Showing 45001 words to 48000 words out of 253142 words

Chapter 16 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18443

min Ammy

Fuskar tausayi ta bayyana a fuskar Ammy.

 Baka fada min baka sonta ba a lokacin da na hada aurenku ba ba zan cilasta maka ba, Allah kadai ya san kalar azabar data sha a hannunka da masarautarku, baiwar Allah

Ya dago yana kallon Ammy cike da mamaki, shi a tunaninsa idan na fada mata duk wannan zata tausaya masa ne, madadin haka sai ta kara jin tausayin Emily din ma.

 Haka ne, kaskanci ne auren wanda ba bata tashi a addinin musulunci ba, kuma wanda ba yarenka ba, ba yar sarauta ba ina mai baka hakuri akan hakan Dan sarauta

Ta mike tsaye ta fice daga dakin.

 Da ace zan samu damar yin ido biyu da Emily a yanzu, tabbas zan bata hakurin saboda Ammy, amman bayan kwana biyu sai na hada ita da bokanta na kashesu, yarinya kamar mayya gaba daya ta tafi da zuciyar Ammy, ita wacan katuwar kafirar maganin be kamata ba sai Ammy, ni kadai ta haifa a duniya amman yanzu ta tsane ni saboda wata shegiyar yarinya.. 9'1 9DJC J' %EJDJ,
 9'1 9DJC

Yama fadar yana wargar da hannu, be san kaskanci da wulakanci ba sai da Emily ta duro gidansu, tashi yayi ya fice daga dakin ya shiga dayan dakin yayi waya da matarsa da mahaifinsa sannan yayi wanka ya fito falon.

 Tun kamin na yi aure, ina addu'ar idan na yi aure Allah ya bani ya mace, sai gashi kuma da na yi auren na haifi namiji, sai ya zama ba zan sake haihuwa ba, a lokacin da Aysha ta zo gidan nan sai na ji kamar addu'ar da nake yi ce a can baya Allah ya karba min ya ba ni ya mace ta wani bangaren da ban yi zato ba, yarinyar nan ta tsaya min a rai

Labarin da ya sauko ya samu Ammy na bawa Jawahir kenan, Jawahir din kawai ya kalla yana ayyana munafurcinta a zuciyarsa ya fice ba tare da ya taba abincin da aka jera masa a dinning ba. Bayan fitarsa Jawahir ta kalle Ammy.

 Dan Allah Ammy ki yi hakuri ki cire Aysha a zuciyarki, ki kaddara ta mutu, ki shirya da Ya Turhan ku dawo kamar yadda kuka a da, Wallahi tausayi yake ba ni

Ammy ta kalleta tana murmushi.

 Baki san waye mahaifin Turhan ba shiyasa yake baki tausayi, larabawa suna da zuciya mai tauri, shi kuma ai jinin mahaifinsa, nonon ma na larabawa ya sha ba nawa ba, kar yi mamaki idan aka ce miki ya sake aikata kuskure bayan wannan

Jawahir ta sauke ajiyar zuciya tana girgiza kai cike da tausayi.


ALIYU POV.

 Tun jiya da aka kawo ki asibitin nan kike fushi da ni, ko dan rantsuwa da alkawarin da na daukar miki ai ya kamata ace kin yarda da ni

 Cikin alkawarin da rantsuwar ai na ga chat dinku

 Ke yanzu ko a mafarki aka ce miki ina son Emily zaki yarda

Ta dube shi kamar zata yi kuka.

 Har ka rike sunanta ma

 Turhan fa ya auri yarinyar nan kuma har sun haihu da ita, Turhan kuma abokina ne mahaifiyarsa kamar uwa take a gareni, taya zan iya soyayya da ita ma balle har nace zan aureta? Kuma addininmu ba daya ba, ba abun da kike tunani ba ne

 Yanzu dai gashi nan ai ka janyo min nakuda Edd na be cika ba amman gashi nan nakuda ta same ni, kuma gashi sun ce idan ban haihu da kaina ba za su min CS

Ya rumgumeta.

