Showing 69001 words to 72000 words out of 190762 words
Chapter 24 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
gaske take damun mu, kuma ina so in kawo kukana ne a gabanka kai tsaye saboda kakan yara ya ki ya dube mu bale ya tsayar da abin, .....haka kuma na fi ace a gabanta na fada idan har na yi mata karya sai ta musa....."
Da dan mamaki yake dubanta, sai dai bai ce komai ba, Mufeeda kuwa da ta ji wannan abin gabanta banda dokawa babu abinda yake yi, tashin hankali da tsoro na shigarta da tarin tunanin me kennan? yanzu idan har suka kawo kararta wani irin hukunci zai yanke mata? basu san halinsa bane da zasu kawo kararta wajensa? ai baba suke fadawa duk abinda ta yi musu ba shi ba ko? innalilahi
Hajia zainabu ta Ιora da fadin" Ka ga, a duk lokacin da Mufeeda zata zo gidan nan, sai ta nemi wani abu na cin kashi ta yi mana, bata girmama kowa a gidan nan, bata bamu daraja, ka yi hakuri ba na fada dan in hadaku bane, ina so ne ka sanar mata ta gane mun san cewa gidan nan naka ne, kuma mun san cewa ko bayan ran Elhaji in dai mu muna raye zaka rike mu, dan Allah ta bamu lafiya da mu da iyayenka mu yi zamanmu lafiya, in abinci ta tarda wani na ci sai ta yi masa gori, in ac ta tarda a kunne sai ta kashe, in zance ta tardo yara na yi sai ta nuna a kan me za'a tsaya ana zancen a filin gidan mijin da zata aura, ka ganta nan a yanzu haka shigowar nan da na yi zagina ta yi wai na zo maula, shin mantawa take yi da karfin zumunci ne? ko maular na zo ai babu ruwanta tunda ba aljihunta zan taba ba ko....." Sai kawai ta shiga gargadar murya hadi da sakin hawaye tana jan hanci
Khalisat kuwa ta sada kai tana jin haushin mufeedan nan sosai a ranta
Shi gaba daya abin daure masa kai yayi, ya dago ya kalli Mufeeda da ta yi tsuru tsuru ya fi a irga, yana sake kallon su Hajia murya na rawa Mufeeda ta ce" bab walahi ba haka bane, Ni ba.........."
"KARYA ZATA YI MAKI?" Ya katseta da muryarsa a hankali, sai dai a mugun kausashen da ya saka idannuwanta cika da kwalah
kallon da ya kafeta da shi kuwa mai tsauri ne wanda ya sake daga mata hankali
dauke dubansa ya yi a kanta ya dubi Hajia
A hankali ya ce" Waye yace maki nan gidana ne?, eh sunnana ke saman takarda, shima dan Elhaji ya ki cewar in maida sunansa........, ban ja da shi bane dan ban san akoy ire iren su Mufeeda a jikina ba"
Ya dan dakatar ransa na tafarfasa sosai, domin yayi mamaki matuka da abin nan, wai a haka bata fayyace masa wasu abubuwan ba, a haka idannuwansa basu ga wasu abubuwan ba, takaicinsa shine a kan gida take musu wannan abin? ikon Allah ita da ya dace ace itace tsani da zasu hau su tarda shi da dukkan bukatunsu? domin sarai ya san wani lokacin sunna jin kunyar samunsa shi yasa ya kasance mai yawan kyauta da yawan kyautata musu koda ba sallah ba, ko wani bikin ba, domin kakanin nasa babu wace ba'a saka mata isasshen kudi du karshen wata a account dinta, su kuwa iyayen nasa yakan yi musu kyauta mai daraja a duk lokacin da hakan ya kama..........., in banda shirme irin naa Mufeeda tana tunanin zai yi aure ya zauna a gidan nan da iyalinsa ne? wannan gidan ya zamo familly Hause ne, duk wanda yake da bukatar zama kofa a bude take zai samu wajen zama da abinci da wuta da ruwa in dai yana raye kuma Allah ya ci gaba da buda masa, sai dai in dukiyarsa ta kare ne hakan zai ragu, ama ba wai ace da ransa da lafiyarsa ba matar da zai aura wace yake da burin ta zamo mace mai kyauta mai sadaka mai girmama wani ma ba nasa ba, itace ke aikata haka? subahanallah.........
A tausashe ya dora da fadin" Ama daga yau, in sha Allah zan sake zaunawa da shi in kwatanta masa cewar gidan nan naku ne, kunna da iko da shi, ba wai ku ba hajia ko wani yake da bukatar taimako a nan ya zo, gaba dayanmu mutuwa zamu yi mu barshi a duniya......."
