Showing 105001 words to 108000 words out of 190762 words

Chapter 36 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3993

wata daraja ta sake hawa kansa a karro na biyu, daraja ce, domin aure sunnar ma'aiki ne, babar daraja ma kuwa mai wuyar sha'ani......, gashi dai ya ji sunnan matar da aka zaba masa, sunnan da sai da ya dan zabura a lokacin da aka fada domin wannan sunna dai da baba Hamza ya zaba ya aura masa sunna ne mafi daraja a cikin zuciyarsa, boyayan sunnan mafi daraja mafi soyuwa kuma wanda ya fi wahalar da zuciyarsa a duniya, Bai san yaya aka yi daga Karima da baba ya taba fada, sunnan ya koma Khadeeja ba, abinda ya Sanni shine sunnan nan in har ba sosai shakuwarsu ta zarce misali da baba Hamza ba, ba zai taba zabarsa ba, domin shine sunnan matar da ta saka shi kuka da girmansa da komai sannan yayi alฦ™awarin ba zai taba yafe mata ba, yayi alฦ™awarin a duniya zasu yi gaba kuma a lahira su tsaya a gaban Allah, yayi tirrr da ita kuma ya koreta, ya saka katanga mai tsaurin gaske ta karfe a tsakaninsu, yayi rantsuwar ba zata ji dadin haihuwar da ta samu da babansa ba, yayi rantsuwar AL'WALID nasa ne babu ita babu shi, yace idan ba dan sunnan da take da shi sunna ne mai daraja a duniyar masu daraja ba da harta sunnanta sai ya la'anta, sai ga wani abin mamaki sunnan da baya kamawa yau ya aura masa?......., sunnan MAHAIFIYARSA ne take dauke da shi, wato NANA KHADEEJA....., Uhum

Kasa kasa ya ce" Ka tashi mu tafi mana Baba?"

Baba Hamza ya dan girgiza kai ya ce" Ni ai a nan zan wuni Elhaji karami, wannan yaron idan yana taro ko abinci baya ci, ama in ina nan yana ci, ai gidan da jama'a su kawunka du sunna cen, ku je ku yi wunin ku zuwa yamma ko dan sahu ne na shigo in zo, a gaba a fitar da kunnu , wani kunnu mai daษ—in gaske da Hajiar gidan nan ke yi, wai shi mardam sai na sha shi tukunan"

Ido AL'WALID ya zarro yana kallonsa, a lokacin ne kuwa malan Abdullahi ya iya mikewa da kyar jikinsa yayi masa mugun nauyi a yanzu da ya gama gane abinda yake faruwa, ya juya jikin nan nasa ba karfi ya yi tafiya mai dan nisa sannan ya sha kwana yana ta tunani da tarababi a zuciyarsa ya ciri wayarsa da tunanin yayi kiran d'an uwan nasa dan ya ji shin yaya sun gama daidaitawa ko? dan bai taba tunanin mijin da Y'ar wajen Elhaji Ya'u ta samu ba shine AL'WALID din MUFEEDA.

Kira yayi ta yi da kyar ya daga yannayin muryarsa a bace ya ce" Haba yaya kaima tunda ka yi kira sau daya ban daga ba ai ka san ina cikin wani abin ne ko?"

Malan Abdullahi ya ce" Aya yi hakuri Elhaji, dama kira na yi in ji yaya lamarin nan na y'ar tawa?"

Elhaji Maiga ya ce" Gatanan muna asibiti ama yau zasu sake mu, lamarin ta kuwa ba sauki gaskiya saboda abin nan ya taba lafiyarta , yanzu haka cikin rarashinta ne muke yi ka yi kira"

"Subahanallah subahanallah subahanallah, asibiti? eh lalle abin yayi tsanani, subahanallah, ta yi hakuri komai na duniya maganinsa Allah, kuma tunda ka ga an yi haka to fa ba shine alkhairinta ba, ta yi ta addu'a Allah zai fitar mata da wanda ya fi shi alkhairi nesa ba kusa ba, kennan a cen asibitin ta Niamey kuke? sannu Allah ya sanyaya"

Elhaji Maiga ba wani darr yace" A nan Damagaran muke gamunan a clinik lafiya, kuma maganar wai wanda ya fi alkhairi ai ba zai yiwu ba, shine dai alkhairin nata, gatanan ai na fada mata kar ta daga hankalinta yanzu zan sake komawa , kuma na sa a bincika min da yarinyar da yake fita bayan Mufeeda, zan samu iyayenta ko biyansu ne a yi su janye, kawai fa saboda sun samu y'ar matsala ne dan ta yi fada da wata khaleesat a gidan nasu ne ya yi mata haka, kakansa dama ba sonta yake yi ba, ba laifi da ya san irin son da yarinyar nan ke masa da ba zai taba yin wasa da ita irin haka ba, zan yi kiran ka ina zuwa na baza ne a min bincike ko y'ar waye suke soyaya yanzu zan tarda ubanta!"

