Showing 183001 words to 186000 words out of 253142 words

Chapter 62 - ABOKIN RAYUWA Hausa Novels by Khadeeja Candy.doc

23 Nov 2025

18444

ta zauna tana sanye da short gown da sarkar cross a wuyanta, AB ya zauna kusa da ita.

"Zauna mana, ni sai nake ganin kamar na san fuskarki"

Emily ta zauna tana rike da hannayenta.

"Mun taba haduwa wata rana a Sudan, ke kika zo da ni Nigeria"

Da mamaki matar ta sake kallon Emily.

"Anyi haka, ke ce? Wannan baiwar da aka ba ni sadaka?"

Emily ta daga kai, AB kuma ya shiga rudani.

"Kun taba haduwa?"

"Yeah, kai ya ka hadu da ita?"

Ya fada mata, sai ta kalli Emily tace.

"Meyasa kika gudu a gidan matar da na hada ku?"

"Saboda na miki karya a wacan lokaci na fada miki an siyar da ni, ba siyar da ni aka yi ba, wani na aura dan sarki garin shi kuma yaje da ni a matsayin baiwa"

"Zan iya saninki? I want to know more about you, why do you lie"

Emily ta fara hawaye.

"Saboda ba zaki yarda da ni ba idan na fada miki dan gidan nake aure, kuma ba zaki yarda ki taimake ni ba"

Dr AB ya kalli mahaifiyarsa.

"Momy wannan ba lokacin da ya kamata ayi wannan maganar ba ne please"

"Why? Ya kamata mu san wacece ita, saboda ita ka yi ma mijina karya ya bada jirgi aka dauke ta, and because of her ka roki mijina ya kula da duk wani responsible nata tun daga kaduna har zuwa nan, ya kamata mu san da wa muke zaune a nan"

"Yeah amman ba yanzu ba, she's Cristian"

"Matsalar bata addini ba ce, idan kana son mu'amala, kawance ko aure musulma ko wanda ba musulma ba, wannan ba matsala ba ce, matsala shi ne mu san wacece ita"

"Zan iya baki labarina idan kina so"

Dr A-B ya mike tsaye da sauri ya koma kusa da Emily ya zauna tana hawaye ya rumgume ta.

"No ba yanzu ba"

Momy ta kalleshi kamar bata jidadin rungumar da yayi ma Emily ba ta mike tsaye.

"I'm sorry Son bana nufin bakanta mata, kuma karki dauki hakan a matsayin wani abu, as long as my only son was the one bought you here you're welcome"

Dr A-B ya bata rai alamar be jidadin Momy ta yi ba, ita kuma bata sake cewa komai ba ta koma dakinta. Emily ta daga kai ta kalleshi.

"Ya zan yi da rayuwa? Ji nake kamar zuciyata zata tsaya"

Ya kara rumgume ta.

"Ya isa haka"

Ta share hawayenta ta raba jikinta da na shi.

"Zan iya komawa dakin da ka sauke ni"

"Yeah"

Ya bita da ido har ta fita falon, sannan ya mike tsaye ya shiga dakin da Momynsa take. Tana fitowa falon ta fara saukowa kasa tana hawaye madadin ta tsaya hawa na biyu inda ya sauke ta sai ta sauka kasa gaba daya tsabar hankalinta baya jikinta, ta shiga wani dakin dake falon na farko tana shiga ta ga ba nan ba ne ta fito ta bude dayan dakin nan ma ba sha ba ne nan ma kuka ya ci karfinta ta durkusa tana kuka, laifi take dorawa kanta domin da ace bata biyewa so ba da yanzu Khaleefa be kaita ya baro ba domin shi ne silar faruwar komai.

"Ba haka ake tarbar bako ba, abun da kika yi a yanzu kin kara jefata ne a damuwa kuma baki san iya halin data shiga ba, ba ita ta nemo ni ba ni nake ta kokarin shiga rayuwarta"

Ta aje littafin dake hannunta.

