Showing 147001 words to 150000 words out of 190762 words

Chapter 50 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3984

dake rike da hannun Khadeeja wace ke langwabe a jikinta , kasa kasa ta ce" Ka tabatar da ka ci wani abin......, Shareefat me yake damun yarinyana? kawota nan kusa da Ni....."

Ta fada a kan kunnayensa dan ya gane cewar an kawotan kuma ya san cewa za'a bata kula in dai tana tare da su din

A hankali ya kashe kiran ya zauna saman kujera yana sake lumshe idannuwansa.........
Bai san dalili ba, haka kawai ya damu da son Sannin Allah ya sa ba fushi ne ya sa ta ki cin abincin ba .



Khadeeja ta zauna da kyau a kusa da Hajia inna tana tunanin kamar an kawota dakin nan, sannan ta sake gaisar da Hajia inna wace ta sa aunty shareefat ta kawo mata kunu mai dumi

Hajia inna na hankalce da irin yadda take yin iya yinta dan ta zauna da kyau ama kuma ta gaza, sai ta dan dauke dubanta tana yin murmushi a lokacin ne kuma aunty shareefat ta dawo da kunnun tana zama ta ce" Daughter, asibitin nan da dole ne mu je, jikinta da zafi inna kuma wai ba za'a tafi asibiti ba"

Hajia inna ta yi murmushi ta sake duban Khadeeja da ta amshi kunnun ba tare da ta yi musu gardama ba, a tausashe ta ce" Kin sha pain killer ne? koda paracetamol?"

Khadeeja ta kalli Hajia inna da sauri, sai kuma ta kalli aunty shareefat wace da farko bata wani dauki maganar a kan komai ba har sai da Khadeeja ta yi duban nan ne ta dan dubeta da kyau tana dan buda ido

kai ta sada tana fadin" Ciwon kai ne inna zai wuce"

Inna ta gyada kanta a tausashe ta ce" ALLAH ya baki lafiya, Duda haka mamansu sama mata abinda zai dauke mata zugi, ciwon kan nan sai da magani Allah ya baki lafiya"

Aunty shareefat ta mike ta fita tana murmushi, Khadeeja kuwa gaba daya sai ta tsargu, ta ringa jin kamar ta ringa rantsuwar cewar ciwon kai ne kawai ke damunta, sai dai Hajia inna ta yi shiru tana dan jan carbinta

Ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da shan kunnun fukawar domin yayi mata dadi a bakinta, dama ita mutun ce mai son abubuwa na ruwa ruwa

A tausashe Hajia inna ta ce" Wani abu ya faru ne yarinyata?"

Khadeeja ta sake duban Hajia inna, ta mike tana ajiye kofin Kunun nan ta zo ta dauki abinda ake gogewa Hajia inna bakinta ta duka ta goge mata da kyau ba tare da kyankyamin komai ba sannan ta koma ta zauna tana sada kai ta ce" Ba komai inna"

Hajia Inna ta yi murmushi zuciyarta na amsar Khadeeja sosai da sosai, a tausashe ta ce" To kwonta mana kya fi jin dadin jikinki"

Khadeeja kam ta gama sarewa, ta dubi inna tana marairaicewa ta ce" Inna babu komai fa, dana waya ce aka bugo na daga na ji Muryar wata na fadin bata da lafiya ta yafe masa , tana cewa GUDALIYA...to shine ya daga min hankali dan kamar bata da lafiya sosai ne"

Hajia inna ta dubeta da sauri saboda sunnan da ta fada

Sunnan nan ai sunnan da mahaifiyarsa ce kawai ke kiransa da shi, wanda ta rada masa tunda ta haife shi, tana kiransa GUDALIYA dan haka ta dubeta ta ce" GUDALIYA? kin tabbata sunnan da kika ji kennan?"