 Zaki haihu da kanki lafiya In Shaa Allahu

 Me yasa ba zaka fadawa Turhan gaskiya ba, bayan kasan nemanta yake idan har baka da wata manufa akanta? Ka san yadda Turhan yake son haihuwa amman baka fada masa yana da ya ba, idan baka da wata mummunar manufa akansa miyasa ka yi haka?

Tana maganar tana cige baki tana numfashi da karfi.

 Idan Allah yasa kin haihu lafiya wan warware miki komai

 Allah dai yasa na haihu lafiya, Allah yasa na tashi Wallahi babu wanda zata aurar min miji Wallahi Allah kuwa na rantse

Shi dai kallonta kawai yake be yi zaton tsananin kishinta ya kai haka ba sai yau.

 Ummi bata iso ba har yanzu?

 Ta iso kin san ai ta fi kusa, ta sauka gida ne sai ta yi wanka zata zo, su Hajiya ma suna hanya

 Ka min addu'a Aliyu

 Ina ta yi

Ya shafa kanta yana ta karanta mata addu'o'i.
Misalin karfe goma sha daya na safe iyayen Kameela suka iso asibitin, a lokacin nakudar ta taso mata gadangadan ya fito waje sai addu'a yake yana kai da kawo. Da waya ya kwatanta musu gurin da yake har suka iso, kana kallon mahaifiyarta zaka fahimci tana cikin tashin hankali haka ma yayarta. Cikin ladani ya gaishe su kamar yadda ya saba mahaifiyar ta amsa rai a hade domin Kameela ta labarta mata komai ta waya.

 Hajiya ai da kun wuce can gidan kun dan huta tun da ni ina nan

 Aa kara dai zamana kusa da yata, tsayuwarka a nan wani amfani yayi mata, ba kai ne sanadin duk wannan ba

A take Anty Shafa wacce ta kasance yayar Kameela ta karbe zancen Hajiya ta dora da nata.

 Gaskiya Aliyu baka kyauta ba, kasan matarka tana da ciki be kamata kana yin wasu abubuwan ba

Aliyu ya kalli Anty Shafa da duba na tsanaki.

 Me tace na yi.?

Ta yi shiru bata ce komai ba, sai dauke kai da tayi. Ya ciro wayarsa yana amsa kiran mahaifiyarsa.

 Okay Ummi bari na zo na dauke ki

Ya sauke wayar, ya kalli sarakuwarsa.

 Zan je na dauko Ummi daga gida yanzu

 Toh

Ta amsa masa a takaice cikin bacin rai. Aliyu ya saka kai ya fice cikin rashin jindadi, daman ya san za a rina domin Kameela bata da sirri ko kadan mu'amalar auratayya ma sai ta fadawa kawaye ta, be yi mamakin dan ta fadawa iyayenta sanadin nakudarta ba, wannan halin nata na rashin sirri yana bata masa rai sosai.
Ko da ya isa ya samu Ummi a harabar tana jiran isowarsa.

 Ummi madadin ki zauna a ciki kika fito waje

 Idan ka iso ai zaka iya dadewa shiyasa na tsaya jiranka a nan, mu tafi

Kamin ta shiga motar ya fito da sauri ya zagayo ya rumgume ta.

 I miss you Ummiiiiii

 Kai wai baka san ka girma ba, baka jin kunyata

 You're my best friend my first love

Ya je zai sumbance ya ta tureshi ta bude motar ta shiga, dariya yayi ya koma motar yaja suka fice daga gidan, suna tafi suna hira har suka isa asibitin ya zagaya ya bude mata ta fito ya suka jera zuwa gurin da ya bar su Hajiya dazun.
Ummi na hango Hajiya da Anty Shafa ta kalli Aliyu.

"Kasan ka fadawa iyayenta sun zo to ni miye na fada min na zo?

