Showing 228001 words to 231000 words out of 253142 words

Chapter 77 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18411

wanda tun tashin farko ba su so auren da shi ba, a yanzu ma taki ta bawa wasu kofa ne amman ana nuna mata kauna, gata kyakkyawar bazawara sakin Wawa, babu Wa balle abu ya dame ta.

Sai da ta bari kowa ya gama karyawa sannan ta sauko ta nufi dinning kanta na tsarawa kamar zai fashe, ta zuba madara da suga a cup ta zuba ruwan zafi sai kuma ta ji ba zata iya sha ba.
Ta zauna a kujerar tana kallon Anty Shafa dake kwashe kayan wasan yaranta.



EMILY POV.

Kusan wannan ne karon farko da aka daura aurenta ta kwana da cikakke farinciki. Wacan auren nata na farko anyi shi ne a lokacin da iyayen mijinta basa so, kuma bata da wanda ya tsaya mata, tsabanin yanzu da komai kishiyarsa ne, na biyun kuma an daura da wanda bata so be san darajarta ba...

But Aliyu ya zama wani na dabam a gareta, ya nuna mata farinciki da jindadin data kasance matarsa, gashi mahaifiyarsa tana sonta, ga shi yan'uwanta sun shaida. A yau ta kara sanin darajar yan'uwa da dadinsu. Ta farka cike da farinciki, da kuzari tana gama Sallah asuba sakon Aliyu ya shigo wayarta.

"Barka da safiya matata mine and mine only, farar mace mai farar zuciya"

"Barka da safiya Aliyu?"

"Wato Aliyu ko? Idan na zo sai na horar da bakin nan sai na masa hukunci"

Ta yi dariya.

"I'm sorry"

Ta rubuta masa.

"I love you"

Ta maida masa amsa da heart Emoji guda biyu. Sannan ta dauko karatun da suke fara karantawa, sai ga kiransa ya shigo ta amsa tare da amsa sallamarsa.

"Amince ya tabbata ga kyakkyawar yan mata ne mai zazzakar murya, da tattausar zuciya"

Ta yi murmushi mai sauki.

"Tare da jarumin da ya tare komai ya wanzar da farinciki a zuciyata"

"Zai wanzar dai, yanzu ne zai fara aikin, ina nan kwance ina ta tunaninki, kuma na san idan na dako sammako Ummi zata gan ni, dan haka na jira na ji muryarki"

"Na gode da ka kira ni"

"Aa ranki ya dade na gode da kika amsa, za mu iya karatu ta waya? Ko sai na zo?"

"Zaka iya?"

"Ta ina zuciyarki ta samu kwarin guiwar tambayar abun da ba zan iya ba saboda ke?"

"Ina sonka Aliyu"

Ta fada da kwalla a idonta.

"Ni kam kaunarki nake Amaryata wacce ta fi ta kowa, bude littafinki ki fada min abun da kika iya"

"Ni ba na gane komai idan baka kusa da ni"

"Ki sassauta kalamanki, inda ba son kike zuciyata ta fashe da kaunarki ba, da kuma kewarki da na yi a yau fiye da kullum"

Ta yi dariya. Sannan ta fara karatun bakin inda ta iya ya dora matada wani. Bayan sun yi sallama ya aiko mata da sakon.

"I love you"

Ta aika masa da sakon heart.

"No ki ko yi fada min I love you, yana kara damkon kauna kuma ni mijinki ne"

"Okay" as reply

"Okay??"

I love you ta tura amsa.

"I love you more"

Ya maido mata da amsa. Ta kwanta a gurin tana ta kalmomin cike da kaunarsa. Misalin karfe takwas na safe ta fito dakinta ta sauko kasa cike da kunya ta shiga Kitchen domin ta ya Ummi aiki kamar yadda ta saba.

"Yanzu nake kokarin cewa a kiraki, ki shigo ko kara koyar abubuwan da mijinki yake so"

"Ummi ina kwana"

"Lafiya ?alau, an tashi lafiya?"

