Showing 81001 words to 84000 words out of 190762 words

Chapter 28 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4022

abin da yake hange har ya saka shi fadin" Subahanallah, Elhaji ina fatan ba bincike aka yi aka ga tamu y'ar bata cencenta ba?"

Baba Hamza ya yi shiru kansa a kasa, shi dai ba yaro karami bane, a shekarunsa ya gama gane babu abinda zai tsinta idan ya yiwa bawa karya, sai dai mu Hausawa an sanmu da aljunya da jin kunyar mutun sosai, wannan ya sa ya gaza magana sai Elhaji sabitu ne ya fitar da numfashi a tausashe ya ce" malan Abdullahi, zan so ka dauki hakan matsayin hukuncin Ubangiji sannan mu yi kyakkyawar addu'a, ko menene Allah ne bai hukunta ba, kuma ba ana nufin babu maganarta ba, dan kuwa akoy maganarta lokaci ne bai yi ba"

Malan Abdullahi ya gyada kai a nutse ya ce" Hakane, Allah ya sanya alkhairi, Ubangiji ya tabatar da alkhairi, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alkhairi"

Su baba suka ringa amsawa sannan suka mike suka yi masa salama domin wajajen da zasu je da yawa


Bayan fitarsu ya jima a zaune a dakin karbar bakin nasa, domin gidansa dan madaidaici ne mai dauke da dakuna uku, biyu a cen ciki wajen iyalinsa sai daya daga bakin shigowa na baki ne da samarin ya'yansa


Yana zaunen nan ya rasa ta inda zai fara , dan harta mikewar ya gaza yi, yaronsa baba Muhammadu ya shigo dan gaisar da su, ya fara shiga nan dan ya ga takalman mahaifin nasa , domin magidanci ne shima, kuma dan kasuwa ne, yana samu ba laifi kuma yana tsaye a kan lamarin iyayensa sai san Barka

Gannin mahaifin nasa a damuwa bayan sun gaisa ya shiga tambayar ba'asi da son jin ko bashi da lafiya ne?


Malan Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya ya shiga sanar masa abinda ya faru, ya dora da fadi " Na rasa madafa, baban tashin hankalina yadda zan sanarwa Mayga maganar nan, gashi dole in sanar masa, koda sun nuna ba sunna nufin ba zasu nemi aurenta bane Ni ban ga wani anfanin a rike yarinya a hannata kula wani kuma a fito da wata maganar marar kan gado, gaba daya ba'a yi mana adalci ba, dama sun san ba zai aureta ba kuma yake kula ta?, bayan wanna ai namiji ne koda biyun suka so in har da gaske zasu aura masa ita din ai sai su hade da ita ta wajen namu ko?"

Shiru Muhammad yayi yana sauraron Mahaifinsa, haka kuma yana tunanin ta hanyar da zai bi dan ya sanyayar da zuciyar mahaifinsa ba tare da ya bata masa rai a kan maganar d'an uwansa da yake ji a ransa ba, bayan shi d'an uwan nasa ZUMUNCIN ba haka yake daga bangarensa ba

Ba zasu ce Baba Mayga baya zumunci da mahaifinsu ba, sai dai zumuncin a bayane yake ba mai kudi da talakan mai kudi ne ake yi

Baba Abdullahi ya girmi baba Mayga, ama a rayuwa ba zaka ga takanas baba Mayga yayi kiransa dan ya ji yaya yake ko iyalinsa ba, sai idan yana son aikensa yi masa wata hidimar,sun riga sun kulaci zumuncinsu saboda suna kallo mahaifinsu ya zamo kamar baran gidan kanninsa ne, Ita da kanta yarinyar da yake magana kanta tunda suke sau daya ta taɓa takawa gidan nan shima a lokacin da ta zo da mahaifinta , a ranar da suka zo ko zama bata yarda ta yi ba, tana tsaye kikam kuma ko ruwan gidan bata sha ba, du irin hidimar da mahaifiyarsu ta wuni yi saboda tarbar baki, da girki mai rai da lafiya da gyaran daki a tunaninta a nan zasu sauka ama yarinyar ta nuna ita zama ma ba zata iya yi a gidan ba bale ta ci abincinsu harma ta kwana a dakinsu, karshe girkin sai su suka cinye sunna shagalinsu......ama a lokacin ma sai Baba Abdullahi ya daure fuska babu wanda ya isa ya fadi laifin d'an uwansa ko na ya'yan dan uwan nasa
Haka ake tafe, da wayon su da hankalinsu babu wata sabga dake tashi ka ga iyalin baba Mayga, kulun cikin nuna uzurin sun yi tafiya ko makamancin haka, shi din da kansa in an ci Sa'a yana gari ne yake zuwa in baya nan baya zuwa sai dai ya tura sako, sakon da basa jiran ficikarsa dan hidimar gidansu, kwarai talakawa ne su, ama alhamdulilah sunna da rufin asiri daidai gwargwado da wadatar zuci