 Ke ma ai mahaifiyarta ce

 Idan ba mahaifiyarta a kusa ba

Ummi ta dan sham kamshi domin ko kadan bata son raini. Anty Shafa ce ta fara gaishe da Ummi sannan Hajiya ma ta miko mata gaisuwa.

 Lafiya kalau

Daga Hajiya har Ummi babu wanda yacewa wani an iso lafiya.

"Allah dai yasa ta haihu da kanta, idan ba ita ba haushe zaka dauki halin da namiji ka saka a zuciya

Cewar Anty Shafa. Ummi ta yi kasa da ido tana saurarenta, kamin ta dago ta kalleta tana murmushi.

 Shafa ya yaran? Ya Step Mom dinku? Har yanzu dai shiru kin ki kawo mana kati?

 Ina nan ina lalabe Ummi kin san mazan sai a hankali, yara suna lafiya

Ta amsa cike da gatse.

 Haka ne Allah ya kawo na gari

 Ameen

Ta amsa. Aliyu ya ciro wayarsa dake ringing ya fice daga gurin, Ummi kuma ta nemi guri ta zauna Hajiya nata safa da marwa tana daga hannu tare da rokon Allah ya saukar da Kameela lafiya.

 Ameen ya rabbi, idan ba sakarci irin na Kameela ba, yaushe namiji zai maka alkawarin ba zai kara aure ba ka yarda, gashi nan ta jawa kanta nakudar dole

Hajiya ta juyo ta kalleta.

 To miye laifinta? Allah dai ya bude mana idonta lafiya?

 Ameen

Ummi dai bata ce komai ba sai saurarensu take, ta san kuma saboda ita ake yi dan ta ji. After like one hour Kameela ta sauka lafiya sai dai abun da ta haifa be zo da rai ba. Hakan kuma be hana iyayenta mijinta da surukar murna ba domin ita dai ta haihu lafiya bayan ta sha wahalar nakuda.
Sai da Aliyu ya rada ma yaron suna sannan aka yi masa sallah aka binne shi a makabarta musulmi dake garin Part-harcour.
Ko kadan Aliyu be jidadin yadda yaron ya zo babu rai ba, sai dai babu yadda xa'ayi da hukuncin Allah sai hakuri, ganin yanayinsa ya saka Ummi ta hade maganganunbda take da su a zuciyarta ta daga masa kafa.
[4/22, 9:24/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/GATlsEHRyd2HW1OjrdF5AL




*? Khadeeja Candy*

SARAC STARS. C - Pen...
'?


Page 1?? 5??

Ta hado tea ya kawo ma Ummi.

 Ni ba irinka bace, me zan yi da tea yanzu da yamma"

Murmushi yayi ya zauna yana updating status dinsa domin sanar da duniya matarsa ta haihu amman dan be zo da rai ba. Bayan ya gama ya aje wayar ya kai hannu zai dauki tea kiran Kameela ya shigo wayarsa, fasa shan tea yayi ya dauki wayar.

 Hello...

"Kana ina

 Ina gida

 Tare da wa?"

Ya kalli Ummi sannan ya amsa mata

"Tare da Ummi"

"Na ji Hajiya tana maganar wai zata tafi da ni gida gobe idan an sallame ni

 Kamar al'ada ce ko mace ta koma gida idan ta yi haihuwar fari

"Bana son na barka, ni bana son tafiya, za a iya min komai a nan mana"

"Haka ne amman idan ta nuna tana son tafiya dake ba zamu iya hanawa ba

 Ina son idan ta maka maganar tafiyata kace mata aa kana son na zauna a nan din"

Yayi shiru be ce mata komai ba jin hakan ya saka ta kashe wayarta, domin ita ma ta san mijinta ba kasafai take saka shi abun da be yi niya ba.

"Kameela ce?

 Bata son tafiya gida, ni kuma ba zan iya jayayya da iyayenta ba, bana son abun da zai kawo mana rashin jituwa musamman da Hajiya

"Rashin jituwa na nawa kuma? Bayan wanda aka sha kamin auren?

 wacan ai ya wuce Ummi, kuma tun daga lokacin sun san ni ba kanwar lasa ba ne, Aliyu kike ji fa Ummi

Ya fada yana murmushi, Ummi ta tabe baki.

