Showing 174001 words to 177000 words out of 190762 words

Chapter 59 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3997

goron da su Sadik suka kai mata yanzu cewar wai an aurawa Karima dan shaye shaye ta nufo gidan nan dan ta san a yanzu kaf damagaran babu wanda zai iya tsawatarwa mutumen nan dama da wannan bawan Allahn, shine ta zo da muradinta a karo na biyu cewar ya sa a sakar mata y'a su ba shi suke so ba, ta shigo idannuwanta na gannin dishi dishi ta dago zata yiwa hajia zainab magana idannuwanta suka sauka a kan mutanen dake falon

Huhun goron ta saki, lokaci daya ta kalli hajia zainab a zabure, ta juya da nufin ficewa ta ji an barar da ita kamar an yi watsi da kayan wanki

A furgice ta nemi mikewa daga yashen da take lokaci daya da ita din, da baba hamzan, da malan Abdullahin, da hajia zainab din sunna furta innalilahi

Da sauri baba Hamza ya furta" Kai, yaron nan, kai, kar in gani , kar in gani"


Ina ai Aba sai ya zama kurman da gangan, ya riki wuyan maman Karima ya matse da kyau ya ringa kasa mata mari yana fadin" Ban shiga tsakaninki da ahalina ba? Ban ce da ke idan kika kuma shiga lamarin gidana sai na wulakantaki ba?, au ji kike yi da wasa nake? To yau zaki ga bariki tabas yau sai na summar da ke....., kin zata na yi sanyi da baki ganni a gidanku ba? Ai dama na san ko yaya zaka yi da jaki sai ya ci kara shi yasa na yi hakuri har ki tardo Ni dan gimbiya tace idan fada kai aka tardo a wajen iko sunnansa attaque a domicile, ni da nake so in summar da ke in karkatar da ke kuwa in dai bana son rigima da iko ai na yi jira ki zo, ta yabuwa Ni zaki tardo gidan ubana ki zageni? Yau sai na daidaitaki ta yabuwa yau sai na ci kakan ubanki ta yabuwa......"

Da kyar baba Hamza ya iso inda suke , su malan Abdullahi sai ihun ya saketa suke ya musu kunnen uwar shegu, yana zuwa ya samu ya riki hannunsa ya daga dayan yace " idan baka saki yarinyar nan ba zan dauke fuskarka da mari!"

Ya dantse lebe yana hararan gefe yayi wuyuuuuuuuuuuuu zai danna mata cizo baba Hamza ya sake tarewa sama sama ya ce"


(Innalilahi, su'ali......shin aba dama kwontan bauna ka mana har muke tunanin ka shiryu?????😭😭😭, innar karimar zaka ci kakan ubanta??????😭😭😭😭)









😍🥰🥰🥰🥰🥰, morning nah people🥰, muna daf da shafa fatihar farkon gannin idona🥰🥰🥰🥰





50
07/12/2024, 17:38 - samiraharounayacouba: Baba Hamza na tarewa ya ce" La, malan Abdullahi kama shi ya tashi kama shi, cizonta zaka yi?, Ama d'an nan ka ji kunya, tayar da shi"

Malan Abdullahi ya duka ya nemi jijikar aba, ama ya kasa sai da baba Hamza ya daga hannu zai kwade shi sannan ya dafa ya tashi da kafa ya harbeta a boye yana dantse lebe ya je ya harde hannu ya zauna

Baba Hamza yayi kugin kiran mai aiki da suke ta neman lekowa ama sun kasa saboda tsoron kar ace me suke nema a nan?........,

Da sauri daya ta karaso tana satar kallon Aba da kuma maman Karima dake baje, hajia zainab jiki sai rawa yake ta kasa tsaye ta kasa zaune sai kawai ta saki salati ta kalli Aba ta kuma dubi ta yabuwa a baje , danma mutun ce mai saka irin dogon wando a cikin tufafinta ai da ta yabuwa yau a fili take Alkur'ani

Baba Hamza ya ce" Je kirawo min Binta !"