Malan Ya'u da sauri ya budi baki yana zarro ido ya ce" A'a, Elhaji........"

Kittttt ya ji an katse kiran

Da sauri ya ringa bin kiran hannayensa na rawa, sai dai ba'a dagawa karshema sai aka saka layin a Black list dan kuwa yaron wajensa ya fada masa idan ana fadin haka ana nufin an saka layi a Black list ne, shi Bama wai dan ya ji d'an uwan nasa na gari ba ama ko nemansa bai yi ba tsabar wulakanci ya dame shi ba, a'a, ko daya, abinda ya dame shi shine maganar da d'an uwansa yayi cewar zai samu yarinya ko y'ar waye ya tarda ita yayi gagawar dakatar da shi tun kafin ya raina kansa, domin kuwa tarin direba da masu bada tsaro ba zasu hanna Elhaji Ya'u gigita rayuwarsa ba, shi bai san aikin gama ya gama bane har an daura aure? Bayan wannan shi bai san waye AL'WALID bane da zai yi wannan garajan? gwara ya bi a hankali ta yiwu ya aure Mufeedan daga baya, kuma in ba rashin hankali ba kai ina ruwanka da aikata wannan abu? kwarai da gaske da lawan na kara ke ce masa yawon bin mata da hulda da su da zama a baban gari da sake da ibada ya taba kwakwaluwar Maiga hakane, to in ba wannan ba in ka san kanka ka san wani ne? Elhaji Ya'u direbobi ne bai dauka ba, bai kuma dauki masu yi masa hidima ba, ama idan kana neman boyayan mai mahaukatan kudi in ka zo nan ka tsaya, dama du manyan mutanen mu na kauye ai basu cika bayana dukiyarsu ba, gashi gidan balaki, idan bai nada masa duka ba lalle ya auna arziki, domin shi dai Maiga d'an uwansa ne abinda ba zai iya fada a kansa ba tarin dukiyar sa dan bai san adadin da ta kai ba, bayan wannan ya san rago ne na karshen zamani ga tsoro, sai burgar kudi, Elhaji Ya'u kuwa shima ya sanshi farin sani, shine ja gaban malaman sa Da suke yi masa rokon Allah harkar kasuwancinsa da kuma harkar ya'yansa, innalilahi wa inna ilaihi raj'une yaya zai yi ne?

Cen tunani ya fado masa ya juya ya dawo da tunanin fara gannin su Elhajin sannan yayi gagawa ya dauki adaidaita ya je clinik din tun kafin Maiga ya janyowa kansa rigimar da zai bar garin nan da kaffafuwansa

A lokacin da ya iso Elhaji AL'WALID na kallon baba a kausashe shi kuwa sai kai kofin kunnu yake bakinsa yana sha , abin kunnun du ya shafu a dan gefe da gefen bakinsa sunna fira da Elhaji Ya'u dariyarsu kawai ake ji, shima da kofin kunnun a hannunsa, Elhaji Ya'u yace" Kunnun nan na gimbiya dadin na taron sabga daban da na gida wanda take min fa tsoho, kai dai Allah ya mata albarka"

Baba Hamza ya ce" Amen, ina fata ta zuba na babanta?"

Elhaji Ya'u ya mike yana baza babar riga ya ajiye kofinsa kusa da baba Hamza ya ce" Bari in koma cikin dai in gani ka san yau ba kanta tana nan sai walwali take yi a cikin jama'a su gimbiya an aurar da y'a, bari in koma in gani Allah ya sa ta zuba din , inma bata zuba ba ai Khadeeja ta iya tana zuwa sai ta ษ—ora tukunya ta yi maka."

Baba Hamza ya kama baki ya ce" Ka ga fa wani balakin, amaryar? kai dai Allah ya shiryeka"

AL'WALID ya dauke kansa a ransa ya ayana' Kaima Allah ya shiryakan ai, Ni kam har yanzu na kasa gane kusancin nan naka da bawan Allahn nan, ama a yanzu na fara fahimtar soyaya ce daga Allah, sai a yi muku adu'a kawai'


A mutunce suka gaisa sosai, AL'WALID ya bashi hannu suka gaisa sosai domin ya gane shi, uncle din Mufeeda ne, har ya shiga tunanin kennan ya san Elhaji Ya'u?


