Showing 123001 words to 126000 words out of 190762 words
Chapter 42 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
a bayana in ja abinda ya dace in ja sai kuma ki ce a'a? mutumen nan har nan ya tardoni ya wulakantani a gaban yan anguwa, kin san irinsu kuwa idan suka sakoka a gaba ka kyale ka shiga uku?, to dai ki ji da kyau walahi gadin y'ata zan yi, kafarta kafata, yanzu zan shirya in fita saboda tsaro, kuma ki sani daidai nake da ke da duk wani wanda zai ce a'a, aikin banza ma kennan a tardoni har nan in ce a'a? baki isa ba gimbiya, kin yi tsugul, kuma ya batun da muka yi da ke na kai karar uban Mudansir? ai mun ce in an gama bikin nan zamu ke ki samo mana wani mai ilimin munafukan yahudawan ya yi mana tsaye a rufe uban yan iska, yaya kina kan batun ki ko Ni zaki cuta ki min halayar masu jan kunne?"
Mama ta yi tsuru tsuru, a zuciyarta fadi taken Innalilahi na shiga uku, ashe bai manta abin nan ba?, mu kai ฦarar baban Mudansir? na shiga uku Ni Usaina mutumen nan sai ya kasheni hankalinsa zai kwonta?'
A bayane kuwa ta dubi yaran ta ce" Kai ku tashi maza ku je ku yi shirin makaranta, ku ajiye min kayan nan a nan!"
Sumui sumui suka mike suka yi waje, ta juyo inda Aba ya rike kugu tana kallonsa a tausashe ta ce" Haba mana baban su Sidiku, jiya jiyan nan fa ka karra rike daraja a gari ka yi suruki, kuma sai a hangoka kana dambe fisabililahi ba zaka ji tsoron sirikin naka ya gani ba?"
Aba ya zabga mata harara ya ce" A'a!" sannan ya nufi ciki
Mama ta zarro ido tana kallonsa ta bi bayansa a tausashe ta ce" Da kunya mana, haba mana, kaine fa sirikin AL'WALID guda"
Aba ya ja ya tsaya ya juyo ya nuna mata yatsa ya ce" Kin ga gimbiya ki rabani da jaraba? kin ga ko? in kin hanna y'ayanki bina ai Ni kadai na isa in janyo maki fitinar, Allah kuwa sai na je, sai fa na hadu da mutumen man na masa jijigar da zai raba y'arsa da mijin y'ata dan karya ne a mana kishiya Allah kuwa!"
Ya shige dakinsa ya mako kofar ya bar Mama baki sake da hanci kamar ta yi summar tsaye
Ikon Allah, wanzan baka so a jikinka kennan, kishiya dai kishiya ce yake nufi ? lallema, lallema
Tana nan zaunen nan ya fito ya sha dakakiyar shada sabuwa dall, sai buga kanshi yake ya kafe hula a kansa ya harareta da gefen ido kasa kasa ya ce" Aikin banza da bata kishin mijinta, bari in je a ja gaban garar nan mu kai , in yi dukkan abinda ya dace , babu fa wanda zai dagawa y'ata hankali in kyale shi ko waye shi!"
Ya yi gaba ya bar Mama baki bude tana kallon sa
Da ya fito ya samu Mama Fateema da Hajia iya sun zo sun sha shiga ta alfarma , sai kawai yace su tashi su tafi
Mama FATEEMA ta mike tana fadin" To yaya bari in sanar da Hajiar, bata dakinta ne"
Aba ya wani dauke kai ya ce" Wai wace wancan? Ni zata wulakanta ko FATEEMA? Ni zata hanna fada ? kyaleta kawai mu yi tafiyarmu wancen bata kishin mu mu je, mu tafi"
Mama fateema a dole ta bi bayansa saboda guguwarsa ba zata iya ba, suka fita suka shiga babar motarsa ya shige gaba yana hararan ya'yan da hannu ya musu alamun zasu hade ya warci motarsa ya karra gaba, shi da yan uba sai dai hange!