Daga haka ya sake komawa gefe yana duban Aba da hararansa da kuma duban Hajiya zainab yana nazarinta

Ba'a jima ba hajia Binta ta karaso da baban hijab dinta

Tana zuwa ta shiga yin salalami hankalinta a tashe ta ce " Lafiya wannan wacece ke nishi haka? Me ya faru?"

Baba Hamza ya dubeta ya ce" Binta, so nake ki zama sheda saboda ita wannan ban san abinda yake damunta ba, koda yake kuma na ga kamar a cikin lamarin nan take!"

Da kuma wani yannayin na a fusace yake ya dora da fadin" To kam babu ruwana, ba zai yiwu ace kulun ana bin yaro da fitina ana neman karya masa kara a ido ba dan an ga ba abinda yake cewa a nemo daga masa hankali, kin dai ga a jiya yarinyar nan waya ta ba y'ar wajen ta, har take ikirarin ko ta wani hali y'ar Tata sai ta auri elhaji karami....bayan nan ta zo ta sakani gaba muka je ta ce y'arta bata son elhaji ƙaramin tana da saurayinta wanda take so, yanzu dan jiya an aurawa y'ar saurayin nata kuma yanzu ta dawo da wani batun......., ba zai yiwu a Hanna masa jin sanyi ba, ba zai yiwu a Hanna shi tarbiyantar da ya'yansa ba, kina ina lokacin da yake fadi tashi da abinsa? Me kika sani a jin kai da tarbiyya da tausayin ya'ya ke? Matar da take rike da y'arki tun tana zanen goyo take fadi tashi da ita ce zaki nunawa yatsa ke? Ai kuwa idan ba'a cewa Usaina sannu ba, ba za'a zageta ba, dan Ni nan da kika ganni Mutun ne mai matukar girmama mutane masu adalci......, bana son fitina ko kadan....., yaron nan kuwa ba yankashi zan yi in cinye ba, du abinda kika ce yayi na masa fada da farko a yanzu kuwa banda abun fade sai fatan alkhairi da addu'ar Allah ya sa auren ya zama alkhairi......"

Ta yabuwa a birkice tana nishi ta dubi baba Hamza ta fashe da kuka ta ce" Yanzu baba du irin dukan nan da ya min zai tashi a banza kenan harma a ga laifina?, baba shine kadai d'anka kennan?, wallahi ba zan yarda ba sai an bi min hakina, saboda ko hukuma ta ga yadda jikina yayi hulu hulu da shedar mari sai sun rufe shi!"

Baba Hamza ya kame baki ya ce" Ba mai rufe shi, gidansu kika tardo shi ai, kuma ki ji da kyau y'arnan Ni baban kowa ne, Ama idan baka da gaskiya Ni ba ruwana da kai, ki je ki yi hakuri ki sha magani idan kin warke ki dawo mu zauna , Ama yanzu kam a fusace nake da ke"

Hajia Binta ta dubi hajia zainab ta ce " Kamata ta tashi mana hajia, kamata....., a yi hakuri kakan kurma , a yi hakuri baban kurma, Allah ya huci zukata, ku mu je"

Baba Hamza ya sake dauke kai ya ce" Ke kuwa zainab zaki min bayanin wannan lamari, kin ga yanzu nake tunanin ranar da kika rakata kika ce dakin y'arta ta zo gani, kuma gashi kin rakota yau ta sake kawo karar an aurawa y'arta mijin da ba na kanwarta ba....., kin ga idan na same ki da wani laifi ba zan kyale ku ba gaskiya, dan bana son du wani abin da zai zama fitina a cikin yayana!"

