Showing 156001 words to 159000 words out of 190762 words

Chapter 53 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3980

Ke fa nake nema, ashe kina falo? Dan in ce maki ne mu saka wannan abayar ta wajen aba wace aka kawo mana a cikin kayan saudiyar da aka bugo masa, zamu fi yin kyau"

Karima ta yi murmushi ta nufi dakinta tana fadin" To"
Daga haka bata karra komai ba, ita kuwa lubna ta rakata da ido kafin ta juya ta shiga dakinta ta rufe ta zauna bakin gado

Ta jima tana dan tunani kafin ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" Allah ya sa wannan karon ki yiwa kanki adalci, Allah ya sa a cikin halayyar masu harin zuciyarki ki iya jajircewa ki dubi zahiri ki yiwa wace ke rungume da ke adalci Karima"

Sai kuma ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye rigar ta mike ta shiga shirin shiga wanka

Lokaci daya kuma ta sauke ajiyar zuciya hadi da murmushi mai tsada a lokacin da ta tuna firarta da mama a jiya da dare, tambayar da ta yi mata kan idan tana da wanda take so? Da ta tabbatar mata cewa babu, sai ta tambayeta shin zata iya zaman aure da ƴaƴansu na bangaren mahaifiyarta? Wato dan mijin mamanta ne baba, lauya ne mai zaman kansa , sannan dan kasuwa , kuma bai taba yin aure ba har yanzu dai yana jira ne tun lokacin da ya cewa babansa yana sonta akace yayi hakuri har ta girma sai yayi hakurin, kuma cikin ikon Allah aba ne da kansa da maman tace masa to lubna fa? Sai yace lubna ai da mijinta , shin ta manta wanda ya yiwa alkawari? Shi yasa ai ya zabawa AL'WALED khadeeja dake bi mata saboda ita da mijinta ai, .....abinda ya tsayar da lamarin aurensu suma na Karima da ummi ne kawai........., Ummi yace zai bata dama ta hadu da wanda ya zaba mata idan sun daidaita shikenan, Karima ce har yanzu ya ki ya ba saurayinta fuska, yaron kuwa kamar wanda ya fada jarabawa a kan karimar, hatta mahaifinsa jira yake yi yace an basu damar su nema masa aurenta dan kuwa sun gane da gaske yake ba da wasa ba.

A nutse ta shiryawarta, sannan ta bude dakin da ake ta buga mata ummi na fadan WALAHI zasu yi tafiyarsu ne idan bata fito na, dan kuwa har sha daya ta yi basu fita ba

Sai da mama ta yi musu nasiha sosai sannan ta ce" Ta yiwu ku samu su Fatima a cen, dan sun tafi su tuni da kayan nata, Allah ya dawo da ku lafiya"

Lubna ce karshen mikewa ta amsa da" amen mama, ai kuwa bari mu yi gaggawa saboda mu tayata ayyukan gyara kayan nan"

Daga nan suka karasa mota suka shige, Abubakar ya ja su

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi, wato Karima bata zubawa mahaifiyarta abincin ba, bata wani rike a ranta ba saima zuwa da ta yi ta duba asibitin da zata yi aiki yau ta hau shiri saboda tana son fara fita aiki a yau.


Kofar gidan su Karima suka tsaya, suka fita gaba dayansu suka shiga gidan ba tare da sun sanar mata da zuwan su ba, domin Karima dai a yanzu ba waya a hannunta shi yasa ko uwar sai da ta bi ta wata hanya kafin sako ya samu gimbiya cewar bata da lafiya saboda ta sani ta hanyar nan kawai ce zata iya gannin y'ar Tata har su yi maganar da take so su yi, ba wani rashin lafiya kalau take, ta bi duk wata hanya ne dan ta samu gannin Karima abin ya gagara shine ta biyo ta nan ko a dace

A filin gida suka same su sunna shan innuwar dalbejiyar dake cikin gidan, kakar Karima na yamutsa tafasa da kulli, mamanta kuwa tana shan koko a kwano da ludayin roba

