanzu ba"

Ummi ta yi kamar bata ji ba ta zuba masa ba da yawa ba.

"Ka daure da kai ka ci"

Ya karba yana kallon mahaifiyarsa, sai kuma ya saki murmushi kadan yana jindadin da shi ta shi uwar ta kasance a tare da tare. Ya fara cin abincin yana tuna wasu kalamai da Emily ta fada masa lokacin da ya kawo ta gida daga gurin aikinsu.

"Yarinyar ta yi kokari, ban san irin rayuwar da mahafiyarta ta gani ko ta ji ba daya saka ta jefar da ita, amman dai ita Emily ta tsaya tsayin daka akan yayanta, daga wanda ya mutu har wannan Fatima babu wanda bata sha wahala gurin rainon ciki da haihuwarsa ba, amman bata gudu ta bar ko daya ba, har London da yake da lalura ma, wata kila saboda ta san yadda ake ji ne idan babu kowa na su a kusa da su, saboda ita sa dandana dacin haka, ita kadai sai irin mutanen da suka tashi a irin yanayinta suke iya fahimtar yarenta, amman dai abun da na sani Emily Jaruma ce, ma manta ban fada mata wannan ba"

Ya kai abincin a bakinsa ya tauna ya hade amman baya jin dandanonsa ko kadan, kawai dai yana ci ne saboda ya ranta ran Ummi.


TURHAN POV.

Ammy na tsaye balcony tana kallon Turhan da ya fito motar abokinsa Manir ya doso entrance cikin yanayin damuwa.

"Sannu Manir an gode Allah yayi albarka"

"Ameen sai da safe Ammy"

Yaja motar ya wuce Ammy ta juya ta shiga falon ta zauna kusa da danta.

"Ba wani labari ne?"

Ya dago jiki a sanyaye, murya kamar ba tasa ba.

"Babu, na yi report har gurin police, amman dai har yanzu ba ace an ganta ba, ni da manner mun zagaye rabin garin nan ba mu ganta ba, mun tafi har wata unguwa nemanta, muka kwatanta na nuna hotonta sai suka ce mana ta zo amman da dadewa kusan shekara bakwai da suka wuce, wai mahaukaciya ce sun fada mana irin rayuwar da ta yi a gurin da ciki, ina kyautata zaton bayan ta bar Sudan ne, saboda sunce tana tare da yaro"

"Wata kila da cikin Fatima ne, ta fada min ta zauna a unguwanin duk suna mata daukar mahaukaciya"

Turhan ya duba agogon falon dake nuna karfe 11pm ya sauke ajiyar zuciya.

"Ammy na cutar da yarinyar nan, na gode da baki bar ni sai da na nemo ta, sai dai yanzu ban san wane hali zata fada ba, a ina take?"

Ya soke kai kasa ya dafe cike da damuwa. Ammy ta kai hannu ta shafa kan danta.

"Alhamdulillah, ka gane gaskiya shi yafi komai kyau ai, na jidadin haka, kuma In Shaa Allahu zata dawo, uwa ai bata iya tafiya ta bar yaranta, komai zai daidaita"

"Ina fatan haka"

Ammy ta sumbance shi, tana jin kaunar danta sosai ga kuma jikarta dake dakinta tana bachi abun burgewa.

"Gobe zan bar garin nan da karfe 10am, saboda kiran da Abie yake min"

"Toh Allah ya kaika lafiya ya tsare"

"Amman ina son na tafi da Fatima Ammy"

Ammy ta janye hannunta a jikinsa.

"Aa, ba zan yarda ka sake tafiya da kowa ba, haka ka tafi da uwarta labari ya canja"

Ya kalleta.

"Wannan baya ne, Wallahi yanzu ba Emily ba ko dankwalinta na tafi da shi ba zan bari ya wulakanta ba, balle kuma Abunda ta haifa min"

"Aa ka barta anan dai, kai ma zaka fi jin karfin dawowa"

Baya son ya musa mata, dan haka ya amince ba dan ransa ya so ba ya mike tsaye yana sauke ajiyar zuciya ya haura sama, dakin Ammy ya fara shiga ya zauna bakin gadonta yana kallon Fatima dake ta bachi rumgume da teddy, ya matsa kusa da ita ya kai hannu yana shafa fuskarta, matar da ya wulakanta ya kaskantar ita ce yau ta ba shi farincikin da yake nema kuma wanda ba a siyarwa.

