Showing 144001 words to 147000 words out of 190762 words
Chapter 49 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
sakakiya ce sosai ya ringa yin sama da hannayensa ya halastawa kansa taba ababen da tunda suka fara tsiro a kirjinta ko ita dake dauke da su bata yi musu kallon kurulah bata gane yaya ainahinsu yake domin wani lokacin ko wajen wankesu sai ta ringa jin kunyar su, a yau ya dage rigar jikinta gaba daya ya zuba musu ido, ya yi musu kallon kurulah kafin ya lumshe rikitatun idannuwansa jijiyar goshinsa ta motsa a hankali ya idasa kashe yar karamar wutar jikin gadon ya nemi haukata mata tunani ya hade lebensa a dokin wuyanta ya ringa aikata mata aiki da garaje wanda ke sakata shidewa....lokaci daya ya kafe bakinsa a wajen nan da tunda ya rike bai saki na, hakan ya sa ta idasa sadakarwa ta rike damatsunan hannayensa numfashinta na sauka a gagauce a gagauce.......
Tun tana hardacewa har abin ya girmami tunaninta, du juriya da dauriyarta suka kare a lokacin da ya yi addu'ar saduwa da iyali ya tabbatar da ita a matsayin gonarsa a lokacin ne ta rainawa kanta wayo har ta yarda cewa mata sun iya tarar aradu da kai da har suke yiwa abin nan fadi tashi sunna kokarin ganin sun zama karshe a zuciyar abokan rayuwarsu ashe ba komai a lamarin sai wahala? ita kam an shamaceta an yi daya da ita ba kari, Du irin yadda suka samu horo a wajen Aba ta daina ihun kukan dukansa tun tana karama a yau sai gata baba da ita da komai ta aniya ihun neman ceto? ashe idan ana ja in ja abin jan ne bai samu ba? HUM...........
Ajiyar zuciya take saukewa na tarin wahalar da ta sha , rungume a cikin kirjinsa bayan tsayin lokacin da ya dauka yana faman koyar da ita tukin babar motar da bata taba hawa ba.
A hankali ya bude nauyayun idannuwansa ya zuba a kan fuskarta da ta dauki ja, a sanyaye ya furta" so sweet Hajiahhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh..... plz zan karra....."
To ai hikenanðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ abinci ce Hajiar? iyi?
42.
07/12/2024, 15:26 - samiraharounayacouba: KHADIJA ta sauke ajiyar zuciyar galabaita kirjinta na dokawar balaki a ranta ta ayana' Sai dai idan kasheni kuma kake so ka yi Aban litle"
Murmushi yayi gannin ta rintse idannuwan ruffffff, ya saketa a hankali ya mike ya nufi bayi da tawul dinta a hannunsa ya shige ya karasa wajen pampo ya shiga tsaftace jikinsa
A nutse ya gama dukan abinda ya dace ya fito ya suturce jikinsa sannan ya yaye bargon a hankali ya rike hannunta da ta kawo da sauri zata rike tana neman fashewa da wani kukan murya a raunane ta ce" Dan Allah kar ka karra, ba zan iya ba, ban taba yi ba......""
Tausayinta ya kama shi, aya, ta yarda cewa karawar zai yi kennan, haba dai ya fi kowa sannan bata taɓa Sannin wannan lamari ba, yaya zai karra ? ai du maitarsa a kan abin dole zai hakura har waje ya saba idan ya so sai a sasaba yadda ya dace, a tausashe ya rungumota jikinsa kasa kasa ya ce" Ba zan karra ba hajia karama, zan tayaki kimtsa jikinki ne saboda idan har da halin tsaftace jiki bayan wannan lamari ya fi a tsaftace shin fiye da a kwanta da shi "
Lufff ta yi tana sake sauke ajiyar zuciya cike da jin kunya, Duda ya dan rufa mata tawul sai dai jinta take a bude sosai a gabansa daga ita sai tawul.....
