Showing 111001 words to 114000 words out of 253142 words

Chapter 38 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18412

kika masa ne, ni zan kira shi, zan yi magana da shi duk abun da za ayi karki biye kanenki da yayyenki domin su ba son Aliyu suke ba, ke kuma kina son mijinki, duk yadda za'ayi ki daina bari ana jin kanku, ita mace gona ce ga namiji ka yi gina ka rufe duk abun da kake so babu wanda ya sai idan ta fitar, shi kuma namiji sutura ne ga mace babu mai ganin tsiraicinta sai idan ta bayyana ko ya bayyana, karki nuna masa ma kin fadi abun da ke tsakaninku, kina son komawa dakin mijinki?"

Ta daga kai.

"Ina son Aliyu sosai Wallahi"

"Indai har kina sonshi to ki shirya fuskantar duk wani kalubale akansa, ni zan kira shi da kaina zan yi magana ta fahimta daga ni sai shi, idan ya kama har mahaifiyarsa zan yi magana da ita, amman bana son ki bar Hajiya ta sani"

"Ba zan fada mata ba"

"Yauwa yanzu na gamsu kina son mijinki, saka min number sa a nan zan kira shi mu yi magana ba zan ma nuna masa kin san na kira ba"

Mama Baraka ta mika mata wayarta Kameela ta karba ta saka mata number Aliyu.

"Amman fa sai kin taya ni yakin, domin idan ya zo ya nuna yana son ki koma toh ki nuna kina son mijinki kuma kina son komawa idan ba haka ba yan dakinku za su kara bata abun ne kawai"

"Na fahimta Mama Baraka"

Na fada tana duba dp Emily dake whatsapp ta nunawa Mama Baraka hoton Emily saboda ta ji dadin shawara da karfafa guiwar da ta yi mata.

"Kin ga hoton yar iskar yarinyar nan"

Mama Baraka ta yi saving number Aliyu sannan ta karbi wayar Kameela tana duba hoton.

"Tsohuwar Matar Abokinsa ce fa Turhan har da ya a tsakanin su yanzu haka Turhan din nemanta yake sosai, wai mahaifiyarsa ta yi fushi da shi saboda ita, ni ban gamsu ba wata kila dai ta gudu masa da ya ne, ko da yake Aliyu yace wai be san yana da yar ba, kuma ban san miyasa ya ki ya fada masa ya ganta ba, wata kila saboda sonta yake ko? Idan ba haka ba ai zai fada masa, wata kila kuma ya boye min ne, amman ko minene dai sai na bincika, yanzu ma bake jin karfin guiwar komawa dakin mijina"

Duk dogon rattaba zancen da Kameela take Mama Barakat bata ji ko daya ba, gaba daya hankalinta ya tafi gurin kallon hoton Emily kamar mai son tantance wani abu.

"Ya sunanta"

"Emily amman Aisha ake ce mata"

"Tana PH ne tare da shi?"

"Eh yanzu tana PH amman yar Lagos ce a wani gidan marayu ta tashi a can ta girma aka ce, kamin ta auri Turhan din ko a ina suka hadu ma Oho"

Mama Baraka ta hade abu da karfi yanayinta gaba daya ya canja, ta kurawa hoton ido kai kace ranar ta fara ganin mutane.

"Bata fiki da komai ba, hasken fata kawai zata nuna miki, wannan ai bata kai ta kwace miki miji ba, karki daga hankalinki akanta, kuma ita ai ba musulma bace da alama ga Cross a wuyanta"

Tana maganar idonta ya cika da kwalla sai dai bata bar Kameela ta gani ba.

"Eh kafira ce"

"Wata kila ma duk abun da kike zato ba shi ba ne, Aliyu da hankalinsa ai ba zai yarda ya rabi kafira ba, zan yi magana da shi na san zai saurare ki kwantar da hankali"

Ta mika mata wayar.

"Tashi ki koma bangarenku kar ayi zaton wani abun muka shirya ma"

"Tohm"

Ta mike tsaye ta fice daga falon tana jin bakinciki dake zuciyarta yana raguwa saboda shawarar da Mama Barakat ta bata da kuma matakin da tace zata dauka, a yanzu kuma tsoron ta daya kar ya fada mata ko mahaifinta cewar ta saka masa guba a abinci, idan kuma har Ummi taji ta san auren ta da Aliyu ya kare har abada, ta san bata kyauta ba, be kamata ta aikata hakan ba kuma ta yi kuskure, da yanzu ta kashe shi wa gari ya waya? Ai ko mahaifiyarsa ba zata fita jin zafin mutuwarsa ba, haka dai ta yi ta sake sakenta har ta shiga bangarensu ta shige dakinta ta kama hoton Aliyu tana kallo da wasu videos da suka yi a tare tana ta jin kewar mijinta da kuma nadamar abun da ta aikata domin ta fi kowa sanin Aliyu yana sonta, ta san ba dan yana sonta ba wata kila da sakinta zai yi gaba daya ba zai tsaya cewa za a duba kwakwalwarta ba ko ya turata gidansu.



