Showing 201001 words to 204000 words out of 253142 words

Chapter 68 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18431

mike tsaye ya sauka balcony yana safa da marwa a gidan kar kace ba karfe 3 dare ba ne, ya dade a haka yana ta sake sake sannan ya juya ya koma ciki ya rufe kofar, dakinsa ya shiga yayi alwala ya fito daga bandakin ya nufi corner da yake ibada a dakin ya fara sallah.

Daman Larabawa sukan ware wani bangare a dakinsu da suke shimfida Carpet su aje qur'ane ana saka turare domin ibada.
Be daga daga carpet din ba har aka yi sallah asuba. Bayan ya gama sallah bachi mai nauyi ya dauke shi, be farka ba sai da ya ji yatsun Ammy cikin kansa, ya bude ido ya kalleta sai ta yi murmushi tana cigaba da shafa kansa.

"bab% al-khayr y Ammy"

Ya furta da murmushin karfin hali, ta amsa masa cike da kauna irin ta uwa da Wa.

"?mil shinu y walad+? Allh yi%fa?ak l+. y %ab+b+ y walad+? Keif %lak?"

Ya daga kadan ya kwantar da kansa kan ciyarta.

"Babu dadi Ammy"

"Ka raya dare da damuwa ko? Ni ma jiya na ji babu dadi saboda Fatima bata gidan, amman dai yau za mu tafi gidan"

Ta sauke kansa.

"Kwanta ka samu bachi, kana da bukatar kuzari Wana, Allah ya maka albarka"

Ya lumshe ido bayan ya amsa da Ameen, Ammy ta tashi cike da tausayin danta da kuma bacin ran halin da yake ciki ta fice dakin.
[8/6, 11:10/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: *

*? Khadeeja Candy*



Page 6?? 3??



"Ya kamata na koma haka, ance sun dora wani ma"

"Ba fa inda zaka je sai an kama yaron nan, mutumen dake neman ranka zaka koma garinsa ka zauna da sunan aiki, daman can ni bana son aikin da kake a kuda mutanen nan ba su da kyau"

"Abun da Allah ya rubutawa bawa baya wuce Ummi, kuma ai yanzu guduwa yake ba zai iya komai ba"

"A nan din ma kasan ko yana nan yana haka maka rame? Ba zan barka ka koma ba, idan ma suna son aiki da kai su dawo da kai Abuja ko nan Kaduna"

"Idan kuma suka ki fa"

"Sai ka bar aikin dole? Ina za a kusa kai da kai a kasar nan baka samu aiki ba? Ga ka da cancanta kuma ga alfarma ta ko'ina, kasan ko bangaren President muna yan gaba gaba"

Aliyu yayi murmushi mai sauti.

"Ummi wato dai abun da ake fada na yan siyasa da gaske ne, daga kansu sai iyalansu?"

Ummi ta yi dariya.

"Gurin Surukinka muka koya, kasan ya fi kowa son kai"

Aliyu yayi murmushi, shi da Ummi suka juya suka kalli kofar falon da aka turo. Ammy ce ta shigo da sallama fuska ba yabo ba fallasa, Ummi ta amsa mata ita ma tana dan sham kamshi domin abu daya ne Ummi bata yarda da shi ba, shi ne raini wayo ko wulakanci, bata daukar rashin girmamawa daga gurin kowa wannan dalilin ne ya saka suke kara samun rashin jituwa da mahaifiyar Kameela.

"Ammy ce a gidan ba mu?"

"Ai dole za ku gan ni tun da surukata tana nan, ya muka iya da abun da ya fi karfin wuta, fatan na same ku lafiya"

"Lafiya ?alau sai Alheri da ke ta shigo mana"

Ammy ta yi tsaye bayan Ummi ta amsa mata.

"Bismillah Ammy ki zauna"

"Aa ba zama ya kawo ni ba, Aisha tana ciki?"

Ummi ta yi murmushi.