Khadeeja ta fuskanci irin firgicin da ya samu inna, dan haka ta sake fuskantarta da kyau ta ce" Eh walahi haka aka fadi"

Inna ta lumshe idannuwanta, ta sake budewa, ta dubeta a hankali ta ce" Mai kiransa GUDALIYA mutun daya ce, wato KHADIJA ce Mahaifiyarsa......, ama a ina take? me yake damunta? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ya Allah ka sa yaron nan kar ya hadu da tabewa irin ta rashin kusanci da mahaifiya, ya Allah ka sa kakansa ya gane abinda nake nuna masa, ya Ubangiji ka taimakeni ka sa ya gana da mahaifiyarsa kafin su koma gareka"

Khadeeja ta ji maganar Hajia inna ta sake sakata a tunanin tabas akoy wani baban abu dake faruwa mai girman gaske, sai dai damuwar a nan itace anya ita ta isa ta ji maganar? idan ta jin tana da wani power na neman mafita kuwa?, mutumen nan daga tambayarsa Wacece ke kira gayanan ya sa kafa yayi tafiyarsa ba ruwansa da ita bale ya ji yaya jikinta......, to dama ai auren hadi ne, eh auren hadi ne ai, ta yiwu wace ya cewa zai nema din nan ya je nema.............Ya Salam

Jikinta ne yayi sanyi sosai tana duban yannayin da inna ke ciki, domin hawaye ke bin kumatunta

A hankali ta karasa ta kama Hajia inna a nutse ta jinginar da ita tana yi mata sannu, sannan ta ciro tissu ta zauna daf da ita tana sake duban yannayin jikinta tana tunanin tun yaushe take cikin paralyse? ikon Allah

A tausashe bayan ta goge mata har zuwa bakinta a sanyaye ta ce" Ki yi hakuri Inna, ki daina kuka, ko menene mafita zata fito in sha Allah, dukkan tsanani yana tare da sauki....., to ama inna dama Mama tana raye?"

Inna dake sauke ajiyar zuciya ta dubu Khadeejar, a hankali idannuwanta suka sake cika da kwallah ta ce"











43

🥹🥹🥹🥹🥹🥹🥹😔🥰
07/12/2024, 15:32 - samiraharounayacouba: Murya a raunane sosai Hajiya Inna ta ce" Tana raye,.....khadeeja na raye sai dai ban san a duniyar da take ba, rabona da ita tunda ta fito daga prison ta zo aka hannata shigowa gidan nan a lokacin shi Alhaji karamin baya kasar ma" Sai kuma ta dakatar da maganar tana ta sauke ajiyar zuciya hawaye na bin kumatunta

Jikin khadeeja ya karra yin sanyi hankalinta ya tashi ainun, a hankali ta kama hannun Hajiya bayan ta fitar da kayan aune aunenta tana dubanta a tausashe ta ce" ki yi hakuri Hajiya, in sha Allah dukkan tsanani yana tare da sauki"

Hajiya kam ta kasa rike hawayen idannuwanta saboda abu ne da ya fi komai daga mata hankali a kusa kusan nan, a yanzu bata da wata damuwa sama da wannan, saboda ko ciwon ta ta yi waje ta ajiye shi bata tuna shi bale ya daga mata hankali, ta riga ta hakura da lamarin ciwonta ta mayar da hankali wajen sake kusanta kanta da Allah fiye da tunanin zata samu lafiya wata rana a duniya, to wacece wata ranar ? Ai an dauki shekaru ma, ko WA'INDA basu yi doguwar jinya irin Tata ba sunna iya rasa kaffafu a irin shekarunta bale ita da ta dauki shekaru a kwance. Damuwar halin da wannan yaron ke ciki ya fi komai daga mata hankali, domin ita fa babu wata magana da zata shiga tsakanin tunaninta a kan lamarin nan, karewar magana wanda abin ya faru da shi ya budi baki yayi ta nanata Ya yafewa matarsa, tana kuka yana kuka har ya bar duniya shikenan sai sunne zasu dauki gaba da shi su saka d'anta na cikinta a cikin lamarin? To kuwa tana tsoron a yi daya cikin biyu, idan ita bata je ta tarar da fushin Allah ba, tabbas su sa je su tarar more specially shi d'anta na cikinta, domin ba'a hada kowa da UWA, fin karfin yayi yawa, fushin yayi tsanani da yawa, kuma Alhaji Hamza ya kasa gane tsananin biyayar da yaron nan ke masa ba iya kaishi ga halaka , duniya na ta ja har sai an wayi gari a lokacin da ba za'a iya samun wata dama bane za'a nemi yin dana sani ko mene? Subahanalah.

