Showing 159001 words to 162000 words out of 190762 words

Chapter 54 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4006

ya irga uku a cikin hudun da zaman gidan nan bai zame musu dole ba ya fito masa da su, a sume ko a hayacinsu, ama shine Sadik ke tafe a nutse dan uban babansa kamar yana curt?

Dawowa yayi fuuuuuuuu ya tankada keyarsa sama sama ya ce" Habu ubanka, zaka daga kafa ko sai na ci uwaka gimbiya a gidan nan? Dan ubanka sai sun kashewa anmy aure zaka san balaki ake shirin hada min a ciki? Dan ubansu to kukan da suke tayata na ba zasu fito ba na wani munafurcin ne? Ka sanar da su, su fito ko in shigo na rantse sun san Dukansu a nesa da gimbiya ba karamar azaba zasu sha ba yan kundun uba kai!"

Da gudu yaya Sadik ya shige get din farko yana shasheka, daidai baba Hamza ya zo yana fadin" Duka? Yau da an daure mu daga Ni har kai dan WALAHI kakarsu tace in sanar maka idan ka daki jikokin ta ba zata kyale ka ba, kuma ka dai ga a fusace take"

Aba ya kalle shi shekeke ya ce" kai fa kamar tsoron marar cen kake ji fa ko?, mu je mu dake sun a yi abinda za'a yi"

Baba Hamza ya girgiza kai ya ce" mu dai je mu rarashe su, haka kaima"

Da mamaki ya kame haba ya ce" A yi haka? Ai da kunya in shiga gidan anmy in ji gimbiya "

Baba Hamza ya girgiza kai dan takaici kawai ya nufi ciki yana fadin" Ai sai ka yi"

Aba ya wani wawaiga sai kuma ya shiga bin bayan baba Hamza a ransa yana ayyana ' ai bata nan , idan ta ji kuma ƴaƴanta suka fada mata zai daki hancin yaro ne, shi ba shashasha bane ehe !'

Samun su yaya Sadik yayi sun yi shiru da kukan, kowace kumatunta sun mata ja, sunna zaune kawunansu a kassss, AL'WALED na murmushi saboda amsar da khadeeja ta bashi da ya tambayi ba'asin kukan bayan ya sa sun yi shiru tace Karima ce ke kuka kuma ta ki fada musu abinda aka yi mata

Salama yayi, suka gaisa da AL'WALED da kula saboda sun san junna sosai tun daga ranar daurin aure, sannan ya karasa daf da su ya duka kasa kasa ya ce" kwa ci ubanku ne, zaku yi na kirki kukan ga ɗan larabawa cen shigowa, in ba masifa ba ku ba zaku yi abinku ku kadai ba sai kun sako wani a ciki? Du y'ar da ta ja min duka sai na rama a kanta ne!"



47
07/12/2024, 17:29 - samiraharounayacouba: A tausashe sosai ya ce" Yi hakuri kakan kurma, babu fa wanda ya taba maka uba, shine dai da rigimarsa"

Aba ya girgiza kai ya ce" Elhaji tabbas an taba min shi, kuma jikkata ba kurma bace"

AL'WALED yayi murmushi yace" to a yi hakuri, Allah ya huci zuciyar kakan litle, ce masa ya tashi mu je bangarensa dan gaskiya kamar yau rikicin nasa mai girma ne sosai kuma bana so"

Aba ya turo baki yana harare harare ya karasa ya kama baba Hamza ya mikar da shi yana fadin" ko in goyaka ? Ni kam da an bamu dama mu ba wace ta ki shan maganin nan magani dan bana son du wani abinda zai hada shi da lumshe lumshen nan"

Shi kam murmushi kawai yake yi yana biye da su a nutse suka wuce ɓangaren Baba hamzan tare