Gaisheta suka yi su duka , sannan suka tambayi jikinta

Kakar Karima dake mamakin gannin ya'yan elhaji ya'u su duka ta kalli y'arta a dan tsorace da tunanin yauwa ga dalilin da ya kawo ya'yan elhaji gidan nan gaba dayansu

Lubna a tausashe bayan sun zauna maman Karima na yi musu tayin kokon ta ce" alhamdulilah mama, ai sai da muka karya sannan muka fito ma"

Maman Karima ta tabe baki ta ce" Dama na san ai ba iya sha zaku yi ba lubna bismillar dai na muku saboda ido , ina zaku je haka?"

Lubna jikinta yayi sanyi dan ita ba haka take nufi ba, a hankali ta ce" Gidan anmy ne zamu je"

Maman Karima ta Dube ta a yatsine ta ce" kina nufin gidan khadeeja?"

Lubna ta dago ta Dube ta, ta dubi Karima, sannan ta dubi ummi da Sadik

Maman Karima ta girgiza kai ta yi murmushi ta ce" uhum, koda yake ai dama HAKANE idan mai kudi aka aura har uwar yarinya sai ta je bale yayunta, Ama kuwa elhaji ya bani mamaki da har zai tura ku gidan da kanwarku ke aure, koda yake ba komai shi din a gaban mai gidan kanwar taku shima ba kowa bane face mai neman arziki da neman sunna"

Abubakar ya dubeta da mamakin halaya irin na matar nan, sai kawai ya mike yana fadin" Ga dukkan alamu lafiyar ta samu, Allah ya sa a wuni lafiya, idan kun tashi ina mota"

Sai kawai ya wucewarsa dan ba zai iya zaunawa matar nan na zagin iyayensa a banza a wofi ba, shi yasa sam baya son harkarta, ta cika fitina da neman balaki, yaya za'a yi wai ka zagi uba a gaban d'ansa? Yana daf da ajiye fadan mama gefe ya fara tijara a kan darajar su WALAHI!

Yana fita lubna ta yi murmushi bayan sun raka shi da kallo ta ce" Allah ya karra lafiya maman gidan iya, zamu wuce"

Daga haka ta mike tana riko hannun ummi suka kama hanyar fita basu tsaya sun jira abinda zata ce Bama bale har ya bata musu rai

Karima a sanyaye ta ce" Mama, baban namu ne kike zagi haka? Kin san ai ba zasu iya jurewa ba ko mama? Haba mama"

Mamanta ta zabga mata harara ta ce" ke dan Allah rabani da gafalalun yan uwan nan naki yan bakin ciki, kin san ai ba tsoronsu nake ji ba bale in kasa fadin gaskiya, Ni yanzu maganar da nake so mu yi da ke a kan wannan auren da aka kwace a hannun ki aka ba wancen y'ar gidan jajayen mahaukatan, kin yi tunanin abin yi ne ko shima sai na maki?"

Da mamaki ta dubi mahaifiyar Tata da kyau sannan ta dubi kakarta, a hankali ta ce" Mama ban gane ba"

Kakarta ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya ta ce" ke kya fada, ai lamarin uwarki ba karami bane, sai fatan Allah ya rage wahala"

Rai bace ta yabuwa ta ce" kin ga dai iya ba da ke nake ba, ke Karima dubeni nan, kin san dai ba zama zaki yi kina ji kina gani khadeeja na aure a gidan nan tana auren elhaji AL'WALED ke kuwa a hadaki da wanda bai taka kara ya karya ba ko?, dan a wulakancin ubanki yana iya baki yaron shagonsa dan kawai ya wulakanta Ni ya nuna min iyakata"