shigowar aunty shareefat ta same su khadeeja na zaune a kujerar nan a nutse tana sake duba magungunan Inna da komai da komai bayan ta aunata ta duba date na expire din magungunan ta ga har lokacinsu ya cinye ta sake duban Hajiya Inna da mamaki , zata yi magana aunty shareefat ta ce" Ah ga dukkan alamu jiki da sauki daughter AM, ga maganinki ki sha , Inna lafiya ake hawaye ? " ta karasa ta talabi Hajiya Inna da kyau tana dubanta hadi da taba jikinta, duda zata yi mamaki kwarai matuka idan akace saboda jikin ne Hajiya Inna ke kuka, domin ita dai a kusa kusa bata ga mai juriyar babarsu ba a kan ciwo da jarabawar rayuwa, du halin da take ciki takan yawan yin murmushi ta furta alhamdulilah ala kulli halin. Gannin hawayenta yanzu ya sa ta ji hankalinta na neman tashi ama sai ta yi iya yinta ta dane

A hankali khadeeja bayan ta hadiyi maganin ta ajiye kwalbar ruwan ta fuskanci aunty shareefat a tausashe ta ce" Mama, magungunan Hajiya du na ga date din su ta wuce, ko wa'inda take sha a wani wajen ake ajiye su ba a box din asibitinta ba?"

Aunty shareefat ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan sake riƙe hannun Hajiya a tausashe ta ce" Daughter AM, Hajiya ai ta jima rabonta da shan magani, shi yasa kika gansu a nan a ajiyen nan"

Khadeeja ta dubi Hajiya da dan mamaki, ta sake duban aunty shareefat wace ke ta hankalta da yanayin Hajiyar

A hankali ta ɗora da fadin" Kin ga Hajiya ko? Rana daya ta ce a barta haka, a lokacin da ciwon nan ya sameta kin san hauka hauka muka yi, mune wannan asibitin, munne wannan likitan, munne wannan kasar, munne wancen kasar, munne na Hausa, ya zamo kulun cikin huda ta ake yi kuma kulun cikin hadiyar magunguna take, ga na Hausa a gefe a lokacin ko malaman sai mu basu taimakon magunguna saboda irin yadda baba ya cika dakin cen nata da magungunna na taimako daga mutane mabanbanta daga kasa kasa, sai dai cikin ikon Allah sauƙin na shaƙar numfashi ne kawai, sannu a hankali ya zamo komai bata iya yi, har sai da ake ta faman yi mata massage ne aka samu take motsa hannayen ta da kanta ita da kanta....., to a lokacin da yake yi mata ne ta dakatar da komai tace ta gaji, a barta haka, a kyale ta haka, babu yadda bamu yi ba take ta gaji ita fa a barta haka, a lokacin Alhaji karami ya kusa shekara bai yi tafiya ba, kulun cikin nacin lalaba da rarashi kan dan girman Allah ta yi hakuri a ci gaba da neman magani sai Hajiya tace ita fa a barta ciwonta ai kawai na rai ne, ciwon da ake neman magani baya sauki kawai kaima ka san abokin tafiya ne, dan haka a barta, karshema ya zamo da mun dauko maganar magani sai ta fara mana kuka, gashi hawan jinnin da hankalinta ya tashi yake motsawa, sai kawai muka hakura muke bi da adu'a sai idan mun ga ciwon ya tashi sai mu yi kiran likita idan ya zo ya dubata ya bata dan abinda zai kwantar da ciwon shikenan "

Ta karashe maganar tana dan shafa gefen fuskar Hajiya Inna a raunane ta ce" Innata, bari in kirawo maki docter, kin ga jikin ki ya motsa ko? In je in kirawo shi?"

