Showing 39001 words to 42000 words out of 253142 words

Chapter 14 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18439

yi yawo duk inda ake saka ran za a samu yarinyar nan ba a same ta, da har nace yau zan dawo gida, sai kuma mutumen da ka hada ni da shi yace na yi hakuri mu sake bincikawa daga yau zuwa gobe, idan ban same ta ba, sai na hakura

"Toh ya zaka yi da Ammy?

 Ba dan Ammy ba, taya zan bata lokacina ina nemanta, kawai dai ina hakuri ne saboda Ammy mahaifiyata ce ba yadda zan yi, amman su ma iyayen suna shiga hakki yaya wani lokacin Wallahi

 Wata kila Ammy ta ji ko ta gani ko tana tunanin ka munana mata a zamanku ne, shiyasa ta gagara shiryawa da kai

 Kaddara ma ace hakan ta faru, amman ai ni danta ne, be kamata ta juya min baya ba a kowane condition, taya zaka fifita wani fiye da naka? Kuma tun farko ita ta cilasta min auren yarinyar nan ni gaba daya bana sonta

 Amman ka cutar da ita?

"Sau nawa zan amsa maka tambayar nan ne Aliyu? Shi daman zaman aure sai an yi hakuri, saboda zo mu zauna zo mu tsaba ne, kuma al'adarmu da addininmu ba daya ba, kuma yarinyar nan bata da asali

 Ban fahimta ba

 Ba a san su waye iyayenta ba, kuma ko da na zauna da ita zuwa can gaba idan an yi zuri'a baka tunanin zata iya juyar da hankalin yaran zuwa addininta?

"Ita miye laifinta dan an haife ta a inda be dace ba, ba a shawara da mu kamin a zaba mana iyaye ko irin rayuwar da za mu yi kai kasan haka

 A haka din kuma addinin musulunci ya hore mu da auren mai asali, abubuwan da suka faru dai sun faru shikenan, sun wuce yanzu kuma nemanta nake na shirya tsakanina da mahaifiyata

 Allah yasa a dace

Ya fada sannan ya aje wayar ya kalli Kameela dake ta leken motar tana dora kunnenta a jikin gilashin ita ala dole sai ta ji da wa mijinta yake magana. Murmushi yayi ya bude motar ya fito.

 Wannan ba halinki ba ne

"Kai ma ai ba halinka ba ne idan kana waya ka boye min, me yasa baka son na ji

 Dole ai kin san akwai sirrin da zan yi da yan'uwa ko abokai ba zai yayu kiji ba ko? Kamar yadda ke ma na san akwai abun da ba zaki fada min ba

 Ni ai bana boye maka komai?

 Uhmmm

Ya sumbance ta sannan ya kama hannunta suka shiga cikin gidan.

 Baka yi breakfast ba ka fita, kuma gashi ka dawo da damuwa, yanzu kuma ka yi waya ban san da waye ba ka rufe ban ji komai ba

 Be shafe ki ba ne ai

"Abun da ya shafe ka ai ya shafe ni, ka fada min minene dan Allah dan Allah"

Allah da ta hada shi da shi sai ya ji ba zai iya boye mata ba, kamar yadda ba zai iya fito mata da komai a zahiri ba. Yaja mata kujera ta zauna ya fara zuba musu abun karyawa sannan shi ma ya zauna. Cin abinci kawai yake baya jindadinsa ba dan matarsa bata iya girkin ba sai dan bacin rai da ya fi kama da damuwa dake tare da shi.

 Dan Allah ka fada min

Ya kalleta yana murmushi.

"Kina da son gulma, toh akan Yarinyar da Turhan yake nema ne

 An same ta ne?

 Be same ta ba har yanzu, yana cikin damuwar rashin samun nata, hakan kuma ya shafe ni

 Toh ai be kamata hakan ya shafe ka ba, damuwar wani be kamata ace ta zama damuwarka ba

Ya aje fork din hannunsa ya kama hannunta

 Ki daina wannan tunanin, indan akwai tausayi a tare da mutum dole ko da ba musulmi ba ne ya shiga wani hali marar dadi zaka ji babu dadi balle kuma musulmi dan'uwanka

 To wai shi ba zai je ya nemi yarinyar da kansa ba sai ya rika dora maka lalura waya sani ma ko yarinyar kyakyawa ce?

Ta fada tana turo baki, hakan ya saka shi yin murmushi.

 Idan kyakyawa ce fa?

"Idan kyakyawa ce ko ka ganta ai ba zaka fada masa ba"

 Baki yarda da mijinki ba?