_________________________________________
Barci mai cike da mafarkai irin wannan ta jima rabonta da irinsa, sai dai lokacin sallar asubahi na yi ta farka da kasala da ciwon mara na al'adar da ta dan dawo mata kamar yadda ta saba yi mata
Wanka ta yi na kirki ta darji jikinta sannan ta fito ta bude akwatinta ta ciro fari kal din leshhh da Abansu ya musu tsarabarsa daga Dubai dandatsetse mai sanar da darajarsa da an kalle shi
A nutse ta kimtsa domin ta san ko yayane a yau tana iya yin bakin fuskar da zasu dan kawai su kalli amarya domin amarya akoy farin jinnin wannan
Zama ta yi ta shiga hada allurar da zata yiwa cinyarta tsigar jikinta sai tashi take yi saboda ba son allurar take yi ba, sai dai kuma rashin son nata ba zai bari ta bar kanta cikin ciwo ba tana ji tana ganni a irin wannan gidan kare kukan ka
Ta gama hada allurar ta ji dan kwankwasawa, tun bata bada damar a shigo ba aka murda aka shigo hakan ya sa ta yi tsaye tana kallon mai shigowar hadi da dan kashe girman idannuwanta
A nutse ya shigo, da salamar da ta fito daga makoshinsa kawai ya dan tsaya ya sauke dubansa a kanta
Walwalin da leshin ke yi kadai ya isa ya dauki hankalin mai kallo, ga wani dauri da ta kashe da ya saka shi sake binta da kallo kafin ya dan kalli wajen kaffafuwanta sai kuma ya dauke dubansa ya karasa inda ta mike tana dan kallon gefe da gefe zuciyarta na kwasar barin nan irin na dazu
Allurar dake hannunta ya bi da kallo, kafin ya sake kallon gashinta dake sake a bayanta
Kadara ce mai zafin gaske, subahanallah rikakiyar kadara ce mai zafin gaske yarinyar
A hankali ta bude bakinta kasa kasa ta furta" Barka da safiya"
Murya ce a sanyaye, murya ce mai zakin gaske, murya ce mai nutsuwa........Ya Salam.
Kasa amsawa yayi, ya dan dubi agogo ya ga karfe tara ce ta yi, dama ya shigo cikin dare ya ji jikin da zafi, ya jima ma a zaune kafin ya tafi dakinsa dan kar ya katse mata barcin, da asubahi kuwa da zai je masallaci sai da ya nufo dakin nata ya ga fitila a kunne sai kawai ya wuce dan an fara tayar da Sallah ,sai yanzu ya dawo bayan ya ga baba Hamza da Hajia inna sun yi fira sosai, a bangaren Nasa ma ya samu litle da aunty shareefat, sunna falon kasa yanzu haka, shine ya hayo ya shigo dan ya ga jikin nata ya kuma sanar da ita bakinta dan ya ga kamar abin kari ne suka kawo
A hankali ya mika hannu ya amshi allurar , yana kallonta da kula sosai ya ce" Mu je asibiti"
Khadeeja ta lumshe idannuwanta, ba zata iya ba, bafa zata iya da bugun zuciyar nan ba, du idan ya budi baki sai kirjinta ya doka......................... innalilahi wa inna ilaihi raj'une
A hankali ta ce" Allurar ce zan yi "
Sauke seringin yayi daga saman allurar a nutse ya dan sake kallonta sai kuma ya girgiza kansa kawai bai sake ce mata komai ba ya nufi inda kayanta suke ya dan tsaya cike da tunanin abinda ya dace ya yi?, sai kawai ya dauki abinda yake kyautata zaton hijab dinta ne, ya juyo inda take din nan ya karaso
Yakan samu nauyin harshe dan bai san sunnan da zai yi kiranta da shi ba, a lokacin da ya budi baki zai yi magana wayarsa ta ringa neman agaji
A nutse ya ciro ya karra a kunnensa a hankali ya furta" Babah"
Kanta ta daga tana kallon sajen fuskarsa , da amon muryarsa, a hankali ta ษora dubanta a jajayen lubanansa a lokacin da ya furta" Gara kuma?"
Baba Hamza ya ce" Eh walahi ka ga manyan motoci biyu sun shigo shake da abinci , gayanan shi uban yan rigimar ya min tsaye sai shasheka yake wai ya gaji da loda buhunnan shinkafar a bashi ruwa ya sha, Ni kam ya raina min wayo Allah kuwa, wai Gara, bayan nace masa kar a yi"
Karbar wayar kawai Aba yayi yana sakin murmushi ya ce" Asalamu alaikum wa rahamatulah wa barakatuhu "
AL'WALID ya dan yi kasa da dubansa, irin yadda ta zuba masa fararan idannuwanta masu ษauke da kwali sai da tsigar jikinsa ta tashi, haka kuma ya samu kansa da dan riko hannunta lokaci daya ya dan sado ta yadda zata ji Muryar a tausashe ya ce" Wa alaika Salam wa rahamatulah, Barka da safiya Aba"
Aba ya wani saki murmushi ya ce" Fatan an tashi lafiya , ya gajiya, ya taro? ina Hajia ฦaramar fatan tana nan tana biyaya sau da kafa ko in ci ubanta?"