Karima ta yi wani sakalau, kafin ta ce" To mama ko wa aba ya zabi yanzu ai sai mu masa biyayya, kin dai ga rashin yi masa biyayar abinda ya janyo, bayan wannan Mama ai anmy haka Allah ya tsara itace matar elhaji AL'WALED din, Ni yanzu kin ga adu'a nake yi Allah ya sa a min zabin alkhairi mama, Ama ina ga kamar mudansir ne za'a bani saboda ko jiya sai da Mama ta min tambayoyi a kansa"

Rai bace maman Karima ta ce" Ki yiwa Allah ki min shiru da maganganun rashin sanin ciwon kai irin naki, ke in ba nemawa kai balaki ba yaron da akace dan iska ne shine zaki wani ce shi? To ko ubansa waye a gaban mai aikin gidan elhaji AL'WALED bale shi elhaji AL'WALED din ? Ke ki saurareni da kyau, ba zaki taba auren yaron nan ba na fada maki, elhaji AL'WALED zaki aura "

A zabure ta dubi mahaifiyarta, Muryarta na rawa ta ce" mama, to ko dai Ni ba y'ar baban mu bace?"

Iya ta juyar da kai tana share hawaye ta ce" sai ki bata amsa, sai ki amsa mata, ko dai ita ba jinninsa bace? Saboda maganganun ki kamar na mahaukaciya ko kuwa wace bata je islamiyya ba, ke ko baki je islamiyya ba ai kin san a addinin musulunci yan uwan junna basa auren miji daya in ba daya ta rasu dayar ta maye gurbin yar uwarta ba?"

Rai bace maman Karima ta mike ta kama hannun Karima suka shiga ciki, a tsaye ta dubeta ta ce" Karima ki dubeni da kyau ki saurareni, na tabbata elhaji AL'WALED ba zai dubi yarinyar nan a yanzu ba, saboda ta yi kadan ya dubeta har ya haɗa shinfida da ita a yanzu, idan har kin yi abinda nake so da ke to kuwa y'ar uwarki zata kada duniya ke ki maye gurbin ta, Karima ke Ni fa sai kin shiga gidan nan da ranta ko babu, kece matarsa, ke aka fara ambatawa ba ita ba, tsafin uwarta da bin bokaye da kisa ne ya sa ta cusa y'arta ke aka mayar da ke gefe ake son hadaki da ɗan dan isaka a cuceni, ke kadai nake da ita a duniya WALAHI sai kin auri mai kudi, ga wannan wayar da na ajiye maki, karama ce na siyeta na saka maki layi , ki boyeta a jikin ki kar ki yarda a sani, Karima na tabbata elhaji AL'WALED irin namijin da kike so ne, ga tsayi, ga kyau, ga kwarjini, ga dukiya, ke ce kika ce cencenci jan ragamar gidan nan ba wancen yarinyar ba , kin fahimta?"

Yadda ka san wace aka kumcews nitikan kai haka Karima ke kallon mamanta har Muryar Abubakar ta karade gidan yana fadin" Karima zamu wuce fa, idan kin gama kya biyo mu"

Wani ashar mamanta ta lauyo tana fadin" dan banza mai mugun hali ai ka bari mu yi magana , gatanan fitowa "

Shi dai ya yi tsaye yana kallon dakin har ta girgiza Karima tana fadin" kina jina kuwa?"

Karima ta yi luuuuuuuuuu kamar zata fadi, ta rike kofa da kyar sannan ta gyada kai

Mamanta ta yi murmushi ta ce" yauwa yar lelena maza wuce ku tafi zan yi kiran ki in kara baki bayanan da suka dace, ki tabbatar da tun yau kin fara abinda ya dace dan fitar da wancen y'ar nacin, yau yau zan je ƙauyuka neman taimako maza jeki kar su tafi su barki su hadaki da wancen marar adalcin mai zabuntar ya'yan "

Da kyar take daga kafarta ta fito ta nufi inda Abubakar ke tsaye yana kallon yannayinta

Gaba ta yi ta fito ta karasa wajen motar ta tsaya ta kasa shiga, har sai da Abubakar din ya bude mata motar yana kallon ta ya ce" ki shiga mana"

