Showing 21001 words to 24000 words out of 190762 words

Chapter 8 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3972

fa ya zabawa shine zata yi gaggawar katsewa cikin hikima, bata dan kyar nake kallonta ba, in sha Allah zata ga ci gaba kuma zan koma dakina ya zamo Ni na amshe Babanku a hannunta ke kuwa kin auri wani gagarumin Elhajin , sshikenan kakarmu ta yanke saka , likafa ta gama tashi sai Turai"

KARIMA ta yi dariya dan yannayin da mamanta ke fada abin dariyar ne, kwarai kuma ta yarda da shawarar sai dai wani abu na soyayar saurayinta na mintsininta a cen kasan zuciyarta, Mudansir ya kai a so shi fa domin Allah kenan , da wannan ta yi gaggawar komawa ta labe a cikin makarantar har aka tashi suka fito da yan uwanta suka shishige aka nufi gida da su


Koda suka zo gida yau shirun ya fi na kulun yawa, har zuwa lokacin da mahaifinsu ya dawo gidan ba haya haya domin daga shi har mama kowa ya kame kansa sunna yiwa junna hangen nesa, dan idan ya kai kararta wajen ta larabawa ya san ya yi mata abinda ya fi komai bata mata rai bai cika shiga sabgarta ba, sai da aka so addu'a da asubahi dan ya sake sakawa ta yi masa wata rashin kunyar ya dubi tsabar idannuwanta ya ce" Yauwa maganar da muka yi jiya tana nan, ina kyautata zaton yau zan ji daga wajen uban angon, in dai komai ya tabbata zai zo su gana nan da dan lokaci shikenan komai ya daidaita sai ki shirya kai y'arki dakinta"

Mama dake rike da alkur'aninta ta rike shi a hannunta da kyau ta dage kafadu bayan ta mike ta kama hanyar da zata kaita bangaren ta bata ce da shi um bale um'um ba, hakan ya sa ya rafka uban tagumi bayan ya rakata da kallo , yana juyowa ya ga ya'yan du shi suke kallo da sauri suka sasada kawunnansu

Ido ya zuba musu yana kallonsu, kai lokaci yayi da zai yiwa samarin nan gini a kofar gida su koma, yan matan nan kuwa lokaci yayi ya rabu da su, to ko ANMY ai ta gandame ashe bai kula ba, ashe ashe yaran sun ba ashirin baya? zai samowa kowace miji a mata aure su tafi dan walahi shi ba zai yarda yaya su kawo masoya ba sai kace a gidan yan iska

Sai kuma ya dan kame baki a ransa ya ayana' da ace gimbiya ta ji kace a gidan yan iska ake kawo masoyi a yarda da ka shiga uku, dan walahi cewa zata yi ka zagi iyayenta bayan ba haka kake nufi ba, kai innalilahi kiri kiri dai matar nan ta fi karfina , tana min rashin kunya ina mata biyaya, Allah na tuba Allah ka ci gaba da sakawa gimbiya tsorona a ranta kar a zo in ringa mata biyaya in shiga uku, koda yake zata ga Nine mai gidan in na daurawa y'ar nan aure, bari dai ya zo ina kyautata zaton yau zai zo garin, shi yasa ko shigar da zan yi yau daban ce, zai gaisa da sirikinsa, du takamar malan bahaushe kuwa a gaban sirikinsa akoy alkunya da karra sosai da kuma girmamawa, Karima yarinya kin gama hayewa ke ta yiwu karshen zamanki a Nijar ya tabbata'

Da kuma yace" Ku je ku tafi makaranta, kai wai har yanzu baku gama karatun ba? har yanzu babu ma'aikaci a cikinku?"