Daga shi har itan ido suka zarro, da sauri ta hade hannayenta idannuwanta waje har hancinta ba gogar nasa kasa kasa sosai ta ce"
07/12/2024, 15:15 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na talatin da biyar (35)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐0912 262 1080
LABARI
"Dan Allah kace eh ina yi, Abanmu zai iya zane ni da safiyar nan, gashi zazabi nake yi" Ta furta kasa kasa sosai, furucinta na dukan fuskarsa,
A hankali ya samu kansa da lumshe idannuwansa, a hankali yana dan sake dubanta kasa kasa ya ce" Alhamdulilah Aba, ama ka ga ai irin haka ke sakamu yin addu'ar kary....."
Da wani irin sauri ta zarro ido ta saka hannunta ta rufe bakinsa tana girgiza masa kai
Ido ya tsura cikin idannuwanta har sai da ta sada dubanta ba shiri
A tausashe bayan ya yi aiki da hannun nata ya dan ciji yatsar ta saki bakin nasa ya ce" Ganinan fitowa dan Allah kan maganar garar nan, yaya za'a bamu mutun kuma a bamu abinci?"
Aba ya wani cira kai ya ce" Kai haba dai, ai abinda yake faruwa ka ga an riga an gigitamu da harkar garar nan, ka kuwa san har saki ake yi saboda garah? Shine dai aka dan kokarta karba zaku yi kar ka biyewa tsohon nan "
AL'WALID ya katse kiran saboda gaba daya yarinyar nan so take yi ta shiga jikinsa dan ta ji me Aba ke fadi, gaba daya yarinyar nan ta gama hadewa da shi sai faman mane kunnayensu da junna take yi dan ta ji da kyau abinda ake fadi a ta dayan barin
A hankali ta dago da ta ji shirun yayi yawa ba amon Muryar Aba, shima kuma yayi shiru
Dan baya ta ja tana fadin" A'uzubulahi" haka kuma tana dan kikifta ido da janyewa daga jikinsa
Dubanta yake yi dai bai iya cewa komai ba,
A hankali ta ce" Walahi ban san har ka manemin ba, ina jin Muryar Aba, subahanallah ya zaka mane min?"
Ido kawai ya dan fitar yana dubanta, sai kuma ya yi murmushi ya dan nuna kansa, har zai yi tambayar da take harshensa sai kuma ya juya da dan hanzari saboda ba fa zai yiwu a bashi garah ba, yaya za'a yi wai a baka y'a sukutum kuma a hada maka da abinci? kennan ance ka ci ka koshi ka kirta mata rashin mutunci ko?
Har ya kama kofar ya dakata ya juyo , a hankali ya ce" Hajia karama, ki saka hijab din ki sauko mu je asibitin....., ba shawara na nema ba fa..........."
Daga haka ya sakar mata kofar ya fice
Khadeeja ta saki bakinta harda karkata kai bayan ya bar dakin
Gaba daya jikinta kanshin turarensa yake yi, innalilahi idannuwanta kuwa har gizo suke yi mata
A hankali ta dauki hijabin tana kallo, lokaci daya kuma ta saka, ta dauki jakar hannunta ta rataye ta rataya ta juyo a hankali ta nufi hanyar matakala tana ayana magana kamar haka' Inama ya'yan gidanmu su ganni da jakar nan a haka ina saukowa? hahahaha su ga matan aure na saukowa daga dakinsu"
Hango iya da ta yi da mama fateema ya sakata saka dariyar farin ciki da gudu gudu ta karaso tana fadin" Wayo Allahna dadi, iya? mama? wuni kuka zo min hala?""
Iya ta zuba mata ido tana sake jan mayafinta ta dan leka inda su aunty shareefat suka nufa sunna kokarin kawo abincin kari kasa kasa ta ce" Zan ga Annabi idan na yi hali na gari, to wai ko irin yadda kudi ya rasa daraja hakama budurci? y'ar nan mu ai sai mu yi sati a karkace ama ya'yan yanzu sai ki ga daram abinsu sunna da wata wakar yan soyayya"
Mama fateema ta kawar da kai tana yin kamar bata ji ba, Khadeejama ta yi kamar zata nutse kasa, haba dan Allah, wani budurcin kuma? wai ita iya bata gannin babar mutun a zaune ne?