"Tohm zuciya ita kuma ai bata da kashi"

 Wai ke da na yi ma alkawari na yi ma rantsuwa aka yi abun har a rubuce cewar ba zan kara aure ba, ina ruwanki da duk inda zan shiga"

"Shedan fa yana nan kusa zai iya sakawa ka karya alkawarin nan, kuma yadda kake da kyaun nan kake wanka idan zaka fita, ai dole hankalina ya tashi

"Wallahi Kameela ba zan miki kishiya ba, ba zaki taba sharing dina da wata da sunan kara aure ko akasin haka ba, shikenan?

Ya sumbance ta sai ta yi murmushi ta kwanto jikinsa.


[4/20, 10:01/ AM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL




*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 3??


Masu tambaya daga farko zaku iya duba channel dina https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

Ko kuma wattpad @KhadeejaCandy

Masu tambayar free ne ko na kudi, toh Free ne, yan bati sun hada kai da Iya sun min kiranye ya kamani tare da hadin kan Ummu Faisak yayar Wasim =??

Asha karatu Lafiya >?p?


***.? ? ***.? ? ***


VITO POV.

Falon ya shiga ya zauna, can kasan zuciyarsa ya ji babu dadi na dukan da yayi ma Emily, ya saba samun kansa a irin wannan yanayin a duk lokacin da ya duke ta, sai dai kuma dukanta a gaban ko ma waye abu ne da ba zai iya hana kansa ba, ba zai iya rike hannunsa daga taba jikinta da sunan duka a duk lokacin da laifi ya fito ta tsagenta ba.
Kamar yadda ba zai iya fin karfin zuciyarsa a duk lokacin da wani yayi mata kallon banza ko na soyayya ba, yana sonta ya sani, yana tsananin kishinta irin kishin da shi kansa yana tsoron kar yayi masa illa wata rana.

 Ban san ko kana bukatar ruwa ba

Chidimma ta miko masa cup da gorar ruwa a tray cike da ladabi da kuma gudun bata masa rai. Ya kalleta kawai ya kalli gurin da zata aje ruwan, sai ta risina ta aje a kasa ta daga gorar ruwan ta bude ta zuba masa a cups sannan ta dora ruwan a kan side table. Ruwan ya fi da kallo yana mamakin yadda ya kasa yi ma Aliyu komai a dazun har ya tafi, me yasa ma ya daki Emily bayan kuma Aliyun ya kamata ace ta hukunta domin shi ya nemi addireshinta ya biyo sawunta har gida? Ya kawo karnukansa da nufin idan Aliyu ya shigo gidan ya rufe gate din ya sakar masa su, amman duk be samu nasarar yin hakan ba.

A zahirin gaskiya Vito wani kalar mutum ne sa kallonsa kawai zaka yi ka firgita, saboda rashin annurin dake fuskarsa da kuma shigar da yake ta tufafi, amman sam be ga alamar hakan a tattare da Aliyu ba, toh miyasa ma ya biyo ta har gida? Me yake nema a gurinta? Ya kai hannu ya dauki ruwan da Chidimma ta zuba masa ya kai baki yana sha sai wani sanyi ya sauka a zuciyarsa wanda ya kara taimaka masa gurin hararo dalilin Aliyu na bibiyar macen da ba ma addininsu daya ba.

'Tana da kyaun da kowane kalar namiji zai iya cewa yana sonta ko son mu' alama da ita`

Zuciyarsa ta bashi amsar da yake bukata, mikewa yayi tsaye ya nufi kitchen din da Chidimma take, tana ganinsa ta juyo da sauri.

 Kana bukatar wani abu ne ranka ya dade?

 Me kika shiryawa London na karyawa?

 Gashi nan

Ta dauko big basket ta risina kasa ta aje masa, zai kai hannu ya dauka sai ta riga shi.

 Bari na kai maka mota ranka ya dade

Be ce mata komai ba, ya juya ta bi bayansa har gurin motarsa sai da ta saka masa mota sannan ya yi mata key ya fice daga gidan. Sai a lokacin Chidimma ta nufo Emily dake kwance a gurin rumgume da Fatima ta tsaya kanta.

 Bana son na batawa daya daga cikinku rai ne, bana son daukar bangaren Sir Vito na bar naki, abu kadan zai iya sakawa ya koreni ko ya hukanta ni, shiyasa bana iya tarewa idan yana dukanki, ki yi hakuri

Uffan Emily bata ce mata ba, ita ma kuma bata jira cewarta ba ta juya ta koma ciki ta cigaba da aikin da take.
Yana faka motarsa harabar asibitin wayarsa ta yi ringing, ya amsa kiran har lokacin ransa babu dadi saboda dukan da yayi ma Emily, mahaifiyarsa ce take sanar masa jirginsu zai taso yanzu daga Murtala Muhammed International Airport (MMIA) dake Lagos zuwa Port Harcourt International Airport. Daman ta sanar masa da zuwanta tun kwanan baya.

