Showing 108001 words to 111000 words out of 190762 words

Chapter 37 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3983

a ransa ya ayana' Na zata tsabar fitina da rashin ji ne? idan dai yadda yake haka haka yake da su sai ta nemi tsari kam....., ko tana ina? ta yiwu ana cen da kawayensu ana gwali da murnar auren yayarta.....'

Sai kuma ya dan yi tsai .....ya samu kansa da ayana' Zan so ace ......, yannayinsu ya zo daya....., ko ba komai......akoy fira'

Murmushi ya sake yi a lokacin da Aba yake gyarawa baba Hamza rigarsa da kyau ya rufe musu mota sannan ya ja baya kadan yana fadin" Sauka lafiya tsoho, sai na kawota"

Baba Hamza ya dafe kai a lokacin da mota ke tafiya ya ce" Ka zama shaida idan ya kawo Hajia karama da kansa yau sai na mareshi"

Murmushi AL'WALID ya masa bai ce komai ba......., lamarinsu yana matukar dadada masa zuciya, ya zamo wani time da yake tsaye masa a rai cikin abubuwan da idan ya tuna yake samun nutsuwa da kwonciyar hankali a zuciyarsa

Sunna da dan ja tsakanin gidan Aba da gidan Elhaji Hamza, hakan ya sa sun dauki kusan minti talatin a hanya kafin su karasa

Sunna zuwa suka samu zama ake yi irin na bikin yan gata sosai da sosai a kofar gidan, jama'a cike take masha ALLAH, ana ta ciye ciye da shaye shayen kayan dadi ana fira mai ma'ana, karasowarsu ya sa dangi suka yi musu caaaaaaa, Bama kamar cousins da abokan da suka zo wajen taron, hakan ya rike shi ya zauna wajensu ana ta faman fadin ana son gannin amarya ance ba Mufeeda bace? wace wannan ta ciri tuta haka? shi dai sai dai yayi murmushi domin shi dinma yana cikin jerin wa'inda basu san amaryar ba, har sai da Jameel ya zo ya dan yi masa zance kasa kasa sannan ya mike ya musu salama da nufin yana zuwa

A nutse ya taka ya nufi bangarensa, Cen ya samu Baba Hamza da Elhaji Maiga sunna zaune a falon da yake tarbar baki

Yana shigowa Elhaji Maiga ya mike yana bashi hannu, shima ya amsa suka gaisa a mutunce kafin su zauna ya fuskanci Baba dake fadin " Ashe jikin yarinyar nan haka yayi tsanani? ance tun jiya da ka baro wajenta ta fadi a summe har yanzu ba ta yadda take, subahanallah ban ji dadin haka ba ko kadan, Baiwar Allah, Allah ya bata lafiya "

Elhaji Maiga ya ce" Amen, walahi sai ka gani Elhaji , sosai take cikin wani yannayi marar dadi, kuka take yi kamar ranta zai fita, idan aka samu ta dan farka din bata ji bata gani, fadi take yi idan ba'a aura mata shi ba tana iya mutuwa, abin nan ban san yaya zan yi ba, na rasa gane girman laifin da ta yi, ko menene da ace an sanar min tun kafin a dauki matakin nan da na tsawatar mata ta fasa abinda ba'aso take yi din, a yafe mata a daura da ita dinma in sha Allah ba zata kuma ba"

Baba Hamza ya wani karkatar da kai ya furta" Allah sarki, wayo baiwar Allah, ashe dai abin har haka yayi tsanani, innalilahi "

A nutse AL'WALID ya dube shi, da yannayin girmansa da yayi ya fara yi masa magana, da girmama shekarun dake tsakanin su, bayan wannan da bai san me zai iya fada masa na amsar tambayarsa ba

A nutsen sa ya ce" Yanzun ma, ka tsawatar mata saboda ko mijinta nake bata da iko da Ni........, Nd ban shirya kara wani nauyin iyalin a kaina yau ba, a bani time domin yannayinta ya sakani a shakun in har matar da zan aura Ni ne ko wanina bcz Ni mai dangi ne ., Allah ya bata lafiya!"