A tausashe ya ce" Baba, dan Allah ka yi hakuri da abinda zan fada, zan fadi ne dan kar ka saka damuwar haka a ranka ka kuma samu wani ciwon da zai daga mana hankali "

Muhammad ya dora da fadin" Baba, a zamanin nan, babu wanda yana gannin kashi da rana , zai zo ya saka kafarsa da dare sai wawa, domin an zo zamanin da samarin ke zuga yan matan su kaisu su baro su zagaye su aure wasu masu mutuncin "

Baba Abdullahi ya dube shi a kausashe ya ce" Ka yi gagawar janye maganar ka in har abinda nake tunani kake nufi, kana nufin y'ar tawa ce bata da mutunci?"

Muhammad ya sada kansa a hankali ya girgiza kai ya ce" Ka yi hakuri baba, ba haka nake nufi ba, Baba ka ga wanene ELHAJI AL'WALID,, mutumen da Allah ya sa suke tare baban mutun ne mai daraja da ya dace ace da tana da wayo ta kame ta kilace kanta ya zamo ganninta sai mai sa'ar gannin, ba ta zamo tamkar piyawata ba, kowani gaula na iya saka datar hansin ya ganta tana tikar rawa a yanar gizo, kwaliyar da zata kashe makudan kudi da isa da takama itace zaka gani a yan cenjinka har ka shiga cmmnt section ka zageta ka zagi danginta hankali kwonce...., Baba yaran nan sun zubar da kima da daraja tasu ta ya'ya mata ta hanyar ta'amali da zamani suka shige suka kanainaye har suka fi mai kora shafawa, ya zamo harta bayin dakinsu babu wanda bai san kalarsa ba, sutura kuwa sai dai wace ba'a dinka ba, ama duka kaf wace aka dinka duniya ta sani, almajiran gidan nan sunna da vidios dinta a wayoyinsu inda take dirka rawa ...."

Ya dan dakata dan babansu bai cika daukan abinda ya shafi dan uwansa da wasa ba

A tausashe ya dora da fadi " Ta fito duniya ta nuna ita bata da wata kima da daraja da kamun kai, kuma ta fito ta yi wasa ta sanar da duniya mutun mai girma da daraja irinsa shine ke neman aurenta, kar a dauki bangaren mugwayen halayar da Allah baya so kuma take yi, a barta iya wannan ma ya isa ya sakata a damuwar da zata yi kuka, shin baba iyayensa basu da tunani ne da zasu tashi su yarda da aurenta haka kawai? ko dan shine mai abin hannu a gidansu zai zamo sunna ji sunna gani a kawo musu wannan badakalar a gidan su?, ai matar farko mai karko ake ajiyewa baba, idan yaso in har ya zama wajibi sai ka karra sai ka ajiye du wace hali ya kama, idan ta yi kyau halas in ta ɓaci kuwa baka da damuwa sai ta je inda ta fi wayo ko baba?"

Babansa na sauraronsa, gaba daya abinda yake fada ya san gaskiyar yake fada, sai dai zuciyarsa ta ki yarda ta yarda cewar su Aba a kan gaskiyar su suke

A sanyaye ya ce" Muhammad, na ji du abinda ka fada, ama ai ba shi zai basu damar rike yarinyar nan su hannata baiwa wani damar neman aurenta ba kuma su zo da wannan maganar ko?, fisabililahi da sun bata dama na tabbata da ta samu malamuncinta ko?"

Muhammad ya ce" Baba, ka tabbata su suka riketa?, baba malamuncinta fa? da ba dan ina jin kunyar nuna maka Wacece ita ba da yau na shiga Tiktok din nan na fitar maka da su waye ya'yan nan, ai in dai kace kai wannan abin zaka bi ko? walahi kana cikin tashin hankali a rayuwa, Baba sai dai ta samu abokin lalacewar ba dai mijin aure mai nagarta ba"

"Muhammad!" Mahaifinsa ya fada a kausashe

Ya sada kai a hankali ya ce" Ka yi hakuri"

Malan Abdullahi ya dauke kai yana fadin" Samo min numbar Elhajin ka bani shi mu yi magana ina son zuwa gidan Elhaji Ya'u , dazu yace a harhada malamai a je a fara sauka tun yau, y'arsa ta yi miji"

NUMBAR ya lalubo ya danna masa kira ba tare da ya yi musu ba, sai dai a ransa yana ayana' Allah ya sa ya daga, abinda sai in masa kira ashirin bai daga ba, a tunaninsa maula zan yi? Allah ya kiyaye, Allah ya rabani da mataciyar zuciyar da zata sa in ringa maula a wajen kowa, gwara in yi dako'


Ai kuwa da kyar Elhaji Mayga ya daga, shi kuwa bai yi masa magana ba kawai ya ba yayan nasa wayar ya fice a dakin ya basu space


Murya ba dadi suka gaisa, malan Abdullahi ya sanar masa cewa yanzu su Elhaji Hamza suka fita daga gidansa

Elhaji Mayga ya yi murmushi yana fadin" Su din da kansu? ko dai abin ya tashi ne na daughter? , dan na san kayan abincin nan da ake kawowa ai turowa ne ake yi a kawo maka ko?"