Kai ta jijiga ta daga kafar da kyar ta shiga , ya rufe motar ya shiga ya ja su, yana tafe yana kallon ta ta madubi yana sake sake a ransa, yan uwanta kuwa da suka cika da haushin tsayar da su din da ta yi sai suka saki gannin yannayinta, ama sun yi mata dukkan tambayoyin da suka dace ta ki basu amsa sai kawai suka yi shiru sunna kallon hanya

Sun iso lafiya ya saka motar har ciki suka sauka sannan ya fito ya nufi shagon mahaifinsa dan ba shiga zai yi ba shi

A falonta baba suka same su, harda mama fateema bata tafi ba saboda mai kitso da kunshin da ta zo da su ake yanyatsarawa y'ar Tata duda yannayin galabaita da ta sameta a ciki na bakuwar rayuwa da rashin sabo da abu, bai hanna ta sa ta sauko an shiga yi mata kitso da kunshin ba, bayan ta yi mata shayi mai kauri ta bata magani sai kawai aka shiga yi mata shiri irin na amaren a yau.

Ba ƙaramin farin cikin gannin yan uwanta ta yi ba, har sai da suka yi hawaye da suka rungume junna suka kasa sakin junna , wannan ta taɓa kumatunta, wannan ta taɓa hannayenta , idan wannan tace ta rame sai wannan tace ba wani ta dai karra haske ne kamar zabaya, har sai da Mama fateema ta sa suka zauna sannan aka ci gaba da kitson a tsaye , wato mai kitson ta mike tsaye ta ci gaba da kitsawar , su kuwa sunna tayata tufke jelar kitson ko a gama da wuri sai hakuri suke bata na rakin da take yi cewar zafi kitson

Karima a zaune take a tare da su, sai dai gaba daya bata tare da su

Yarinyar kamar bata cikin hayacinta ne, du ihun da suke sai dai ta saki murmushin yake wanda ya sa mama fateema lura da yannayinta har ta yi mata tambayar ko bata da lafiya ne? Nan su lubna suka sanar mata kalau take, daga gannin jikin mamanta dai suke ta yiwu ko jikin maman nata ne, da wannan suka jajanta mata da bata hakuri , Ama ina ita gaba daya kwakwalwarta a hautsine take bata gane komai

Kasancewar kitso ne na kwarariya kuma mai sauri zuwa karfe biyu tuni an gama kannanun kitso yasss tamkar an yi su da allura, mai kunshi kuwa dama ta jima da gama daura mata dan itama akoy sauri kuma ga mama fateema a gefe na tayawa hakan ya sa suka gama aka saka mata matashi ta ringesa kadan suke shan fira da sisters dinta domin Mama fateema ana gama komai suka tafi da masu kitson da kunshin zata mayar da su da salamarsu da AL'WALED ya bari tun kafin ya fita , ta sanarwar khadeeja zata sake duba jikin hajia Inna da na baba Hamza kafin ta wuce

Firarsu suka ci gaba da yi, khadeeja dake ta hankalice da yannayin y'ar uwarta a tausashe ta ce" mimi what hpn? Shirun ki yayi yawa, kuma sun ce maman gidan iyar a zaune kuka sameta, baki da lafiya ne?"

Sai da ummi ta tabbata ta zabura ta kalle su ta ce" na'am?"

Kallon junna suka yi da mamaki, khadeeja ta ce" baki da lafiya ne?"

A hankali ta girgiza kanta, sai kuma ta mike tana fadin" Lubna mu tafi, kaina ke masifar ciwo"

Da mamaki lubna ta ce" da tsakiyar ranar nan? Kanki kuma?"

Khadeeja ta dago tana dubanta ta ce" ke wai lafiyarki kuwa? Bakya gannin yadda jikin ki ke rawa ne?"