Ya sake ajiye maganar da Muryar mai sauki, ya dora da fadin" Ki yi hakuri, in sha Allah babu wanda zai sake zagin ku da fuskata"
Farin ciki ya mamaye zuciyarta, daga ita har khalisat, domin abin nan yana daga musu hankali, idan akace yana gari kowa baya sakin jiki yayi abinda ya ga dama dan sun san tana kusa da gidan, idan ta shigo ta ga wani abu tsaf zata wankeka a gaban ko waye, kuma Elhaji Hamza yace su kyaleta wata rana sai labari
Su dinma hakuri suka ringa bashi sannan suka mike suka tafi bayan sun yi salama
Shiru wajen ya dauka bayan tafiyarsu na wasu yan mintuna kafin ya mike ya juya ya nufi hanyar coridor din dakinsa
Da sauri ta mike ta bi bayansa muryarta na rawa, tuni hawaye sun bale mata ta ce" Ama, ai ta kamata ace ka tambayi Ni me suke yi min ko? bai dace ace ka goyi bayansu daga fada maka magana ka yarda ba ko?"
Dakatawa yayi, domin ba zai so ta bi shi dakinsa na barci ba, uwa uba ba zai so wani ya ganta a wajen dakinsa da irin wannan shiga Tata ba, Duda ya san abinda suke fada kasa kasa , ya kyale kowa ne dan babu wanda ya halice shi bale ya ji tsoron sa
A hankali tana dubansa ta ce" Dan Allah ka yi hakuri kar ka dauki fushin nan naka da Ni, ka ga yau fa kace zaka same Ni a cen gidan , baka je ba, kuma na zo zamu yi fada? Ni bana so mu yi fada, ka yi hakuri su suke jana nima na rama"
A kausashe ya ce" Mufeeda! ki kama kanki, ki bani space in gane Wacece ke, domin a yanzu ya zama dole in sake duba wacece ke!"
Yana gama fada ya juya
Da sauri ta ce" Yanzu nice baka san Wacece Ni ba kuma yau?"
Ya juyo yana dubanta ya furta" Yes!, ban sanki ba, dan kina boye min abubuwa da yawa, ki kalli shigar jikinki, a haka kika fito kika zo inda nake, an gaya maki ni shashasha ne da zan auri macen da bata kishin kanta?, why zaki ringa tardoni gidanmu a irin wannan time din? ke bakya tsoron kadaicewa da ni ne ko sabawa kika yi? excuse me but dole in tambayeki bakya tsoron mu tsaya daga Ni sai ke a wajen da komai ke iya faruwa ne ko sabawa kika yi?, nd Mufeeda ashe kina da bakin zagin ahalina?????, ashe baki da kunya?????......., thank you fr al, yanzu ki tafi dan bana son in juye maki a nan!"
Ya karashe yana daga mata murya dan baya so ta karra koda second daya ne tana yi masa musunta na rainin wayo
MUFEEDA jikinta rawa yake yi, domin tunda take da shi bata taΙa gannin bacin rai a fuskarsa irin haka ba
Da sauri ta juya, ta fara tafiya ta dakata ta juyo tana kallonsa hawaye wasu na sake bale mata, shi kuwa a tsayen nan da yake ita din yake kallo shima , ama kuma ba wani alamu ko diz na tashin hankalin yannayin da take ciki a tare da shi, dan kuwa mamakin ta ya fi komai damunsa, har tunani yake yi dama a cikin mature akoy shashashai?, shi da yake son daukan mace mai shekarun da suka zarce na yarinya dan baya son ire iren halayar nan ne, baya son mace mai raini, baya son macen da saboda rufe jikinta kadai sai ta hadasa masa ciwon kai, ashe suma manyan akoy masu irin halin nan? ya salam,....to ko abinda ya sa Baba ya kuge kan maganar auren nan ne?........
'AURE.....' zuciyarsa ta sake maimaita masa, ya sake bude idannuwansa a kan Mufeeda wace ta fashe masa da kuka sosai tana tsugunne dan kuwa ta sani ba zata iya tafiya a haka ba, idan ta tafi ta barshi a haka zuciyarta bugawa zata yi, idan har ta tafi da kalaman nan da ya fada ba zata iya rintsawa ba yau
'Ya maganar auren ? har yanzu yana kan bakansa?............' ya sake tambayar kansa, sai kawai ya dauke idannuwansa daga kanta ya juya ya nufi ciki, ba dan bashi da zuciyar tausayi ba, ko daya, dan kawai ya sani ne idan ba mugun fushinsa ya nuna mata ba ba zata daina abinda take yiwa ahalinsa ba, shi kuwa a kan su sai ya daina kowace mu'amala da ita, dan baya son raini sam!