Baba Abdullahi ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Eh, ba kayan abincin bane, sun zo min ne da wani tashin hankali, kan maganar tsakanin shi Elhaji AL'WALID din da Mufeeda ne, sun ce wai za'a daura masa aure jibi ama da wata yarinya, shine suka zo su fada min wai ba sunna nufin an fasa fa ita bane, za'a yi da ita din daga baya"

Da farko Elhaji Mayga ya daga kiran ne a cikin mutane, kuma yana amsa masa ne irin a gagaucen nan yana son komawa cikin mutanen, sai dai abinda ya fada ya saka shi dauke wuta na dakikai kafin ya ce" Yaya, dan dakata , Ni fa du ban gane ba, wai kana nufin shi Elhaji Hamza din ne ya zo da wannan maganar?"

Malan Abdullahi ya tabbatar masa da haka din ne

Zufar da ta fara tsatsafo masa ya ringa sharewa, sai kuwa yace da shi yana zuwa, ya kashe kiran ba tare da ya tsaya ya ji daga gareshi ba

Shiru malan Abdullahi yayi na dan lokaci sai kuma ya mike ya shiga ciki saboda su je gidan Elhaji Ya'un, wayar dai ya rike a hannunsa saboda ta yiwu dan uwan nasa ya yi kiransa ko da wani aike ne da ya danganci Mufeedan, yana tausayawa yarinyar nan sosai saboda halayar da d'ansa ya fada gaskiyar kennan, yau ko yaya iyayen zasu iya da ita? ko yaya zasu yi da ita idan ta ji wannan magana? gashi abu kwana kusa jama'a yaya za'a yi da rigimarta? ( Wato shi Baima san tana garin kwana da kwanaki ba)
...........................................................



A irin wannan lokacin yammaci bayan AL'WALID ya yi sallar la'asar a masallaci suka koma boutik da abokinsa suka sake zaunawa kan abinda ya shafe su sunna tataunawa a kan harkar kasuwanci ne kawai, Bayan sun gama AL'WALID din ya mike yana mika dan tarin gajiyar da yake ji, bai yi barci yadda ya saba ba, baya tunanin zai iya yin barci nema yadda ya kamata shi yasa ya fito yake wannan aikin da yaransa ne ke yi masa, yau yake yi da kansa , wato yana bin manya manyan butik dinsa da ake masa tsaron harkar shige da fice yana dubawa da yannayin kasuwancin hajojinsa dan kawai tunanin da yake yi ya kauce masa, ama abin mamaki ko dan bako yake a lamarin gaba daya sai abin ke neman yi masa karan tsaye cakkkk a cikin zuciya

Ya yi rayuwa ta shekara uku da matarsa, rayuwa ta soyaya, rayuwa ta kula da junna, soyayar da bai taba tunanin gannin katsewarta kwana kusa ba,
Bayan shekara biyu da aurensu a lokacin tuni ita ta shige damuwar rashin gannin fashin sallah a tare da ita, shi kuwa har ga Allah a lokacin wannan bai wani dame shi ba dan ya san Yaushema aka yi auren, kuma budurwa ya dauki matarsa cikakiya , dole komai sai a hankali zai samu, shi yasa ya ringa nuna mata wannan fa ba matsalarsa bane, yana fatan in lokacin a samu yayi Allah ya basu mai albarka, haka kuma idan har lokacin bai yi ba ba zai daga hankalinsa ba

watani kadan bayan yan rigingimunta suka samu karuwar da ake so, a lokacinma yana cikin karin yawaitar dukiyarsa........., domin ko a lokacin basu cika zama ba, sunne wannan kasar, sunne wancen
Maman kurma bata yi wata jinyar laulayi ba, hakan ya sa suka ci gaba da more lamarinsu cike da kuma da kaunar junna, du irin yadda yake business man bai hanna shi bata full time din da ya dace ba, idanma tafiyar da ta dara sati ce itama ta sani ƙafarsa kafarta

A haka haihuwa ta same su, a haka babar jarabawa ta same shi, domin nakuda maman kurma ta yi har ta tsayin sati biyu da kwana uku, kuma da zarar ya nuna abin ya ishe shi a yi mata tiyata saboda likitar ta nuna idan sunna so ana iya yi mata tiyata domin wani lokacin ba'a son doguwar nakudar nan, sai kawai ta kiya, hakama mahaifiyarta da take gidanta sai ta nuna bafa za'a fasa yarinya ba, a barta tana haihu da kanta.