"Wata mahaukaciya? Mai ciki? Ana tunanin cikin an mata shi ne ko kuma asiri aka mata, wacan shagon ta yi zama lokacin ba ayi gina a gurin ba"

Haka yayi ta tuna yadda mutanen suka yi ta labarta masa Emily. Ya kai bakinsa ya sumbanci Fatima hawayensa ya zuba a kan fuskarta.
[7/25, 8:28/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


*

*? Khadeeja Candy*



FOLLOW ME ON =?G?
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

WATTPAD
https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy


Page 5?? 7??


Jirginsu na sauka mutumen dake kusa da ita ya kalleta ya ce

"Ki biyo ni zan miki ragora, Dr A-B ne yace a kula da ke"

Ta kalle shi sai, tun da ta zauna yake a gurin amman be ce mata komai ba sai a yanzu. Yana tashi ita ma ta tashi ta bi bayansa duk inda ya shiga tana biye da shi har suka isa gurin motar da aka kawo, sai ya bude mata baya ta shiga shi kuma ya shiga gaba ya shiga ya rufe aka ja motar, Emily dai na zaune shiru har suka isa unguwar manyan mutane, ba ka ganin komai sai gine gine daga hawa biyu sai uku sai ka tona zaka ga mai hawa daya.
Gaban wani katafaren gida direban motar ya tsaya yayi horn security ya bude masa gate, gida ne babba sosai mai dauke da gini mai kyau na burgewa ga shuke shuke ta ko'ina amman ko kadan hankalin Emily be kai can ba saboda tunanin yana wani gurin dabam, direban na fakawa aka bude gefen da take data dago kai sai ta yi arba da Dr AB fuskarta dauke da murmushi ya miko mata hannu.

'Haka rayuwa take tafiya da ni? Daga wannan sai wacan?'

T??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a tambayi kanta tana kallon hannunsa kamin ta mika masa nata hannun ta rika shi ta fito motar. Tsaya ta yi a gabansa yana ta kallon fuskarta zuwa cikin idonta, kallon karantar damuwarta ne yake, idonta ya nuna alamar bata samu bachi ba, fuskarta kuma na nuna alamar damuwa, sukuku kamar wanda aka yi ma mutuwa.

"How are you Emily"

Ta daga kafadunta ta tabe baki kadan kamar mai son fashewa da kuka.

"Na shiga damuwa, komai ya chabe min"

"Is okay"

Ya rika hannunta yaja ta tafiya mai nisa sannan suka isa entrance din shiga falon ya taka yana rike da ita ya tura kofar falon ya shiga yana janye da hannunta, falo ne babba mai dauke da kawa da abubuwan burgewa amman Emily bata kula komai ba, ita dai tana biye da shi har suka haura sama hawa na farko ya tura wani daki ya shiga da ita, da kansa ya zaunar da ita kan gadon dake dakin.

"Nan ne dakinki, akwai bandaki ki shiga ki yi wanka wardrobe tana cike da tufafi ki saka marar nauyi, za a kawo miki herbal tea ki sha, kamin ki ci abinci, zan tafi asibiti ana jirana daman saboda ke na dawo"

Ya mike tsaye ya dauke hannayensa daga kan kafadunsa.

"Na gode"

Ta furta, sai ya juyo ya kalleta cike da tausayi be ce komai ba ya fice daga dakin. Kwantawa ta yi akan gadon tana tunanin duk wani abu da ya faru da ita na farinciki wata rana da ta yi farinciki sai fa Emily ta tuna ta a ranar sai gata tana murmushi da hawaye, can kuma ta kai hannunta ta murza wuyan hannun tana tuna agogon da Aliyu ya bata ko a ina ta jefar da shi bata sani ba. Ta mike tsaye ta share hawayenta ta shiga bandakin ta tube tufafin jikinta ta kunna shower ta zauna a kasa ruwan yana dukanta ta rufe ido tana maida numfashi a hankali. Ta dade a haka sannan ta yi wanka har kanta sai da ta wanke sosai sannan ta fito daure da tawul ta bude wardrobe din ta cire doguwar riga mai yalwa marar nauyi ta saka.

Wata Cristian maid ce ta shigo sanye da short skirt da bakar riga ta kawo mata tea, daga baya kuma ta shigo mata da abinci da ruwa. Emily ta dauki tea ta shanye ta zauna bakin gadon tana jin ina ma bata jefar da wayarta ba da ta kalli hoton yarta ko zata ji sanyi. Bata ankaro ba ta fara jin bachi sai ta kwanta tana lumshe ido da hamma kamin kace me bachi yayi gaba da ita.
Bachi ta yi sosai na tsawon awa hudu ko da ta farka yamma ta yi sosai. Tashi ta yi zaune tana murza ido madadin ciwon kan ya sauka sai ta ji ya karu, ta sauko da kafafuwanta kasa kenan AB ya turo kofar dakin ya shigo rike da leda, ya zauna kusa da ita.