Daga haka ya mike ya barwa baba Hamza babar rigar tasa a nan baki sake ya daga kai ya rakashi da kallo har ya gama hayewa matatakalar dakinsa ya wuce ciki

Ido hudu suka yi da junna, bayan ya bacewa ganninsu, baba Hamza ya rasa me zai ce sai kawai yake kallon Elhaji Maiga a lokacin da yake fita da hannunsa, murya a hargitse ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ko me ta yi? dan Allah Elhaji a bashi hakuri a kuma yi hakuri ko menene zata cenza, zata daina"

Tausayinsa ya kama baba Hamza, domin ƙarara zaka ga tarin soyayar y'arsa dake dawainiya da shi

A tausashe ya ce" In sha Allah zan yi masa magana kuma zai hakura, bi'izinillah idan ka ga bai aureta ba ka saka haka cikin kadarar Ubangiji ba ta wani ba, dan kuwa du yadda kake tunanin wani abu ne ta yi ya sa aka ki hada aurensu sai in Allah ya yarda ne za'a ki hadawar, abinda nake so da kai daya ne, idan kun samu nutsuwa ka yiwa Mufeeda tsawar da zata ji ka da kunnen basira, ka sanarwa Mufeeda cewa Ni Elhaji Hamza na ji magangannun da ta yi a ranar da aka kwontar da Hajia inna asibiti, na ji wanda ta yi a ranar da aka kawo kurma bata da lafiya tana amai har aman ya taba jikinta saboda ita da mahaifin kurmar suka daukota, ka sanar mata cewa na ji magangannun ta a ranar da na tsawatar musu cece ku ce ita da yaran gidan nan samari, kuma ka sanar mata na ji magangannunta na shekaran jiya ita da yan matan gidan nan, ka sanar mata Ni na yafe mata, haka kuma ina iya amsarta a ahalina idan har ta cenja, domin mutun ce ita kuma yarinya, sai dai ka sanar mata a yanzu fa a wani gaba ake da shine ya murje ido a kanta, ka sanar mata duk wani abu da ayyukansa ke hanna shi ganni a yanzu yana iya ganni saboda zan bashi umarnin idan har da hali a yi da ita din itama, ka sanar masa abin nan da take dauka mafi karami ta dauke shi abu ne na wasa take yinsa a vidio tare da kannenta idan har ya ganshi sai ya fara gigita lamarinta kafin ya barta bari na har abada, ka fada mata Ni Elhaji Hamza Nine ke dakatar da wasu lamura na fushi nasa, wa'inda idan suka taso masa nima ba barina yake yi ba dan kuwa ya sha tafiya sai ya huce in ganshi, idan har ta yi wasa a yanzu da yace sai yayi nazari a kanta bincikensa ya kaishi inda zai ga wasu abubuwan du isata da shi ba zan saka shi yin dole ba, dan shi a *FARKON GANIN IDANNUWANSA* zai dauki matakin da ya dace a kan lamarin, ka yi hakuri, ka yi hakuri a matsayinka na uba mun taba zuciyarka, ka yi hakuri ,, sannan kar ku je gidan mahaifin yarinyar da aka daura aure da ita yau, kar ku je, zuwan ba zai haifi d'a da ido ba ka ji? Allah ya muku albarka a gaishe min da ita da jiki"

Mikewa baba yayi hakan ya sa dole Elhaji Maiga mikewar shima, zuciyarsa cike da dacin wannan lamari, ya rasa yaya zai bilowa abin, abinda ya sani shine sai da ya nemi uban yarinyar nan, ko nawa yake so zai iya bashi ya sa a saki y'arsa, idan kuwa ya ki ta laluma walahi zai ga ta tsiya, domin du hanyar da ta dace ya samawa Mufeeda nutsuwar zuciya zai bi, da farko farko ya zamo mai kwabarta a kan lamarin nan, daga baya shi da kansa ya gane y'arsa fa ta yi baban kamu, tun daga lokacin da aka bashi check din da ya gigitashi a gidan nan ya gama yin saranda da kansa yake fatan gannin lokacin da y'arsa zata zamo mata a wajen AL'WALID.