*** *** ***

Mama Barakat ta bi bayan Kameela da kallo har ta fice fuska a raunace, ta yunkura zata tashi kafarta ta hagu ta yi mata nauyi sosai ta gagara daga kafar, zuciyarta ma ta yi nauyi sosai kamar an dora mata dutse.

"Aleeya Aleeya Aleeya... Samira Samira..."

Ta kwalawa yaranta kira Sameera ta sauko da saurinta tana dariya hannunta rike da waya da alama wani abun take kallo a wayar.

"Mama gani zuwa, Aleeya bachi take"

Mama Baraka ta daga kai tana kallonta har ta sauko.

"Rika ni ina son zan shiga dakina na"

Ta fada mata da yaren yarbanci daman da yarenta take magana da yaranta idan su kadai ne a gidan wannan ya saka suke jin yaren sosai. Sameera ta yi hanzarin aje wayarta tana kallon Mama Baraka.

"Mama Lafiya?"

"Kafata ce ta rike, ina son na tashi na kasa"

Sameera ta rika ta cikin karfin hali domin bata iya dagata gaba daya, Mama Baraka mace ce mai jiki, ta mike tsaye daker ta cije baki ta taka dayar kafar dayan kuma ta daga ta, da taimako Sameera suka haura sama suka shiga dakinta Sameera ta dora ta kan gadonta.

"Mama ko asibiti za mu je?"

"Aa zai saki, ai bata taba min haka ba sai yanzu, tafi dakinku zan kwana na huta"

"Okay"

Ta fice daga dakin, Mama Baraka ta kwanta saman gadon ta yi ruf da ciki ta danne zuciyarta take mata nauyi ta lumshe ido tana maida numfashi a hankali.
[6/16, 2:18/ PM] null: https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_writing




*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 3?? 5??


Ta hade yawun bakinta tana kallon agogon da Aliyu ya bata.

***? ? ? ? ***.? ? ? ? ***.

"Matar da na faWa gidanta neman taimako, har aka ba ni abinci ita ce mahaifiyar Turhan, a lokacin da na bashi shinkafa sai ya dauke numfashi, hankalina ya tashi sosai na yi zaton London ya mutu a wacan lokacin a take na fara girgiza shi ina ihu, matashiyar yarinyar da ta kawo min shimkafar ta fito da sauri tana tambayar lafiya, ya mutu shimkafa na ba shi sai ya dauke numfashi, na shiga uku na mutu ba ni da kowa sai shi. Shi ne abun da nake ta fada ina hargowa, sai ga Hajiyar ta fito tana tambayar me ya faru? Bana iya amsawa sai sambatu nake ina ihu, sai tace a kira direba ta shiga da kanta ta dauko mayafinta ta karbi Yaron ta shiga mota na shiga direban yaja mu zuwa wata babbar asibiti, muka zuwa aka karbi Ibrahim suka bude nasa file suka masa duk abun da ya kamata, likitar data karbe shi mace ce a take ta rufe ni da fada a wane dalili zaki ba shi shimkafa jariri kamar wannan, baki da hankali?

"Ba ni da ruwan nono ne kuma ba ni da wani abun ba shi"

"idan baki da abun bashi sai ki bashi abinci yaushe kika taba ganin an bawa jariri abinci? Haka kika ga ana rainon jarirai"

Na girgiza mata kai ina hawaye.

"Ban san yadda ake ba, ba a taba haihuwa a gabana ba, ba a taba rainon jariri a gabana ba"

Na bata amsa, sai Hajiyar ta dube ni.

"Daga wace duniyar kike?"

"A gidan marayu na taso, ban san duka wadannan abubuwa ba"

Na durkusa kasa ina mata godiya

"Na gode Hajiya na gode"

Sai ta rika ni ta mikar da ni tsaye.

"Sunana Ammy karki damu ki kula dai ko ruwa karki sake ba shi"

"Amman idan be ci komai ba ai zai iya mutuwa ko?"

"Za a kawo abincin da zakiba shi, yanzu zaki zauna ki yi jinyarsa har zuwa lokacin da za su sallame shi, akwai wanda kika sani nan?"

Na girgiza mata kai.