"Tana nan waje, idan kika fita ki zagaya dama kadan gurin Garden tana can ita da jikarki"

"Ammy ina wuni"

Aliyu ya gaisheta yana sirina.

"Lafiya"

Ta amsa tare da juya bata ko kalleshi ba. Sai da Ammy ta fice sannan Aliyu ya sauke ajiyar zuciya.

"Ammy fushi take da ni, ban jidadin yadda abubuwa suka zo ba, ko kadan Kameela bata kyauta min ba, na so na tsara abun nan cikin hikima ba tare da kowa ya ga laifin kowa ba, Allah ya sani da zuciya daya na yi wannan abun ban yi nufin cutar da Turhan ba, na shiga tsakiya ne kamin na hankara tausayin Emily ya rinjaye ni, sai na fi fifita matsalarta saboda ina ganin ita ce tafi shiga matsala, har gobe idan na tuna abun nan sai na ji zafin abun da Kameela ta aikata"

"Ai ni ba karamin taimaka min ta yi ba da ta yi haka, da yanzu ban san miye yake faruwa ba sai idan ka mutu ace ai ka ci guba, ko kuma ka ta daba maka wuka, ka ga masu shegen kishin nan tun wuri ana ganin abun da suke iya aikawa daga musu kafa ake ana ganin kamar ba komai ba ne, da yanzu bata yi wannan shirmen ba ba zaka fada min ta zuba maka guba ba, kuma ai ka kasa sakinta"

"A lokacin ina kokarin bata hakkinta ne, hankalin namiji baya taba zama iri daya na mace, ina daga mata kafa da uzurine amman ko a lokacin na yi alkawarin ba zan sake cin abincinta ko kwanciya daki daya da ita ba, and zuwa nan da na yi saboda ita ne Mama Baraka ta kira ni, da na zo kuma mahaifinyarta ta wulakanta, sai kuma ta aikata min abun kawai sai na zabi sauwake mata domin samawa kaina salama"

"Aiko gashi yanzu abun yana cinta, babu safiyar bata aiko min sako ban hak'uri, ni kuwa ko ba ni da rai Wallahi ba zaka zauna da Kameela ba, yarinya ta yi yunkurin kasheka kiri kiri sannan ga iyayenta ba son auren suke ba, tun farko ni damam na runtse ido ban ga kyau a makanta ba, domin iyayenta ba masu dattako ba ne, kai kuma ka tsaya kai da fata ai ita tana sonka tana da tarbiya, ga abun da ta haifar maka ai, daman yaushe iyaye za su bada shawara aki bi kuma a ga daidai?"

Aliyu yayi dariya.

"Yanzu dai ba zan sake zabar mata ba, ke zaki zabar min"

"Aa kai da kanka zaka zabo, ni nawa bincika ne da duba dacewa"

Ya mike tsaye ya nufi kitchen ya bude firjin ya dauko ruwa ya kafa gorar a baki ya sha, sannan ya fito rike da ita ya dawo falo ya zauna.

"Ni yanzu ban san ya zan yi na shirya tsakaninsu ba"

Ummi ta dauke kanta daga kan wayarta ta kalleshi.

"Ina ruwanka da shirya tsakaninsu? Dan iya? Tun farko daman ai bata son Turhan din, kuma sai ga shi yayi mata abin da yayi ta ji ta tsane shi, kai kasan yadda mutum yake ji idan baya son wani kuma ya zo ya kara zalintarsa? Kai da ka gode Allah auren soyayya kuka yi da Kameela, haka din ma yanzu da ta yi maka ba daidai ba yanzu ya ka ji? Ka ce ta komawa mijinta ta ga kamar kana matsa mata? Yarinya ta sha wahala yanzu har bada son wari maza ai ta ma yi kokari da take kallonka, da ni ce ko hanya ba zan sake hadawa da namiji ba, idan ta ga wanda take so har zuciyarta ita zata yi magana, kuma ni yanzu ko mijina tace tana so ai sai na tattara ni da kai mu bar mata gidan ita ma ta samu jindadin rayuwa"

Aliyu ya kyalkyale da dariya.