A dakin HAJIA Inna kuwa khadeeja bata saki hannunta ba, haka HAJIA Binta na zaune daf da ita bayan ta gama yi mata kuka da rantsuwar sai ta amshi magani sannan a tausashe ta ce" In dai shi din kike so mu yiwa rikici ai ba da lafiyar ki zaki yi mana wasa ba, ki sha maganinki idan ta kama mu gudu mu buya wani wajen zamu gudu, na san me yake damun ki na san cewa dama akoy ranar da zaki gaza kawar da kan da kika jima kina yi a kan gaskiyar ki, ki yi hakuri yar uwata"

Khadeeja ta yi mamaki matuka da gannin wannan lamari, dama wai akoy abokan zaman dake yiwa junna magana irin haka har ya zamo furucin bakinsu abin daɗin sauraro ne saboda fitar amonsa dake tafe da kauna da mutunta junna? Ikon Allah, to ai su a gidansu ko su ga ana gaba da junna ko kuwa su jiyo maganganun da suka saka suka gama yarda cewar kishiya masifa ce daga nan ba ragi ba kari, domin har fata suke yi a tsakaninsu cewar idan sun yi aure Allah ya sa mazansu ba irin mahaifinsu bane daga su kar ya karra musu wata wace zata fitine su ta hanna musu zaman lafiya a cikin gidan auren su

HAJIA Inna kam ajiyar zuciya take saukewa har doctor ya zo, ta kuwa amince din ya dubata sosai sannan ya bata magani bayan ya sake yin nasiha a tausashe wace zata saka hankalinta ya kwonta harma ya yarda ya danka magungunan a hannun khadeeja a lokacin da ya gane cewar likita ce , likitar ma mai baban mukami

Sunna nan tare da ita har barci ya dauke ta bayan ta sha maganin saboda yana saka barci ne, sannan suka gyara mata komai suka fito

A nutse khadeeja ke biye da Mama b, har suka zo baban falon inda suka tardo mutanen gidan du a falon sun yi jigum jigum sunna jira

Murmushi ta yi bayan du sun hada baki kan masu tambayar yaya jikin sai masu tambayar ko ta yarda likita ya ganta?

A tausashe HAJIA Binta ta ce" Alhamdulilah, har ta samu barci, ku tashi ku je ku yi shirin sallar nagariba lokaci ya matso , SHAREEFA ke ki zauna min in je in kimtso in dawo , sannan ki sake ba y'arki magani itama jikinta fa da zafi kuma Please idan na zo sai a rakata ɓangaren ta huta, bai dace tun yau ta hadu da dagawar zuciya irin haka ba"

Du yan matan da samarin gidan suka wuce sunna yiwa HAJIA Inna fatan samun lafiya aka bar aunty shareefat kadai da khadeeja, wa'inda suka dauro alwallar suma suka gabatar da sallar a nan aunty shareefat na jira HAJIA Binta na zuwa suka mike dan ta raka khadeeja bangaren ta saboda ta huta

A nutse suka koma bangaren nata, tana jin irin yadda kaf gidan ke kanshi, suka karasa falo sunna amsa sannu da zuwan da maman baby ke musu ana jere musu abin sha da na ci

A nutse aunty shareefat ta fuskanci khadeeja bayan sun zauna a falonta ta ce" Daughter, Ni in ba dan kin gaji sosai ba da mun yi magana mai mahimmanci"

Khadeeja da har Muryarta ta yi laushi sosai ta ce" A'a Mama, muna iya yi ban gaji ba"

Aunty shareefat ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" ban san ko idan na fada maki abin nan zaki ga kamar abin bai shafe ki ba, ko kuwa ki yi tunanin a kan me zan fada maki? Ni da kaina zan fada maki abinda tunda baba Hamza yayi mana kashedin ko da wasa baya son zancen a gidansa muka haka rami muka birne maganar , wato a yau zan taka dokar nan saboda na fuskanci tabasss zuwa gaba abin na iya neman fin karfin mu , dan ina tsoron fushin wanda baya fushi, haka kuma ina tsoron maganganun ta saboda gaskiya ta fada, zan sanar maki abinda yake faruwa tsakanin mijinki da mahaifiyarsa da kakansa.....ta yiwu ke ki iya yin wani abu a kai domin ko ba komai kusancin mace da miji ya fi karfin wasa"

