Showing 168001 words to 171000 words out of 190762 words

Chapter 57 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4002

ai zata yi kiran gidan ne ta yiwa Karima rashin mutuncin kukan da ta saka su...., sai dai a cen cikin zuciyarta ta san akoy abinda yake faruwa, akoy abinda Lubna ta Hanna Karima fada, wannan maman wannan maman sai ta kashe y'arta da masifa kala kala, yanzu in ba neman ta kashe y'ar ba a kan me zata bata waya? Du irin abinda ya faru ta manta kenan? Han.




Cikin gaggawa suka karasa gidan , sunna tafe Karima na fada musu irin abubuwan da mahaifiyarta ta fada mata, wanda gaba daya ya tsorata su, harma Sadik ya yi aiki da wayar Tata yayi kiran mamansu dan ya ji ko tana asibiti? Da ta shaida masa sai gobe zata hau da sasafe sai kawai ya karasa da karkashin sa, jikinsa na rawa, harma da irin abubuwan da amarya ta fada baya jin yau zai kyale ta!,

Tsakanin shigowar su gidan da shigowar aba tazarar bata fi ta minti goma ba, shima dan AL'WALED ya dan dakatar da shi ne da ta yiwu su yi kawowa daya saboda uban gudun da ya yi da motar

Yana zuwa ko kashe motar bai iya tsayawa yayi ba ya fice ya shige gidan da sauri ya nufi bangaren Mama dan ya tabbata du inda suke sunna dakinta

Da mugun sauri amarya ta duke ta shiga tsince tsincen karya a kofar dakin Mama saboda a labe take dan ga ji dalilin da ya sa suka shigo hannayen junna a rike Karima na kuka kamar ance ta yabuwa ce ta rasu

Tsayawa yayi yana kallon ta da wani mugun takaicin ta, sai kuma ya bude ya shige dakin na mama ya bar kofar a bude hammmmm ya karasa inda gaba daya suka yi bayan Maman suka rukunkumeta kowane gabansa na faduwa sunna faman fadin "Aba dan Allah ka yi hakuri"

Kai ya dauke daga irin yadda ya ga Mama na kallonsa da shirin ko ta kwana, ta yiwu gimbiya ta kai dukka a kan ƴaƴanta, dan haka sai ya zauna din yana ta tuna maganar Baba Hamza da AL'WALED, da baban cewa yayi sai ya biyo shi ma, shine ya kiya saboda ba fa lafiya gareshi ba.

Zama yayi a kan kujera yana duban Mama a hankali ya ce" wai me yake faruwa?, kin ga shi yasa ban so fitar yaran nan ba, gaba daya so ake yi a lalata min tarbiyyar yarana, me yake faruwa ne dan Allah?"

Mama ta sake duban yannayinsa, kwarai maganarsa a hankali ta bata mamaki, dan haka ta nutsu a hankali ta ce" Dan Allah ka yafe mana ka yi mana uzuri, sannan ka yi hakuri ka saurari yarinyar nan, ina rokonka idan ka ji ko menene ka yi abinda ya dace cikin nutsuwa babansu"

Aba ya gyada kai yana kallon Karima da aka nuna a ransa ya ayyana ' na shiga uku, yauma itace? To wannan ko dai ita zata kasheni?'

Karima murya na rawa ta ce" Aba, dama dazu ne da safe aunty amarya ta tareni a falo tana cewa........"