..............Wannan kennan
07/12/2024, 15:14 - samiraharounayacouba: *FARKON GANIN IDONA*


PAGE 31

TALLAH TALLAH TALLAH TALLAH

*Zumar 3in1 zumace ingantacciya mekyau megyara jiki sosai zatasaka kayi bulbul breast sugyaru hips yafito kiyi yar duma duma hajiya bazakigane abundanake fadaba dai kinshata zakigane*
*08030861857*
*Zumar breast Zumar hips duk munadasu masu inganci sosai da sosai*

*Akwai pills na 3in1 shima aikinsu Daya da zumar 3in1 gawayanda basashan zumane mukayi daminsu*
*08030861857*
*Infection flusher Ingantacce maganine mai magance dukwata matsalar mara Kai harda rashin haihuwa yanayi banahaufi akai don angwada angani mace indai rashin niima ne na cutar sanyi yararaketa kuraje kaikayi dattin mara zonabaki infection flusher kisha mamaki yar uwa Insha Allah zakigodemin*

*Kayanmu guarantee ne sai angwada akansan nakwarai location gombe munaturawa koinah Insha Allah* *08030861857* Kira KO WhatsApp Insha Allah



LABARI


A lokacin da AL'WALID ya shige dakinsa direct bakin bed dinsa ya karasa ya zauna a hankali ya shiga cakuda gashin dake kansa a hankali idannuwansa lumshe

Lebensa da ya dan dantse ya karra daukan launin pink, a nutse ya ciro hannunsa ya kwonta saman bayansa yana sake lumshe idannuwansa lokaci daya ya shiga dogon tunani.......
Yana kewa a duniyarsa, yana kewa sosai ta mahaifiya, haka kuma yana kewar matarsa
Yana jin kamar ba cike yake ba a kulun idan ya tuna da mahaifiyarsa

Wayar nan ya ciro daga aljihunsa a hankali ya shiga wajen msg dinta

A jere suke , kowane da kwanan watansa da time din da ta turo masa

Ya zamo idan tafiya zai yi yakan yawan duba wayarsa dan jiran sakon da ta saba tura masa, haka idan zai dawo ko in ya dawo yakan farka da tunanin samun sakonta Duda ba amsa mata yake yi ba

A hankali ya danna numbar ya tura kira, sai kuma da sauri ya katse kiran yana sakin wayar a saman cikinsa hadi da rintse idannuwansa

Kasantuwar ko yaya ka aika kira in dai ya dauki second biyu zuwa uku sai an nunawa mutun da ka yi kiransa lokaci daya wayar ta fara ringin, sai dai ana gannin an yi kira sau biyu bai daga ba sai aka turo masa da msg kamar haka "KA YI HAKURI, KA YAFE MIN, KA YI HAKURI GUDALIYA"

Msg din ya karanta , a hankali ya lumshe idannuwansa yana jin irin yadda zuciyarsa ke dokawa

Mikewa yayi da kansa a nutse ya shiga bin dakunnan dake saman, bayan ya gama dubawa ya dauki wayarsa yayi kiran aunty sharifat, a nutse ya ce" Umani, kunna iya zuwa ku ga dakunan, Ni zan fita"

Aunty sharifat dake ta dakon jiran ya basu damar su duba dakunnan nasa dan su ga wane za'a warewa amarya sannan su ga abinda za'a saka wanda yake da bukatar sabo kuma su ga idan dakin nada bukatar wani gyaran , domin baba ya ce da su fa a nan zata zauna kafin ya bada damar a kaita gidanta wanda su Dukansu sun san ba a nan familly Hause zasu rayu ba, a tausashe ta ce" Ok son, ganinan"

Daga haka ya katse ya shige bayi dan yayi wani wankan, cikin kankanin lokaci ya shirya cikin lalausan yadi sannan ya dauki ky din farar motarsa dake baya wajen dawakai, ya fito daga dakin nasa yana rike da kys din dakunnan kaf