Iya ta sake dubanta ta ce" Kin ga, zuwa na yi in karra jaddada maki kin ga shigo ko yaji idan kika yarda kika daka sai mun kifar da d'an iska, ba zaki min bakin cikin ziyara ba, ah to, ina fatan kina tune da lesson din da kika dauka a saman majalisa"
KHADEEJA ta sada kai kasa kasa ta ce" Iya dan Allah ki bari mana"
Iya ta saka y'ar shewa suka tafa ta ce" Allah mai alkhairi dama y'ar nan da kisarta aka haifota kuma ta rike koyarwar samun mafita, ki ga dan Allah yadda ta yiwa ido Fati"
Mama FATEEMA kam ta ga abin ba na karewa bane ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Uhum, yaya jikin naki? ban kirayi mai kitso da kunshin ba nace sai na zo mun ga sauฦin jikin"
KHADEEJA ta shagwabe ta koma jikin Mama Fateema ta ษora hannunta a wuyanta ta ce" Mama karama taba wuyana, sai ki gasa biredi a jikina , ai sauki kam babu gaskiya yanzu haka asibiti za'a je dan Allah kar a min kitson nan"
Murmushi aunty shareefat ta saki bayan sun karaso tana nunawa kurma Khadeeja ta yi mata alamun itace ta je mana su gaisa, haka kuma lokaci daya tana amsa gaisuwar da Khadeeja ke yi mata da kula, sannan ta sake fadin" Litle jeki mana, ga maman naki, ki je...., daughter ya kwanan sabon gidanki? ina fata jikin ki da sauki?"
Khadeeja dake kallon kurma, itama kurmar ita take kallo, a dan nesa da ita domin a tsorace take da matan da ake haษawa da mahaifinta, Mufeeda na yi mata kisan mumuke ne, ta taษa amsar ipad dinta ta rubuta mata sai ta kasheta da wuka idan tana zuwa inda suke fira da babanta ta tarda su, ta sha fakar ido ta dungureta da karfin tsiya, kuma bata yi mata a gaban mutane shi yasa yanzunma a tsaye dai take ama ta kasa zuwa kusan Khadeeja
Khadeeja ta dubi aunty shareefat dake hada mata kayan kari a wasu plate na alfarma a tausashe ta ce " Aunty, kanwarki ce? bata magana ne?""
Aunty shareefat ta yi murmushi ta ce " Kurma ce, ama tana karantar lebe, kuma tana rubuta amsa a ipad dinta....., no ba kanwata bace, jikata ce, y'ar Elhaji karami ce wato AL'WALID "
Da sauri Khadeeja ta kalleta tana neman karin haske, domin mamaki ya kamata da tambayar kanta nan take cewar dama yana da wata matar?
Aunty shareefat ta dan dubi kurma ta ga ba ita take kallo ba dan haka ta ce" Mahaifiyarta ta rasu ranar da ta haifeta"
KHADEEJA ta Dubi kurma zuciyarta na cika da rauni da tausayin yar matashiyar yarinyar wace kamar ka tabata jinni ya fito tsabar hutu
Dan matsawa ta yi a gefenta ta kalli wajen ta ga zai isa ta zauna ta dubi Litle a hankali ta nuna mata gefenta sannan ta ce" Zo ki zauna....., kin ji? yaya sunnanki?"
Kurma sarai ta karanci me tace, ama ta kasa motsawa, sai ta kalli aunty shareefat ta kalli su Mama Fateema da aka yi sevng din abinci sannan ta kalli Khadeeja, har sai da Aunty shareefat ta dubeta da kula sosai ta ce" Je mana litle, ba nace maki mamanki ce ita ba?, je mana ta miko hannu kar ta gaji ko?"
"ki je ki fada mata sunnanki ko ?" ta karashe tana ajiyewa Khadeeja nata abincin bayan ta janyo dan karamin table
A hankali litle ta karasa kusan Khadeeja
Khadeeja ta kama hannunta a hankali ta dan rike shi da kyau tana kallon fuskarta ta ce" Me sunanki?"
Litle ta ciro ipad dinta ta shiga wajen rubutun wps ta rubuta mata sunnanta kamar haka "My name is Rahamatulah AL'WALID"
KHADEEJA ta zubawa sunnan ido, haka kawai sunnan ya birgeta da mahadinsa, ta sakar mata murmushi tana dubanta ta ce" Ni kuma i'm NANA KHADEEJA EL YA'U"
litle ta dan dubeta a dan tsorace saboda sunnan da aka yi mata hannin kamawa koda wasa, sai kuma ta kalli aunty shareefat da sauri ta yi rubutu a ipad dinta ta mikawa aunty shareefat
KHADEEJA na kallonta da dan mamaki ta ce" Aunty me ta rubuta?"
Aunty shareefat da jikinta ya dan yi sanyi ta dago daga karatun abin ta dan dubi Khadeeja tana basarwa ta yi murmushi ta ce" Ba komai daughter, ki karya mana"
Mama fateema ta ce" Ai fa in dai Anmy ce idan ta samu fira ba lalle ta tuna cikinta ba, dauki ki karya mana ke da baki da lafiya?"
Da sauri kurma ta amshi ipad din ta mikawa Khadeeja ta dan