Kula ya bata mai cike da tsafta da tsantseni, a lokacin da ya gama dukkan abinda ya dace ta fannin kularta ido kawai take binsa da shi cike da mamakinsa......., ko dan ya taba yin aure? kai a'a, tana gannin wannan kulawar da yake yi mata an bashi tarbiyyar haka ne, domin da ba'a bashi ba a irin yadda yake da dukiya ba zai taba na bi ta kan mace ba wai dan sun samu kadaicewa, sai dai ta yi ta kanta .
A hankali ya duko inda kanta yake yana kallon idannuwanta da ta lumshe
A tausashe ya ce" Likita.....ko kin karu?"
Idon ta rintse da karfi a hankali ta ce" Ya rab Aban litle plz....."
Ya saki murmushi ya ce" Daga tambaya? wai dan in kirayi doctor"
Idannuwan nata ta bude tana dubansa, a hankali ta ce" A'a ba sai an kirayeta ba............zan ware ne in sha Allah "
idannuwansa ya lumshe mata matsayin amsa, sai kuma ya dan dora yatsarsa a kusan girarta a hankali ya ce" Babu abinda ya kai rike mutunci wahala a wannan zamanin, shi kuwa mutuncin nan yana da matukar girma a duniya ta........, Karamah thank you..............zan kula da ke, zan girmamaki, zan darajanta ki, zan kare dukkan martabarki ........."
Ya dan dakatar da magana ya saka idannuwansa cikin nata a tausashe ya ce" Zan kaunaceki mudin rainah"
Wannan bakon yannayin da take ji tunda ta hadu da shi a gidan nan matsayin miji ne ta karra ji, a hankali ta lumshe idannuwanta tana jin sanyi na ratsa gaban jikinta, a hankali ta sada kai kirjinta na amsawa Duda a kwonce take sai take ji kamar yawo ake yi da ita, hakan ya sa ta gaza daga idannuwan nata tana jin yadda yake shafa wajen girar nan nata har barci mai dadi ya fuzgeta
Gefenta ya koma ya kwonta sannan ya sakata jikinsa, dan zai so yayi mata mugun sabon da wasu mazan masu shegen wayo ke yiwa matansu, wato kwonciya cikin jikinsu, saboda wayo irin nasu ko dai ace neman fitina duk inda mace ta je barci zai iya gagarar idannuwanta, idanma kuma aure ne ya karra ya haÉ—ata da bushewar ido duk daren da zai kwana nesa da ita.....wannan sabo yana da wahala sosai da sosai (Rijalu yan baiwa)........
Da safe bayan ya gama da bangaren su Hajia ya fito ya dawo bangarensa dauke da flsk din da aunty shareefat ta kawo ya nufi dakin Khadeejar a nutse ya kwonkwasa
Rurin kurma ya saka shi dan zarro ido ya bude dakin ya shiga da tunanin su litle nan aka diro? tun dazu yake nemanta akace yau fa da wuri ta fita wajen mai kosai shine ya dawo da nufin zai lekata ta window din dakinsa ya ga me take jira bata shigo ba duba da kakan nata bai fito shago ba warhaka ai
A tunaninsa idan ya shigo zai sameta a cikin abin rufa ne tana fama da kanta sannan ya samu Kurma na damunta, sai ya same su zaune saman cafet sun saka plate sun zuba kosai mai zafi Khadeeja na dan karkace domin zamanta ba irin na kurma bace ta dauki guda ta dangwala yaji tana faman sai kurma ta bude baki ta saka mata shine kurma ke ta dariya tana nunawa ita fa ba baby bace, Khadeeja kuwa ta nuna baby ce mana gatanan yar karama, shine suke gardamar kurma sai ihu take a matsayin firar kenan
Turaran wutar dake bin dakin ya saka shi kai dubansa inda bed din yake, sai ya ga an cenza zannin gadon da na rufar, gaba daya an cenza komai , dakin ya kawatu sosai
Murmushi yayi a nutse ya karaso inda kurma ke gaishe shi da yarenta, Khadeeja kuwa tana murmushi tana kallonta tana sada kai har ya zauna a gefensu yana kallon kosan ya furta" Me ? cinyewa zaku yi ku barni?"
