Showing 75001 words to 78000 words out of 190762 words
Chapter 26 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
babu wnada zata saurara , babu wanda zata yiwa biyayya, ana iya samo mata wani mijinma ta je ta ringa yi masa rashin mutunci ta nuna auren dole aka yi mata, barni da su"
Mama bata iya cewa komai ba, sai da baban ya dan nisa ya ce" Kuma zancen auren na Anmy ne, in sha Allah jibi za'a daura auren"
Da sauri Mama ta dube shi, zata yi magana amarya ta shigo ta dayar kofar da salama ta sha uban ado sai kanshi take yi ta karaso inda suke ta zauna tana wani iya yin nan ta ce" Elhaji Barka da safiya, yaya sauΖin jikin?"
Mama ta dauke kanta daga kanta tana duban baba ta ce" jibi jibin nan fa? ya da sauri haka ? na zata za'a bari har a je baban hutu babansu?"
Aba ya girgiza kai yana mikewa ya ce " A'a gaskiya, in sha Allah jibin dai za'a daura mata auren, ki shirya kawai ki sanar da du wanda ya dace kin ji gimbiya? bari in zo, zan je in ga malan a sa a fara saukar Alkur'ani a tarbi abin da addu'a saboda duk wani makiyi Allah ya rufe idannuwansa ya sa sai an gama komai hankalinsa zai dawo kanmu a lokacin kuwa daidai nake da kowa alkur'an a kan Anmy babu abinda ba zan ba!"
Yana fada yana tafiya ne, ya bar Mama sake da baki
Ajiyar zuciya ta sauke ta dauki wayarta ta zauna ta shiga saka numbar Hajiar Larabawa ta aika kiran ,sai dai tana ringin bata daga ba sai kawai ta yi kiran kanwarta ta sanar mata abinda yake faruwa, Mama karata tace yanzu kuwa zata shiga ta sanarwa Hajiar kuma gatanan zuwa dan su fara shiri su san abinda zasu yi na tarbar baki
Tana ajiye wayar jikinta sanyi kalau ta dubi amarya dake zaune tana kallonta
Mikewa ta yi, saboda tunda ta dawo babu abinda ya shiga tsakaninsu koda na gaisuwa ne,
Ta juya zata tafi amarya ta ja wani tsinanen tsakin da ya sa Mama dakatawa ta juyo tana kallonta da mamaki
Lalle in ba aure mai sakawa la hadu da kowace shara har ta mayar da kanta daidai da kai, me zai hadata koda maganar fatar baki ne da wannan yarinyar? ama gayanan dalilin sunna auren miji guda sai ta ringa kirta mata rashin mutunci tana kallonta
Kai ta girgiza ta sake yin gana zata tafi, amarya ta mike ta ce" Dan Allah idan dare ya yi haki na barinki ki iya rintsa ido?"
Mama ta sake dakatawa ta juyo da matsanancin mamaki ta zuba mata ido
Amarya ta rintse idannuwanta sannan ta bude ta ce" Kwana daya kacal, ko in ce wuni daya jal kika je kika yi a gidanku ama shine aka sake kulo min wata masifar da ta fi ta da, me yasa bakya tsoron Allah ne? me yasa kike so karfi da yaji sai mijina ya sake Ni ne? tashi tsayenki ya sa ba ruwansa da Ni, ba ruwansa da lamurana a yanzu an kai wajen da ko magana nake yi baya dubanna sai ke kadai, ko menene ke kadai ce mutun, ke kadai kike da daraja a idannuwansa, sai ki je ki godewa bokayenki ki kuma kara musu kudi saboda gaskiya sunna yi miki aiki, ama ki sani walahi sai na karya, ko me kike takama da shi sai na karya shi, nima sai mijina ya dube Ni, kuma duka kaf abinda kike hadasa min kema sai na hadasa maki, zaki gani in dadi ne!"
Har ta zo zata gegi mama ta wuce, Maman ta saka hannunta ta janyota gefe sannan ta dubeta ido cikin ido ta ce" Kina ji? ki ringa kiyaye shiga sabgata, saboda abubuwan dake kaina yawa ne da su, kuma dukkan abinda ya zamo na bashi mahinmanci ina yi masa duba na kirki ne, ki je cen ki karata da mijinki, wannan ba hurumina bane, sannan ki kula ba kowa ne yake yin abinda kike yi ba, harkar boka da malan ke kika sansu ba Ni ba!"