Hajiya Inna ta bude idannuwanta da suka rine sosai, a hankali ta ce" Shareefat, ba zan ga likita ba , ko ya zo ba zan gan shi ba, in dai har babanku ba zai janye fushinsa a kan mahaifiyar yaron ki ba , ba zan ga likita ba, ba kuma zan sha maganin ba, dama ai na zame masa kaya idan na mutu tai zuwa gobe shikenan sai a kaini a birne sai ya ci gaba da kwana rayuwar da ya fi so wace babu wanda ya isa ya kwabe shi ko ya bashi shawara "

aunty shareefat hankalinta ya sake tashi, hakama khadeeja saboda irin yadda jinnin hajiyar ya hau , ko mai kannanun shekaru ce tana bukatar magani da wuri, bale ita da take cikin jinya

A hankali aunty shareefat ta ce" Innata, kar ki hada ciwon ki da fushi, dan Allah yauma ki yi aiki da halayyar ki da ta fi komai burge mu da zame mana abin koyi wato hakuri da adu'a , ina da yakinin Allah ba zai bar big son cikin wannan rayuwar saboda shi din mai addini ne, mai alkhairi ne, mai jin kan talaka ne, mai tausayin marayu ne,"

"SHAREEFA kina sane da labarin wanda sallah ce yake yi da karatun Alqur'ani a kebatacen waje dan samun nutsuwar yin ibada cikin nutsuwa da kwanciyar hankali , ama saboda mahaifiyarsa ta zo ta kirayi sunansa sau daya, ta sake dawowa, ta kuma dawowa da bai amsa mata ba ranta ya bace ta yi fushi ta yi addu'a cikin fushin nan, karshe du ibadar tasa Allah ya jarabe shi da kaucewa layi?, ai ba'a garaje da lamarin uwa, duk wanda ya dauki uwa da wasa walahi walahi ya gama tabewa, komai talaucin mahaifiyarka, komai mummunan halayanta , ka yi kokarin ka ka yi mata biyayya har Allah ya raba ka da ita lafiya, idan ka kuskure ka yarda ka saba mata Allah ne zai hukuntaka, SHAREEFA in tambaye ki, idan AL'WALED ya rasu a yau kunna da abin yaki ko Muryar da zata daga amo ku daka tsawa a saurareku a wajen da aka halicce ku ne? Ku yi kokari ku yi ta kanku fa, walahi walahi ita ta ji dadi saboda wanda ta yiwa a gaban ku ya yafe mata, kuma hukuma ta amsheta ta je ta yi kaso har na shekaru goma sha takwas, sauran maganar kuma inaga tsakaninta da Ubangijin ta, wanda in dai zata yi kyakkyawan tuba zai yafe mata, shi kuwa fa d'anta? Menene hujarsa na rashin kasancewa da mahaifiyarsa da yi mata biyayya a kan hanyar da bata sabawa Allah ba a gaban ALLAH?" Hajiya Inna ta katse aunty shareefat ta fadi maganganun nan tana fashe mata da kuka

jikin aunty shareefat na rawa ta juya da sauri ta fita dan nemo babansu, domin idan Hajiya Inna ta rikice din nan tana daga musu hankali sosai ne.


Khadeeja kanta jikinta rawa yake yi, ta zauna daf da Hajiya Inna ta rike hannayen ta , hawayenta na zuba ta gefen kumatunta a raunane ta ce" Inna, dan Allah ki yi hakuri, in sha Allah komai zai daidaita kin ji Inna? Ama idan kika tsayar da shan magani da gannin likita Inna ciwon tsanani zai yi, Inna idan ba rai ya bar gangar jiki ba'a tsayar da neman magani, bale ai Bama cire rai da rahamar Allah ko a cikin tsananin azaba muke, da ace an yarda an ci gaba da massage din nan Inna ina mai tabbatar maki cikin ikon Allah da yanzu ke da kanki kike yiwa kanki komai saboda gayanan jijiyoyin sunna saki har sun saki na wuta da hannaye, wallahi da sosai an samu kuzari, Inna muna yaki bakin rai bakin fama ne fa, koda yanzu zamu mutu idan muka anfani kanmu da kanmu zamu fi jin dadi fiye da ace muna kwance ne munna jira, Inna babu abinda ke saurin kashe bawa irin tunani, damuwa da tashin hankali dan Allah Inna ki bani dama docternki ya ci gaba da zuwa ya bani kula da massage din in ringa maki a hankali har Allah ya bamu nasara a samu ki ringa motsawa da kanki, dan Allah innnn"