"Karima banda wannan, ki fadi iya na ke da mamanki dan Allah" Mama ta fada a tausashe tana dubanta

Aba ya dubi Mama, sannan ya dubi Karima ya ce" Ki fada min komai, in dai adalci ake so in yi cikin nutsuwa a fada min komai, idan ba haka ba wallahi nima ba zan daga muku kafa ba"

Karima da sauri ta ci gaba da fadin duka kaf abinda amarya ta fada mata, sannan ta kawo kan na mahaifiyarta jikinta na rawa tana kuka shima ta fada ta idashe da fadin" Aba, sai su ringa cewa zata cutar da mu, zata wulakantamu, Aba idan har tana cutar da mu ai da ta jima da rabamu da duniya, su masu fadin sunne suka ci kashin mu da fitsarinmu?, Aba masu fadin nan mu da su in an hadu ne kawai a kitsa mana abubuwa.... , mama itace komai namu, lafiya da rashin lafiya, dadi da rashin dadi, Aba Ni ba mahaukaciya bace ina hankalce da abubuwan nan tunda na bijire maka, ita maman namu ta manta itace ta sa na ƙi auren ama yanzu take nuna wai laifin mama ne da kai? Aba ina take so in saka raina, yaya zan yi? A kulun idan ta sakani abu in na dan so kwatanta mata haza furucin bakinta ke dakatar da Ni domin idan ta budi bakinta furucin da take yi yana daf da wace ke iya tsine min a kan kudurinta....wayo allahna......"

Karima ta karashe tana ɗora kanta a saman kafar mama ta fashe da wani kukan mai zafin gaske

Aba ya jima yana kallon Karima, kafin ya daga dubansa ya sauke kan fuskar Mama dake hawaye saboda kukan ya'yan nata, ya mayar da dubansa kan yaran nasa baki daya

Tunda yake bai taba jin mutuwar jiki da tashin hankali mai raunata zuciya irin na yau ba, da kyar ya iya daidaita kansa a hankali ya ce" Ba komai, ki daina kukan hakanan kin ji karimar Aba???"

Kai......, ai hatta Mama sai da tsigar jikinta ta tashi, ita fa ta shirya ne ta san zai hade su ne yau ya ci uban kowa a dakin nan, sai kuma suka ji haka?

A tausashen nan Aba bayan ya girgiza kai ya ce" Karima, tashi ki dubeni nan mu yi magana"

Karima ta tashi kanta a kasa ta rakube jikin Mama tana sauraron aba

Aba ya ce" Kin san dalilin da yasa na ki aura maki wannan yaron? Saboda binciken da na yi a kan jajayen idannuwansa ba na komai bane sai na shaye shaye da yayi......, eh ya yi zamu ce saboda a yanzu baya yi........, ko a abinda Elhaji AL'WALED ya sanar min ance rabonsa da harkar tunda rigimar nan ta kutso masa........, Ni damuwata a lamarin nan kar aje daina shan da yayi dan ya shiga halin a yarda da shi cewar baya sha ne...., kar aje in dauki y'ata da na dauki shekaru ina bata kula in mikata hannun mashayi, ......kin san meye ilar auren mashayi , ba zan so ace kin fada hannun mashayi ba Karima...., sai dai kuma dole zan yi masa uzuri in bi shi da kyakkyawar addu'a da kyakkyawan zato duba da irin yadda yake zarya a kofar gidan nan, kuma tunda na saka masa dokar kar na ji kar na ga ya sake yin magana da ke bai sake din ba, bayan yana son yin hakan....sai nake kyautata zaton ta yiwu idan na bashi din ya kula min , ya tausaya min , ya rike min...., saboda a duniya bani da sama da ku daraja a zuciyata , Bani da sama da yayana da mahaifiyarku gatanan a cikin zuciyata, Allah shine shaidata kuma....."

Ya ajiye maganar a hankali kamar yana tsoron kar wani ya ji, inda gaba daya suka wara idannuwansu a kansa

A hankali ya ce" Idan har kina son shi, ki san da zaki iya zuwa ki tarar da halayyarsa kala kala da ba zasu iya birgeki ba, wa'inda zasu iya baki wahala sosai, kin san halin yan hayaki akoy wuyar sha'ani, Ama idan kin jure kin kawar da kai, kin yi addu'a zaki zauna da abinki lafiya harma ki ga cenji wata rana...., in dai zaki yi koyi da mamanku Karima babu namijin da ba zaki iya zama da shi ba ina mai tabbatar maki, saboda ita ta zauna da Ni da zuciya daya du halayana ta zauna da Ni Karima....."
Ya sake ajiye maganar yana kallon Mama wace ta ringa jin wani katon miki na cikin zuciyarta na wankewa a hankali a hankali......, duhun dake tsakanin fuskarsa da idannuwanta ya ringa yayewa....., a hankali ta ɗan langwabar da kanta tana dubansa

Aba ya fuskance ta da kyau ya ce" kina son mudansir ? Zaki iya zama da shi?"