Khadeeja ta sauke ajiyar zuciya tana yiwa Allah godiya da ya sa zata ji abinda take son ji din nan cikin sauki ba tare da ta jigata da neman hanyar da ta dace ta fara bi ba, dan kuwa ta sani in ba sani din ta yi ba bata da wani abinda zata iya yi, kuma ba'a yi sabon da zata budi baki ta ringa musu tambayoyin nan, shi din da kansa wuni ta yi tana tunanin shin idan har ta nemi shiga lamarin nan ba zai iya taka mata birki mai tsananin gaske ba? Duba da ko auren su ai na hadi ne bale tace son da yake yi mata ya isa ya sa ya saurareta koda baya so, abu daya ta sani ba gudu ba ja da baya dole sai ta dauki matakin da ya dace a kan lamarin

A tausashe sosai ta ce" Shekarun da suka shige, kusan shekara talatin da tara kennan a lokacin da ran baban yayanmu ɗan gidan HAJIA Inna, wanda shine namiji daya tall a cikinmu, har yanzu kuwa da aka yi aura Khaleesat Allah bai kawo wani namijin ba, ........., Khadeeja kin san shakuwa kam dole za'a samu tsakanin marigayi da baba Hamza, sun shaku sosai da sosai shakuwarsu a bayyane take khadeeja, akoy soyaya mai tsafta da biyayya a lamarin wanda ya sa Baba ke daraja duk wani abu da ya shafi yayanmu....."

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Kin san jarabawar bawa babu irin yadda bata zuwa, a lokacin da Allah ya bashi matar aure sai ya jarabeshi da mace mai tsananin kishi, kishin da ya kazanta, kishin da ya wuce gona da iri...saboda khadeeja a lokacin da baiwar Allahn nan ta shigo ahalinmu hatta shakuwar dake tsakaninmu da shi sai da ta nuna bata san zancen ba, ina hadin mace da namiji duniya ta riga ta rikice kawai idan ya zo sanunsa in baya nan a yi hakuri banda kiraye kirayen waya da bin sawu da nufin ba'a ganshi ba an zo a ganshi ne......wannan lamari ya gigitamu Daughter am, saboda a lokacin shi daya ne namiji a cikinmu, shine yayanmu kuma ya ja mu a jiki fiye da tunanin ki, Bama kamar Ni, saboda du irin yadda take korata idan na nufi inda suke bana iyawa sai na buya ya fito, idan ya ganni yayi ta masifa , dan a kaina ya taba yi mata saki daya saboda wani lokaci da ta mareni ta zageni bata san tare da shi muka zo gidan ba ya ji komai ya ga komai"

Ta sake sauke ajiyar zuciya ta ce" shi yasa ake so, ko me bawa zai yi ya ringa sasautawa, domin duk abinda aka ce za'a zazafa sai an ga ba daidai ba Khadeeja...."
Kwalar dake idannuwanta ta share Muryarta na rawa ta ce" Babu abinda bai tsare mata na zaman duniya ba, ci, sha, sutura , bukatun badangarci na yau da gobe wa'inda suka zamo gishirin zaman rayuwa domin yana son matarsa shima, duda irin yadda ta fita a ran iyayenmu mata harda mazan , karshe ta sa Baba ya zuba mata ido saboda fitintinun da ya budi baki wani lokaci yayi mata nunin ta kama kanta, idan aure d'ansa yayi niyar yi zai yi ne, ya zamo a hankali ta fara yaki da baba ta hanyar kauce duk wani abu da zai hada su, ta dauke duk wani kokari dan girmamawa da samun zuciyar baba, ta sake ninka fitintinunta na tsananin kishinta, ya zamo ta yi da yan gida, ta yi da yan anguwa, ta yi da yan office, duk wani wanda ya ratsa duniyar mijinta in ba HAJIA Inna bace sai ta nuna cewar mijinta za'a so.....sannu sannu karamin abu har ya giga ya zama katoton da lokaci ya kure har mai aukuwa ta auku....."