 Safe journey"

Ya fada as Answer sannan ya cire wayar daga kunnensa ya bude dayan side din ya dauko basket din da Chidimma ta saka masa ya nufi cikin Asibitin. Ko da ya shiga ya samu Nurse nata lallaba London ya fito daga kasan gadon majiyanta da ya boya amman yaki sai ihu yake mata.

 Heyyy my boy

Vito ya fada cikin muryarsa ta manyan mazaje, London na jin muryarsa sai ya leko suna yi arba ya fito da sauri yaje gurinsa ya rumgume shi. Murmushi ko nuna farinciki ba al'adarsa bace balle kuma a yau da yake cikin damuwa, kan London kawai ya iya shafawa ya daga shi zuwa kan gadon Asibitin suka zauna.

 Tun dazun yake labe a gurin baya yarda da kowa, idan ka matsa kusa da shi sai yayi maka ihu

Ta fada tana kallon London din da murmushi a fuskarta, Vito be ce mata komai ba, ya kai hannu ya dauko abinci ya bude ya fara ba shi da kansa, tana ganin haka sai ta fita ta bar musu dakin. Sai da London ya ci abinci ya koshi sannan Vito ya fara masa maganar Emily.

 Meyasa ka yi ma Momy Ihu jiya?

 Ina fushi da ita

 Na fada maka Momy tana sonka ba zata aikata abun da zai bata maka rai ba, duk laifinta akan kuskure ne, ka yafe mata ka ji?

Ya daga kai, sai ya shafa kan yaron...

 Ina son mahaifiyarka, duk kuwa da kasancewar ta haife ku, na kula da ku na nuna mata soyayya da gata, amman ta kasa ganin hakan

Yayi shiru yana kallon London.

 Wata kila kuma ta gani, kawai dai bata shirya karbata ba ne

Ya ja numfashin da ya gagara saukewa.

 Uhmmm zan mata uzuri har zuwa lokacin da ta dibarwa kanta, sai dai ina da tabbacin abu daya, idan ban samu mahaifiyarku ba, wani ba zai same ta ba, idan ban mallake ta wani ba zai ci galaba a kaina ba

London yayi murmushi domin be fahimci yaren ba. A hankali idonsa ya kai a kan card da Emily ta jefar a dakin. Mikewa yayi tsaye ya nufi card din ya dauka Dr A-B ne rubuce a jikin katin da kuma address din gurin aikinsa sai Email da number wayarsa. A take ya fara jin zuciyarsa ya tafasa, jimke katin yayi ya juyo ya kalli London.

 Chi chi zata zo ta kula da Kai bari na je na dawo ka ji?

London ya daga masa kai alamar amsuwa, be bar dakin ba sai da ya kira Chidimma a waya ya fada mata ta bar duk abun da take ta zo yanzu asibitin gurin London, bayan ya shafa kansa ya sumbance ya fice.

Kamin ya isa gida ya kira daya daga cikin yaransa ya fada masa ya tafi gidan ya dauke dog's da aka kai, yanayin yadda ya faka motar a harabar ya fito kadai ya isa ya sanar da bacin ransa balle kuma yadda ya turo kofar falon ya shigo, sai da Fatima dake zaune tana zane ta firgita. Yana kallonta ya dauke kai ya nufi upstairs.

 Dukanta zaka sake yi?

Ya juyo ya kalli makiyiyarsa Fatima, domin ya fi tsanar ta fiye da kowa a gidan, sai dai duk da haka be taba unkurin kai hannu ya doketa ba, no matter what ta yi masa sai dai ya mata fada ko ya wani hukuncin na dabam amman ban da duka.

 Momi zata yi kudi, tana aiki zata samu kudi mai yawa zata gina gida zata maida mu can mu rayu a can ba tare da kai ba, ba zaka sake ganinmu ba balle ka dake ta, i hate you

Ta fada cike da fitsara da tsageranci irin yadda ta saba yi masa, jimmm yayi yana kallonta kamar mai nazari ba tare da ya ce mata komai ba, kamin ya juya ya haura saura zuwa dakin da Emily take...



EMILY POV.

 Meyasa kake son saka kanka a hatsari? Baka san wacece ni ba, kuma baka san da wa nake tare ba, kuma ya kamata kasan ni ba musulma bace, babu abun da Zai hada ni da kai, domin mutanen da na tsana irin musulmai, karka sake bibiyata karka sake shiga rayuwata, idan ba haka ba zaka jefa kanka a bala'i

Ya mayar mata da amsa a take.