"Alhamdulillah"

Ta amsa tana jin tsananin kunya abun da bata saba ba. Suna tsaka da girkin ne, daya daga cikin ma'aikatan gidan ya kwankwaso kofar ya sanar da Kulu dake mopping din falon cewar ana sallama da Emily. Kulu ta shiga kitchen ta sanar da Ummi.

"Wake sallama da ita?"

"Ban tambaya ba Hajiya"

"To ki tambaya mu ji, yana ina?"

Kulu ta juya, bata jima ba ta dawo.

"Wai Hajiya Baraka ce"

"Ah ah tana ina?"

"Can wajen gate"

Daga Ummi har Emily fuskar mamaki suka yi.

"Bata shigo ba?"

Emily ta tambaya.

"Eh haka yace tana can waje"

Ummi ta dan yi shiru sannan ta amsa.

"Toh gata nan zuwa"

Sai da Kulu ta fice sannan Ummi ta kalli Emily ta ce.

"Wata kila tana son ta yi wata magana da ke bata son mu ji ko mu gani, ki tafi ki same ta"

"Okay"

Ta amsa sannan ta bude kofar baya ta kitchen din ta fice daman jikinta a lullube yake da Hijab. Ta nufi gate din ta bude a hankali ta fita, ta yi zaton ganin Mama Baraka ne, sai ta yi arba da Turhan tsaye kusa da motarsa. Da ta duba ko'ina bata ga alamar Mama Baraka ba sai ta juya zata koma.

"Ba zan samu damar da za ki saurare ni ba Aisha?"

"Wata kila zaka fada min magana marar dadi ne"

"Aa dan Allah ki saurare ni"

Ta juyo ta matsa kadan ta tsaya tana rumgume da hannayenta. Da ya kalleta sai ya ji kamar be san miye so ba sai a ranar. Cikin yanayi na sanyi jiki da damuwa ya soma magana.

"Na san idan na ce ni ne, ba za a barki ki fito ba, saboda ke da mutanen gidan kuna kallona a matsayin makiyinku ne, shiyasa na yi amfani da sunan Mama Baraka"

Ba ta dai ce masa komai ba har ya dora.

"Aisha zan kara da kara baki hakuri na abubuwan da suka faru tsakaninmu, kasancewarki a rayuwata ya koya min darasi mai yawa, na san zafin so, na san zafin rashi, kuma na san zafin da kika ji lokacin da na juya miki baya, saboda a yanxu ina jin fiye da abun da kika ji, ke kin ji zafi ne kawai amman ba dan kina so na ba, ni kuma yanzu ina fama da tsabanin haka ne. Jiya da dare ban yi bachi ba, ina ganin abubuwan da suka faru kamar a mafarki, amman yau da safe sai na fahimci wani abu, idan kana son mutum ai zaka so farincikinsa ko? In har zaki yi samu farinciki da ni na kasa baki a gidan wani ne, me zai saka ba zan so haka a gareki ba? Idan na ce miki ban yi bakinciki ba na yi karya, ban kuma ce zan warke ba, amman sannu a hankali zan samu salama"

Ya hade yawu.

"Na gode Aisha, da kiyayyata ko tunanin abun da na miki, da wahala bata saka kin zubar da cikina ko jefar da yata ba, na gode da kika kula da Fatima, na gode da kika yi ma Ammy biyayya gurin aurena, a yayin da ni na kasa yi mata biyayya gurin rike amanarki, kuma ina fatar a duk lokacin da wani abu ya taso na Fatima idan na sanar miki za ki shiga ki tsaya mata kamar yadda kika saba, na kawo ne saboda anjima kadan jirgimu zai daga, zata zauna gurinki na dan lokaci, idan na dawo zan dauketa zan tafi Sudan da ita, na yi magana da Ammy ta amince kuma ina fatan ke ma ba za ki, ki yarda ba, ki yi hakuri amman ba zan iya barin yata ta zauna a gidan wani ba"

Hankalin Emily ya tashi.