Malan Abdullahi a hankali ya ce"






*GA MAI BUKATAAR TALLAH IN SHA TA YI MIN MAGANA SAMAN NUMBANA KAMAR HAKA 93811618, DOMIN DAGA PAGE 30 TALLAR FARKO TA KARE IN SHA ALLAH, NA GODE*
07/12/2024, 15:14 - samiraharounayacouba: ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ
*FARKON GANIN IDONA*
๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ๐ŸŒธ๐ŸŒบ


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ช

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐Ÿ˜*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦŠAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦ˜IN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na talatin (30)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*


https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ
๐Ÿ‘‰0912 262 1080





LABARI



Malan Abdullahi a hankali sannan a sanyaye bayan ya zauna Kamar yadda Elhaji Hamza ya nuna masa wajen zama da dan mamaki yana fadin" To ikon Allah,malan Abdullahi kennan ka san yaron nan nawa? Elhaji Ya'u? ai yarona ne"

Malan Abdullahi a sanyayen nan nasa yayi murmushi ya ce" Eh baba, Elhaji mai mai gidana ne , tare muke"

Sai kuma ya dan sarara dan babban na addu'ar masha ALLAH haka ake so

A hankali ya ce" Dama baba dangane da maganar wajen Mufeeda ne, shine nace wai tana asibiti da babanta , yanzu na same su"

Baba ya dube shi da kula sosai ya ce" Subahanallah, asibiti? zazabi take yi?"

AL'WALID ya dan juyo ya kalli Malan Abdullahi

Malan Abdullahi ya girgiza kai ya ce" Lamarin nan ne ya Kwontar da ita, yanzu haka da na kashe yace wai zai tardo Elhaji ne dan ya sa a masa bincike, kuma ka san yaron naka shima ba baya ba, shine nace bari in sanar da kai dan a yi gagawar yiwa tufkar hanci saboda kar wata baraka ta shiga lamarin babu dadi"

Da dan mamaki AL'WALID ya furta" Zai tardo Kakan kurma yace masa me?"

Malan Abdullahi ya ce" Yana nufin su sasanta a daina maganar daurin auren ne, shine nace karma ya fara gwada a katse shi dan bana tunanin abin zai zo da sauki"

Mamaki ya karra kama AL'WALID, ya dauke kansa daga kan Malan Abdullahi yayi dan murmushi kawai...'', wauh, wauh, wauh, abin mamaki, gaskiya abin mamaki, to shi Maiga a wa da zai shiga hurumin aurensa da wata? ko y'arsa ya aura yana da damar yanka masa irin wannan neman cin zarafin? what? yaya aka yi haka ta shiga tsakaninsu? bari shi ya same shi ya fada masa ya taba tsayar da shi ya masa alkawarin y'arsa kar ta kula kowa sai shi dan zai aureta? shi fa bashi da wannan, shi ba mahaukaci bane kuma ba mai son kansa bane, shi yasa baya ajiye kafa a gidan su yarinya yayi ta kai kawo, ko Mufeeda da ya yarda suka fara gannin junna dan ya yi niyar aurenta a lokacin kai tsaye ne, matsalar da ka samu tunda ta fara zuwa gidansu wajensa sai kawai baba Hamza ya ringa yau gobe yau gobe da maganar auren,

Baba Hamza ya ce" Ikon Allah subahanallah, to, a'a a'a, kar yayi haka sai a zubar da mutincin junna , hakan kuwa babu dadi, in ba abinsa ba aure aka yi ai ba lalata ba, kuma meye hadinsa shi uba da mahaifan yarinya? kun ga kar a sako Khadeeja a lamarin nan, ko menene kawai ya same mu , inaga ka same shi kace ina kiransa, ai Ni zai gani Nine baban AL'WALID ba kowa ba ko?"

Malan Abdullahi ya gyada kai ya ce" Hakane, to in banda abinsa shi da ake so a kawo masalaha ko menene a samu jituwa da fahimtar junna ai bai dace ya biyo ta haka Bama, gashi ina ta kiran layinsa baya dagawa, bari dai in tashi in je in same shi kawai tun kafin ya aikata wani abin"

AL'WALID ya sake zubawa malan Abdullahi ido, kwarai shine mutun na farko da ya fara sani matsayin mahaifin Mufeeda kafin ya hadu da wanda ya haifeta, kuma a haduwarsa da wannan bawan Allahn ya ji a ransa Mufeeda matar aure ce, domin zuwansa na farko sai da aka masa binciken danginta ya samu tarba ta mutunci a wajen mutumen, a yanzu kuma ya idasa gane nisan bambancin halayarsa da ta d'an uwan nasa

A tausashe ya ce" Ka barshi kawai ya zo din"

Da sauri baba Hamza ya dube shi yana girgiza kai yace" Ya zo ina? ka kuwa san kakan kurma? tab, kana ji malan Abdullahi, ka same shi a wayar kawai kace ina kiransa ko ka je"

Malan Abdullahi ya mike yana fadin" To to to shikenan bari in yi gaggawa in hau dan sahu ya kaini asibitin, an gode an gode Allah ya saka da alkhairi ya karra girma"

Har ya juya zai tafi AL'WALID ya mike a nutse ya dan bi bayansa

Sunna tahowa ya dubi direba guda ya ce" Abashe, kai shi inda zai je ka yi jiransa ya gama ka dawo da shi gidansa"

Malan Abdullahi ya ringa godiya yana karawa , hakan ya sa AL'WALID ji a ransa tabas zai zo da kansa ya yiwa bawan Allahn nan wani abin da zai saka ya ji dadi koda na wuni daya ne, bi'izinillah zai ganshi , dan yana son mutun mai daraja irinsa.