Daga haka mama ta saki hannun nata da karfi ta juya ta yi tafiyarta, dan wallahi karya matan Elhaji suke ta ci kashinsa ta ci nasu, karya suke, banza dan ita ta saba bin bokayenta an gaya mata kowama haka yake kowa bashi da aikin yi kuma baya tsoron Allah ne?
Amarya ta ringa murza hannunta da mama ta rike da karfi zuciyarta na kunna, ita gaba daya abinda ya fi dagula mata lisafi irin yadda kamar rikicin da suke yi da Aba ya yi sanyi, kamar maganar daurin auren nan yana nan ama kuma babu wanda ya san da wa sai ita sai shi, domin tun a jiya da ta zo inda yake yace mata ta tafi kawai shi zata bari a asibiti ta yi tafiyarta, ba damuwa dama ya san ita matar in ta yi dadi ne, yama gode da ta sa matar shan wahala zuwa inda yake , ama ta bashi waje bashi da bukatar ganninta idan ya huce sa zauna, da wannan haushin ta dawo dakinta ta yi kwonciyarta, kuma yau tunda safe ta yi kiran Malaminta wanda ke yi mata aiki ka'in da na'in a kan a karya asirin mama, dan ya tabbatar mata Mama bakin asiri ne take yi a kan Aba da ya'yansa da dukiyarsa, ita kam matar nan so take yi ta gagareta du yadda take tunanin zata iya kwatar gidan Elhaji da ragamarsa matar nan so take yi ta fi karfin ta, ama ba komai sai dai su kashe junna ba tashi tsaye bane? zata gani gannin idannuwanta!
Mama kuwa tana zuwa bangarensu ta samu Lubna ta gama yi mata aikace aikacen da ta sa su yi ita da Khadija
Tana nufar ciki ta ce" Ina khadijar ne kike aiki ke kadai? idan kun gama ku yi wanka ku ci abinci , ina sauran suke ne, ina zuwa"
Inda inda Lubna ta shiga yi dan kuwa sunna cikin aikin khadijar ta dauko hijabinta tace mata bari ta leka kofar gida ta dawo kafin Mama ta fito, gayanan har ta gama aikace aikacen gidan bata dawo ba
Jim kadan maman ta fito da waya a kunnenta, sai ta ga Lubna tana zurma hijab cikin gaggawa
Dakatawa ta yi tana kallonta har ta zurma ta juya zata fita
A nutse ta ce" Ina zaki je ke kuwa?"
A zabure ta juyo tana zarro ido, sai kuma ta shiga kame kame na marar gaskiya
Mama ta dakatar da kiran da take yi kai tsaye tana dubanta da kyau ta ce" Ke zo nan"
Lubna ta juyo ta zo hankalinta na karra tashi
Mama ta ce" Na ce ina zaki je?"
Lubna ta nuna waje ta ce" Mama dama cingan nace Anmy ta siyo, shine bata dawo ba zan bi sahu"
Mama ta zarro ido ta ce" Anmy? Anmy? ta fita? innalilahi yayan nan sai kun ja min abinda ya fi karfina? ta je ina? zaki fada min gaskiya ko sai na wanka maki mari?"
Lubna da sauri ta ce" Walahi Mama ban san ina ta leka ba, cewa ta yi yanzu yanzu zata dawo fa"
Mama ta dantse harshe ta nufi ciki ta shiga neman katon hijab dinta tana kuma lalubar numbar inna tsohuwa
Ringin daya inna ta daga tana fadin" Mata ku saurara in ansa kira, hello asalamu alaikum wa rahamatulah"
Mama ta amsa a tausashe ta ce" Inna, Anmy na gidanki kuwa?"
