Showing 225001 words to 228000 words out of 253142 words

Chapter 76 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18403

share hawayenta. Sun kusa rabin awa a dakin har aka fara kiran Dr A-B saboda Alhaji Bulama zai bar gari kuma tare za su tafi. Ya mike tsaye kenan sai ga Aliyu ya turo kofar dakin ya shigo da sallama duk suka amsa masa ban da Emily da kanta yake kasa, tana ta lissafin rayuwa. Idan Aliyu ya juya mata baya shi kan ita kam ta gama rayuwa kuma makiya za su mata dariya. Dr A-B ya kama hannun Emily ya mikar da ita tsaye ya kama hannunta ya kama hannun Aliyu ya saka hannunta cikin na Aliyu.

"Ga amana an baka, ta wahala ka sani, muna fatan daga kanka ta dace, a gaban iyayenmu ta zabe ka ta bar wanda shi ya so ya aureta a yau, dan Allah karka bata kunya. Sannan zan tunatar maka a yanzu Emily tana da uwa, dan'uwa da kuma uban da zata sani nan gaba kadan, karka kuskura ka ce zaka taba ta. Ta fada kai take so kuma na tsaya har yanzu ne saboda na tabbatar da cikar burinta, na sauke nawa nauyin, ni zan tafi ina muku addu'ar Allah ya baku zaman lafiya na bar ku lafiya"

Ya dauke hannunsa daga kan na su ya nufi kofa ya fice daga dakin, Mama Baraka ta mike tsaye ta bi bayansa. Aliyu ya kama hannaye Emily duka biyu ya rike yana kallon yadda take hawaye.

"Na san nisar tafiyar da kika yi, a hanya kin taka kaya, kin tsallake rame, kin yi dingishi kin karaya, na san zafin wutar data kona ki, na san buri da mafarkinki, ka karanci zuciyarki na san kudurinki, kin yi rayuwar kadaici. A yau ni da ke mun zama iyali, zan zame miki mijin da baki taba tsammanin samu ba, zan cika duniyarki da farinciki har sai kin manta da damuwarki, kuka ya kare hawaye, ba zaki sake zubar da hawaye akan Wa namiji ba, fargaba ba zata sake kusantarki ba, kin zama jinina, farincikina, kaunarki ce rayuwarta, ina mai tabbatar miki baki yi kuskuren zabe ba"

Ya sake hannunta ya matsa baya kadan ya zube kasan guiwoyinsa ya hade hayyansa.

"Na gode da kika yarda da cewar zan iya! Na gode da kika ba ni wannan damar, na gode da kika yarda a dora min wannan nauyin na gode da kika yarda na zama silar warakar duk wani ciwo naki, na gode da kika so ni, na gode da kika aminta da ni, na gode da kika aure ni, na gode Saruniyar mata, mace mai hakuri da kyakkyawar zuciya, na gode Ayusher na gode... Na gode... Na gode na gode..."

Ta kasa komai wasu hawaye na dabam suna sauko mata, sai ta lumshe ido tana maida numfashi. Aliyu ya mike tsaye ya matsa daf da ita har yana jin fitar numfashinta.

"Bude idonki ki kalli mijinki, mijin da be san komai sai ?aunarki, mijin da samunki ya zama babbar kyauta da rahama a gareshi"

Ta bude idon ta kalleshi ido cikin ido daf da daf gab da gab das da das...

"Ayusher ina ?aunarki, ke tawa ce ni ne ABOKIN RAYUWARKI"

Ya rada mata cikin wata murya da be san yana da ita ba, furucin yana fitowa ne har can kasan kasan kogon zuciyarsa. Ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta. Sannan ya ware hannayenta.