"Ummi Allah ya bar min ke, duk matar da zata yi kishi da Ummi ai sai ta shirya, taya ma Emily zata ce ta so Daddy"

Ummi ma ta yi dariya.

"Aa wai a misali dan na nuna maka ta cancanci farinciki, kuma kishi da ni wata wahala ce? Ni fa ba zan cutar da kai ba, kuma ba zan zuba ido ka cuce ni ba, magana kuma a fada min daya na rama da goma"

"Aa ni ba tsakaninta da Turhan zan shirya ba, tsakaninta da Ammy, tsakanin Emily da Turhan wannan wani abu ne da kowa be kamata ya saka kansa ba"

"Yanzu na ji maganar hankali, Allah ya bata wanda zai riketa amana mai sonta tsakani da Allah kuma babu cutarwa"

"In Shaa Allahu, daman ai bayan wuya sai dadi, kuma Allah da kansa yace dukkan tsanani yana tare da sauki"

Ya sake kurba ruwan ya aje ya mike tsaye ya haura sama.




EMILY POV.

Tun bayan tafiyar Mama Baraka Emily bata fito ba sai da Ummi ta shiga ta lallasheta, da kalamai na karfafa guiwa ta fada mata yanzu ai komai ya wuce, be kamata ta rika tuna baya ba, kamata yayi ace ta fuskanci gaba.
Da lallabawar Ummi Emily ta samu gwarin guiwar cin abinci ita da Fatima ta shiga ta yi wanka ta saka doguwar rigar Atamfa, sai Ummi tace ta fita ita da Fatima waje su bawa itatuwan gardens ruwa, daga bada ruwan ne ta fara jika Fatima tana dariya, sai Fatima ta yi mata gwalo ta boya a bayan itace ita kuma tana binta ta watsa mata ruwan, sai nishadi take kamar ba ita ce ta gama kuka dazun ba.

Tana rike da tiyo ta ji kara bude karamin gate din da aka saka a gurin sai ta juya idanuwanta suka yi arba da Ammy. Emily ta dan rage murmushin da take tana kallon Ammy har ta karaso kusa da ita, Fatima ta fito daga inda ta boya da sauri ta rumgume Ammy tana mata oyoyo.

"I miss you"

Ammy bata damu da tufafin a jike ba ta daga ta sama ta hade da jikinta.

"i miss you too, ya kike rabin rai na"

"Lafiya lau, ina Dady"

"Yana can bakin gate cikin mota gidan kin fita zaki gan shi"

Ta sauke ta kasa Fatima ta zura da gudu tana murna ta fita gurin. Emily ta saki Tiyon hannunta.

"Ina wuni Ammy?"

Ammy ta yi murmushi.

"Lafiya kalau yata, ya mai gudun uwarta, kin dawo lafiya?"

Emily ta yi murmushi.

"Lafiya ?alau"

"Ina kika shiga kika boya? Kin daga mana hankali, kin dagawa Turhan babu inda be shiga nemanki ba har gurin da kika zauna kamin ki haifi Fatima, ita ma Fatima bata bar mu mun huta ba"

"Yanzu ai na dawo, komai ya wuce Ammy"

"Haka ne sai dai a fuskanci gaba, fatan dai babu wata matsala yanzu ko?"

"Babu"

"Tohm Alhamdulillah haka nake son ji, yanzu hankalin Turhan zai kwanta na yarki ma ya kwanta ni ma kuma sai na samu farinciki"

Emily ta yi shiru bata ce komai ba.

"Jiya Turhan be yi bachi ba, gaba daya ya bi ya damu saboda ba shi ya gano inda kika shiga ba, tare da shi muka zo na ce ya jira na fara shigowa na yi magana da ke, kin san saboda Aliyu baya son shigowa gidan nan"

"Ammy akwai abun da nake son na fada miki"

Emily ta fada, sai Ammy ta kara matsawa kusa da ita.

"Ina jinki yata"

"Mu zauna a can"

Suka nufi gurin da kujerun zama suke suka zauna Ammy ta dora jakarta kan teburin.