Inna ta yi murmushi ta ce" Wai y'ar albarka? ai bata fashin majalisa sai in ta zama dole, gatanan tana rabon lemu wa matan kirki mata masu rike miji da karfin ikon Allah"
Mama ta sake dantse lebenta a tausashe ta ce" To shikenan, inna ki ce mata babansu na nemanta dan Allah, ki ce mata ta san ai yana gida bai fita ba ta fita, ta gaggauta dawowa inna"
Inna ta ce" To shikenan bari in sanar mata Hajia, Ni dinma zan shigo in an jima saboda wata magana da ta zo ta sanar min ita tana murnar wai ko an fasa, Ni kuwa haka kawai nake ji a raina inama an yi, Duda bamu san mijin ba ama ina da yakinin Elhaji ba zai yiwa y'ar nan mugun zabe ba"
Mama ta gyada kai tana sake dantse lebenta, dan walahi ita kadai ta san irin dukan da zata yiwa Anmy yau a gidan nan, wato har ta je ta yi yamadidi da sirin gidan nan ko? ita dai in dai ta fice to a sameta a gidan inna, tunda aka kawo karin gayyatar zaman majalisar gidan inna ita aka kawowa , bata amsa ba dan abubuwan dake gabanta sun sha kanta, kai inama take da lokacin zuwa koyar dabarun zaman gidan miji? ai ita zama in ya yiwu a yi, in ba zai yiwu ba a watse babu abinda aya dameta, ama cikin ikon Allah Anmy ta amshi katin, kuma take zuwa, karshe ma ko sisinta ba'a amsa, har nemanta matan anguwar nan suke yi in ta kwana biyu bata je ba....., lalle yau zata zauna da Anmy ta fada mata abinda ake koya mata, kuma yau jikin Anmy sai ya fada mata
Bulala Mama ta samu ta kirki ta rike a hannunta ta zauna a falo tana jira
Ba'a jima ba Baba ya shigo da masu gyaran gida, suka duba du inda ya dace a kawo gyara komai kankantarsa suka tafi da nufin dawowa su fara aiki a yau yau
Baba ya raka su kennan ya dawo sai dariya yake yi da farin ciki ya dubi Mama a zaune a falon da amarya domin tunda ya zo ta fito ya ce" In sha Allah bana da ku za'a sake yin haji, na baku kyautar kujerar Makka Allah ya nuna mana"
Buda amarya ta saka, Mama ma ta saki murmushi tana furta" Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi ya idasa nufi...."
Daidai nan Khadija ta shigo tana rabe rabe saboda tun dazu ta shigo jin kamar Yah baba a falon nasu ya hannata shigowa, karshema sai ta tarki wanke wanke da goge gogen bango, ta cire hijabin ta daura a kugunta tana aikinta ka'in da na'in
Tana shigowa falo ta wani sune kai ta yi dan murmushi ta ce" Barka da hutawa ina baya ina wanke wanke ne ai" kamar wace aka tambayeta
Aba ya saki wani murmushi mai dadi ya ce" Allah ya miki albarka uwata, sannu da aiki ama ki daina daga yau kin ji? Allah ya karra maki albarka uwata!"
Daga Mama har amarya sai da suka kalle shi kafin mama ta cire kai
Sumui sumui ta so shigewa shegen mamaki na kamata na lamarin addu'ar nan da aka basu idan sun yi laifi su yi ba za'a dake su ba, kai wannan addu'a akoy karfi innalilahi
Mama ta mike ta ce" Kin ga Anmy amshi nan"
Khadija na dawowa tana wani sake sada kai bulala ta sauka a gadon bayanta, ta hannun da bata shirya ba, domin zasu jima Mama bata daki fatar jikin su ba, kuma bata iya duka da bulala Bama
Ihu ta sa ta gantsare tana furta" Annabi ka ceceni innalilahi wa inna ilaihi raj'une Mama me na yi?"
A zabure Aba ya mike yana furta"
07/12/2024, 15:02 - samiraharounayacouba: πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*FARKON GANIN IDONA*
πΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊπΈπΊ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*π³πͺ
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you π*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ΖAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAΖIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da biyu (22)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*ππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌππΌ
π0912 262 1080
LABARI
A zabure Aba ya mike ya nufo su, yau dai bulalar dake sauka a jikin Mama idan yana dukan yayansa, a tsautsayi ta daga zata laftawa Khadeeja ya tare ta sauka a hannayensa, ai kuwa ya yarfe ya sake yarfewa, da sauri ya shiga murzawa yana fadin" La'ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi Sallallahu alaihi Wa Alihi wa Salam ta zane Ni, gimbiya ta zane Ni"
Da sauri ta saki bulalar tana fadin" Subahanallah dan Allah ka yi hakuri me yasa ka sako hannunka, ka bari in zane mata jiki tunda na kula sun riga sun zama jakai du in ba bulala ta hau fatar jikinsu ba , basa yin hankali, ka san cewa daga waje take? daga gidan inna take wajen majalisa? ina jin ka san labarin majalisar inna tsohuwa ta anguwar nan? wace kace ba zan je ba kar a koya min rashin kunya ko? cen yarinyar nan ke zuwa, walahi yanzun nan ma daga cen take"
Khadija dake susa tana ihun saukar bulalar nan sai ta hadiye tana yiwa Mama kallon ashe zaki zamo sanadiyar mutuwata? to sanadiyar mutuwarta mana, da ta fadawa baba wannan ai gwara ta yankata kowama ya huta
Ta tatare buje tana shirin dankarawa da gudun balaki Baba ya riko hannunta yana duba wuyanta da bulalar ta sauka ya ce" Gimbiya tabas sai na yi maganinki, tabas sai na yi mummunar saba maki, ashe haka kike yi mata idan bana nan? wai dama zaka haifi Ιa ka tsana? yarinyar nan bata baki tausayi? baki ga kalar fatarta ba ta duka bace? yanzu kumatun nan da kika saka suka dauki ja kin ji dadi a ranki? sam bakya tsoron Allah matar nan, ki ce kina son zane Ni dai kika hada uban da y'ar kika daki banza, to yarinya tunda an san inda take ma ai shikenan, yawo mai anfani ne ai, kin ga wuce bangarena in zo in baki man zafi ki murza ki yi barci tunda na kula so kike yi ki gigita min ita sai ta koma dakinta na bangarena ta yi zamanta, walahi ku ji da kyau du mai dukan min y'ayana ba zan iya yafe masa ba, wannan ai balaki ne, gimbiya mun gode Allah ya saka da alkhairi!"