"Ina tsarin Allah daga shedan la'ananen, duk wani abun kin, ko na cutarwa da zai shiga tsakanina dake, ina neman tsari Allah daga duk wani abun da zai saka na bata miki rai, kuma ina rokon duk wani alheri da zai kara mana zaman lafiya da kaunarnan junanmu, ina neman rahamar Allah a duk inda za mu saka gaba, ina neman rahama daga Ubangijin da shi ya hada mu, ya kawo mu a nan kuma ya nuna mana wannan ranar mai muhimmanci a rayuwarmu, Allah na gode da wannan kyauta da ka yi mini, da sunan Allah mai rahama mai jinkai"

Ya rumgumeta halal hug ya saka a kirjinsa, wani irin rumguma yayi mata sosai kamar za a kwace masa ita, ya yi squeezing dinta har sai da abayar dake jikinta ta dage, yayi sama da ita kafafuwanta suka dage. Emily ta yi shiru..... Hawayen suka yanke mata, numfashinta na fita a hankali yana shiga da kamsh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?in turaren jikin mijinta, ba a taba rumgumarta ta ji damuwarta da fargaba sun gushe mata ba sai a yau.
Babu wanda ya taba rumgumarta ta ji hankalinta ya kwanta ya samu sukuni ba irin Aliyu.

Yanzu ta san me ta rasa, sai a yanzu ta san what truly halal hug means, ka so a so ka so na hakika dabam yake, auren wanda yake kaunarka kaunar ta gaskiya ta hakika a dabam take, son wanda yake sonka so na hakika dabam yake, lallai akwai wata irin rahama da farinciki, jindadi da cikar buri a auren soyayya. Ranar yau kadai ya nuna mata tana da muhimmanci, wunin yau kadai ya shafe duk wani fargaba da take, ta share duk wata damuwa da ta fuskanta.

Lallai macen da miji yake so Sarauniya ce, a yau Aliyu ya furta mata kalaman da babu wanda ya taba yi mata su a ranar aurenta, shi da kanshi yake gode mata, a yau ta shaida soyayyar gaskiya marar algussu. Aliyu be kalleta a matsayin mace da ta taba aure biyu ba, be kalleta a matsayin ta haihuwa biyu ba, ya kalleta a matsayin macen da yake so, lallai mai son be ganin ramarka, a yau ta dandanin miye auren so da masoyin gaskiya.

"Meyasa ban hadu da kai ba tuntuni?"

Ta tambaya tana murza kanta a kirjinsa kamar zata tsaga kirjinsa ta shige cikin zuciyarsa. Sai ya bata amsa cikin rada shi ma idonsa a lumshe cike da kwalla, auren soyayya suka yi da Kameela amman ko ita bata nuna masa kaunar haka a ranar aurensu ba kamar Emily.

"Ita ce tambayar da na dade ina yi ma kaddara, miyasa bata hada ni da ke, tun farkon da ta bude miki shafi"

"Aliyu ina ?aunarka"

Ya bude ido ya sauketa ya rika fuskarta yana kallon cikin kwayar idonta.

"Duk wata kauna ta furuci ko ta aiki, ko wanda take zaune a zukanta masoya, Ayusher na fi kauna, kaunarki, na fi numfashinki son kasancewa da ke, ni da ke ABOKAN RAYUWA ne, sai da mutuwa"

Ta yi sauke wani sanyayen numfashi ya lumshe ido tana murmushi.

 Madalla da kasancewarka cikin rayuwata, ka zamo min tauraro mai haske. Madallah da ABOKIN RAYUWA irinka"

Ya kai goshinsa ya hade da nata, hancinsa a saman nata, ya saka yatsunsa na dama cikin nata, na hagu ma haka suka tsarkafe yan yatsunsu cikin juna.

"Abokiyar tafiyata, har tsawon rayuwa, Madalla da ABOKIYAR RAYUWA irinki"

Sun dade a haka sannan ya sake ta ya matsa baya. Ta kalleshi tana murmushi a yau ta san yadda rumgumar masoyi take mantar da damuwa, ya sameta tana kuka ya maye mata gurbin hakan da murmushi.