"I didn't ask her to leave, i didn't say she's not welcome, all what i asked her is who she is, ya kamata musan idan ya cancanci duk abubuwan nan da kake mata, kuma ya kamata mu san da amintacciya muke zaune"

"Kina da gaskiya, amman ba a irin wannan lokacin da yanayin ya kamata ki yi wannan maganar ba, kina ganin ganin yarinyar nan kin san akwai damuwa a tare da ita, ni na san yadda damuwa take, ta kan saka mutum ya hauka ko ya fita hayyacinsa, wani ma baya iya bayyana matsalar sa saboda yana jin kamar ba za a fahimce shi ba, tun farkon haduwana da yarinyar nan Allah ya hada wata alaka mai karfi a jinina da nata, na ji ta yi min ta kwanta min a rai, and duk lokacin da zan sake haduwa da ita sai na karanci damuwa a tare da ita, shiyasa nake ta shiga rayuwarta saboda ma taimaka mata"

"Aikinka shi ne duba masu damuwa ka ba su magani not to take their responsibility"

"I thought you want me to get married? Ko da yaushe kina fadar kina son na canja, why all this now?"

Ta yi shiru kawai tana kallonsa. Sai ya juya zai fice.

"I'm sorry Son I'm sorry, bari na yi magana da ita a falo"

"Already ta sauka, ba sai kin yi ba i will talk to her"

"Bari na sauka da kaina na yi magana da ita"

Ta mike tsaye ta aje littafin dake hannunta fice daga dakin ta fito falonta, ta sauka hawa na farko Dr A-B yana biye da ita, shi ya fara shiga dakin ya duba ya duba be ganta ba, ya leka bandaki bayan yayi knocking nan ma bata ciki sai ya fito ya duba sauran dakunan da suke jere da nan bata cikin ko daya ya sake sauka kasa gaba daya ya ya bude dakunan dake falon na kasa, yana bude daki na biyu ya same ta kwance a kasa tana hawaye.

"Emily"

Ta dago da sauri ta kalleshi tana jin zuciyarta na mata wani mugun ciwo.

"Na manta dakin ne I'm sorry"

Ya karasa inda take ya rikota ya mikar da ita tsaye, sai Momy ta karasa kusa da ita.

"I'm sorry, bana nufin bata miki rai, ki yi hakuri na yi kuskure, amman ina fatan zaki fahimce ni bari na rakaki dakinki"

Ta kama hannun suka fara tafiya.



TURHAN POV.

Shiru yake a jirgi har suka sauka, saboda ya bar zuciyarsa a gidan Ammy be tafi da ita ba, wato Fatima ko da ya bar gidan ma tana bachi bata san ya tafi ba, sai sumbantarta yayi ya dauki hotonta ya tafi shi ma baya son ta ga tafiyarsa tace zata bishi Ammy ta hana. Ya sauka airport din yayi waya aka zo aka dauke shi kamar yadda aka saba, sai dai abun da be saba ba shi ne fara ganin mahaifinsa bayan sauka gida, a yadda al'adarsa take idan ya dawo yana shiga bangarensa ya huta ne sannan ya fito gaishe da mahafinsa, amman wannan karon motar na isa masarautarsu ya umarce direban ya faka harabar fadar mahaifinsa, yana jin kamar ba shi da natsuwa idan be ji dalilin kiran da mahaifinsa yake masa ba.

Ko da ya shiga fadar ya samu mahaifinsa da baki, haka ya zauna har sai da mahaifinsa ya samu sarari sannan ya doshi can cikin fadar bayan ya saka an sanar masa da bukatarsa ta son ganinsa. Kamin ya karasa Ammy ta kira wayarsa ta fada masa Fatima ta fara kuka saboda be dawo ba, ta mata karya cewar ba nesa ya tafi ba.

"Kuka take ne?"

"Eh tana tashi bachi dakinka ta fara lekawa ta fito baka ciki sai na fada mata ka tafi ka dawo, tun dazun take tambaya yanzu kuma ta fara kuka"

"Bari na kira Video Call sai ki ba ni na yi magana da ita"

Ya katse kiran ya kirata FaceTime sai ta kara masa Fatima dake kuka yayi magana da ita yana rarrashinta Ammy na fassara mata har ya samu ta yi shiru. Ya tabbatar mata da gobe zai dawo.

"Idan ka dawo ba zaka sake tafiya ba?"

"Eh, ba zan sake barinki ba Fatima na yi alkawari, i love you"

"I love you too"

"Zaka zo tare da momy? Zamu zauna a nan?"