"Ban san kowa ba"

"Labarin yana da tsaye kuma idan na fada miki ba lallai ki yarda ba"

"Zan yarda, saboda na yarda Ubangijina ba zai bari a cutar da ni ba, amman tun da kin ce labarin yana da tsayi ki aje har zuwa lokacin da za mu samu zama"

Na amsa mata da tohm sai ta tafi tare da likitar aka bar ni a gurin, can kuma sai ga likitar ta dawo tace na tafi Ammy tana jirana gurin mota wai zan bita mu koma gida saboda jariri zai zauna a hannunsu ne har ya samu sauki, zuciyata bata gamsu da haka ba dan haka na ki yarda saboda ina tunanin kamar sace min yaro suke son yi, ganin haka ya saka dole aka bar ni a asibiti, Ammy tasa aka kawo min abun shimfida da abinci, aka kawo madara ta jarirai ana bawa yaron, kullum za a kawo min abinci, amman bana iya ci saboda hankalina yana gurin yarona, aka kwana biyu sai Ammy ta dawo duba ni a lokacin ne take tambayata ko na san yarona yana da wata rashin lafiya nace aa, sai tace min likitoci sun fada mata yarona yana da sickle, ban ma fahimci ciwon ba sai da ta yi min bayanin cewar jinina da jinin mahaifin yaron ne ya zo daya, tace min kar na damu zata dauki nauyin maganin yaron, haka kuwa aka yi naira biyar ban taba kashewa ba a tsawon zaman da na yi na asibiti na wata daya, a tsawon watan da na yi asibitin nono be kawo ba saboda bana iya cin abincin kirki kullum cikin tunanin butulci da Khaleefa yayi min da kuma makomar yarona, ban san ina da hawan jini ba sai a lokacin kuma? ashe idan mace ta haihu wanka ake mata da ruwan zafi ko kuma a bata magani ban sani ba hakan ya saka na yi ta kumbura, ina jin akwai canji a jikina amman saboda babu mai kula da ni ban damu da lafiyata ba, har sai da Ammy ta same ni ta tambaye ni ina da wani ciwo ne da yake saka ni kumbura haka domin na zama wata babba uwar mata, nace mata aa sai idan abun ya same ni ban sani ba, sai saka aka bude min file aka bincika ni, a nan aka gane hawan jinin da na samu da cikin dana be sauka ba, kuma ba a gasa min jiki ba shiyasa nake ta wannan ciwon. Ni ma gadon suka ba ni ana kula da ni, a tsawon wata daya da na kara a asibitin Ammy ce take kula da ni ni da dana, ta saka mai aikinta tana jinyata har na samu lafiya amman jiki be sauka ba.

Da aka sallamo ni sai na amince na dawo na gidanta na bar London a asibitin, ta ba ni daki daya a cikin dakunan da suke cikin gidanta kuma suke kusa da dakinta, daman tun ina asibiti ta kawo min tufafi sai ta kara min wasu tace idan ina son abinci na sauka na ci kuma na sake jiki kamar gidana. Na jidadi ta karammani a lokacin ba tare da sanin wacece ni ko daga ina nake fito ba. Kwana biyu da dawowata aka sallamo London sai aka dawo da sh????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? i gida, sai ta siya masa tufafi kusan kala goma sha biyu bayan pampers da madara da ta karo ta siya masa gadon yara da tawul, mai aikinta take masa wanka ta goya shi wani lokacin kuma ita da kanta zata dauke shi ya wuni a hannunta.

A haka na kwashe wata uku a gidanta, kuma a tsawon lokacin nan bata taba tambayar labarina ba, bata tana nuna min banbanci ba, idan ta ga ina ja baya gurin shiga lamuran gidan sai ta rufe ni da fada, wai na kasa sakin jiki, ita ta lura da wani bangare na ibada ta daya kamata na gyara sai ta fara koya min a lokacin take tambayar a gidan marayun da nake ba a koya mana ibada ni. A ranar na fayyace mata komai na yadda kaddara ta tsara min rayuwa. Ta yi kuka ta tausaya min kuma ta yi min alkawarin zata zame min uwa, itace ta fara saka ni a makarantar islamiya na fara koyon addini.
Sannu a hankali na sake jiki na zama kamar yar gidan, wata rana ina zaune falo ta same ni tace Aisha ina jinki kamar yata daman ina sha'awar ya mace Allah be bani ba, samunki a yanzu ya saka na ji kamar Allah ya maye min gurbinki da wanda ban samu ba ne, fadar hakan da tayi sai ya kara karfafa min guiwa na jidadi, ta fada min yaro daya ta haifa amman baya hannunta matashiyar da na gani a lokacin mai suna Nana rikonta take, yanayin yadda take mu'amalantar danta abun sha'awar ba dan na gani ba sai dan labarin da ta ba ni da kuma yadda take idan ya kirata ko ta kira shi, na fahimci tana matukar kaunarsa ne ta yadda take fada min hallayensa da dabi'unsa, har ta fada min idan ya kan shekara biyu kamin ya zo gurin, amman wnnan karon idan ya zo akwai shirin da ta yi masa, ban fahimci me take nufi ba ashe aurena da shi take son ta hada amman bata fada min ba. Sai dai tana yawan ce min musulmai suna da dadin zama kuma Allah zai min sakamako da miji na gari.