Daga gimbiya har amarya baki sake suka raka shi da kallo har sunna kallon junna abin tausayi basu ankara ba tsabar firgicin birkitacen mijinsu
Ya kama khadija da ta yi sumar tsaye har tana karra duban fuskarsa da kyau dan ta gane wai ko dai ba a hayacinsa yake ba, sai dai cikin ikon Allah garas yake suka yi bangarensa sai sake fadi yake yi" Kin ga hannuna ya dau ja nima, gimbiya ashe haka take da zafin hannu? Allah ya taimakeni ba mace ce mai rama duka ba ai da na ji jiki subahanallah haka take dukan ki?"
Khadija ta yi wani kiskirim a zaune saman kujera, kana gani ka san a darare take, har ya fito da man zafin ya miko mata yace ta murza
Ta kuwa murza din ya ce ta je dakinta na bangarensa ta yi kwonciyarta
A raunane ta ce" Babanmu, zan je wajen aunty Lubna in har ba zan bata maka rai ba"
Ta fadi haka tana dan ja baya, dan ta tabbata yanzu zai kawo mata mari , dan cewa zai yi tama raina masa wayo,
Ga tarin tashin hankalin damuwarta sai ta ga ya wani yi mata murmushi, murmushi jama'a sannan ya ce" Je ki tunda cen din kika fi so, tafi ki huta in an jima sai a kawo maki kaza ki ci in kina so, idan kin ga zata dake ki zo ko sanarwa babanki Ni zan ja da Gimbiya bata isa ta gigita min zaman lafiyarki ba"
Khadija ta yi tsuru tsuru, da kyar ta ja kafarta ta fita
Tana kusa da dakinsu ta fashe da kuka ta bude ta shige ta karasa inda su Lubna suke, ita da Karima da Ummi sunna fira
Du a tsorace suka kalleta da sauri Lubna ta shiga neman hijabinta ta ce" Yar banza ta dawo zata ja ya haΙa har mu ya ci ubanmu, idan ya gama dukan namu sai na rama Anmy, walahi sai na rama a kanki"
KARIMA ta fashe da kuka tana kallonta ta ce" Yanzu Anmy ki janyo maganar ko rasa inda zaki je sai dakina bayan kin san ya tsane Ni yanzu? ko so kike yi ya kashe Ni?"
Ummi kam tuni ta shige karkashin gado tana cin alwashin idan duka ya sameta sai ta rama a kan Anmy
Khadija ta ja tsaki tana zaunawa ta ce" Dilla kai ku tsaya ku ji, walahi babanmu ya kusa mutuwa, innalilahi ta yiwu a yau ko a gobe mu zama marayu"
A tsorace Lubna ta ce" Innalilahi, bashi da lafiya ne? yanzu fa muka jiyo muryarsa da su Mama a nan coridor da masu gyaran gida fa"
Khadija ta yi dan tsai ta ce" Gyaran gida za'a yi? lafiya?"
Lubna ta dungure kanta ta ce" zaki fada mana dalilin kukan ki ko sai mun rufun miki mun jigata ki?"
Khadija ta girgiza kai ta ce" A'a, ku rufawa kanku asiri, anya a kaina yanzu Aba ba sai ya daki d'a da babarsa ba? koda yake ta yiwu kuma yana son naku yanzu, Ni dai abin ya bani tsoro ya dace mu fara binsa da adu'ar samun sasauka, dan kuwa da gani aba an kusa , ke wai fa hannuna ya rike yace kar a kuma dukana bayan an sanar masa daga