Khadeeja ta saki murmushi tana duban wayoyi har uku da ya ajiye a daf da ita a hankali ta furta" Barka da safiya, ya gajiya"
kosan da ya dauko ya nufi bakin litle ta zarro ido tana dubansa hadi da turo bakin shagwaba ita a dole ta girma ya saka shi yin dariya yana boye bakinsa dan kar ta karance shi ya ce" Dama mamanki nake son ba, dan kar ki ga ana soyaya ki fasaramu ne Litle, Madame ha in baki...."
Khadeeja ta yi dariya saboda yadda yake boyewa kar kurma ta karamceshi abin dariyar ne walahi, lokaci daya tana kallon yar karamar wayar dake ta ruri tana neman agaji ama ya ki dagawa ta ce" Kaikaikai, Aban litle zan fada mata fa"
Dariyar yayi shima bayan ya dago ya dubi Litle da ta tsare su da ido, ya dan dubeta da kyau a nutse ya ce" Zaki je gidan mamy? "
Kurma ta dube shi da mamaki, gidan mamy yace fa?, wato kakarta ta wajen uwa, gidan da idan dai tana son zuwansa sai dai a yi ta shirya irin tambayar da za'a yi dan kar ransa ya ɓaci saboda haka, domin ba so yake yi ba, sai gashi da kansa yana cewa ko zata je,?
Khadeeja ta dube shi ta ce" Ina ne gidan mamy?"
AL'WALID ya yi murmushi ya ce" Gidan kakarta"
Khadeeja ta yi dan tsai ta ce" Aban Litle, ka barmin ita mu gama sabawa mana plz, "
AL'WALID ya dan tabe baki sai ya juyar da kai a hankali ya ce" Ni din fa?, sai mun gama sabawa....kin cenza min sunna daga Aban litle zuwa zumana misali.....ko wani wanda ya fi shi dadin amo haka......., shikenan sai ta dawo ama yanzu duba fa fisabililahi safiyar da Litle ta yi, to kin ga babu wanda ya isa ya hannata gabanan zuwa kawo maki kosan nan na gado, fisabililahi kuma ai akoy abincin safe da ya dace ace zuwa gaba kadan ana ba Maraya AL'WALID yana ci......."
Khadeeja ta rufe baki da sauri tana zarro ido ta ce" Innalilahi na shiga uku da baban Litle "
Yayi yar dariya yana sake kallon wayar nan ya mike ya nufi bayi dan wanko hannunsa domin shima sai yayi ra'ayin cin dagben da Aunty shareefat ta yi musu da hannayensa
Kiran nan kuma ke ta shigowa, Khadeeja ta sake kafe kiran da kallo tunani kala kala na shiga zuciyarta,
Ko dan basu saba saurin samun waya a hannayensu bane ya sa ta ji ra'ayin dagawa? ko kuwa dai wani abu a ranta ke so lalle sai ta daga din?, ita dai kawai ta ji ra'ayin dagawar dan haka a nutse ta janyo wayar ta daga ta karra a kunnenta a lokacin da kurma ta zarro ido a tsorace ta shiga yi mata alamun a'a , a'a, kar ta daga, ba'a taba wayar nan, babu mai taba masa wayar nan, yayi hanni da taba masa wayar nan, ita kuwa bata gane ba sai wata murya da ta jiyo , Muryar na rawa, Muryar kamar ta datijuwa a rikice ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, gudaliya ka daga kirana yau? Alhamdulilah alhamdulilah Alhamdulilah innalilahi wa inna ilaihi raj'une, tabas ko yanzu ciwon nan ya kaini kiyama zan je ba tare da tunanin nan a raina ba, ka sani na yafe maka duniya da kiyama, sai dai gudali bani da lafiya , sosai banda lafiya gudali dan Allah ka yafe min nima, ka bari in ganka"
A tsorace Khadeeja ta juyo inda ta ji motsi a bayanta ta zuba masa ido kamar yadda ya tsaya yana kallonta da sauraron abinda ake fada a cikin wayar
"Hello GUDALIYA? AL'WALID dan Allah ka min magana, idan muryarka nake son ji sai dai na yi ta sauraron na rediyo? dan Allah ka min magana yau daya ka ji?" Daga dayan bangaren aka fada ana dan sakin shashekar kuka
Jikinta ne ya dauki rawa hadi da mutuwar gaɓɓai
A hankali ta mike ta karasa inda yake tsaye ta mika masa wayar kasa kasa ta furta" Ka yi magana, Aban Litle?"