"Fatima ta yi kankanta ka tafi da ita masarautarku, har yanzu bata san ta banbance daidai da rashin daidai ba, ta yi kankanta ta fuskanci kalubale"

"Kina tunanin zan iya bari a wulakanta ke da kike mahaifiyarta, balle kuma ita? No babu abun da zai faru"

Yana rufe baki Aliyu ya iso kusa da gate din gidan da motarsa. Ya bude motarsa ya fito ya tsaya inda suke, yana kallon Emily da karantar yanayinta sai dai be ce komai ba, ba shi da nufin zafafa domin Turhan uban yarta ne matukar ba yayi kokarin wuce gona da iri ba ne, dole zai bar wata karamar kofa a tsakani. Turhan yayi murmushi yana kallon Aliyu.

"Ina taya murna, ka yi nasara, amman ka sani, ba a cin amana kuma a zauna cikin salama, kai ma nadama zata tambaye ka kamar yadda ta tambaye ni a yanzu"

"Ba zaka fahimce ni ba, amman Wallahi ban tsare wani abu daga gareka ko daga Emily da nufin na raba tsakaninku ba, kuma ban boye komai da nufin na mallaketa ba, ni da kai da ita, muna zagaye ne da kaddara, a jiya da iyayenka suka zo, Wallahi ban tsammaci zan same ta ba, indai har zan iya cutar da kaina to zan iya cutar da kai Turhan"

Turhan ya kalleshi sama da kasa kawai yayi murmushi, ya juya ya bude motarsa ya riko hannun Fatima ya fito da ita, yayi mata alama da ta tafi gurin Mamanta, ta kalli Emily da ke miko mata hannu tana mata murmushi.
A gurin Fatima ta murje ido ta rike rigar Babanta da hannu biyu ta juyawa Emily baya.

"Fatima sweetheart, za ki zauna gurin Momy yanzu kin ji?"

Ta girgiza masa kai ya kara rike rigarsa. Ta kalli Aliyu ta shige da fuskarta a jikin mahaifinta.

"Wani abun ka fada mata?"

Emily ta tambaya tana jin babu dadi. Turhan ya girgiza kai.

"Ban fada mata komai da zai saka ta tsane ki ko ta juya miki baya ba, kina kallona a matsayin makiyinki ne kawai, amman abun ba haka yake ba."

Emily ta matsa ta kai hannu ta riko sai Fatima ta buga hannun Emily tana hawaye ta kara rike Babanta.

"Tun da bata son zama, zan koma da ita idan ta bukaci ganinki direba zai kawota, ina miki fatan alheri ke da sabon ABOKIN RAYUWA"

Emily ta kasa cewa komai idonta ya cika da hawaye bata yi zaton haka daga gurin yarta ba. Turhan ya bude mata mota ta koma ciki ta zauna, ya rufe sannan ya zagaya ta shiga yaja motar ya bar su a gurin tsaye, yana jin wani irin bakinciki da be taba ji ba, amman idan ya juya ya kalli yarsa sai ta ji sassauci.
Emily ta bi motar da kallo tana hawaye har ta daina hangota.

"Kowa na zauna da shi sai ya juya min baya, har da ya..."

Aliyu ya rufe mata baki da sauri, ya juyo da ita ya sakata a kirjinsa ya rumgume, yana shafa bayanta a hankali, babu kalma ki yi hakuri rumgumar kadai sai ta ji hawayenta ya yanke, ta haka take iya gane Aliyu ne ABOKIN RAYUWARTA...
Ta dago kai ta kalleshi sai ya sake ta ya saka hannayensa biyu ya share hawayenta.

"Kuka be miki wahala ko? Zai na zane hawayen nan da suke bata fuskar matata"

Ya bude mata gate yana rike da hannunta.

"Shiga gida"

Ya saki hannunta ta shiga ciki sannan ya koma motarsa ya yi horn aka bude masa ya shiga ciki. Da ya faka harabar gidan sai da ya tsaya ya jira Emily ta iso ta shiga falon sannan ya bi bayanta. A lokacin da ya shiga falon ya ga babu kowa sai ya jidadi yayi hanzarin kamo hannunta ta baya ya juyo da ita.

"Hajiya ba ki gaishe ni ba fa"

"Mun gaisa dazun"

Ta amsa cikin rada kamar yadda yayi mata. Ya rufe baki ya kashe mata ido.