 I'm sorry for what happened earlier, bana nufin jefa ki a matsala, akwai wani tsauni ne da na hau ba kuma zan iya sauka ba har sai da gamsantsun amsasoshinki, shin zan iya sanin wani abu akanki? Wata kila hakan zai taimaka ya gina wata katangar da zata katange ni daga fadawa mai nemanki gaskiyar a inda kike

 Ni uwa ce da bata da aure mai zama a karkashin inuwar wani mai karfin kudi da iko, uwa ce da ta haifi yaranta ta raine su ba tare da taimakon kowa ba, ni din na tashi a gidan marayun ne ban san uwa ko ubana ba, balle ayi zancen yan'uwa, bana da kawaye bana da kowa sai Vito da yarana, ni din wata ce da wani musulmi ya yaudara, mummunar kaddara ta yi min dabaibai hada ni da mutanen da bana kirki ba, a yanzu kuma ni christen ce mai alfahari da jindadin addininta, mai kokarin gina kanta da rayuwar yaranta, bayan wannan sai me kake son ka sani?

 Ina son na san a lokacin da kika wanzu tsakanin rayuwa da mutuwa ne, ina son na san komai akanki, ta ina lamarin ya fara? Taya kika kawo har yanzu? Su waye suka munana rayuwarki, miye dalilin komawarki addinin Christianity? Su waye suka saka kika tsani musulmi da addinin musulunci? Miyasa baki son Fatima ta san tana da mahaifi? Wacece ke Emily? Na damu na na sani, kuma na damu da ke

Taja numfashi tana karanta sakon hawaye na cika idonta, kai ta daga sama ta lumshe ido ta bude sannan ta maida idonta a kan wayar, tana kokarin rubuta masa amsa ta WhatsApp din Vito ya turo kofar dakin ya shigo, sai ta yi saurin saka wayar a lock ta dora ta a kan madubi.

 Miye hadinki da likitan da zo duba London da har zai baki card dinsa? Idan wani abun da ya shafi rashin lafiyarsa ne ai da ni zai yi magana

Ta juyo idonta a kumbura ta kalleshi hawaye na sauko mata.

 Waya kalleki? Waya miki magana? Gurin wa kika je? Da wa kika waya? Me ye hadinki da wannan? Ina zaki je? Shi ne kawai abun da ka iya

Ta matsa kusa da shi cikin ihu ta fara fashe mata kurcin dake mata ciwo a zuciya.

 Ni ba ni da ikon kaina, da wa zan yi mu'amala, su waye masu aikina da masu gadina, su waye makota na, a ina zan zauna, duk kai kake zaba min, ka hana in yi abota da kowa, ka hana na yi mu'alama da mutane kamar kowa, takamarka saboda ina zama a karkashinka ne, takamarka saboda ka tsamo ni daga rana zuwa inuwa ne, idan na yi magana sai kace kana so na ne? Taya ina aka soyayya da son kai? Miye banbancinka da sauran ne? Miye banbancinka da Khaleefa sa ya cusa yarda da soyayya a zuciyata ya aureni saboda kawai ya yaudare ni? Banbanta min banbancinka da Turhan mutumen da ya aureni saboda cika umarnin mahaifiyarsa ya maida ni kaskantacciya a cikin bayinsa, sai yaushe ni zan samu yancin kaina? Sai yaushe zan yi farinciki na har abada?

Yin sa'insa da ita ba abu ne da ya saba yi ba, musamman idan ta ci galaba akansa da hawayenta, saboda haka ya zubar da makaman yakin da ya zo da su ya karasa gurin da take tsaye ya rumgume ta. Sai ta cigaba da zubar da hawayen da take.

 Ina tsananin sonki Emily, ban taba son wata mace ba sai ke, kina da kyaun da maza ba za su iya dauke miki ido ba, shiyasa zuciyata ta kasa natsuwa da wasu abubuwan, ina kokarin baki kariya ne, saboda ina jin cewar ke kadai ce mace a duniyar nan, bayan ke babu wata

Ta daga kai tana kallonsa ta san yadda yake ji domin ta taba tsintar kanta a makamancin halin da yake ciki a yanzu, a lokacin da ta yi soyayya da Khaleefa bata ji bata ganin kowa sai shi. Ya sumbancin tsakanin girarta guda biyu sai ta lumshe ido tana tausayinsa da kuma kanta.



ALIYU POV.


Da abincin dake gabansa yayi feeding dinta daman ba wani son cin abincin yake ba a safiyar nan. Sai da suka gama sannan ya hada kayan ya dauka ya kai kitchen, kamar jira ake ya aje plates din sako ya shigo wayarsa kasancewar data sa kullum a bude take. Ciro wayar yai daga aljihunsa ya duba sakon da ya shigo yanzu. Sakon Emily ne da take gargadinsa tare da shimfida masa dokokinta. Bayan ya gama karantawa ya bata amsa, ta sake rubuto masa wani ya aika mata da tambayar abun da ya fi damunta, ta zayyana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login