Aunty sharifat ya samu zaune da wayarta a hannunta

Da murmushi ta tarbe shi a tausashe ta ce" Son, Barka da saukowa"

Karasowa yayi har inda take ya zauna ya ce" Umani Barka da warhaka, ya hidima"

Ta yi yar dariya ta ce" Alhamdulilah muna sha, yanzu muka gama waya da mahaifiyar amaryar ma ance wai a tura motoci daukan gadajenta, shine nace baba kuma yace kar a dauko wai, ban san yaya za'a yi ba yanzun"

Ya yi dan tsai, a ransa yana mamakin ita wannan yarinyar komai nata sai an saka tsayaya? , sai kuma ya ture tunanin ya mika mata kys din baki daya ya mike yana fadin" umani, Ni kam bari in tafi inada wani uzuri mai girma a gabana, yadda kuka yi "

Karba ta yi ta mike tana yi masa addu'ar Allah ya tsare bayan ta gama yi masa maganar a'a shi ango ina shi ina fita yau?, shi dai yayi murmushi ya tafi, dan abubuwan sun masa yawa kuma baya jin dadin zaman dakin haka kuma baya son tarin kwaramniyar dake waje, zai dai dan je gidan gona ya huta kadan sai ya dawo daga baya

Aunty sharifat tare da yan uwanta suka bi dakunnan daya bayan daya, har ga Allah kowani daki dauke yake da set din gado da kujeru da cafet , kuma kaya ne rantsatsu, idanma da abinda za'a cenza bai wuce kafet da zannuwan gado ba, dan haka nan da nan ta yi kiran kamfani ta sa a kawo kafet kala kala da labulaye, zannuwan gado kuwa khalisat ta je da kanta baban store ta kwaso ta kawo , nan suka kwabe kwaliya suka shiga gyara domin akoy kura, guga ta kirki suka yiwa dakunnan sannan suka ajiye zannuwan gadon da sauran su, zuwa lokacin har yama ta yi suka saka kafet din da su labulaye sannan suka wadata gidan da turaran wuta da airfrchner suka rufe suka yi bangaren su Hajia


Sunna zuwa tuni magariba na sanyo kai, dan haka kowace ta nufi bayi dan daura alwallah da kuma yin shirin tarbar amarya.


Mahaifiyar khalisat bayan ta gama sallar magariba ta dauki wanka iya wanka ta baza turare sai walwali take ta sha dandatsetsen lesh, ta dauki jakarta da wayarta a ranta tana ayana' Hum, kawata kennan, na wuni cirrr dan in ga ko zata neme Ni ama shiru, zan ga iya gudun ruwanta, ace auren nan da Elhaji karami aka daura shi ama ba zata yi kirana ta min godiya ba? ta manta Ni na mata hanyar gannin Elhaji Hamza har ya tsawatarwa Elhajin auren da zai hada da y'ar Tata da aka ba Elhaji karamin yanzu da wani? mutane kennan, zan ga me take nufi da Ni'

Ta samu baban filin gidan Elhaji Hamza cike makil da dangi, samarin sun yi shigar tufafi fari ne dan zuwa dauko amaryar, Duda auren nan basu shirya masa ba haka dai suka sanar du mai tufafi fari ya saka dan zuwa dauko amarya, aka yi Sa'a kuwa kusan kowa yana da shi, matan kuwa kowace ta saka abinda gareta dan tarbar amarya

Shigewa ta yi cikinsu bayan ta tambayi Hajia Binta ba'a fitar da Hajia inna ba? ta sanar mata ai tana daki an mayar da ita dan ta huta, baba Hamza ma yana ciki saboda hayaniyyar ta yi yawa, ga dai kurma cen ana daura mata dan kwali

Ta hangi kurmar tare da Raisa na yi mata dauri, ta samu waje ta zauna saboda su jiran amarya zasu yi, a lokacin ne kuma wayarta ta ringa neman agajin a daga

