Showing 165001 words to 168000 words out of 190762 words

Chapter 56 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3971

ya bata musu rai

Karima a sanyaye ta ce" Mama, baban namu ne kike zagi haka? Kin san ai ba zasu iya jurewa ba ko mama? Haba mama"

Mamanta ta zabga mata harara ta ce" ke dan Allah rabani da gafalalun yan uwan nan naki yan bakin ciki, kin san ai ba tsoronsu nake ji ba bale in kasa fadin gaskiya, Ni yanzu maganar da nake so mu yi da ke a kan wannan auren da aka kwace a hannun ki aka ba wancen y'ar gidan jajayen mahaukatan, kin yi tunanin abin yi ne ko shima sai na maki?"

Da mamaki ta dubi mahaifiyar Tata da kyau sannan ta dubi kakarta, a hankali ta ce" Mama ban gane ba"

Kakarta ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya ta ce" ke kya fada, ai lamarin uwarki ba karami bane, sai fatan Allah ya rage wahala"

Rai bace ta yabuwa ta ce" kin ga dai iya ba da ke nake ba, ke Karima dubeni nan, kin san dai ba zama zaki yi kina ji kina gani khadeeja na aure a gidan nan tana auren elhaji AL'WALED ke kuwa a hadaki da wanda bai taka kara ya karya ba ko?, dan a wulakancin ubanki yana iya baki yaron shagonsa dan kawai ya wulakanta Ni ya nuna min iyakata"

Karima ta yi wani sakalau, kafin ta ce" To mama ko wa aba ya zabi yanzu ai sai mu masa biyayya, kin dai ga rashin yi masa biyayar abinda ya janyo, bayan wannan Mama ai anmy haka Allah ya tsara itace matar elhaji AL'WALED din, Ni yanzu kin ga adu'a nake yi Allah ya sa a min zabin alkhairi mama, Ama ina ga kamar mudansir ne za'a bani saboda ko jiya sai da Mama ta min tambayoyi a kansa"

Rai bace maman Karima ta ce" Ki yiwa Allah ki min shiru da maganganun rashin sanin ciwon kai irin naki, ke in ba nemawa kai balaki ba yaron da akace dan iska ne shine zaki wani ce shi? To ko ubansa waye a gaban mai aikin gidan elhaji AL'WALED bale shi elhaji AL'WALED din ? Ke ki saurareni da kyau, ba zaki taba auren yaron nan ba na fada maki, elhaji AL'WALED zaki aura "

A zabure ta dubi mahaifiyarta, Muryarta na rawa ta ce" mama, to ko dai Ni ba y'ar baban mu bace?"

Iya ta juyar da kai tana share hawaye ta ce" sai ki bata amsa, sai ki amsa mata, ko dai ita ba jinninsa bace? Saboda maganganun ki kamar na mahaukaciya ko kuwa wace bata je islamiyya ba, ke ko baki je islamiyya ba ai kin san a addinin musulunci yan uwan junna basa auren miji daya in ba daya ta rasu dayar ta maye gurbin yar uwarta ba?"

Rai bace maman Karima ta mike ta kama hannun Karima suka shiga ciki, a tsaye ta dubeta ta ce" Karima ki dubeni da kyau ki saurareni, na tabbata elhaji AL'WALED ba zai dubi yarinyar nan a yanzu ba, saboda ta yi kadan ya dubeta har ya haɗa shinfida da ita a yanzu, idan har kin yi abinda nake so da ke to kuwa y'ar uwarki zata kada duniya ke ki maye gurbin ta, Karima ke Ni fa sai kin shiga gidan nan da ranta ko babu, kece matarsa, ke aka fara ambatawa ba ita ba, tsafin uwarta da bin bokaye da kisa ne ya sa ta cusa y'arta ke aka mayar da ke gefe ake son hadaki da ɗan dan isaka a cuceni, ke kadai nake da ita a duniya WALAHI sai kin auri mai kudi, ga wannan wayar da na ajiye maki, karama ce na siyeta na saka maki layi , ki boyeta a jikin ki kar ki yarda a sani, Karima na tabbata elhaji AL'WALED irin namijin da kike so ne, ga tsayi, ga kyau, ga kwarjini, ga dukiya, ke ce kika ce cencenci jan ragamar gidan nan ba wancen yarinyar ba , kin fahimta?"