"Da farko da zan fara da miki godiya, na abun da kika min ni da Wana a shekarun baya, na rike ni ba tare da kin sani ko kin san inda na fito ba, na gode Sosai, hakan ya saka ni auren Turhan da nufin na rama alheri da kika min, har abubuwan da suka faru suka faru, kowace jarabawa a rayuwa darasi ce ta kan koyar da kai wani darasi ne da baka sani ba, na kara jirmama abun da kika min ne da sanin muhimmanci a yanzu da Mahaifiyata ta bayyana"

"Mahaifiyarki?"

Ammy ta katse ta sai Emily ta daga mata kai Idonta na cika da hawaye. Ta tsakura mata abubuwan da suka faru. Emily ta rika hannunta.

"kin yi kokari da kika rika ni, kika taimaki Wana, a lokacin da mutunen da ya rabo ni da inda nake samun walwala ya wulakanta ni, danginsa suka ki ni, na rasa inda zan dafa, na gode Ammy na gode"

Ammy ta yi murmushin jindadi.

"Alhamdulillah da kika fahimci haka, ko kadan bana nufin cutar da ke, hada aurenki da Turhan ma ban yi dan cutar da ke ba, na yi ne da nufin sama miki mafita ta mijin aure ni kuma na samu mafitar Wana a kusa da ni, idan har ina nufin cutar da ke taya zan aura miki dan da ni na haifa da ciki? Shiyasa da na fahimci akwai matsala na sauya masa na kasa saurarensa a dolensa ya bazama nemanki, gashi yanzu har ya gane kuskurensa yayi nadama babu abun da yake nema sai hada kan iyalinsa guri daya, kuma ina fatan zaki fahimce shi zaki yafe masa, ki yarda da shi ko dan yarki"

Emily ta saki hannunta.

"Yara ba su kai su hana iyaye farinciki ba Ammy, su yanzu suke tasowa rayuwarsu suke ginawa, shiyasa mahaifiyata bata bar farincikinta saboda ni ba, balle kuma ni da na yi ma Fatima komai da uwa zata yi ma yarta, idan har zan yarda a yanzu farincikin Fatima ya hana nawa hakan na nufin ni ban gina rayuwata ba kenan, abubuwan da suka faru sun faru kuma na ba su baya a yanzu, amman ba zan bar farincikina saboda Fatima ba, ba zan sake kuntata ma kaina sabida kowa ba"

"Hakan yana nufin babu wani gyara tsakaninki da Turhan?"

"Babu Ammy, ni ban taba son Turhan ba, har yanzu ban ji wani abu akansa ba, kuma bana tunanin nan gaba zan ji, yanzu idan har nace zan sake zama da shi to ni ce zan cutar da shi, kuma na cutar da zuciyata to miye amfanin haka?"

"Aisha ni kika kalli kwayar idona kika fada min baki son Wana?"

"Ki yi hakuri Ammy, kin san inda na fito kin rayuwar da ni, ke ma kin yi makamanciyar tafiya irin tawa, miyasa ba za ki fahimce ni ba?"

"Saboda mahaifin Turhan be yi nadama ba, har yau be nemi ni ko neman afuwata ta ba, amman ke Turhan ya gane kuskurensa ya tuba kuma ya shirya faranta miki har hawaye ya zubar akanki, ya kauracewa abinci, bachi ma baya wadatarshi, da ace saboda Fatima ne kawai ai ba zai waiwaiyeki ba tun da ya same ta, amman saboda yana son ki yana son farincikinki ya kasa hakura, ki ba shi dama Aisha dan Allah"

Emily ta girgiza kai. Sai Ammy ta kama hannunta ta rike.

"Haba mana Aisha, Wana na cikin mawuyacin hali saboda ke, ba shi kadai ba, Khaleefa ma ya munana miki iyayensa ma sun munana amman ni ban miki ba, miyasa ba zaki yafe masa ba, ki ma dakinki ki rumgume yarki da ke son Babanta? Duk wani sharadi da zaki gindaya mana ni na miki alkawarin za mu dauka"

Emily ya sake janye hannayenta.