Aunty shareefat ta lumshe idannuwanta hawayenta ya tsananta , ta bude baki ta ce" Khadeeja, ki kiyayi mugwayen kawaye, ki guji duk wata hanya da za'a ce a bi da karfi a samu biyan bukata, kin ga idan kika rike Allah WALAHI sai dai a daka a bari babu yadda aka isa a yi da ke, kuma bukatunki a wajensa ne kawai zaki samu su biya cikin salama....., khadeeja muna rayuwar lafiya lafiya yayanmu ya so wata yarinya a lokacin ya so aurenta ko Allah zai sa matarsa ta daina abinda take yi ta nutsu, saboda a lokacin AL'WALED fa shekarunsa shida , ama ta kasa dainawa kuma tun haihuwarsa Allah bai kawo wani cikin ba, ko shi yasa ta daure ciki yake tafka ba dadin nan?, ke dai magana na fitowa fitina ta tashi, tashin hankali, wulakanci, rikici, duk wani nau'in balaki sai da ta sauke ko an janye maganar, ama aka ki janyewa, karshe sai ta afka tashin hankalin bin malamai dan a kade abin domin ita fa abinda ba zata taba yarda da shi ba kennan shine a yi mata kishiya!"

"Khadeeja, kin san irin yadda duniya ta rikice, bale a lokacin sosai yayanmu ke karra samun budi, dukiya kuwa kin san dama tana tafe ne hatsari kala kala, a cikin abokan nemansa aka samu wanda ya shiga rigar boka , ya san hanyar da ya bi ya samu yardarta har ya ringa bata karamar gubar da tunda ta fara sakawa yayanmu a abinci ciwo ya sako shi gaba, a hankali a hankali har aka kwonta, abu ya ki ci, ya ki cinyewa sai karra gaba yake yi, ga wani irin amai da yake yi mai baki baki, hakan ya sa likitoci karkata binciken su kan guba duda baba Hamza ya ja ya tsaya cewar babu rami me ya kawo zancen rami? Domin shi baba din ya hanna yayanmu cin abinci a waje, idan ba na hannun matarsa ba to kuwa sai na hannun Hajiya Inna ko mama b, daga su ba'a bashi kowani abinci Daughter am....."

Aunty shareefat ta idasa tana sakin kuka a hankali ta ci gaba da fadin" ashe ba'a isa a zagaye abinda Allah ya kadartowa bawansa ba? Ashe shi yayanmu hannun da ake gannin ba zai taba ciyar da shi wani abin ba shine ke bashi guba?, a lokacin da aka tsare abinci in ba na asibiti ba sai wanda ita kadai ta yi ne aka gane, wai ace yana asibitin a kwoncema bata hakura da dan tsakura maganin mallakar da boka ya bata ba a zuwan ta malake mijinta sai ita sai duniyarta a duniyarsa?, ashe bata san cewa bokan nan Bama boka bane ba? Rana daya aka gane abinda ke boye, a lokacin ne kuma da aka titsiyeta hankali tashe ta fadi abinda yake faruwa harma ta warci abincin ta ci tana fadin yaya za'a yi ta bashi guba? Sai dai ita nata karfin jinnin bai kai nasa domin a nan ta yanke jiki ta fadi har sai da ta sha karin ruwaye daban daban ta dawo hayacinta........."