"Idan akwai abun da kike son aikatawa, ni halalinki ne just do it"

Ta taka one step forward kamar ya san manufarta sai ya maida hannayensa baya ya duko da fuskansa ta sumbanci gefen fuskansa da sauri, ta juya baya tana jin kunya. Murmushin dake fuskarsa ya fadada har ya bayyana hakoransa. Ya nufi kofar fita har ya kusa isa sai kuma ya yanke tafiyar ya juyo ya dawo gurin masoyiyyarsa ya rumgumeta ta baya, sai kuma ya juyo da ita, da sauri ta saka hannayensa ta rufe fuskarta. Hannayen dake fuskarta ya sumbanta ya goga fuskarsa yana dariya sannan ya saketa ya fice dakin ya rufe mata kofa yana jin kamar kar ya tafi ya barta.







TURHAN POV.

A lokacin da ya fito daga falon na Daddy waje ya tsaya jikin motar da suka zo, ya ji duniyar kamar tana juya masa, ko da wasa be yi tsammanin Emily zata juya masa baya har haba ba, kuma a gaban iyayensa. Dadin dadawa kuma ta furta sunan wanda take kaunar a gabansa cikin kunnensa.
Miya yayi ma Aliyu? Ita ce tambayar data fara zuwa masa a rai. Miyasa ya dauki bata masa ta wannan hanyar? Wace irin kiyayya Emily take masa har haka? Be samu amsoshin tambayayinsa ba Sarkin ya fito, kamin ya shiga motarsa Alhaji Bulama ya fito tare da Mahaifin Kameela, shi dai ya san ya shiga mota, yadda aka yi suka kama hanya har suka isa gidansu Ammy shi ne abun da be san yadda aka yi ba.

Ya zauna cikin falon yana sauraren yadda Alhaji Bulama yake labarta mata abubuwan da suka faru, yana jin mahaifinsa yana magana da ita amman be fahimce me suke magana kai ba, a yau ne karo na farko da yaren larabci ya subuce masa a kai.

"Aliyu... Aliyu... Aliyu..."

Furucin Emily nata dawo masa, be san yaushe aka mahaifinsa ya fita ya dai ji Alhaji Bulama ya dafa shi yana fadar maganar da be gane ba, yana zaune a falon kowa ya fice be san an yi ba sai da Ammy ta girgiza shi.

"Turhan nan?"

"Ammy me na yi ma Aliyu? Ina ta kokarin tariyo rayuwarmu ta baya zaman da muka yi, me na masa? Ashe ko ba ni da rai bancanci yayi min hallaci ba?"

Ammy dake tsaye ta zauna idonta cike da kwalla.

"Ka yi hakuri Turhan, ba a taba cin amana aka yi nasara ba, muna nan da kai hakki zai bayyana"

"Miyasa ita ma ba zata fahimce ni ba? Ko. Kalaman ne nawa ba su kai ba? Wallahi ina sonta ina kaunarta Ammy, kuma ba zan sake cutar da ita ba, Wallahi na yi alkawari ba zata sake zubar da hawaye akaina ba"

Hawaye ya sauko ma Ammy, ko wace uwa bata son ganin danta cikin damuwa balle kuma Ammy da Turhan kadai take da shi, bata tana ganin tsananin damuwa a tsare da shi data gusar masa da hankali ba irin yau.

"Tashi ka tafi ka yi sallah"

Be haura sama ba sai ya fice falon a masallacin yayi alwala yayi sallah, suna fitowa masallacin mahaifinsa ya kira shi akan ya shirya, jirginsu zai tashi karfe 5pm, daga shi sai DR A-B ake jira saboda Dr A-B yace ba zai bar garin ba sai an daura auren Emily da Aliyu kuma karfe 4:30pm za a daura. A nan ya ji wani labari da yafi furta sunan Aliyu azaba a zuciyarsa. Daker ya iya kawo kansa falon Ammy. Yana shigowa ya nufi agogon dakin ya tsaya yana kallo yadda dakika take juyawa ta zama minti. Jikinsa yayi ma kafafuwansa nauyi yana ta lilo jiri na dibansa kamar zai fadi.

Yana ta kallon agogon da second din ke dis da bugawar zuciyarsa yana jin wani dubu na haye masa kai. Har agogon ya nuna karfe 4:30pm. Turhan ya rufe ido, Ammy dake tsaye bayansa tana kallonsa ta karaso ta rike Wanta tana jansa baya a hankali har ya zauna kan kujerar dinning.