Wayar ya amsa a hankali ya datse kiran sannan ya dora idannuwansa da suka cenza launi a kanta a hade ya furta" Kar ki kuma taba wayar nan"
Daga haka ya soke wayar a aljihunsa ya fice a dakin
Tunda ya fita daga dakin ta zubawa kofar ido ta kasa kwakwaran motsi har sai da kurma ta kamo hannunta ta dawo da ita inda ta tashi suka zauna ta yi mata nuni da ta ci abincin mana?
A nutse ta kalli abincin sai kuma ta kalli kurma ta mika hannu ta dauko ipad dinta, domin zuwa yanzu ta iya rubuta abu a ciki saboda kurma ta koyar da ita
A hankali ta rubuta abu kamar haka ' Me yasa ba'a taba wayar nan?, Wacece ke magana ta cikin wayar? koda yake baki ji me take fada ba ama akoy wata na magana ta wayar"
Kurma na karantawa ta dubeta, sai ta rubuta amsa kamar haka' Mai sunnanki ce, Maman Abana ce, an hannani yin maganarta , kema idan Aba ya ji ki sai ya yi maki duka baya sonta "
Maganar nan ta doke ta sosai wace kurma ta rubuta mahaifinta baya son Mahaifiyarsa, gaba daya hankalinta ya tashi ta rasa inda zata saka ranta, kashema sai ta haye gadonta ta bar abincin da kurma ta kawo da na mahaifinta a nan ta ki kula komai.
Wasa farin girki, kusan karfe goma sha biyu aka hayo mata da wasu girkin, Nanma ta bada umarnin a fitar da shi saboda ba zata ci ba, wanda dukkan abinda yake faruwa ana sanar da shi komai da komai, tun daga kan abin karin da aka fitar Aunty shareefat ta yi fadan ba'a ci ba me yasa basa cin abinci? hankalinsa ya kai kan abin, nan ya binciki kosan nan ya ga shima ba wani cinsa aka yi na, shine ya ba maman baby umarnin lokacin cin abinci na yi ta tabatar da an kai dakin Hajia karama, kuma ta sanar da shi idan ta ci, shine ta sanar masa cewa bata ci ba, ya bada umarnin ta je ta ji ko wani abu take sha'awar ci ne?
A nutse Maman baby ta dawo ta nemi izini ta shiga ta samu Khadeeja na zaune jikin abin gadonta
A nutse ta rage tsayinta dan girmamawa ta ce" Madame, ko a girka maki wani abu ne?"
Khadeeja ta dubeta, damuwar da ta sakawa ranta ce ta yi sanadiyar zubowar zazabinta, ga ciwon da take da shi a kasa ga kuma kin cin abinci....., uhum, lallema mutumen nan bai san cewa tana iya kai gobe bata ci ba? ya sunna magana da farin ciki dan an daga wayar da take kyautata zaton waya ce mai darajar da ta fi komai daraja a duniyar dan Adam duba da mai kiran mai darajar ne, sai ya ja kashedi yayi tafiyarsa? ikon Allah, taba sane ta ki shan maganin ta ki yin komai sai kwonciya kawai da take famar yi
A hankali ta ce" Maman baby mike mana dan Allah, a'a ki barshi bana jin yinwa ne"
Maman baby hankalinta ya tashi, saboda tunda Khadeeja ta zo bata wulakantansu ba, hakan ya sa suma suka damu da ita
A tausashe ta ce" Hajia ko jikin ne ba dadi a kirawo likita???"