"Khadeeja, tun daga lokacin KHADEEJA ta fita hayacinta, tun daga wannan lokacin ta idasa firgicewa saboda tashin hankali, ta gaza yarda cewar guba ce take ba yayanmu ba, gashi inda tace take gannin bokan an je komai ba'a samu ba dake nunin an taba rayuwa a wajen, bincike ake yi ba ji ba gani hakan ya sa ita dinma idannuwan hukuma ke kanta, ga tsangwama da tsana daga wajen mu baki dayanmu, ba'a maganar Baba hamza dan a lokacin da ace ba'a yi da gaske ba sai dai yayi kason ranta......, bamu tana shiga tashin hankali irin na lokacin ba, KHADEEJA bata taɓa shiga tsakanin mutuwa ko rayuwa irin na lokacin ba, kuma ina mai tabbatar maki daga lokacin bata kuma samun nutsuwar zuciya ba har zuwa yau, domin an hannata gannin d'anta, an hannata gannin wanda mu sheda ne so din nan fa tana yi masa mai tsananin gaske, ta rasa dama a wajen danginta, sai ya zamo ta shiga tsaka mai wuya mai wutar fasara"

Aunty shareefat ta fuskanci khadeeja da kyau ta ce" kin san me yasa na baki bayanin nan tun daga farkon sa?"

Khadeeja ta girgiza kai tana duban aunty

Aunty shareefat ta ce" saboda ki fahimceni da kyau, domin saura kwanaki biyar yayanmu ya bar duniya Allah ya bashi sauki irin sauƙin da yawanci masu jinya ke samu idan lokacin tafiyar ya matso, domin har zaunar da shi aka yi, ya sha madarar da baba ke bashi da kansa, a lokacin gana dayanmu muna dakin nan, a gabanmu ya nemi izinin baba ya bashi dama ya ga matarsa, da baba ya kiya ne yayi furucin da ya sa Baba dubansa ya kasa magana, har HAJIA Inna ta je da kanta ta janyo hannun Khadeeja ta kawo ta dakin, a gabanmu bayan ta duka gabansa tana kuka ta sanar masa komai da yanayin mutumen nan ya lumshe idannuwansa a sanyaye yayi mata nasiha sosai da sosai , khadeeja a gabanmu ya mika mata hannu ta je inda yake ya rike hannayen ta ya janyota jikinsa , a gabanmu ya furta mata kalmar yafiya, shima ya nemi tata yafiyar, khadeeja ya yafe mata laifin da aka bi ta kanta aka aikata, kuma ya fadi sunan mutumen wanda har yanzu yake rufe a gidan kaso, khadeeja tun daga lokacin matarsa ke gefen sa, du irin fushin da baba ke ciki bai iya hannawa ba, saboda a hankali jikin ya karra rikicewa lokaci ya tafi har mai aukuwa ta auku....., yayanmu ya rasu..., rasuwar da ta kasa fita daga ran Baba, saboda a lokacin da aka kai yayanmu gida bayan matarsa ta farfaɗo kamar zata yi hauka tana kuka kamar ranta zai fita, a lokacin ne kuma baba Hamza ya yi mata iyaka da gawar mijinta, tana ji tana ganni aka tafi da mijinta gidan gaskiya, bayan an yi kwana uku tana zaune a falo zata ba AL'WALED abinci baba ya shigo falon ya kwabe abincin, a lokacin ne ya yanke mata hukuncin da ya shiga tsakaninta da d'anta"


"Daughter am, a lokacin ne baba ya sanar da ita ba ita ba abinda ta haifa da cikinta, a lokacin ne ya raba hannayensu, ya nuna mata kofa bayan ya kwashi takardun dukiyar mijinta kaf ya watsa mata , ya sanar da ita bata da wani muhalli a duniyarsa da ta jikansa, A ranar ne kuma aka kamata , aka saka mata ankwa aka kai aka garkame, bayan doguwar Shari'a aka yanke mata hukuncin kaso na shekara goma sha takwassss da diyar dukiya , shi kuwa wanda ya bata abin aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai..........."

Aunty shareefat ta dubi khadeeja da hawaye ke bin kumatunta a sanyaye ta ce" KHADEEJA, tabbas maganar HAJIA Inna gaskiya ce, idan aka yi wasa wace ake yiwa jifan mai laifi na iya tsira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login