"Aw haka na tuna"

Ta cire hannunta da sauri ta nufi hanyar kitchen. Shi kuma ya nufi stairs yana murmushi. Dakin mahaifiyarsa ya shiga ya same tana daura dankwali.

"Ummi ina kwana"

"Lafiya kalau an shigo?"

"Eh, Ummi sai na samu Ayusher a waje"

"Eh Hajiya Baraka ce ta zo tana sallama da ita"

"Waye yace Mama Baraka ce? Ba ita na samu a waje ba Turhan ne"

Ummi ta kalleshi da sauri.

"Turhan? Wanda aka aiko ce mana yayi Baraka ce"

"Ummi baku bincika ba kuka barta ta fita, yanzu da wani ne da zai cutar da ita fa? Da yanzu ni za a bari a matsala"

"Na yi zaton ko tana son magana da ita ne Private, ita ma da ta fita ta ga ba ita ba ce ai sai ta dawo"

"To ina zata san wannan idan tana son magana da ita ai ga dakuna ko kuma ta aiko a dauketa, amman sai a bari ta fita a bincika ba kuma ba a bi bayanta"

"Aisha ce ba zata san ta dawo ba?"

"Eh mana, duka duka nawa Ayusher take? Wannan tunanin ba zai zo mata ba, yanzu ne fa kwakwalwata take girma"

Ummi ta saki baki tana kallon Aliyu da a bakin gaskiyarsa yake maganar.

"Toh za a kula next time, yanzu dai ka dawo da ita ko yaya?"

"Ai ba zan bar yarinya karama a waje ba"

Ummi ta yi murmushi kawai ta nufi kofa ya biyo bayanta. A falo suka rabu ta nufi bangaren Daddy shi kuma ya nufi dinning din da matarsa take zaune tare da Nafeesa. Nafeesa na gaishe shi ta mike tsaye ta fice dinning din domin ba su damar karyawa su kadai ba tare da takura ba.

"Kika yi serving kanki? Baki bari na zuba miki ba?"

Ta mike tsaye.

"Bari na zuba maka"

"No it's my duty to feed you, zauna zan zuba da kaina"

Ta koma ta zauna tana murmushi. Ya zuba ma kansa tana cin abincin yana kallonta har ta aje spoon.

"Kin koshi?"

Ta daga mishi kai.

"Ba ki ci da yawa ba, ko wani abun kike so dabam?"

"Aa"

Ta amsa, ganin Nafeesa ya saka ta jin kunya sai ta mike tsaye.

"Bari na dauko wayata"

Aliyu ya juya ya kalli Nafeesa.

"Idan kika aje plate din ki dauko mata wayarta"

Nafeesa ta amsa da tohm. Emily ta koma ta zauna tana dan jin kunya. Nafeesa ta dauko mata wayar ta kawo tana mata wani kallo na zolaya. Emily ta karba ta rike

"Thank you"

Nafeesa ta yi murmushi kawai ta koma ciki, sai a lokacin Aliyu ya sake kallonta ya ce.

"Kamata yayi ta ce you're welcome Mrs Aliyu ko?"

"Idan Ummi ta zo ta same ni a nan zata ce ba ni da kunya"

"Haka fa, ke ce mai kunya ni ne marar kunya ko?"

Ta yi dariyar da bata shirya ba ta sauke kanta kasa tana taba wayar. A nan ta yi arba da sakon da ya sauya murmushin fuskarta zuwa tashin hankali. Tuna Aliyu na gabanta ya saka ta yi kokarin boyewa da murmushin dole.

"Miye?"

"Ba komai"

"Vito ne? Ko Kameela?"

"Miyasa ka zarge su?"

"Saboda Turhan be jima da barin gidan nan ba, ba zai yiyu ya miki wani sako na tashin hankali da zai bayyana a fuskarki ba, ko mutuwa yayi ba ke za a sanarwa ba, amman Kameela zata iya aiko miki da sako marar kyau, haka ma Vito, cikin biyu dole a samu daya"

"Vito ne"

Ta fada kamar zata yi kuka. Aliyu ya tashi daga inda yake zaune ya zagaya gefenta ya karbi wayar.