Yadda ka san wace aka kumcews nitikan kai haka Karima ke kallon mamanta har Muryar Abubakar ta karade gidan yana fadin" Karima zamu wuce fa, idan kin gama kya biyo mu"

Wani ashar mamanta ta lauyo tana fadin" dan banza mai mugun hali ai ka bari mu yi magana , gatanan fitowa "

Shi dai ya yi tsaye yana kallon dakin har ta girgiza Karima tana fadin" kina jina kuwa?"

Karima ta yi luuuuuuuuuu kamar zata fadi, ta rike kofa da kyar sannan ta gyada kai

Mamanta ta yi murmushi ta ce" yauwa yar lelena maza wuce ku tafi zan yi kiran ki in kara baki bayanan da suka dace, ki tabbatar da tun yau kin fara abinda ya dace dan fitar da wancen y'ar nacin, yau yau zan je ƙauyuka neman taimako maza jeki kar su tafi su barki su hadaki da wancen marar adalcin mai zabuntar ya'yan "

Da kyar take daga kafarta ta fito ta nufi inda Abubakar ke tsaye yana kallon yannayinta

Gaba ta yi ta fito ta karasa wajen motar ta tsaya ta kasa shiga, har sai da Abubakar din ya bude mata motar yana kallon ta ya ce" ki shiga mana"

Kai ta jijiga ta daga kafar da kyar ta shiga , ya rufe motar ya shiga ya ja su, yana tafe yana kallon ta ta madubi yana sake sake a ransa, yan uwanta kuwa da suka cika da haushin tsayar da su din da ta yi sai suka saki gannin yannayinta, ama sun yi mata dukkan tambayoyin da suka dace ta ki basu amsa sai kawai suka yi shiru sunna kallon hanya

Sun iso lafiya ya saka motar har ciki suka sauka sannan ya fito ya nufi shagon mahaifinsa dan ba shiga zai yi ba shi

A falonta baba suka same su, harda mama fateema bata tafi ba saboda mai kitso da kunshin da ta zo da su ake yanyatsarawa y'ar Tata duda yannayin galabaita da ta sameta a ciki na bakuwar rayuwa da rashin sabo da abu, bai hanna ta sa ta sauko an shiga yi mata kitso da kunshin ba, bayan ta yi mata shayi mai kauri ta bata magani sai kawai aka shiga yi mata shiri irin na amaren a yau.

Ba ƙaramin farin cikin gannin yan uwanta ta yi ba, har sai da suka yi hawaye da suka rungume junna suka kasa sakin junna , wannan ta taɓa kumatunta, wannan ta taɓa hannayenta , idan wannan tace ta rame sai wannan tace ba wani ta dai karra haske ne kamar zabaya, har sai da Mama fateema ta sa suka zauna sannan aka ci gaba da kitson a tsaye , wato mai kitson ta mike tsaye ta ci gaba da kitsawar , su kuwa sunna tayata tufke jelar kitson ko a gama da wuri sai hakuri suke bata na rakin da take yi cewar zafi kitson

Karima a zaune take a tare da su, sai dai gaba daya bata tare da su

Yarinyar kamar bata cikin hayacinta ne, du ihun da suke sai dai ta saki murmushin yake wanda ya sa mama fateema lura da yannayinta har ta yi mata tambayar ko bata da lafiya ne? Nan su lubna suka sanar mata kalau take, daga gannin jikin mamanta dai suke ta yiwu ko jikin maman nata ne, da wannan suka jajanta mata da bata hakuri , Ama ina ita gaba daya kwakwalwarta a hautsine take bata gane komai

Kasancewar kitso ne na kwarariya kuma mai sauri zuwa karfe biyu tuni an gama kannanun kitso yasss tamkar an yi su da allura, mai kunshi kuwa dama ta jima da gama daura mata dan itama akoy sauri kuma ga mama fateema a gefe na tayawa hakan ya sa suka gama aka saka mata matashi ta ringesa kadan suke shan fira da sisters dinta domin Mama fateema ana gama komai suka tafi da masu kitson da kunshin zata mayar da su da salamarsu da AL'WALED ya bari tun kafin ya fita , ta sanarwar khadeeja zata sake duba jikin hajia Inna da na baba Hamza kafin ta wuce

Firarsu suka ci gaba da yi, khadeeja dake ta hankalice da yannayin y'ar uwarta a tausashe ta ce" mimi what hpn? Shirun ki yayi yawa, kuma sun ce maman gidan iyar a zaune kuka sameta, baki da lafiya ne?"