Juyawa yayi yana sake sakin wani murmushin, ya ciro wayarsa daga aljihu ya sake gannin msg daga numbar nan dai da ake yi masa msg shekara da shekaru, numbar da an bincika masa an gano da sunnan NANA KHADEEJA take aiki a computer, kuma daga layinsa ance bata neman kowa da wayar, shi dinma msg ne kawai ake yi masa da layin

Karanta msg din yayi a nutse ya fita ya dannawa numbar Elhaji Maiga kira yana dan duban agogon hannunsa

Tana fara ringin Elhaji Maigan ya daga yayi salama hadi da fadin" Barka da warhaka honorable, fatan an tashi lafiya"

A nutse AL'WALID ya furta" Alhamdulilah, ga malan nan zai zo wajenka, ka ce masa na SAMEKA kawai, mu hadu a gidan Baba Hamza nan da awa daya plz"

Mikewa Elhaji Maiga ya yi yana fadin" Ok ok Tom shikenan ganinan "

Kashewa AL'WALID yayi ya juyo ya samu Elhaji Ya'u ya dawo wajen baba sunna maganarsu dai haka

Karasowa yayi ya ji Elhaji Ya'u na fadin" Dama cewa na yi in hakan ya maka fa, Ni kar ka isheni da wa'azi haba malan daga cewa Ni zan kaita dakinta?"

Baba Hamza ya nuna masa hannu ya ce" An ki a Barka ka kaitan, nace an ki a Barka ka kaitan, ina yayunta ne? su zasu tukata a hankali su kawota Ni kuma zan yi jira idan har ran ya kai bayan magariba in kaita dakinta da kaina, in kuwa na mutu mijinta zai kai abinda dakinta, ku ji kai, haka kawai sai ka kawota?"

Elhaji Ya'u ya juyar da kai yana hade fuska ya ce" Kai dai sai neman mutun da fada, Ni ba zan biyaka ba!"

Baba Hamza ya dafa ya tashi yana fadin" Ka biyanin mana, bari ka gani inaga mu zamu tarda mutumen nan asibitin nan"

Elhaji Ya'u ya ce" Wani ne ba lafiya?"

Baba Hamza ya gyada kai ya ce" Yarinyar nan ce Mufeeda akace tana asibiti, to kuma mahaifinta akace wai yace zai tardoka saboda maganar auren nan nasu da Khadeeja, bari dai mu je a sasanta abin"

Aba ya yi turus yana kallon baba ya ce" To, wai uban yarinyar da suke soyaya?"

Baba Hamza ya gyada kai yana gyara hularsa zai mayar kansa

Aba ya janyo tasa hular ya kafa ya saba babar riga yace" To ai mu je kawai in kai kaina"

AL'WALID ya dan zarro ido yana kallon Aba

Baba Hamza ya dube shi ya ce" Ina zaka kai kan naka?"

Aba ya cire kai yace" Wajen nasa mana ka san alkhairin dake kirana?, mu je dama ina son in auna nauyinsa!"

AL'WALID ya dafe haba yana kallon Aba

Baba ya nuna masa hannu ya ce" Kai baka gannin sirikinka ne a gabanka? kai kam Allah ya shiryeka, ba inda zaka je, kuma in aka yi rashin Sa'a ya zo nan in na ji ka yi wani abin Allah Ni da kai ne"

Aba ya dube shi shekeke ya ce" Ka ga dai sai dai in maganin barci zan shiga likitocin gidana su maka min, ya zamo har ya zo ya tafi ban san inda kaina yake ba, in ba wannan ba ai Bama zai taba yiwuwa ba, to me hadina da shi? in yace da wani abin tsakaninmu ai sai mun warware shi tilassssss, ah kai ina!"

Ya karashe yana tafa hannayensa ya wani ja uban muzurai ya hade fuska

Lokaci daya addu'ar da yar budurwar nan ta yi ranar da ya zo gidan ta dawo masa a zuciya

Ya ringa kallon Aba yana auna addu'ar Tata, lokaci daya murmushi ya kubce masa na gasken gaske

Juyawa yayi ya karasa motar da aka bude masa ya shiga ya zauna a nutse ya kai hannunsa wajen habarsa yana duban abin motar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login