Karima ta koma da sauri ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta na rawa sosai

Har rigaye rigayen zuwa inda take suke sai da lubna ta tunawa khadeeja kunshinta sannan ta dakata jikinta na rawa

Lubna Muryarta a raunane ta ce " Menene? Dan Allah fada mana menene?"

Karima sake hade jikinta take yi ta kasa magana sai kukan da take yi , kawai sai suka hade suka shiga yi su dinma, kuka na gaske ba na wasa ba

Du yadda maman baby ta so rarashinsu abin ya gagara sai kawai ta fice ta nufi bangaren hajia Inna dan ba zata iya kallonsu a haka ba

Zuwan ta bangaren hajia Inna ta samu Aba da AL'WALED da baba Hamza a zaune sunna tattaunawa, hajia Inna kuwa idannuwanta a kulle tunda suka shigo bude idannuwan bata yi ba bale tace da su Ku ci kanku

Baya ta ja dan gannin bakin dake dakin, sai dai tuni baba Hamza ya ganta da kula sosai ya ce " Maman baby ce? Shigo mana, "

Jin haka ya sa hajia Inna bude idannuwanta tana dan juyo da kanta barin da maman babyn ta shigo ta duka tana gaisar da iyayen dakinta

Da kula ya ce" Ya aiyuka ya uwar dakin naki? ALLAH ya baku hakurin zama da junna , ina fatan yau dai ta ci abincin ko?"

Maman baby ta yi murmushi ta ce" eh baba yau ta taɓa ai da yake muna da baki Masha Allah a bakinta suka ringa bata ma,"

Sai ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce" Dama hajia, hajia karamar ce da yan uwan nata suke kuka ban san menene ba, na yi na yi dai na gaza basu hakuri shine nace ko a fadawa Maman elhaji karami? " (Wato aunty shareefat)

Hajia ta kalle ta da kula ta ce" Kuka? Ko cewa suka yi zasu tafi?"

Aba ya dubi baba ya fi a irga yana ta so ya ji wai su waye ke kukan ne? Ama abu ya gagara, sai da AL'WALED ya kasa jurewa ya mike yana fadin" Bari in gani, idan kukan kar su tafi ne ai sai kakan kurma yayi hakuri dan gaskiya ba zasu tafin ba"

Yana fada yana ficewa ne, hakan ya sa aba zarro ido a fili ya ce" ji wata jaraba to kukan na uban menene ni ? Oh ya'yan nan idan ba ubansu na ci ba du kansu a tukunya? Ina zuwa"

Sai kawai ya mike ya fice da saurin tsiya, ko baba Hamza bai saurara ba bale hajia Inna da ba'a jin maganar ta da kyau sai an nutsu

A hankali hajia Inna bayan ta turo baki ta ce" ka ga ka je ka hanna d'anka gigita min jikoki, na fada maka idan ya yarda ya dakar min jikoki ni da shi ne, shi da ba'a girma a gidansa, Masha Allah a jikin KHADEEJA ina wajen duka in ba fitina ba?"

Baba Hamza dake neman sulhu ya mike yana fadin" To to bari in ja shi mu je waje ma, Allah ya baki hakuri, ki sha maganin dan Allah, zamu yi maganar na maki alkawari kuma zan yi adalci a maganar"

Hajia Inna ta tabe baki shi kuma yayi murmushi ya fice yana fatan samun saukin rigimar nan a wajen Allah, sannan kamar yadda suke ta dauki na dadi da kakan kurma yanaga ya zama wajibi ya dubi lamarin, ya zama wajibi ya yi hakurin nan, ya zama wajibi ya ba AL'WALED dama ya fuskanci mahaifiyarsa, shi sai dai Allah ya musu hisabi dan baya jin ko a yanzu ya yafe mata raba shi da gudan jinninsa da ta yi a kan ganganci da son zuciya irin nata.


Aba ya juyo ya kalli Sadik ya fi a irga tunda ya janyo shi cikin gidan yace da shi maza ya shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login