"Eh, zamu zauna a tare Fatima zamu zama Family daya"

"Okay bye"

Ta masa waving shi ma ya daga mata yana jin kamar yayi kuka domin yana matukar son yarinyar nan fiye da komai, sai da ya maida wayar aljihu sannan ya kunna kai a karamar fadar mahaifinsa cike da amsar tambayoyin da ya san mahaifinsa zai masa.




_________

Ayi hakuri, muna biki ne. =?O?





_______________________

Sannu  yan uwa mata! Kin gaji da kayan da ba su da salo, ba su da inganci? To yanzu lokaci ya yi da za ki sabunta wardrobe Winki da kaya masu kyau, masu ?ima daga Khadeeja Candy Store

Muna da abaya masu kyau irin na zamani, masu sau?in sakawa da jituwa da dukkanin lokaci whether ki je wurin biki, ko casual outing.

Kuma fa, ba abaya kawai ba muna da bedsheet masu launin kwantar da hankali, masu kyau a gani da taSawa. Idan kina son daki ya zama kamar hotel, to bedsheet Winmu sun dace da ke

Kayanmu masu kyau ne, farashinsu? Ai sai kiyi mamaki sau?i ne sosai. Muna nan a Kano State, kuma muna delivery zuwa ko ina!


Ki danna follow yanzu, ki biyo mu a TikTok https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

da Instagram https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0


Ki ga sabbin kaya masu kyau da rangwame.

Zaki sami kayan Kitchen masu inganci, kayan sakawa na zamani, da electronics masu ?ayatarwa duk a farashi mai sau?i.

Za ki iya saka tufafinmu ki fita lafiya, kitchen dinki kuma ki kawata shi da kayan Kitchen dinmu, da bedsheet dinmu kuma za ki yi barci cikin annashuwa komai daga shagonmu!

Baki da lokaci? Muna da sau?in oda ta waya ko WhatsApp - 08036126660 muna aika kaya zuwa ko ina!

To me kike jira? Biyo mu yanzu a WhatsApp https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


Ba kawai kaya ba ne salo ne, ?ima ce. A Khadeeja Candy Store.
Ki zo yau, ki WanWani bambanci, Khadeeja Candy Store inda kyau da salo ke haWuwa.
[7/27, 8:34/ PM] 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??: https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08


*

*? Khadeeja Candy*



FOLLOW ME ON =?G?
FACEBOOK
https://www.facebook.com/profile.php?id=100008156177914

TIKTOK
https://www.tiktok.com/@khadeeja_candy_store?_t=ZM-8wBOKC1rSVi&_r=1

INSTAGRAM
https://www.instagram.com/khadeeja_candy_store?igsh=bTk2aG13cmFkZjM0

CHANNEL
https://whatsapp.com/channel/0029VaNTEQTFXUuaypyV5O01

KHADEEJA CANDY STORE
https://chat.whatsapp.com/HGRV2NYIoaCF7SIvPOIv08

WATTPAD
https://www.wattpad.com/story/215276233?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=story_info&wp_page=story_details_button&wp_uname=KhadeejaCandy


Page 5?? 8??


Turhan ya zube a gaban mahaifinsa ya gaishe shi, mahaifinsa yayi kamar be san da shi a gurin ba, bayan mintunan da suka bata a zaune wata kalma bata shiga tsakaninsu ba, Turhan ya yankw shirun ta hanyar sake mika gaisuwarsa ga mahaifinsa a nan ma be tanka shi ba. Bayan tsawon lokaci mahaifin ya mike ya shige wata turakar tashi, Turhan ya tashi ya koma bangarensa ya samu balarabiyar matarsa kyakkyawa kamar shi tana zaune cikin bahon wanka tana shuda jikinta da kumfan shower gel mai kamshi.

Ya karasa kusa da ita fuska babu wata walwala ya sumbanci goshinta kamar yadda ya saba, cikin farinciki da zumudi ta mike tsaye ta rumgume shi tana masa barka da zuwa.

"Ban yi tsammanin dawowarka yanzu ba, ya Ammyn take?"