"Ammy a yau na san rashi, na san miye kiyayya, na kuma san miye soyayya, da na sani ?eya, tsanar da Aisha take min ta kai har ta auri abokina ta bar ni? Shin ita bata tafiya ne? Ammy ina son yarinyar nan miyasa kika cilasta na sake ta? Ammy ma rasa Aisha, uwar ?ata na rasa ta, cikon farincikina na rasa shi a yau....!"

Hawaye ne masu zafi suke sauko masa, ko Ammy sai da tsoro da tausayin Wanta suka kamata, domin bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na gasawa da rudani irin wannan ba.

" Dady?"

Ya ji muryar yarsa da sai a yanzu ta filo daga dakinta ta sauko kasa duk abun da ake bata sani ba. Turhan ya saka hannayensa biyu ya dafe kansa baya son yarsa ta ga hawayensa. Fatima ta zo da gudu ta rumgume shi.

"I miss you... Dady ka dawo? Ina Momy kace tare za ku zo ba?"

"Momy ki ta zabi Aliyu Fatima, ta barki ke da Dady, Momy ki ta auri Aliyu bata auri Dady ki ba, tace Aliyu take so ba Dady ki ba"

Ammy ta fada mata tana hawayen tausayin danta gaba daya ta rikice. Cikin tsoro Fatima ta bude hannayen Turhan babu hawaye a fuskarsa amman suna kwance a cikin idonsa, sai kawai ta fashe da kuka sosai ta rumgume. Ya dauke ta ta dora saman jikinsa ya hade duk wani abu da yake ji ya fara rarrashinta. Wayarsa ta yi kara alamar shigowa sako, ya ciro wayar ya duba Dr A-B ne ya aiko masa da sako cewar za su tafi shi ya tsaya sai next week, ya aje wayar ya kalli mahaifiyarsa sai ya sakar mata murmushin karfin hali.
[8/25, 8:41/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*



Page 7?? 1??


KAMEELA POV.

Sosai ta natsu tana sauraren labarin da Hajiya take bata kamar yadda Alhajin ya fada mata yadda abubuwan suka faru.

"Wai kawai sai ta bude baki tace Aliyu... Na ce daman dai hadin baki aka yi da uwarko?"

Kameela ta kai tsaye.

"Hajiya dan Allah karku bari a yi auren nan, Wallahi ina son mijina, kuma na san yana so na, kawai makircin yarinyar nan da uwarta"

"Zancen banza, aure ai tuni aka daura, babanku yace mai gidansa da dansa ba su bar garin nan ba sai da aka daura auren, wai da la'asar sai kace auren kauye"

Anty Shafa ta karba mata.

"Auren kauye ai yafi na wannan arniyar daraja, kuma shegiya ce shiyasa suka daura auren kar ya subuce, dadin dadawa kuma Mama Baraka ai zata iya yin komai saboda ace yarta ta auri Aliyu kin ga ai ta yi gasa da ke"

Kameela ta dora hannu a kai.

"Na shiga uku, Innalillahi... Hajiya ina son mijina ina son Aliyu"

Hajiya ta daka mata tsawa.

"Ke dalla gafara can mahaukaciya, Aliyu autan maza ne halam? Tun da kika aure shi wani farinciki kika samu? Kuma ke da kike ikirarin ba zaki zauna da mai mata ba? To yanzu ai yayi aure, kuma shi be damu dake ba sai ke? Ko kuma mu mahaukata ne da za mu bar ki yi kishi da marar uba? Yarinyar da bata kai rabin matsayinki ba? Daman can ba son auren nan muke ba, shi kuma be shirya rike amana ba, aure be jimawa daga dawowa haihuwa an fara samun matsala"

Ta fashe da kuka tana jin duniyar ta juye mata mijin da take so ya juya mata baya, dakunsa da take kuma ya kare a yau saboda yayi auri abun da bata taba zato ba, gashi iyayenta sun kasa fahimtarta.