Hankalin Mufeeda sake tashi yayi gannin ya kada yayi tafiyarsa, mikewa ta yi tana kukan nan ta juya ta nufi waje, da nufin tarda baba ta fada masa dan kuwa ta sha kaiwa baba karar AL'WALID din, lokuta da dama idan ya juye mata baban ne ke yi masa magana ya dawo daidai
Sai dai tana fitowa ta nufi bangaren baban ta samu Su khalisat da iman da Raisa sunna tsaye sunna magana, kuma abin akaicin sunna ganninta suka bushe da dariya
Zuciyarta, da rabon a yi suka hasalata suka saka ta nufe su rai bace bayan ta sake share hawayenta ta ce" Khalisat, Imane, Raisa, dariya kuke yi min bayan kun hada baki kun hadani da AL'WALID ko? ba damuwa , abinda baku sani ba ina jiran lokaci , idan lokacin tawa dariyar ta yi ku kuka da kanku, ba wai ku ba, a nan duniya inaga babu wace ta fi kusanci da shi kamar musakiyar cen ko? to walahi sai na rabata da shi bale ku, baku da hankali, baku san me yake jiranku ba, fushinsa na dan lokaci ne zai sauko mu sasanta junna, kun san a nan duniya shine gatanku, duk wata takamarku sai na daidaitata ba iya ku ba har wa'inda ke gidajen aurensu ama kuma basu bashi lafiya ba, da Ni kuke maganar!"
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*FARKON GANIN IDONA*
πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*π³πͺ
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you π*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ΖAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAΖIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Ashirin (20)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
π0912 262 1080
LABARI
Zuciyarta, da rabon a yi suka hasalata suka saka ta nufe su rai bace bayan ta sake share hawayenta ta ce" Khalisat, Imane, Raisa, dariya kuke yi min bayan kun hada baki kun hadani da AL'WALID ko? ba damuwa , abinda baku sani ba ina jiran lokaci , idan lokacin tawa dariyar ta yi ku kuka da kanku, ba wai ku ba, a nan duniya inaga babu wace ta fi kusanci da shi kamar musakiyar cen ko? to walahi sai na rabata da shi bale ku, baku da hankali, baku san me yake jiranku ba, fushinsa na dan lokaci ne zai sauko mu sasanta junna, kun san a nan duniya shine gatanku, duk wata takamarku sai na daidaitata ba iya ku ba har wa'inda ke gidajen aurensu ama kuma basu bashi lafiya ba, da Ni kuke maganar!"
Raisa dake da gagawar magana da kuma saurin saka abu a rai tana dubanta ta ce" Aunty Mufeeda ba fa abinda kike tunani bane muke yi a nan, kuma walahi magangannunki sun yi tsauri da yawa, ki ringa yi kina astagfari saboda rayuwa ba'a son bawa ya cika alfahari, ko shi Elhaji karamin Allah ne ya bashi yana iya amsa a lokacin da ya so bale mu, mu mun san da wannan, kin mayar da mu makiyiyarki bayan babu abinda muka tsare maki? mu bamu ce zamu sako ki a gaba ba ama ke kin sako mu?"
Imane ta tari zancen tana fadin" Meye na su bata hakurin? in bata sa an janye numfashinmu ba ta ki Allah, ke a wajen nan idan bamu shake ki muka daki banza ba muka gudu ki ce ba ya'yan halal muke ba, banza da bata da aji!"
Ran Mufeeda ya karra Ιaci, ta nufi imane tana fadin" Ke dan ubanki kin san Wacece Ni? dan kunna ganina a banza kunna tunanin banza ce ni? bari ki gan........."
"UUUUHUMMMMM" ya sauke gyaran murya da dan karfi, sai kuma ya shiga dan tari sannan ya saki tafiyarsa da kyau dan su gane tahowa yake yi
Daga ita har sun sai da suka dan tsorata sannan suka gane baba Hamza ne ke tahowa, dan haka da sauri Mufeeda ta ja gefe ta shiga kukan da ya sa du suka kalleta ido waje da tsoron abinda zai biyo baya
Bata idasa basu tsoro ba sai da ta fara fadin" Ni ban ce dole sai kun girmamani a cikinku ba, ama kuma menene na zagin? shikenan ba zan zo neman baba ba sai ku rufeni da zagi kuma a gabansa ku nuna ba haka ba?"