Hajia zainab da sauri ta sunne kai suka kama ta yabuwa ta mike suka fice suka nufi bangaren hajia zainab da ita

Bayan sun zauna hajia Binta ta dube su da kula ta ce" Me yake faruwa ne zainab? Dan ban fahimci komai ba saboda kin san ai idan ransa ya bace ba tsayawa yake yi a gane me yake nufi ba"

Hajia zainab da takaicin ta yabuwa ya gama kumeta ta ce" Hajia Ni ai ban san abinda zai faru ba kenan, Ni da ta zo hankalinta tashi tace in mata rakiya ne kawai na rakata, Ama kema tunda kika ga yana nan yi baya abinki tunda kin san halayyar mijinki, shikenan sai ki shiga? Kuma wallahi elhaji fa baya wani uzuri a kan abinda ya shafi elhaji ya'u kina gani dai abinda yace"

"To menene elhajin ke cewa za'a lalata tarbiyyar ya'ya?"
Hajia Binta ta fada tana sake duban su

Nan ma sai hajia zainab ta bangarar da zancen, haka ya sa hajia Binta dubanta cikin ido ta ce" Ama kin san ai elhaji baya fada a kan rashin gaskiya, yana dai da wuce gona da iri a fushi Ama bai taba yin na rashin gaskiya ba, me yake nufi da batun yaya ta auri mijin kanwa?"

Hajia zainab ta mike tana fadin" Ta yabuwa tashi kawai ki tafi, hajia Binta a bar maganar kawai ta wuce, shikenan Allah ya sanyaya, abu bai yi dadi ba , ba za'a kuma ba"

Khalisat na tsaye tana kallon mahaifiyarta ido cike da hawaye , mahaifiyar Tata ta juya ta ringa jan ta yabuwa har suka fice

Jiki a mace khalisat ta zo ta zauna daf da Hajiya Binta wace ta raka su da kallo cike da zargin yannayinsu dan tun kafin su fice sun fara fada kamar zasu bigi junna

Murya na rawa ta ce" mama dan Allah ki raba mama da wannan matar, wallahi zata sakata a halin da ba shikenan ba kuma a zo a samu matsala kin dai san baba a kan lamarin big son baya daga kafa, kuma abin ne gaba daya sai kace na wa'inda basu da addini? To mama sai in ce haka tunda iyayena ne ba zan raba musu kalmar rashin hankali ba, mama wai da farko y'arta aka so ba big son, ta Kiya ta sa aka Hanna, yanzu da aka bashi wannan kanwar Tata shine kuma uwar ke so a mayar da abin kan y'ar, har take cewa mama wai ai maman ita Hajia karama muguwa ce, yar bin malamai ce da sauran su ...., kin ga ranar da suka fito din nan daga ɓangaren ta bayan mama ta mata rakiya sun hade da baba ta shigo a tsorace muka yi magana ta ce min shikenan ta fita daga lamarin, Ama kuma kuma kin ganta ko? To wallahi ki fada mata ta fita a batun nan dan baba ba zai kyaleta ba, tana gani dai ko mahaifiyarsa da ya tsorata da lamarinta sai yanzu ya hakura bale ita ko?"

Hajia Binta ta gyada kai ta ce" Gaske, biri yayi kama da mutun....., to ai shikenan ba laifi tashi ki tafi, zamu yi magana da ita ne"

Mikewa ta yi ta yi tafiyarta tana barin kukanta zuwa dan bata ga amfanin wannan rayuwar ba, sam bata da dadi, yau ko ba za'a ce mata komai ba ai zata ji nauyi da kunyar d'an halak.

Hajia Binta jiranta ta yi har ta dawo, tana son sake layancewa ta dubeta da kula ta ce" Bismillah zauna mana Hajia"

Hajia zainab ta zauna gabanta na dan faduwa

Hajia Binta ta dubeta da kula sosai ta ce" Ki yi hakuri, ki kiyaye dan Allah, kin san rayuwa ta lalace, idan kuma kana abu ka fara duba kanka , wani mutumen a ganka da shi ma ba alkhairi bane a kai kanka bale wa'inda kake tare da su, shi kuma dabi'a da kika gani mugun sabo ne da ake dauka a zamantakewar yau da gobe...., kina da ilimi, kina da hankali, kar ki yarda wani abu ya kutso Maki da har wata zata shigo daga waje ta janyo maki zubewar mutunci da daraja a idannuwan yayanki da jikokin ki, shi kuwa du abinda ake boyewa lokaci na falatso shi fili, gwara ki ajiye komai ki yi hakuri ki kuma yi addu'a, na tabbata abinda ya sa kika fara mai girma ne, a yanzu ma ina so abu mai girma ya sa ki daina irin soyayya ta jika da kakarsa wato ke da AL'WALED...., ki yi hakuri shawara ce idan ya bata maki ki gafarceni "

Daga haka Hajia Binta ta mike ta yi tafiyarta , dan ba zata kuma tsayawa jin komai ba, idan har Hajia zainab ta yiwa kanta adalci zata kiyaye, in tana so kuma kar ta kiyaye din duka zabinta ne, hukuncin ta zai zo daidai da irin taka tsantsan din da ta zaba.