Ya kalleta kawai yana murmushi a zahiri a badini kuma yana hango dalilin Ammy ne aura masa Aisha, tun da yake da matarsa bata taba sha'awa tafi gaishe da mahaifinyarsaba, ko a waya sai idan shi ya hada su take gaisawa da ita, ya taba mata tayin tafiya Nigeria sai ta nuna bata da bukata be sake maimaita bukatar hakan a gareta ba, kuma a wacan lokacin baya ganin illar hakan sai yanzu da ya fi fahimtar muhimmancin mahaifiyarsa...
Ya sake ta juya ya fice hakan sai ya bata mamaki domin be saba ganin jikinta a haka ba ba tare da nuna shaukinsa akai ba, amman yau tambayar ma be amsa ba, a take ta wanke jikinta ta daura tawul ta dayan kuma ta daure kanta ta fito daga Bathroom din ta bullo corridor domin babban bandakin dakinsu ba a daki yake ba a mahadar hanyoyi ne dake tsakanin dakunansu. a ranar dai kam Turhan be samu magana da mahaifinsa domin baya amsa ba. Karamin falon ta fara leka bata ganshi ba sai ta dawo corridor ta shiga dakinsa.

"Turwhan... Kana lafiya kuwa?"

Ta karasa inda yake tsaye yana cire rigarsa tana kallonsa.

"Wata kila gajiya ce, amman idan na huta zan mu wata magana"

"Tana da muhimmanci ne har ka bata rai haka?"

"Zan ki iya hada min wani abu na ci?"

"Shaghala (Mai dafa abincin) zata hada maka"

"Shukuran"

Ya saka bathrobe ya fice ya barta a dakin, tana mamankin yanayinsa a yau. Da dare ma sai da ya koma bangaren Mahaifinsa nan ma be yi magana da shi ba. Haka ya dawo bangarensa ya zauna a inda suka saba cin abincin shi da matarsa ya samu an jera abinci a kasan wani farin kyalle da aka shimfida ta zauna ya hade kafafuwansa yana kallon kayan marmari da ka'ida ce kullum sai an aje tare da sweet kala kala. Be ankaro ba ya ji an zauna kusa da shi matarsa ce fuskarta dauke da murmushi tana kamshin EOS Khumra Al Dufra Perfume Oil.
Ya juyo ya kalleta tana sanye da thobe (or toob / toub / *HO(), wata kafaya ce ta al'adar larabawan Sudan, sai ya sakar mata murmushi ya kama hannunta ya rike.

"Kana cikin damuwa ina iya ganin haka daga gareka, ina lura da irin wannan yanayin a duk lokacin da ka dawo daga Nigeria, amman na yau na musamman ne"

"Na kan dawo da damuwa ne saboda neman mafitarta wata hanya ne, a yanzu kuma na samu karshen ta amman ta kasa bullewa da ni"

"Ina gane ko wace kalma da yaren larabci amman ban da tsarke magana a cikin wata magana, fada min Habibi me ya same ka?"

Ya juyo ya fuskance ta da kyau.

"Ina fatan zaki fahimce ni kuma zaki min uzuri, lokaci yayi da ya kamata ki san komai..."

Sannu a hankali Turhan ya yi mata shimfidar da zata mikar da ita zuwa cikin ajinsa har ta dauki karatunsa, tun da ya fara bata ce masa uffan ba har ya kai karshen littafin data kasa fahimtar haruffansa balle ta haddace karatun ciki. Ya fada mata ya aure wata mata matar kuma ita ce wanda ya zo da ita a matsayin baiwa haka kuma ya sake ta a yanzu amman zai dawo da aurensa da ita, haka zalika yana da ya a tsakaninsu, sannan ya fada mata yawan zuwan da yake Nigeria har ya dade yana zuwa nemanta ne. Da farko zancen ya rikice mata ne har ta rasa muhallin dorashi kamin hankalinta ya janyo tunaninta bayan ya nuna mata hoton Fatima.

"Mabsoot bikhibalak"

Ta furta tana jefar da hannu idonta ya fara tara hawaye.

"Ka ci amanata Turwhan, taya zaka yi aure bayan idona? Saboda bana haihuwa? Ko kuma saboda mahaifiyarta bata so?"

"Ki zargi komai ban da mahaifiyata, domin bata taba nuna miki kiyayya ba, matar da baki taba sha'awar gani ba?"