Karima ta sada kanta, kirjinta na bugawa...., gaba daya maganganun mamanta da na amarya suka idasa gogewa a ranta ta ringa ayyana ' ashe mu dukka yana son mu? Ashe dama Aba yana son mu?'

A hankali ta ce" Aba, in dai ka yarda da shi zan zauna da shi, idan baka yarda da shi ba wallahi ko wa ka zaba min zan amsa"

Aba ya gyada kai a tausashe ya ce" Masha Allah, to maza ku tashi ku je ku yi tilawa kafin nagariba ta yi, in sha Allah a yau sai na daura maku aure, Allah ya muku albarka"

Su dukka sai da suka kalle shi da sauri, sai dai ba damar tsayawa daga umarninsa, sai habubakar dake kallon mama cike da tsoron to wai basu gane ba daurin auren harda su ko me? To su kuma ina su ina aure yanzu???? Da yan matan yake ko? Fisabililahi su ai basu kawo zancen mai jan ido a ransu Bama

Gaba daya suka fice a dakin , mama dake kallonsa a hankali ta ce" Yau me yake damun dodona? Sanyin nan ya min yawa Aban Sadik"

Aba ya yi dariya yana kallon ta , a nutse ya ce" Yaya ba zan yi sanyi ba? Gaba daya kin gama da duk wani rigimana....., sai dai daya ba zaki iya Hanna Ni ba, Usaina na saki amarya saki daya, ta je gida ta koyi hankali, idan har ta nutsu ba laifi ma dawo da ita idan bata nutsu ba na gama zaman aure da ita"

A tsorace mama ta mike ta karaso inda yake , a lokacin kuma tana hangen amarya ta gaza zaune ta gaza tsaye sai yawo take yi tsakanin dakinta , kofar dakin Mama da falo, kuma maganar nan radau a kunnayenta dan haka a tsorace ta juyo tana nufo dakin ba tare da ta ankara da hakan ba

Rai bace aba ya ce" ki dakata a inda kike, idan kika yarda ko ke ko maman yaran nan wani yace zai dameni a kan hukuncin nan wallahi wallahi zan cikashe maki uku ....., idan kin je gidan naku ki sanar musu zan shigo ne da kaina, saboda mahaifinki mutumen kirki ne kwarai zan bi sahu in sanar masa duk abinda kunnayena da idannuwana suka ji, idan kina so ki fita ki ce matata ta da na sake ki, Allah ne zai saka mata, ke sheda ce da ba dan ita ba da na jima da yarda kwallon mangoro kuda ya daina bina, tunda har ba zaki gane ba sai ki ci gaba, ama Ni Elhaji ya'u ba mahaukaci bane, sarai na san matar rufin asiri da wace idan da mamora ne zata rabi jikina!"

Daga haka ya mike , sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon Mama ya ce" zan nemi mahaifin mudansir yanzu, su zo da dukkan shedunsu idan sun shiryawa hakan, sannan zan yi kiran mahaifin Usman da Hafiz, ki yiwa yayanki fatan alkhairi in sha Allah ita Karima a yau zan daura nata, su kuwa biyun zan basu damar zuwa gobe in sha Allah saboda ina son saka mai gidan nafisa da mai gidan anmy a lamarin gidan nan zasu ja gaba tare da baba Hamza "

Daga haka Aba ya wucewarsa ya bar amarya nan duke tana rusa kuka mai haɗe da ihu tana bashi hakuri , ama ya yi wucewarsa dan ba fa zai saurareta ba, ta gama fice masa a rai ba zai dubeta ba yau.