Su dai basu ce komai ba suka wuce sumsumsum, to me ya sani a harkar karatun su? mutumen da babu abinda ya sani da ya shafe su sai idan duka ya kama yake yi? kaf cikinsu Khadija ce karama itama a ajin jarabawa wanda da ta gama shi zata shige University take, danma makarantar su na dauke ne da tun daga primary har zuwa karatun da ake yi a University, shi yasa sunna samun takardar nan suke yin shawara da mama su zabi abinda suke son karanta, ita ke zuwa makarantar ta gama komai na biya da komai da komai, kuma ko ana neman yara wani abin a makaranta ita dai ake kira ba'a taba nemansa ba.


A wannan ranar ne Mama na wajen aiki aka yi kiranta daga makarantar yaran ana tambayarta jikin Karima , hakan ya sa ta mike ta bar abinda take yi ta dauki mota ta nufi makarantar da kanta dan sun nuna yauma tace bata da lafiya ta tafi gida, hakan na nufin jiyama an yi haka? to kuwa ai bata san da haka ba, kuma a jiyan din bata dawo gida ba da mai aiki ta sanar mata yau Karima ta dawo bata da lafiya, hasalima tare da yara suka dawo tunda ta rigayesu zuwa gidan, kuma daya bayan daya sun shiga sun gaisheta.......

Hummmmmm ......, ta fitar da huci a ranta tana ayana' Karima, me yake faruwa da ke ne daughter?'
........................''''''''''''''........................
07/12/2024, 14:51 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Bakwai (7)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*

*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja

LABARI



A nutse ta tuka kanta har zuwa makarantar

Tana tunkarar hanyar da zata sha kwana ta shiga makarantar ta ga wata bakar mota karkashin shukar dalbejiya, gefen zaman mutumen da baya tuki a bude kaffafuwa a waje mutumen daga ciki

Kasantuwar a hankali take tukin ne ya sa ta gane takalman kafar wanda ke zaunen ko Allah ne yayi zata ganin? Ita dai a lokacin ta gane du inda takalmin ya fito daga kafar ƴaƴanta ne, domin yau du shi suka saka kamar hadin baki, takalmin na daya daga cikin takalman babar sallah da mahaifinsu ya kawo musu daga shago

Taka birki ta yi ta duba da kyau, ai kuwa idannuwanta suka shiga cikin na Karima wace ta zarro ido lokaci daya jikinta ya dauki mahaukaciyar rawa ta nuno motar lokaci daya ta rarumi jakarta dake bayan motar ta Mudansir ta fito da sauri, sai dai mama bata bata wannan damar ba ta tashi motarta ta yi gaba

Faduwa Karima ta yi a wajen ta fasa kuka tana dora hannayenta saman kanta lokaci daya tana fadin" Na mutu na lalace innalilahi wayo Allahna, shikenan yau sai baba ya kasheni, walahi ba zan je gida ba, idan na je yau kasheni zai yi"

Mudansir da ya fito daga motar yana kallonta ya ce" Baby, ke lafiya? menene?"

Tana kukan ta ce" Maman mu ce ta zo, ta yiwu kiranta aka yi a makaranta aka ce mata banda lafiya, dama idan bamu da lafiya ko wani abin ne ya faru ita ake kira, ta yiwu shi yasa ta zo dan ta ga ko yaya nake ta kamani da kai a mota, innalilahi wa inna ilaihi raj'une "

Tsaki ya ja yana jingina da motar ya ce" Ni walahi har kin daga min hankali, to sai me? mahaifiyar ki ma ta san da zamana kuma ta yarda mu yi soyaya da ke sai wanda ba ita ta haife ki ba abin zai daga maki hankali? dan Allah duba ki ga yadda kike kuka sai kace wadda ta kama mu muna zina? in kika yi haka nema zaki sa ta yi wani tunanin, ki tashi ki je makarantar ki nuna taimaka maki na yi na dauko ki, walahi dan kawai ku sa a raina maku wayo ne zaku ringa irin haka, in ba wannan ba ina hadinki da wata matar uba har ki ringa kuka irin wannan dan kawai ta ganki da saurayinki?"