"Congratulations kin yi aure ko? Kin yi min butulci Emily kuma dole ki dandana dacin hakan, ke da wannan Balaraben da ya aure ki, ke da fitinanniyar yarki"

Aliyu ya ciro wayarsa ya kwafi number ya saka a wayarsa bayan ya gama karanta sakon, sannan ya tura masa da sako da wayarsa.

"Ba Balarabe ne ya aureta ba, ni ne na aureta mutumen da ya janyo ta daga PH zuwa Kd, mutumen da suka yi aiki tare, wawa ka zo ka tare ni mana, miyasa kake tsoro?"

Ya kalleta.

"Daman na yi tunanin zai samu number duk da yake sabuwar number ce, amman mai son abun ka ya fika dabara, kuma zuciyata ta raya min yana bibiyar rayuwarki, amman yanzu an zo karshe da yardar Allah, tun da har giyar hauka ta dauke shi ya turo wannan sakon za a gano inda yake"

Emily ta mike tsaye.

"Kashe shi za'ayi?"

A kokarin Aliyu na kwantar mata da hankali ya ce.

"Aa za a dai kama shi, sai a gabatar da shi gaban kuliya saboda kar ya cutar da kowa, haka yayi miki?"

Ta daga kai.

"Zauna kin ji yan matana, bari na nunawa Daddy wannan sakon, kuma zan sanar da Ammy halin da ake ciki, ba lallai idan na yi magana da Turhan ya saurare ni ba, amman na san Ammy zata dauki abun serious"

Ta koma ta zauna ya nufi hanyar da zata sadashi da bangaren Daddy, sai kuma ya juyo ba shi da nutsuwar barinta a falon jin yake kamar wani abu zai same ta.

"Shiga dakin Nafeesa ki zauna, kuma kar kowa ya sake sallama miki ki fito ko ni ne, mai son ganinki ya zo ya same a nan"

Ta sake tashi, zuciyarsa bata bar shi ba sai da ya rakata har bakin kofar dakin Nafeesa ya bude mata ta shiga.


"Karki bar yarinyar nan ta fito, idan ta bata ke na sani"

Ya bugawa Nafeesa warning, sannan yaja kofar ya rufe ya nufi bangaren Mahaifinsa.




TURHAN POV.


Ammy bata yi mamakin ganin ya dawo da Fatima ba, daman ta lura tun kamin su tafi bata son tafiyar, tun jiya tana jikin ubanta tana taya shi jimami ko abinci sai da ta ga yana ci sannan ta ci.

"Shiga ciki ki yi kallo"

"Dady ba zai tafi ba?"

Ta tambayi Ammy dake bata umarnin.

"Eh"

Tohm"

Ta amsa sannan ta nufi hanyar dakinta.

"Fatima"

Turhan ya kirata sai ta juyo, ya tafi inda take ya rumgumeta sosai yayi kissing dinta ita ma ta yi masa kiss.

"I love you"

"I love you Too Dady"

Ya sake ta yana murmushi, ya bita da kallo har ta shige sannan ya dawo kusa da Ammy.

"Bata yarda ta zauna can, ko magana bata yi da Emily ba"

"Daman na ga alamar ba zata zauna ba"

"Ni zan tafi Ammy, anjima kadan jirgimu zai ta shi"

"Ba zaka bari sai next week ba"

"Garin ne baya min dadi gara dai na tafi kawai, ko zan samu salama"

Ammy ta mike tsaye ta bude masa hannayenta sai ta matsa kusa da ita ta rumgume uwarsa.

"Jikinka da zafi sosai Turhan, baka da lafiya ne?"

"Zazzabi ne kadan na ke ji"

Ta sake shi tana taba fuskarsa da jikinsa.

"Ba kadan ba ne, ko'ina ya maka zafi fa, gaskiya ba zaka yi tafiyar nan a yau ba"

Turhan ya zube kasa ya rike kafafuwan Ammy yana kuka kamar ba shi ba.

"Ammy dan Allah ki yafe min, bijirewa umarninki ne ya jefani a halin da nake a yau, da ace na bi yadda kika tsara, da yanzu ban shiga wannan damuwar ba, da yanzu ban shiga wannan bakincikin ba"

"Na yafe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login