Mama gaba daya jikinta ya idasa mutuwa, ya Salam.....sai ta tsinci kanta a yannayi biyu, farin cikin gannin irin yadda Karima yau ta nuna ita y'ar halak ce har ta tabbatar mata cewar wahalar shan dukan da ta yi a kansu bata yi a banza ba tunda sun dauketa uwa har cikin zukatansu, da farin cikin irin yadda Aba yau ya fuskanci matsala ya samu mafita cikin ruwan sanyi, da farin cikin jin daurin auren ƴaƴanta , sai kuma firgicin sakin matarsa da yayi, wanda rantsuwarsa ta saka doke ta tsaya da neman saka shi mayar da matarsa

Murya a tausashe ta dubi amarya ta ce" ki yi hakuri dan Allah, in sha Allah zai dawo da ke dakin ki "

Amarya ta dago daga duken da take tana duban mama da tarin kiyaya ta ce" ki rike kayan munafurcinki, in kin bar malaman ki sun barni a dakin nawa ko? Da Ni kike maganar Usaina!"

Mama ta girgiza kai bayan ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta ce" Na shaida babu abinda ya isa ya sameni face wanda Allah ya kadarto min a rayuwa, babu abinda kika isa ki yi min wanda Allah bai rubuto min shi a zanen kadarata ba, na zauna da ke da zuciya daya har zuwa yanzu, idan zamanmu bai kare ba ina rokon Allah ya karra bani ikon zama da ke da zuciya dayar nan....ki je ki yi du abinda zaki yi......tawakaltu Allahlah"

Amarya ta sake cije lebe tana wawurar abinda take iya dauka saboda a yau zata je gidansu dan ta dauki matakin da ya dace da irin wulakancin da mama ta janyo mata, koda jikinta duka kunne ne ba zata taba yarda cewar ba mama ce ta sa aka sake ta ba, to ta yayama zata yarda da abinda yace bayan an shanye shi? Yau ai mahaifiyarta zata karra gannin tugun kishiya a fili a bayyane idan ma bata yarda ba yau zata yarda.........( Ai kaza bata jin as as......, abinda kake yi kuma ba zaka taba yarda cewa wani ba shine makaminsa ba a rayuwa......du Wanda ya auri wannan rayuwa kuwa tabasssss zai ga karshensa....... Allah ya rufa mana asiri.........).


Kusan karfe takwassss na dare bayan su baba sun fito daga masallaci sai suka sauka a dakin HAJIA Inna bisa umarnin shi baban

Tunda suka shigo baba ke kallon hajia Binta da hajia innar da mamakin su, a ganninsa an masa laifi kuma a fi shi fushi? Kaka b tsabar fitina ta hade kai da kaka Inna sunna masa fushi bayan shi aka yiwa laifi ......., hum ba komai, ko a yanzu da ya tambayi yau din ta sha maganin ne? Kaka b ta ce bata sha ba harda gyatsina baki da dauke fuska....., kuma dai ga dukkan alamu gaskiyar kennan, saboda gayanan jikin kamar ba sauki

A hankali bayan ya dubi AL'WALED dake kallon tsofaffin nan da mamakin wai da gaske kakansa ne za'a gigita? Ya ce" Ai da ta karbi maganin ta sha komai ma zai wuce ne, Ama shikenan tunda dai Ni ake wulakantawa a kan gaskiyata ba laifi, da hajia karamar ta zo duba lafiyarta ai dai ta yarda ko?"