A wajen baba Hamza ya jima yana rarashin Aba, shi kuwa malan Abdullahi baki bude yana kallon su, baba Hamza ya ce" Malan Abdullahi ina matukar tausaya yaron nan a rayuwa, yana kokari sosai, ka duba fa ka gani dole sai an saka masa y'a a wani hali, da ba dan gyaran Allah ba da me maganar ko ta wani hali zata haifar ?, hum, ciro wayar ka yi min kiran elhaji ƙaramin in sanar masa idan sun fito su same mu gidan naka wajen daurin auren shi da iyalin nasa"

Aba ya ciro wayar yana wani murmushi ana faman fadin hakuri ne da shi , sai kuma ya dago yana duban baba ya ce" Shi da wa?, su kuwa ina suka je aure sati biyu kadai?"

Baba Hamza ya ce" Kai sati Uku ne, sun tafi wajen maman shi elhaji ƙaramin ne"

Aba ya Dube shi da sauri ya ce" La'ila ha ilalahu, ashe dai ka mutu a salihi? Ai na dauka uku zaka sakani ka mutu kana gaba , ashe dai zaka shiryu?"

Baba ya kai masa rankwashi yana fadin" Kai kam an yi fitinane wato Nine zan mutu ina gabar da wani? Ni ai ban taba kwonciya da kowa a raina ba "

Aba ya tabe baki yana buga numbar AL'WALED ya mika masa ya ce" Kai dai Allah ya taimakeni daga yau an fara amsar sallarka, ga elhajin "


51
07/12/2024, 17:39 - samiraharounayacouba: Baba Hamza zai rama ya jiyo Muryar AL'WALED a tausashe yana salama

Amsawa yayi da kula , a tausashe ya ce" Barka da warhaka baban kurma, ya ka samu mahaifiyar taka"

AL'WALED ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Alhamdulilah baba, "

Baba Hamza ya ce" Ya akayi na ji Muryar taka wata iri?"

AL'WALED ya dan mike zai fice ta yi wuf ta mike ta riko hannunsa tana biye da shi, hakan ya sa ya dakata yana dubanta a hankali ya ce" Alhamdulilah, ba komai"

Baba Hamza ya ce" Masha Allah, yauwa dama kana ji, jiya an daura auren mai kukan nan ne, yau kuma zamu daura na biyu, shine nace idan kun fito ku wuce cen gidan mu hade dan nima yanzu wucewar zamu yi mu shiga gyare-gyaren kofar gidan"

AL'WALED ya dan yi murmushi ya ce" Harda kai a gyare-gyaren?"

Baba Hamza ya ce" Eh ka san sai ina dan nunawa, kuma bakin yan daurin aure biyu ne ka ga kuwa taron zai yi yawa ne"

AL'WALED ya gyada kai, a tausashe ya ce" Ok, Ama inaga Ni sai dai daga baya na leka"

Baba Hamza ya ce" A'a fa, kai fa sirikin gidan ne, bai dace ace yanzu ana abu babu kai ba"

AL'WALED ya sake duban mahaifiyarsa dake rike da hannunsa tam tana kallon fuskarsa, a hankali ya ce" Baba......"

Baba Hamza yayi dan tsam, jin yannayinsa..... A hankali ya ce" Lafiya kuwa?, me yake faruwa?"