Riko hannunta da Inna ta yi da dan karfi ya saka khadeeja dakatar da maganar da take yi tana dubanta a lokacin kuma suka jiyo Muryar aunty shareefat na fadin" Khaleesat je wajen kakan kurma idan baba na cen ki kirawo shi, kuma ki cema Mama b jikin Inna ne ya tashi"

A hankali Inna ta ce" Khadeeja....., Ba fa zan sha ba ki yi hakuri, in dai har babanku ba zai janye ba nima ba gudu, ba ja da baya!, idan na bar masa duniyar zai fi jin dadin nunawa jikansa sosaya, makauniyar soyaya!"

Khadeeja hawayenta ya tsananta, kumatunta suka yi wani irin ja sai murza hannayen Hajiya Inna take yi tana jin kirjin ta na mugun bugawa da tarin tsoro da tashin hankalin abinda ke iya faruwa,

Ba'a wani dauki lokaci ba su baba Hamza suka shigo da AL'WALED, wanda zuwansa kennan, ya kasa hakura be a dole ya garzayo ya zo dan ya ga jikin khadeeja

Da kyar ya iya hakuri baba Hamza ya rigayeshi shiga dakin sannan ya shigo, cikin hanzari ya karaso inda khadeeja ke rike da hannayen Hajiya Inna tana murzawa a hankali a hankali ya duka gaban gadon ya hade hannayen duka biyu a cikin nasa, wato na khadeejar da na Hajiya innar a hankali yana murzawa, ta dubi khadeeja wace zubar hawayenta ke kokarin kasara dukkan kuzarin da ya shigo da shi

A hankali ya sake riƙe hannayen a tausashe bayan ya dauke idannuwansa daga cikin na khadeejar wace ya saukar mata da muguwar kasala da wani karin rauni a zuciyarta har ta kasa kallonsa tsai cikin idon, ya sauke kan fuskar Hajiya Inna a hankali ya furta" Ne yake damun zuciyata ne? Me ya daga hankalin sarauniyar AL'WALED ne?"

HAJIA Inna dake jin Muryar baba Hamza na cewa docter ya zo yanzu yanzu ko me yake yi ya bari ya zo ta É—an daga Muryar ta daidai karfinta ta ce" Sai ya zo ya sakani a coma sannan ya dura min maganin ta hanci, au bata baka sakona ba shareefat? Bata sanar da kai ba cewa nima na kiya ba? Alhaji to bari in sanar da kai, na rantse harshena ba zai dandani magani ba idan har baka janye maganar da ka yi shekarun da suka wuce a kan yaron nan da mahaifiyarsa ba sai dai in mutu a haka!"

Gabansa ya yanke ya fadi, hakama gaban Al' Walid

Da sauri ya dubeta hankalinsa na neman tashi, khadeeja ta ja hannunta dan tana din fita domin babu kowa a daki sai su kadai, ama yana rike da hannun ya ki saki kuma gashi kamar za'a yi tashin hankalin da ya girmami kwakwalwarta

Jikin baba Hamza nan da nan ya dauki rawa yana duban ta ya ce" Ama ba nace kar a saki a min maganar nan ba? Me ya haÉ—a maganar nan da rashin lafiyar ki? Me yasa zaki daga min hankali a kan abinda kika san ba zan taba dubawa ba?"

Aba ya'u dake falo sai baza riga yake yi yana dan karkatar da kai sai kuma ya dubi Hajiya Binta da aunty shareefat ta dakatar kasa kasa ya ce" To wai ba asibiti za'a Kaita bane? Khaleesat tace jikinta ne kuma sun yi shiru a daka leko mana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login