Kaka Binta da ta zamo itace mai bada amsar ta wani sake dauke kai ta ce" Bata yarda ba, gaskiyar kenan bata yarda ba, da suka zo ita da kurma basu jima Bama nace su yi tafiyarsu bangarensu ta tafi da y'arta sunna cen, jiki kam sai gyaran Allah kawai"

AL'WALED ya dubi baba, baba ya Dube shi, a ransa ya ayyana ' to fa, ga dukkan alamu harda Ni za'a gigitan, to ai ita maman ta kurma ba idasa sabawa ta yi da ainihin gidan nata ba, baiwar Allah abu sai wahalar da ita yake yi.....ya dace ace du dare tana karbar lelcara a haka za'a tsallake a wuce wajen , Ama idan ana hadota da y'arta tun yanzu ya zama wajibi ta yi tafiya zuwa nesa tare da malamin nata wato Ni, ta haka ne zata iya tsallake wannan lokaci mai tsaikon tsiya har ta zama y'ar garin'

Baba Hamza ya girgiza kai ya ce " Shikenan na gode, ba dai a kan maganar yaron nan da Mahaifiyarsa ne kuke wulakantani ba ko? Har ya zamo abincina masu aiki ne kawai ke yi? Dadin abin Ni ba tsohon da bashi da gata bane, abinda na so zan ci daga hannun d'ana a kuma lokacin da na so, sai ku zama sheda na janye maganar da na yi a kan tsakaninsa da mamansa......, yana iya yin du zumuncin da yake so da ita, ama Ni bana son ganninta, a kiyaye min ganninta, idan gidan nan zata zo a fada min sai in je gidan d'ana in kwana in ta gama na dawo....."

Daga haka baba ya mike ya juya zai yi tafiyarsa

Da sauri hajia Inna ta bude idannuwanta tana duban AL'WALED ta ce" Dan Allah riko mana shi mana dan gidan shareefat"

AL'WALED da abin ke bashi dariya da tausayi dama bai yi niyyar barin tsohon nasa tafiya ba, a tausashe ya ce" Baba, dan Allah ka tsaya"

Baba ya tsaya din Ama ya ki zama ya ce" Me kuma za'a ce in yi ban yi ba? Ina ce shine kawai damuwar?"

Hajia Inna a raunane ta ce" Kai Bama la tsoron in mutu kan safen shine zaka ringa fushi da Ni? Haba dan Allah Elhaji, dan Allah ka yi hakuri, dan Allah ka sassauta zuciyarka a kan lamarin nan, duniyar kanta nawa take?"

Baba Hamza ya nuno yatsarsa ya ce" Kar ki min rashin kunya kuma, Ni ne nan zan fada maki nawa duniyar take tunda Ni yayanki ne, shekara nawa na baki? Kar a nemi a min rashin kunya kuma"

Kaka b ta kame haba tana kallonsa

AL'WALED ya mike a nutse ya kamo hannunsa ya kawo shi daf da gadon ya zaunar da shi sannan ya duka a kusa da shi sosai ya kama hannayensa a tausashe ya ce" Ka yi hakuri baba, Ama furucinka ko Ni ba zan iya yarda cewar ka huce ba, Baba ..... Mama ai y'arka ce, kai sheda ne har ya bar duniyar matarsa a gefensa kuma yana sake jaddada maka ya yafe mata......, idan har lokacin yafiyar ne yayi dan Allah ka yi ta kirki baba, kar ka manta Allah na son mai yafiya, da Allah ya amshe babana ai ya baka mu......., wani kaf Allah ke amsa ya barshi shi kadai ya rayu tsayin lokaci , shi sai yace me baba?......, Please idan har zuciyarka bata saki a kan lamarin nan ba its ok....., a bar maganar....but tsakaninka da su hajia ka yi hakuri ka bar fadan haka na roke ka"

Ya hade hannayensa biyu ya Dube shi da jajayen idannuwansa sannan ya mike a nutse ya ce" Ku yi hakuri zan je in kwonta"

Su duka da ido suke kallonsa, gaba dayansu zukatansu bugawa yake yi, saboda irin yadda fuskarsa ta nuna abinda ke zuciyarsa a kan lamarin nan...., sai dai kamar yadda ya jima da ɗaukan girma ya dauki hakuri ya dauki kawar da kai tun yana da kannanun shekarunsa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login