 Aliyu soyayya? Romeo baban kauna, sharukan din masoya? Mai alkawarin da ba zai iya cikawa ba

Ya kalleta da dan mamaki still yana murmushi.

 Ummi ina kika samo duk wannan kuma?

 Baka yi alkawarin cewar ba zaka kara ma Kameela abokiyar zama ba?

Ya rausayar da kai.

 Ta fada miki ne?"

 Aa ai kasan iyayenta ba yan dattako ba ne, sun fada dan na ji kuma na ji"

Ya shafa kansa.

"Idan baka yi hankali ba, kishin Kameela sai ya halakata ya jefaka a matsala, domin zafin kishin yayi yawa, madadin kai kuma ka nuna mata abun da take yi kuskure ne sai kawai ka shimfida mata tabarma ta hau, akan wane dalili zaka mata alkawarin ka haramtawa kanka abun da Allah da kansa ya hallata maka? Kai da malami ne Aliyu, ban yi tsammanin wannan daga gareka ba

 Ummi baki fahimta ba ne

Ummi ta hade rai.

 Toh fahimtar da ni

Ya gyara zamansa ya aje wayarsa gafe.

 Ummi ke kika haife ni, kin san halina ciki da waje, tun kamin na yi aure ke kin sani, bana da ra'ayin auren mace sama da daya, Allah ya hallata mana auren mace mace sama da daya ne idan zamu iya adalci, shi kuma adalci wani abu ne mai nauyi sai dai mu kwatanta, ni kuma bana son na aikata wani abun da zan tashi a gaban Allah wani dan'adam ya tuhume ni da shi, kuma Ummi kin san iya gwagwar mayar da muka sha kamin iyayenta su yarda su ba ni aurenta

 Saboda an yi fadi tashi sai ya saka ka zo ka yi mata alkawarin da ni na san wata rana sai ka karya shi, mata na mahaifinta yake aure bayan Hajiya? Ina ce matansa uku, ai ta tashi ta ga ubanta da mata biyu ko bayan mahaifiyarta, sai kai dan ta raina ka zata saka ka yi mata alkawarin ba zaka kara aure ba, yan'uwanta ma saboda basu da kunya za su nemi fada min magana

"Wata kila yanayin abubuwan da suke faruwa gidan su na kishin ne ya saka take tsoron kishiya, amman me Hajiya ta fada miki? Sun miki wata maganar marar dadi ne?"

Ya tambaya yana jiran amsarta, karamin aikinsa ne ya daga waya ya kira Anty Shafa da take yayarta ya ci mata mutunci akan Ummi, bayan kuma abun be kai ya kawo ba.

 Wannan maganar suka fada mana, ni ba zance ka kara aure ba, domin Kameela bata min komai ba ta rike ni kamar uwa, family ta ne dai ba su da mutunci shiyasa ake son idan za'ayi aure a nemo yar gidan mutunci, ka karanta ka gani amman duk ka tsallake wannan ka aurota

 Kameela tana da tarbiya Ummi, tana da biyayya daliba tace fa, tana da ilmi daidai gwargwado, ita dai bar ta ga rashin sirrin sai kuma zafin kishi, kuma duk mace ba zata rasa wannan ba, kuma ni ba cilasta ni? na yi mata alkawari ba, na mata alkawarin ne da yakinin zan cika kuma zan iya, saboda ina son kwanciyar hankalinta da farincikinta, kamar yadda Daddy na yake son matarsa

Ummi ta watsa masa harara.

 Dan iskan yaro, ai ni ban hana Daddynku aure ba, kuma ban ce yayi min alkawarin ba zai kara aure ba, kawai be yi niya ba ne, waya isa ya hana Daddynku abun da yayi niya?