Cirota ta yi daga jakarta ta duba mai kiran

Baki ta tabe gannin sunnan mahaifiyar Karima, ta ki dagawa

Sake kira ta yi, hakan ya sa ta daga tana fadin" Ranki ya dade ai na zata ba zaki neme Ni ba ana cen ana cikin abubuwan arziki, ai gamunan muna jiran isowar y'ar tamu"

Mahaifiyar Karima da muryarta ta shake sosai tsabar kukan da ta ci ta ce" Kawata, ba zaki gane halin da nake ciki ba, innalilahi Wa inna ilaihi raj'une "

Da sauri mahaifiyar khalisat ta mike tana dan fita daga cikin mutane ta ce" Subahanallah lafiya nake jin Muryarki haka? "

Maman karima ta fitar da ajiyar zuciya mai zafi kafin ta ce" Yaya aka yi Elhaji Hamza bai sanar min cewa mijin da aka yiwa Karima Elhaji AL'WALID bane? fisabililahi ya mana adalci kennan? walahi da shine Bama zamu taba daga zancen ba, yanzu shine ya yi mana ja gaba muka je muka cewa babansu Bama so karshe aka ɗauki y'ar wannan azalumar da ta rabani da mijina uban y'ata aka ba Elhaji AL'WALID? to walahi ku sani kun shiga uku, idan yarinyar nan ta shigo muku da kisar mahaifiyarta kun shiga uku, domin kunna ji kunna gani sai ta raba ku da shi a duniyar nan, sai ta raba shi da kowa nasa ya zamo in dai ba ita da uwarta ba to fa babu wanda zai rabe shi a duniya"

Cikin Hajia sai da ya nemi rikice mata a tsayen da take, ta ce" Ke ban fa gane ba, kina nufin y'ar matar Elhajin ce aka aura mana? y'arta ta cikinta? "

Maman karima ta ce" Eh walahi ita fa"

Hajia ya dafe goshi tana fadin" Innalilahi, wai dama da Karima ne aka so hada auren? ai kuwa lalle zamu fafata a gidan nan, dan walahi yadda kike fadin matar nan ba zamu taba bari ta ci galaba a kanmu ba!"

Maman karima ta ce" Kawata, Bama zaki gane ba, zan shigo gidan jibi in sha Allah, ki ajiye wayarki kusa dan a barni shigowa, ya zama wajibi y'ata ta shigo gidan nan, idan Karima ta shigo kin san gida a hannunki yake, ya zama dole Karima ta shigo, ba zai yiwu ba, ba zai taba yiwuwa ace Khadeeja ce ta zata zauna da AL'WALID ba!"

Hajia ta zarro ido, sunnan ya bata mamaki ainun, Khadeeja kuma?, to ai ko jikoki Elhaji ya soke sunnan nan bale da kansa da hankalinsa ya aurowa AL'WALID, eh lalle gaskiyar kawarta ne ba a hayacinsa yake ba tuni an gama da elhajinsu innalilahi, sai dai kuma kalamanta suka sa ta ce" To wani irin Karima ta shigo bayan ubansu daya da ita khadeejar?"

Maman karima a kausashe ta ce" Ko ana ruwan muzuru da shaho sai Karima ta shigo gidan nan, dukkan hanyar da zan bi Karima ta halasta a wajensa sai na bi, ba zai yiwu ba, sai dai du abinda zai faru ya faru walahi!, ke dai sai na zo!"

Daga haka ta kashe kiran, maman khalisat ta yi shiru da wayar a hannunta, gaba daya jikinta ya mutu murus, du irin zumudin da take ciki da farin ciki sai ta ji ya koma ciki, to ai wannan an yi gudun Gara an fada gidan zago kennan, innalilahi wa inna ilaihi raj'une, irin yadda kawarta ke fada mata karfin asirin matar nan komai ma ta iya yi gaskiya, cabdijan, bari a kawo amaryar su zauna da sauran su yi magana koda zuwa gobe ne, subahanallah ga sharifat da gardamar tsiya da ace ita wata ce da ba za'a sauki amaryar nan a bangaren AL'WALID ba tun yanzu, koda yake zasu zagine a yi ta musu girki Bama za'a bata damar yin abincinsa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login