A haka har yarona ya shekara daya ina kula da shi, Ammy kuma tana siya masa magani da madara, sai dai ni kam jiki be sauka ba, duk kuwa da kasancewarsa na samu lafiya sosai ga wadata ta abinci, na zama kamar wata babbar mace fari ya fito jan gashina yayi kyau saboda yana samun gyara a yanzu komai a wadace.
Wata rana na yi wanka na shirya cikin shudiyar atamfa wanda ta yi mjn kyau sosai, na fito harabar gidan na zauna ina shan iska, da kuma mamakin yadda har zuwa lokacin Khaleefa ba neme ni ba, ba dan ina da bukatarsa ko wani abu daga gareshi ba sai dan cikin da ya sake ni da shi, da kuma irin halin da ya bar ni, amman be biyo sawuna ba.

Da ace ban hadu da Ammy ba wata kila da ina nan cikin gararin rayuwa amman be damu ba. Be yi tunanin alhakina ba ko na dansa. Ban san ba, ashe ina tunanin hawaye suna saukowa min amman ban jin ba saboda zuciyar ta yi nisa gurin tunani har sai da Ammy ta fito ta zauna kusa da ni tana fadin.

"Me kika tuna? Domin na san kin samu lafiya yanzu ballantana nace ciwo kike ji"

"Bana tunanin komai"

"Ga hawaye a fuskarki Aisha karki cutar da kanki mana, ki dauke ni a matsayin uwa bana son kina boye min komai"

Na kai hannu na taba fuskar sai na ji hawaye.

"Kawai ina tunanin yadda Khaleefa ya juya min baya ne, kuma yadda be waiwaye ni ba har yanzu, be damu ta sanin halin da dansa yake ciki ba"

Sai ta yi murmushi.

"Yarinya ce ke shiyasa baki fahimci rayuwa ba, ai a yanzu ne yake cikin shauki da jindadin yaudara, ba zai neme ki a yanzu ba, sai a lokacin da nemanki ba shi da amfani a gurinsa, kuma ina baki shawarar idan ya dawo miki karki saurareshi ban ce karki yafe masa ba, amman karki yarda ki sake saka kafarki a gurin da aka wulakanta ki aka nuna baki da daraja.
Aisha maza na gari suna tsada, ba kowa ne yake iya aure ya rike amana ba, amman ina mai tabbatar miki nan gaba kadan zaki samu samu wanda zai mantar da ke komai zai so ki ke da danki, ni ma na sha wahalar rayuwa a aurena na farko kuma banbanci abun da aka miki da nawa kadan ne, ke kin yi ma arziki an barki da yaron, ni nawa karbe yaron yayi kuma ya hana na shayar da shi, sai da na shekara ashirin kamin na samu ganin dana a ido shi ma kuma sai da na yi fadi tashi shiga nan fita nan, daker na samu haduwa da nada na samu ana barinsa ya zo gurin ko kuma ni na tafi, bayan Turhan ban sake haihuwa ba saboda maganin da aka bani a gidan mahaifinsa, shi ma haihuwarsa ta zo ne kawai saboda Allah ya kaddara akwai da a tsakani, shiyasa a yanzu na maida shi abokin ban kalle ta sigar dan fari ba, komai a gidansu ake masa abinci da nake ci ma daker ya iya koyar cinsa, idan ya zo nan tufafi kalar da nake so yake sakawa, zamu yi wasa da dariya mu yi hira mu yu yawo kamar ni da kane na ba dana ba, matar da ya aura ma daga masarauta aka zaba masa, kuma har yau be taba kawo min ita na ganta ba, sai a waya, shiyasa ni ma na yi masa nawa tanadin na musamman kuma na san zai so ki zaki dace sosai"

Na kalleta da kamar mamaki jin ta ambace zan dace, sai na nuna kaina.

"Ni"

"Eh, Wana nake yi ma tanadinki, na miki alkawari zai soki zai rike ki amana kuma zai so danki, a yanzu ne zaki san miye aure zaki dace, kuma na san zaki so shi domin shi ma kyakkyawa ne, kusan duk yan mata da nake hada shi da su cemin yake baya sonsu amman ke kam ba zai iya juya miki baya ba, domin kina da kyau kina da haske da gashi kamar matan garinsu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login