AL'WALED ya sake dubanta, kirjinsa na daukan dan nauyi, a hankali ya ce" Tunanin da nake....yadda zata amince mu tafi....,kuma dole sai ta fara gannin likitan.......likitan ............likitan .............hummmmmmmmmmm, dole sai ta ga Psychologue "

Ya fada cen kasa sosai yana dan kawar da bakinsa dan baya so ta ji

Baba Hamza jikinsa yayi wani irin mutuwa da sanyi kalau

A hankali ya ce" Ka kawota nan....., sai mu ga abinda ya dace a yi mata"

Idannuwansa ya bude sosai yana jin wani abu na ratsa zuciyarsa, a hankali ya dan jimke hannun mamansa , a tausashe ya ce" Are U sure?"

Baba Hamza ya ce" Yes, ........ka kawo min ita nan, idan da hali sai ku zo wajen daurin auren, in ba hali idan na dawo ma zauna, Ama ita Hajia karamar ka sa a kawota "

AL'WALED ya lumshe idannuwansa bayan ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Thank you, thank you father"

Baba Hamza ya ji zuciyarsa ta karye sosai har sai da idannuwansa suka cika da kwallah, a tausashe ya ce" Sai kun zo" ya katse kiran yana sauke ajiyar zuciya sannan ya dubi elhaji ya'u dake kallonsa

Aba ya ce" Kuka zaka yi? Menene?"

Baba Hamza ya dan kalli gefe ya ce" Ta yiwu maman nasa ba lafiya ne, nace Dai ya kawota nan dan a kula da ita, "

Aba ya ce" Aya Allah ya bata lafiya, eh ya kawota gaskiya inma aljannu ne sai mu ringa yi mata rukiya, Allah dai ya bada lafiya, tashi mu je"

Baba Hamza ya mike yana fadin" Bari in yiwa marikan nawa salama sai mu tafi "

Shi dai malan Abdullahi mu'amalar bayin Allahn nan birge shi take yi sosai, su ke firar shi kuwa yana murmushi har suka gama suka tafi


A bangaren AL'WALED kuwa ko sallah sai da ya zama sai su khadeeja sun rike ta sunna rarashinta sannan ya samu ya tafi masallaci , shi da kansa ana gamawa yake dawowa ya sake zaunawa su dora firar daga inda suka tsaya, sai ta koro da bayani sak sai kawai ta saki layi ta kamo wata firar cen, idan ta yi haka sai ya samu kansa da rike hannayenta a tausahshe yana dubanta , zuciyarsa na tsintsinkewa, a hankali yayi kokarin dawo da ita maganar da take yi, wani lokacin takan dawo , wani lokacin kuwa ta manta kenan sai dai ya yi hakuri ya lumshe idannuwansa yana ta kama sunnayen Allah da neman taimakonsa da nema mata lafiya a ransa da kuma sake nema mata afuwa .

A tausahshe ya tambayeta idan zata bi shi? Gida wajen baba Hamza?

A dan birkice ta ce" Wajen baba? Baba zai sa a sake rufeni shikenan in daina ganninka, ka ga baba yace nice na kashe babanka wai, yaya za'a yi in kashe babanka? Ai litle ma sheda ce da mai sunnana a lokacin ai sunna nan ko khadeeja?"

Anmy ta sauke murmushi a tausashe ta ce" Mama, ba zaki yi haka ba ai, kuma baba ne da kansa yace a kawo masa y'arsa ya ganki, ba zai sa a rufe mana ke na, muna son ki mama"

Kamar wata yarinya haka ta ringa murmushi tana fadin" Ko khadeeja? Kin tabbata?, baba fa ya tsane Ni fa"

Anmy ta girgiza kai da kula da tarin tausayin mijinta da mahaifiyarsa ta ce" A'a Mama, baba yana son ki, ke y'arsa ce ai ya fada ma"

Mama ta ringa gyada kai, aunty SHAREEFA ta mike ta ja masu aikin mama suka je dakinta suka duba abinda zata anfana du suka kwaso mata, sannan ta saka masu aikinta su shirya summa zuwa dare a zo a dauke su saboda maman da su ta fi sabawa zasu ci gaba da kula da ita a cen dinma...., da wannan suka tarkata suka yi baban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login