"Ki duba ba fa Hajiya, ko irin ya dawo yana bada hakuri din nan be yi ba, gaba daya ya nuna shi daman ba sonta yake ba, kawai iyayensa da shi sun shirya wulakanta zuri'armu ne, idan har yana sonki kuma yayi nadama ai kamata yayi ya kawo kansa yana kuka yana faduwa kasa yana tuba, amman ba ko da ya, sai ma tafiya ya auri marar asali ko dai ya manta waye shi ne? Kuma iyayenwai suka bar shi? Tab"

Anty Shafa ta fada tana tabe baki da jinjina lamarin. Kameela ta tashi ta bar su a falon, dakinta ta shige ta kwanta kasa tana kuka kamar an yi mata mutuwa, bata taba jin zafin azabar kishi da bakincikinsa ba irin yau. Aliyunta ne dai yayi aure? Ta rarraba ta isa bakin gadonta ta kai hannu zata dauki wayarta kuka ya ci karfinta.

" Aliyu ka yi aure? Ina alkawarin da ka yi min Aliyu? Ina soyayyar da na nuna maka?"

Ta kai hannu daker ta dauki wayar ta da sabon layin da take aika masa sako ta gwada kiransa tana kuka, ringing daya ya daga, ba dan be san mai kiran ba sai dan ya shiryawa kiran.

"Sallamu Alaikum"

"Aliyu ina alkawarin da ka yi min? Cewar ba zaka min kishiya ba?"

"Na cika miki, tun da ban miki kishiya da igiyar aurena ba"

"Ina ladar soyayyar da na nuna maka?"

"Na miki sakamako iya yadda zan iya, fadi tashi a tare muka yi har iyaye suka amince muka yi aure, yanayin rayuwar aurenki da zafin kishinki, rashin nazari kamin yanke hukunci sune abubuwan da suka hana zaman aurenmu, kuma ba zan miki Karya ba, kowane namiji yana son kwanciyar hankali da farinciki a gidansa, iyakar hakkinki na baki, har wanda ba naki ba na baki, kin wuce gona da iri Kameela, idan ma na ce zan cigaba da zama dake ba ni da kwanciyar hankali, kuma mahaifiyarta ba zata yarda ba, gashi kuma iyayenki ba so na suke ba"

"Munafiki azzalumi maci amana, can da baka ganin komai sai a yanzu da ka auri karuwa? Yar titi marar uba? Yar zina? Matar da aka haifa na da aure ba? Ai baka yi aure ba Aliyu tun da baka auro yar gidan mutumcin ba"

"Zaki iya zagina ki ci mutumci, amman ban da matata, dan an haife ta ba da aure ba, miye laifinta? Ko kina tunanin dan'adam yana iya tsallake kaddara ce ne? Ko daga sama ta fado ina sonta a haka, dan haka karki sake fadin wata magana marar dadi akan matata, kamar yadda ban yarda a taba mutumci lokacin da nake aurenki ba, ba zan yarda a taba mutumcinta ba"

Ya yanke wayar, Kameela ta ji kamar ta haukace tsabar bakinciki na jin kalaman Aliyu. A daren da bakinciki ta kwana tunani be barta ta runtse ido da sunan bachi ba, ganin abun take kamar mafarki, wai Aliyu yayi aure, a tunanin zai gama kewaye kewayensa ne ya dawo mata. Idan ta tuna yadda take rayuwa da mu'alama da mijinta, ta hango yanzu Emily ce a makwafinta, sai ta ji kamar zata haukace, wani karin bakin cikin ma Emily daga tsatson Mama Baraka take ba, da ace daga wani gurin ne dabam wata kila zata fin saukin kishi.

Yanzu kenan Emily ta yi nasa? Bayan ta shiga tsakaninta da mijinta tun a PH gashi kuma ta aureshi, babbar matsalar ta ma babu mai rataya kishin ita kadai take yakin, tun da yan'uwanta sun gagara fahimtarta. Haushinta da Hajiya ta ji ya saka bata damu ta cilasta mata fitowa ta ci abincin ba, a ganinta akwai mazan da suka fi Aliyu komai nesa ba kusa ba, amman tana wahalar da kanta ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login