Ba zai ɗorawa wannan dalili matsayin sanadiyar matarsa ba, sai dai har yanzu bai ji a ransa cen cikin zuciyarsa zai iya sake sakewa da mahaifiyar matarsa ba, domin ko kai kurma ba shi ya lamunta ba, Elhaji ne ya dora dokar duk sati biyu sai an kai kurma ta yi kwana biyu wajen kakarta sannan a dawo da ita, ba dan ya kulaci kowa ba, a'a, sai dan nacin da mahaifiyar matarsa ta nuna mai tsananin gaske a lokacin da likita ya nuna akoy matsala tana bleading a gaggauta ciro abinda ke cikinta ko a rasa su gaba daya, a zuwan in aka gaggauta din ana iya samun daya a ciki, domin jinni take zubarwa mai yawa, kuma tsabar fitina da duhun kai irin na mahaifiyar matarsa tun da dare ta fara zubar da jinin uwar tace wai ai hakan na nufin abin ya zo, sai da yayi safiya ya je wajenta kamar yadda yake yi, dare kawai ke raba su matarsa tana kuka a boye ta sanar masa karfinta ya kare kuma jinni take zubarwa, wannan dalilin yasa ya ki sauraron kowa ya dauketa suka yi asibiti, ashe tuni lamari yayi nisan da sai dai a samu daya, kuma uwa ta ringa kuka ta ki a fasa wai fashin da idan an yi ake mutuwa? shi dai kadarar rayuwarsa da ta matarsa ce ta kasance a haka domin ana dauki ba dadin nan nakuda ta kankama , Samiha ta samu ta haifo baby ita kuwa jinni ya bale da muguwar balewar da ba'a so duka duka a cikin mintuna ashirin har an yi an gama ta bar duniyar.....


Idannuwansa ya rintse a parken da motarsa take a cikin gidan su MUFEEDA, tunda ya zo ya dakatar da motar a nan ya afka duniyar tunanin abinda ya sa har yanzu ya gaza motsin kirki dan daukan matar aure........, da kuma jinkirin Baba Hamza, domin idan ba zai manta ba nan da shekara da rabi ya taba nuna masa ya dace a je a nemi auren Mufeeda a yi a gama, sai yace da shi yayi hakuri ya bashi lokaci


Tunda ya zo mai gadi Ya shige ciki ya sanar da kannenta cewa Elhaji AL'WALID ne ya zo, hakan ya basu mamaki, daya ta shiga kunna abin kanshi da sauri, dayar kuwa ta yi dakin Mufeeda dan ta sanar mata, domin tun jiya da ta dawo daga gidansa a falo da kyar suka iya rarashinta, kuka take yi hade da fada mai tsananin gaske tana cin alwashin sai ta ga bayan duk wani wanda ke son gannin bayan Tarayyar ta da AL'WALID, karshe dai da mahaifiyarta ta wanke ta tasss a waya sannan ta daina kukan har ta shige dakinta ta mako kofar, ko abinci da aka yi na kari da na rana dakinta ake kai mata nata ana fitar da kayan idan ta gama , dama in ranta ya ɓaci hakan ne, da kyar take saukowa ta fito daga daki


Firgigit ta yi a lokacin da kanwar Tata ta sanar da ita

Dirowa ta yi daga saman gadon, gashin kanta ko ribom babu, jikinta kuwa sanye da rigar barci ne ko gwuiwarta bata kai ba kuma ko pant da breziya bata da shi a kasa, ta janyo wayarta ko bayi bata shiga ta wanke ido bale bakinta ba, ta fito tana dariyar kannenta dake faman zolayarta ta dan dakata ta ce" Yana ina? yana mota ko yana cikin falon cen????, oh my god na san yana so na, na san zai rarasheni".....................



Bata tsaya ta ji amsar su ba ta yi waje, bcz zuciyarta ta riga ta wanke da duk damuwar da take ciki......, a gaskiya idanma da maganar qualities din gayen nan da suka sa ta makale masa ta kasa barinsa akoy maganar soyayar......tana sonsa, tana sonsa sosai da sosai....

kannenta biyu, dariya kawai suke yiwa yannayinta, cikinsu aka rasa wace zata yi mata tunin suturce jikinta idanma ba zata tsaya ta yi wanka ta bi dukkan abinda ya dace ba, a haka din ta yi waje ta nufi inda motarsa take tana murmushi..........
07/12/2024, 15:04 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login