Jikinta bai daina bari ba, tana dubansa ta ce" Kana tunanin idan nace mata haka zata yarda da Ni? dan Allah kana tunanin zata yarda?"

Ya bude motarsa yana jan tsaki ya ciro kudin da suka yi zai bata wanda jiya da dare ta nuna masa tana so, itama babu abinda zata yi da su mahaifiyarta ce ke so kuma ita tace ta tambayo mata a wajensa , ya miko mata ya tayar da motar ransa bace yayi tafiyarsa, dan shi abin ya mugun bata masa rai, meye kare balatana romansa? matar uba ai a ci uwar junna da ita ne kawai ko kowa yayi harkar gabansa, ama zata wani duka tana kukan nan kamar ranta zai fita dan kawai ta ganta a motarsa? mtsssssssss wannan babyn in ba dan sunnan babanta ba kai da ya watsa banza a bola shi baya son harkar yawa walahi

A lokacin da ta shanyo kwana tana rabe rabe a lokacin aka buga karaurawar tashi wace ke ba kowa damar fitowa, tsari da tsaurin makarantar yayi daban da sauran makarantun garin, shi yasa ko sauka ba irin in ka ga dama zaka sauka bane,

Da sauri ta nufi inda direbansu ke ajiye mota ta bude ta shige cen baya ta buya jikinta bai daina bari ba, gashi tana son kiran mamanta ta sanar mata sai dai ta san ko ta sanar mata babu wani abin da zata iya yi mata na ceto daga hannun babansu idan har ya ji maganar nan, wannan din dai da suke yiwa kallon makiyiya itace zata iya karbarta daga hannunsa kanta tsaye sai dai dukkan ya sauka a kanta, gaba daya komai na duniyar ya tsaya mata, hankalinta ya gama tashi fiye da tunanin bawa

Ba'a dauki lokaci ba yan uwanta suka zo du suka shishige, sai dai du wanda ya ganta a ciki sai yayi mamakin ganninta a baya , a bayanma cen boye, kuma kanta a cikin cinyarta tana kuka, duba da ita kulun sai sun yi jiranta in aka tashi kuma kiri kiri take shigewa gaba ta zauna a yi ta balaki tace walahi ta fi karfin shiga bayan mota, tun sunna biye mata su daki junna a hanya sai baba direba ya tsaya ya raba har suka bar mata gaban cen ta karata , sai gashi yau ta shige baya kuma tana kuka

Khadija ta kalleta ya fi sau uku tana jin kukanta na shiga zuciyarta har suka karaso gida suka sauka bayan ya shige da motar har cikin gidan

Direct dakinta ta kufa , khadija na biye da ita har suka shige , a tausashe ta ce" Hala a wani exam kika fadi shi yasa kike kuka? tunda ana ga ai ba dukanmu ake yi a makaranta ba , ko baki da lafiya ne?"

Ta dago zata bata amsa Lubna ta shigo itama tana dubansu ta ce" Wai kukan me kike yiwa mutane? ko laifi kika yi ne?, walahi idan laifin da Aba zai yi duka kika janyo mana ba zan taba yafe maki ba Karima, haka kawai sai ku ringa janyo mana fushin Aba kulun yana saukewa a kanmu, bakwa gannin zuwa yanzu mun kai mizanin da bulala ya dace ace ta daina hawa fatar jikinmu ne?"

Da tarin takaicin abinda ta janyowa kanta ta dago a zafafe ta ce" Sai ki fadawa wace ta kware wajen janyo mana dukan ai ba Ni ba, Ni har duka nake janyo mana? sau nawa na taba janyo mana dukan a rayuwa? ama ita ana rufe sati ne bata je ta janyo mana ba? Allah ya isana ko waye zai hadani da dukan yau walahi !"