"How are you feeling now?"

"Kaina yana ciwo sosai"

"Yeah saboda kin kwanta da tunani ne, kuma bachin be isheki yadda ya kamata ba, amman ga magani zaki ji sauki"

Ya bude ya dauki wani sabon Water bottle da aka kawo mata ta bude ta dauki cup din ya zuba ruwa ya balla maganin ya mika mata ta karba ta sha tare da ruwa, sannan ya bude sabon abincin da aka kawo mata tana bachi ya zuba mata kadan ta sauka kasa ta zauna ta ci, bayan ta gama ya sake bata wani maganin.

"Ki wake shiga ki yi wanka, amman da ruwan normal ba mai dumi ba kuma ba mai sanyi ba, za a sake kawo tea anjima ki sha, zuwa gobe da safe idan kin huta stressed din ya rage sai ki gaisa da Momy"

Ta daga mishi kai, ya mike tsaye ya kunna tv dake dakin ya kama channel din dake nuna abubuwan ban dariya, ya rage sanyin ac sannan ya kalleta ya sakar mata murmushi ya fice, ta bishi da kallo tana mamakin yanzu shi baya cikin wata damuwa shi sam be san wani abu damuwa ko rashi ba, ba kamar ita ba dake da tarin matsaloli. Yadda ya fada mata haka ta yi bayan ta gama ta zauna tana kallon tv sama sama bayan magari aka kawo mata fruit sai madara da ruwa ta ci fruit din rabin plate sannan da shanye madarar da bata da yawa, after like one awa aka shigo mata da tea ta shanye, nan ma babu jimawa ta yi bachi.

Sai tara ya shigo dakin ya kashe tv ya lullube ta ya rage hasken dakin sannan ya fita. Washe gari kamin kowa ya shigo dakin shi ya fara shigowa sanye da kayan bachi, shigowar shi ce ta tasheta daga bachi ta farka.

"Good Morning"

Ya fada da murmushi a fuskarsa sai ta murza idon ta tashi zaune. Ya zauna kusa da ita.

"How are you feeling now?"

"Much better"

"Kan yana ciwo?"

Ta girgiza kai.

"Good, me kike so for breakfast?"

"wannan tea din ina son na yi bachi"

"Zaki yi bachi, ana bin ka'ida ne ba a son bachin yayi yawa ne, kina cin kwai? Domin shi ne best abun da nake son ci da safe kwai sai tea"

Ta daga kafadunta.

"Okay, za akawo miki amman yanzu ki fara shan maganin nan"

Ya dauko maganin ya bata kamar dai jiya ta karba ta sha.

"idan kin karya ki sha irin wanda na baki jiya, zan fita aiki kin san bama samun zama, ina son ko da zan dawo na same ki kin shirya sai ki haura sama ki gaisa da Momy"

Ta daga mishi kai.

"Na gode"

When ever she says ta gode sai ya ji zuciyarsa ta tsinke. Ita kuma tana jin ita din ba dole ne a kula da ita ba, domin mahaifiyar data haife ta ma ta jefar da ita, duk wanda zai ganta ya taimaka mata ya cancanci godiya a gareta.

"Idan na dawo zamu gaishe da Momy karki manta"

Ta daga mishi kai, sai ya ja kumatunta yana murmushi ya mike tsaye ya fice. Be dawo ba sai after ta yi lunch sannan ya shigo da ice cream da chocolate ya kawo mata, sai da ta ci sannan ya riko hannunta suka fito, ta yi zaton kasa za su sauka sai ta ga sun haura hawa na biyu a nan ma wata duniyar ce mai zaman kanta, wani apartment ne guda mai dauke da komai daya yafi na kasa kyau da tsari, banbancin falon kasa ya fi fadi da yalwa ma sama kuma ba wani mai girma ne sosai ba, falo ne har biyu ga kuma dakuna da suke cikin falon, ta cikin falon akwai view din falon kasa da kuma gefe dayan gefen kuma harabar gidan ce.

Ko'ina na view din glass ne da manyan curtains da aka sako aka bude su da wadi sosai iska na kadawa, dama da falon kuma wani center ce mai dauke da books ga chairs na zama, dayan gefen kuma dinning area ne an yi shi sama kadan sai ka tara stairs biyar sannan ka hau guri. Ga wani katon Tv mai kamar majigi, ta ko'ina sanyi ke bugowa, ya zaunar da ita kan kujera sannan ya shiga one of the bedrooms da suke falon babu jimawa ya fito tare da wata mace da gani daya Emily ta yi mata ta gane wacece.

"Barka da zuwa gidanmu"

Emily ta mike tsaye, matar ma kallon Emily take har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login