Ta tsaya cak tana kallonsa kamin ta mike tsaye ta taba masa.

"Barakallahu fika Turwhan"

Ta juya sai yayi hanzarin mikewa tsaye ya rike ta.

"Idan har zaki ji babu dadi wannan abun da na aikata ki yi tunanin yadda matar da na wulakanta zata ji? Kuma na yi ne ba dan kai na kadai ba har da ke?"

Ta juyo da karfi.

"Idan har baka sonta taya ta haihu da kai? Bayan duk wannan yanzu kuma kana fada min zaka dawo da ita? A tunaninka zan iya zama da kai bayan duk wannan abun da ka yi min? Balle kuma har zaka zauna da matar da bata wuce matsayin mai kula da gidana ba? Aure ya kare tsakanina da kai.

"La la la, khalas al-mawdu intiha. Ana  ayza talaaq"

Furta cewar sai dai ya sake ta ya karya masa guiwa sai dai be karya zuciyarsa ba domin a yanzu Fatima kawai yake hange. Ya kama hannunta ya rike cikin sigar rarrashi ya ce.

"Za mu iya fahimtar juna mu gyara komai, ki yi uzuri, ki karbe ni tare da yata"

"Ba zan karbi uzurinka ba, kuma har abada ba zan taba son yar wata ba, har karshen rayuwata, Lihaddy akher nafas fi %ayti"

Ta furta hakan har sau uku tana hade hakora, kalmar ba zata taba son yar wata ba har karshen rayuwarta ya saka Turhan ya saki hannunta domin Fatima yarsa ce, ba yar Aisha kadai ba, be ce ya shirya rabuwa da ita ba, ko rusa aurensa ba, domin ba zai yarda ya maimaita irin wacan kuskuren da ya aikatawa Aisha ba, sai dai kuma hakan ba shi yake nufin ya jure a ciwa yarsa ko mahaifiyarta mutuncin ba. Ta kalli hannunta daya saki ta kalleshi fushi ya dauketa ta fara shure kayan abincin da abinci dake ciki tana ihu tana la'antarsa da kalmomi marasa dadi. Kamin ta fara bin sitting room din ta fara hargitsawa tsabar bala'inta be iya kwana a gidan ba sai fita yayi ya kwana a hotel, washe gari ko da ya dawo be same ta a gidan ba, ya samu ta yi ma gidan barna duk wani abu mai glass sai da ta fasa shi hatta kwalbar turare bata bari ba.

Wanka yayi ya canja tufafi sannan yayi ma khadimansa su gyara bangaren, ya fito ya nufi fadar mahaifinsa ko'ina ya bi kallonsa yan'uwansa suke, sauran Khadiman gida kuma sai ya sauke ido ake satar kallonsa, kowa yana mamaki da abun da matarsa ta fada jiya cikin ihu da hayaniya. Yau ma da ya shiga mahaifinsa be tanka masa ba.

"A gafarce ni, na san ina da tarin laifuka"

Bayan kamar Minti biyu mahaifinsa ya kalleshi.

"Na yi zaton ba zaka zo ba ai, saboda ban isa da kai ba"

"Ban isa ba, kai kayi kira na kasa amsawa, da baka isa da ni ba da ba za a kawo maka rokon abun da a cikin aikata shi babu adalci ba"

"Wata wuta ce aka ce ta kama a wani gida, aka roki na kasheta, da na bincika dalilin tashinta Sai aka fada min har da Wana a gurin assasata, shin hakan gaskiya?"

"An riga ni sanar da kai tashin gobarar data haifar da hayakin sanar da duniya abunda ake ciki ne, amman ina da wannan nufin a yanzu da nake ganin lokaci ne daya dace kowa ya san komai"

"Aka ce ka yi aure? Tatsuniya ce ko kuma dai ana kokarin kunna fitina a cikin masarautar ne?"

Turhan ya natsu Sosai ya sanar da mahaifinsa yadda auren ya afku da kuma yadda boye lamarin har zuwa yau. Yayi zaton zai fuskanci fushi da natsa daga gurin mahaifinsa ne sai gashi ya tsinkayo mahaifinsa na murmushin kasaita ya kalleshi cike da alfahari.

"Wani lokacin akan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login