 Tohm Daddyna zan gado

 gamu gani ai, farin tuwon nan dai cikin bakar tukuyar can ya fito, muna nan da kai wata rana sai ka zo min jikinka na rawa kace zaka kara aure, saboda iyayenta ba yan mutunci ba ne, kuma ba su so aurenka da ita tun farko ba, na lura matukar ba kashe auren nan suka yi ba hankalinsu ba zai kwanta ba

 Haba Ummi ke ma kin san idan na auri mace ta auru Wallahi, aje dai sama a dawo a shiga wuta da ruwa a mutu ayi rai amman ba zan sake mace ba, noooo saki be ma cikin abun da nake magana, ni dai ina son matata, matata kuma tana so na to duk abin da zai biyo baya daman dole mu yi hakuri da shi

Ummi ta tabe baki.

"Allah ya baku zaman lafiya"

"Ameen, Ummi ke ma yanzu dai kamar Kameela ta fita ranki"

"Aa ina sonta, ai tana mutunta yan'uwanka kuma tana sonka tana girmamani, ni kawai familynta ne bana so, abubuwan da suka yi ta yi kamin aurenku har yanzu ban manta ba

Yayi murmushi kawai be sake cewa komai ba, Ummi ta dauki wayarta tana amsa kira, shi kuma ya shiga amsa sakwannin dake shigo masa. Sai dare Ummi ta koma asibitin tare da Aliyu, Kameela ta tarbe ta da hannu biyu Ummi ta zauna kusa da ita tana mata sannu. Sai kusan goma Ummi ta yi mata sallama ta fita Aliyu ya mike tsaye.

"Zan je na kaita gida na dawo, gobe zata wuce jirgin Safe zata bi"

"Okay sai ka dawo"

Ya matsa kusa da ita ya sumbance.

"Sai wani shinning kike kamar ba haihuwa kika yi ba, kumburin nan ma ya miki kyau"

Ta yi murmushi.

"Ba zaka yi ma Hajiya magana ba? Ina jin tana maganar tafiyar fa, gashi sunce gobe za su sallame ni

"Idan an tafi dake zan zo na same ki"

Murda kofar dakin da aka yi ne ya saka shi aurin janye hannunsa a jikinta ya matsa baya. Anty Shafa ce ta shigo tana hamma.

 Yauwa Aliyu Hajiya tace ka hadowa Kameela kayanta a zo da su nan gobe za su wuce idan Allah ya kaimu"

Ya kalli Anty Shafa fuska ba yabo ba fallasa, kamin ya juya ya kalli matarsa.

"Me da me zan dauko miki my love"

Ta dan bata fuska kamar zata yi kuka, ita ganin take idan bata kusa da shi zai kalli wasu matan ne, kuma kamar ta bashi damar magana da Emily ne.

"Ba sai ka dauko komai ba, zan siya a can

Yayi murmushi kawai ya fice. Sai da ya fita sannan Anty Shafa ta zauna tana fadin.

 Abun dai be yi ba, kin haihu ace uwarsa wai zata koma gobe gobe kuma jirgin safe zata bi, kamar dai bata sonki, shi kansa ban ga yana wani daukinki ba

Kameela ta hade rai tana magana a shagwabe.

 Kin ga Anty Shafa ki daina zarga min uwar miji, kuma ni mijina yana so na na sani

 Gaki ga shi ai indai namiji ne, har zai miki alkawari ki yarda, ba gashi kin janyowa kanki ba har kin rasa danki? Farawa da iyawa kenan daga chat da mata sai zancen kara aure, muna nan dake sai Aliyu ya saka ki kuka da bakinciki, ba namiji ba, can talkaminmu suka tsinke"

Kameela dai ta yi shiru bata ce komai ba, sai dai ranta babu dadin tafiyar da zata yi da kuma kalaman da Anty Shafa take fada akan mijinta. Aliyu be dawo dakin hannu sake ba sai da kayan kwalama da kuma akwati daya babba ya saka mata abubuwan da ya san za su mata amfani, ko ba su fada masa ba ya fahimci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login