Lubna ta tabe baki tana fadin" Ni na san ba banza ba kike kuka, kuma na san ba dan makaranta kike yinsa ba, mu dai zamu barki da Allah idan kika janyo mana wata masifar, ke Anmy ki je ki duba hardarki kin san yau da yama muna da harda dan malan yace satin gaba in dai dayarmu bata kawo hardar gaba daya ba tabas za'a yi bikin sauka banda ita, ki barta ta ci kanta tunda ita bata da mutunci"

Khadija ta sauke ajiyar zuciya ta yi waje tana yan dube dubenta da tunanin yau ko ina Mama ta tsaya? duba da lokacin sauka yayi daga asibiti, dan Yawancin lokuta a gida suke samunta in dai wajen aiki ta tafi, sai idan ta biya wani uzurin ko ta je gidan Hajiar Larabawa

Ko da mama ta zo bata nemi dayansu ba, lokacin makarantar islamiyya na yi suka tafi su Dukansu, kusan Karima ta rigayi kowa tafiya, gaba daya jininta a akaifa yake , hankalinta ba a jikinta yake ba, du ta firgice ta fige, ko hardar da aka zo karba kasa bayar da Tata ta yi, malan yayi ta fada saboda an ware su sun kai su talatin da uku zasu yi hardar sauka a ajin manya, dama sun yi saukar to malan baba baya yarda sai an yi harda, hardar ce suke haɗawa kuma sun kusa gamawa domin a bakara suke daga kasa ne suke yin sama, kuma yace sai sun kawo kowace tasss sannan za'a gabatar da saukar, shi yasa suka maida hankali sosai, ama ita yau tana cikin mutun bakwai da malan yace in sha Allah satin nan da zai zo idan basu zo masa da hardar da aka yi yau ba da kuma karashen wace aka biya yau ba ba zasu shiga cikin rukunin masu saukar ba, da wannan suka sauko daga islamiyya kowa ya kama gabansa

Khadija bata nufi gida ba, sai ta dauki hanyar gidan umma tsohuwa dan a irgenta tana iya zuwa a tsaitsaye ta gaishe da ummar sannan ta je gida dan haka ta nufi gidan hankali kwonce

A lokacin da ta dauki Layiin da zai sadata da gidan ne idannuwanta suka yi mata gannin da ta jima bata ji tashin hankali da bacin rai irinsa ba

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, nan take idannuwanta suka so rufewa sakamakon abinda ta gani din

Yaya ne fa, yaya Abdul karim ne fa, tsaye da sabira a kusa da runfar mai pampo sabirar na magana tana murmushi shi kuwa yana tsaye hannunsa cikin aljihun wandonsa yana kallonta ko sauraronta? oho

Da sauri ya dago da kyau gannin wace ke kallonsa a tsaye, gabansa na faduwa shima, dan haka kawai ya ji mugun tsoron hakan ya tsirga masa

A hankali Khadija ta ja ta tsaya, sannan ta juya ta shiga tafiya idannuwanta na son rufewa

Da sauri ya biyo bayanta yana kokarin dakatar da ita, sai dai irin duban da ta juyo ta yi masa ya saka shi tsayawa cak hankalinsa na son tashi sosai yana kallonta a tausashe ya ce" Anmy, ina zaki je bamu yi magana ba?"

Khadija ta sake kallon fuskarsa da kallon da ita da kanta bata taɓa Sannin zata iya kure fuskarsa da shi ba, daidai nan kuma sabira ta karaso yannayin fuskarta zai nuna maka itama tana cikin yannayi na bege ko na me? Allah shi ya san abinda ke cikin nata zuciyar

Bata bashi amsa ba ta dauke kai ta nufi hanyar gida tana jefa kaffafuwanta a duk inda ta samu

Tana shigowa gidan ta yi kicibisss da Lubna dake kai kawo hankalinta du a tashe duba da magariba na gabatowa kuma Khadija bata shigo ba, bayan du inda baba yake ya kusa shigowa gidan shima, dama ga wata banzar cen dake neman jaza musu balaki, ga kuma yar na saba din nan zata janyo musu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login