Hankalin Raisa ya fi na kowa tashi, domin bata son abinda zai batawa mahaifinta rai, yanzu haka da ba dan sun zo sun janyota ba da ba zata fito warhaka nan ba, su imane ne suka janyota suke tsegunta mata abinda ya faru, ko maganar basu gama ba mufeedan ta taho tana kuka ,
Gannin Raisa ta fara inda inda da sauri imane ta rike hannunta, domin tsoronta zai sa ta bude baki ta fadi abinda ya faru dala dala
Baba kuwa a tsayen da yake yake furta" Subahanallah me yake faruwa haka, ku ba ta girme ku ba zaku sakata a gaba ku yi mata raini?" Tamkar bai san asalin abinda yake faruwa ba, bayan tunda ta taho ya nufo hanyar shima dan shigowarsa kennan yana tare da makocinsa sunna tataunawa kan maganar wasu gonakin gado da aka saka kasuwa kuma ake son kudin da wuri shine ya kawo masa tallar bayan sun fito daga sallar isha'i
Mufeeda na kuka ta ce" Baba, walahi ka ga Khalisat da mamanta ne suka kai karana wajensa, suka sa ya min sumul ya koreni kuma na taho in fada maka dan ka yi masa magana su kuwa suke ta dariya sunna ce min karyar banza mai bin namiji"
Raisa ta zarro ido ta ce" Innainnalilahi, kaikaikai, walahi ba'a yi haka ba, ki ji tsoron Allah Mufeeda "
Baba ya ce" Yi min shiru, me kuke yi a nan din da daren nan? maza ku wuce ciki!"
Sumui sumui suka shige ciki, sannan ya maido dubansa kan Mufeeda, ya dan jima yana kallonta, dukkan uzurin da ya dace ace ya bata ya bata a zuciyarsa, ya tausasa zuciyarsa sosai sannan ya fara magana a matsayinsa na uba a gareta
A tausashe ya ce" Ki yi hakuri kin ji? kin san tsakaninku mata sai addu'a, kunna da fitina sosai, ki je ki kwonta ciki, zan masa magana, Allah ya sanyaya"
Mufeeda ta gyada kai ta juya zata tafi
baba ya ce" A'a, ina zaki je?"
Mufeeda ta ce" Zan je bangaren nasa ne baba"
Baba ya sake dubanta da kyau ya ce" Ki yi me a cen? karfe goma ce zata yi fa"
MUFEEDA ta ce" Ky din motata da wayata zan dauko in tafi gida"
Baba ya ce" Da daren nan Mufeeda? ki yi kwonciyarki a wajen iyayenku mana? "
MUFEEDA ta girgiza kai ta ce" A'a baba gida zan je"
Baba ya yi dan tsam, sai kuma ya dawo a nutse ya ce" Shikenan je ki wajen motar bari in dauko maki kayan naki"
Bata so haka ba, sai dai ta san ba zai barta komawar ba, dan haka ta yatsine fuska ta je ta tsaya tana jiransa
Baba bai jima sosai ba ya fito ta ba data daga cikin ma'aikatan gidan ya kai mata kayanta sannan ya sa aka bude mata gidan ta tafi
Ya jima a tsaye a filin gidan, du irin gajiyar da ya kwaso da irin taunar da jikinsa ke yi wanda ya zamo masa jiki yanzun bai isa yayi abu da yawa ba zai gaji har ya ringa haki, sai zuciyarsa ta tsaya a waje daya ta cure
Yana tsoron Mufeeda a lamarin AL'WALID
Du irin yadda AL'WALID ke nuna tsayayyen namiji ne shi, meye meye yana tsoron mace a duniyarsa domin kuwa shi ya san in dai mace ta yi niya babu abinda ba zata yi ba
Allah ne sheda, shi bashi da komai sai abinda ke asusunsa matsayin kudi tuzuzu wa'inda yaronsa ke zuba masa
Bayan su, kadarar da ya mallaka a duniya ba wata bace
uwa uba a zo kan wannan yar yarinyar kurma!
Kakar kurma itama yanzu ta zama riko, bale ta rike kurma
ita kadai take da ita, sai shi AL'WALID din
bai taba sakawa ransa bayan ransa matansa daya zata ci gaba da kula da Hajia da kurma ba koda AL'WALID na ci gaba da sakar musu yadda yake musu a yanzu, domin shi ba makaho bane, kuma