'Ikon Allah, wato su dai a gidan nan kowace tusa a kirayi likita, su basa bari su yi ibadarma ta ciwo da an tabu sai magani?, hum
A hankali ta ce" A'a maman baby ba komai na gode"
Maman baby ta mike ta fice ta je ta dauki wayarsu ta aiki ta yi kiran mai gidan tana rage tsayinta sosai ta ce" Barka da hutawa Elhaji,"
Dan gyaran murya kawai yayi , dan haka da girmamawa ta ce" Inaga Hajia bata da lafiya ne, dan ta ki cin komai, kuma bata sha'awar cin komai"
Idannuwansa dake da nauyi sosai ya bude , a inda yake a irin wannan lokacin yana nesa sosai da gida , ama zai fito ya zo dan ya kula da ita, kafin nan a tausashe ainun ya ce" A sanar da Hajia inna , ko kaka B, ganinan zuwa"
Daga haka ya kashe kiran yana dafe kansa a office dinsa
A yau bai yi niyar nan da nan ya leka ba,, sai dai hankalinsa ya tashi sosai ta yadda ya fita tare da direba ba tare da ya shiryawa fitar ba bayan ya fito daga wajen su Hajia inna
Kuma tunda ya zo din ya zamo baki sai shigowa suke yi, du irin yadda ya sanar ba aiki ya kawo shi ba abin ya gagara
Wayar da ya ajiye ya dauka ya danna numbar mai yi masa bincike ya tura kira
Tana fara ringin ya daga da salama
A hankali ya amsa , sai kuma yayi shiru ya kasa yin magana
Mai yi masa binciken ne ya furta" Elhaji in zo ne?"
AL'WALID ya bude rinanun idannuwansa a hankali ya ce" Bata da lafiya, me yake damunta?"
Sarai ya gane wace yake nufi, domin idan zai yi maganar kowa yana yi kansa tsaye banda nata, dukkan abinda ya shafeta yana hargitsa duniyarsa da gigitashi ne, sai dai ya kasa dubanta saboda abinda ya girma da shi mau zafi a cen karkashin zuciyarsa da ya shafeta
A hankali ya ce" Ban sani ba, rabona da ita tunda na kai mata abincin watan nan ta sigar boye kamar yadda muka saba"
AL'WALID a hankali ya ce" Ka je, idan har bata da lafiyar ne ka kula....."
"Ok sir " ya fada da girmamawa yana mikewa
A hankali AL'WALID ya furta" Ka kula da dukkan abinda ya dace , ka tabbatar da ta samu condition din da take da buƙata "
Daga haka ya katse kiran yana rintse idannuwansa ya bude da sauri saboda hoton da ya fado masa a lokacin a baba Hamza ya dauke fuskarta da mari a ranar da ya ja hannunsa ta ja, ya ja ta ja, ya dauke fuskarta da mari ya hankadata ....a lokacin ne kuma yan sanda suka karaso, ta duke ta mika masa hannayenta tana fadin" AL'WALID zo....., zo in rungumeka, zo yarona......."
A lokacin ne kuma ya tura shi cikin daki ya juyo inda take suka yi maganar da suka yi .............
Mikewa yayi ya nufi wajen frij dan ya jika makoshinsa kansa na sarawa , zuciyarsa kuwa na dokawa da maganar cewa bata ci komai din nan ba
Yana shan ruwan ya dauko wayarsa baba ya danna numbar dakin Hajia inna
Jim kadan aka daga mata kiran aka karra mata a kunnenta
A tausashe ta ce" Aban kurma ya aka yi ne?"
Ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya ce" Wai bata ci abinci ba, tun jiya fa...., hala bata da lafiya ....ko kuma fushi take min?"
Hajia inna ta dan daga idannuwanta ta dubi mai aikinta da ta mana mata wayar, a tausashe ta ce" Na sa mamanku ta kawo min ita nan, zata ci .....kai din ka ci ne???"
Sai yanzu ya tuna cewar shima ai ba cin yayi ba, ama kuma a yanzunma bai ji zai ci ba
Hajia inna ta yi murmushi tana sake daga idannuwanta ta sauke a kan Aunty shareefat