"Ba zan iya ba Ammy ki yi hakuri, ba zan iya rayuwa da mutumen da ya shigo dakina a daren aurena ya tofa min yawu a fuska, ya kalli kwayar ido ya kira ranar da aka daura mana auren da bakar rana a gurinsa, ya shiga da ni gidansa a matsayin baiwa, yana kallo nake goge inda matarsa take takawa, yana sane ake dokana, be damu ya ba ni abincin da nake iya ci ba, ban taba dandanar dacin rashin magana ba sai da na auri Turhan, kuma ba dan bana iya maganar ba, sai dan ya gabatar da ni a matsayin kurma kuma ya saka min sharadin kar na kuskura na yi magana, a gidansa ban isa na saka kayan da nake so ba sai uniform din bayi, ban isa na kwanta a inda nake so sai tare da hadiman matarsa, ya kira ranar da ya kusance ni da bakar rana, ya fada min ba zai taba so na ko son abuj da na haifa ba, mutumen da yayi min duk wannan taya zai dauke ni a yanzu ya nunawa duniya yace ina da daraja? Ai ya gama kwance min zane a kasuwa kowa ya ga tsiraicina, Turhan ya haihu da ni kin samu jika har gobe ban isa na goge wannan ba, Ammy haka ma ya wadatar..."

Ammy ya mike tsaye ba tare da ta kara cewa komai ba ta fice daga gurin. Emily ma ta mike tsaye ta nufi wani ice ta dafa shi da hannu daya dayan hannun kuma ta dafe kanta tana jin babu dadi na tunawa da rayuwarta ta baya. Tana tsaye a gurin bata motsa ba ta ji an kira sunanta

"Aisha?"

Ta juya ta kalli Turhan dake doso inda take tsaye hannayensa rumgume a baya yana tafiya daya bayan daya irin ta jinin sarauta. Ya tsaya gabanta yana kallonta daga sama har kasa for the first time ya ga kyauta irin kyaun da be taba ganin ta yi ba sai yau, duk kuwa da babu kwalliya a fuskarta, sai kuma kwarjininta ya kama shi gabansa har faduwa yake da take kallonsa ido cikin ido kallo irin na wanda ya tanadi amsar kowace tambaya.

"Za mu iya yin magana da Allah?"

"Yau kai ne kake neman izinina akan wani abu?"

"Haba ki bar abin da ya wuce ya zama ya wuce mana Aisha! Na yi kuskure na sani kuma na karbi kuskurena, ke ma a yanzu kina cikin kuskure na barin wanda ba muharraminki ba yana kallon surar jikinki da kyaunki yana magana da ke yana jindadin muryarki, be ma kamata ki zauna a nan ba shiyasa duk abun da na fada ba fahimta kike ba, saboda ba zai taba bari ki fahimce ni ba, kuma ba zaki gane hakan ba sai nan gaba."

"Na fada maka wani? Aliyu ya fi min kai amfani sau dubu, shi be taba fada min magana marar dadi ba, be muzantani ya fada min magana marar dadi ba, be doke ko ya saka a doke ni ba, be kira ni fasika ba, da na ba shi labarina be musa ba, ban roke shi alfarma ya gagara yi min ba, be yarda an wulakanta ni ba, ne gan ni a cikin damuwa ya bar ni balle har ya jefani a ciki, dan haka ba zan yarda wani ya fadi wata magana marar dadi akansa ba"

Turhan ya hade wani abu mai daci da tsayawa rai yayi murmushi.

"Ban zo nan saboda wani da be kamata ko sunansa na furta ba, na zo ne nan ne saboda ni da ke"

"Babu wani abu tsakanin ni da kai, zama ne dai ada mun yi yanzu kuma ya kare, idan har zaka zo mu tattauna wani abu to ya kasance akan Fatima and Only Fatima"

"Aisha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login