Sai da ummi ta tabbata ta zabura ta kalle su ta ce" na'am?"

Kallon junna suka yi da mamaki, khadeeja ta ce" baki da lafiya ne?"

A hankali ta girgiza kanta, sai kuma ta mike tana fadin" Lubna mu tafi, kaina ke masifar ciwo"

Da mamaki lubna ta ce" da tsakiyar ranar nan? Kanki kuma?"

Khadeeja ta dago tana dubanta ta ce" ke wai lafiyarki kuwa? Bakya gannin yadda jikin ki ke rawa ne?"

Karima ta koma da sauri ta zauna ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da wani matsanancin kuka jikinta na rawa sosai

Har rigaye rigayen zuwa inda take suke sai da lubna ta tunawa khadeeja kunshinta sannan ta dakata jikinta na rawa

Lubna Muryarta a raunane ta ce " Menene? Dan Allah fada mana menene?"

Karima sake hade jikinta take yi ta kasa magana sai kukan da take yi , kawai sai suka hade suka shiga yi su dinma, kuka na gaske ba na wasa ba

Du yadda maman baby ta so rarashinsu abin ya gagara sai kawai ta fice ta nufi bangaren hajia Inna dan ba zata iya kallonsu a haka ba

Zuwan ta bangaren hajia Inna ta samu Aba da AL'WALED da baba Hamza a zaune sunna tattaunawa, hajia Inna kuwa idannuwanta a kulle tunda suka shigo bude idannuwan bata yi ba bale tace da su Ku ci kanku

Baya ta ja dan gannin bakin dake dakin, sai dai tuni baba Hamza ya ganta da kula sosai ya ce " Maman baby ce? Shigo mana, "

Jin haka ya sa hajia Inna bude idannuwanta tana dan juyo da kanta barin da maman babyn ta shigo ta duka tana gaisar da iyayen dakinta

Da kula ya ce" Ya aiyuka ya uwar dakin naki? ALLAH ya baku hakurin zama da junna , ina fatan yau dai ta ci abincin ko?"

Maman baby ta yi murmushi ta ce" eh baba yau ta taɓa ai da yake muna da baki Masha Allah a bakinta suka ringa bata ma,"

Sai ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce" Dama hajia, hajia karamar ce da yan uwan nata suke kuka ban san menene ba, na yi na yi dai na gaza basu hakuri shine nace ko a fadawa Maman elhaji karami? " (Wato aunty shareefat)

Hajia ta kalle ta da kula ta ce" Kuka? Ko cewa suka yi zasu tafi?"

Aba ya dubi baba ya fi a irga yana ta so ya ji wai su waye ke kukan ne? Ama abu ya gagara, sai da AL'WALED ya kasa jurewa ya mike yana fadin" Bari in gani, idan kukan kar su tafi ne ai sai kakan kurma yayi hakuri dan gaskiya ba zasu tafin ba"

Yana fada yana ficewa ne, hakan ya sa aba zarro ido a fili ya ce" ji wata jaraba to kukan na uban menene ni ? Oh ya'yan nan idan ba ubansu na ci ba du kansu a tukunya? Ina zuwa"

Sai kawai ya mike ya fice da saurin tsiya, ko baba Hamza bai saurara ba bale hajia Inna da ba'a jin maganar ta da kyau sai an nutsu

A hankali hajia Inna bayan ta turo baki ta ce" ka ga ka je ka hanna d'anka gigita min jikoki, na fada maka idan ya yarda ya dakar min jikoki ni da shi ne, shi da ba'a girma a gidansa, Masha Allah a jikin KHADEEJA ina wajen duka in ba fitina ba?"

Baba Hamza dake neman sulhu ya mike yana fadin" To to bari in ja shi mu je waje ma, Allah ya baki hakuri, ki sha maganin dan Allah, zamu yi maganar na maki alkawari kuma zan yi adalci a maganar"

Hajia Inna ta tabe baki shi kuma yayi murmushi ya fice yana fatan samun saukin rigimar nan a wajen Allah, sannan kamar yadda suke ta dauki na dadi da kakan kurma yanaga ya zama wajibi ya dubi lamarin, ya zama wajibi ya yi hakurin nan, ya zama wajibi ya ba AL'WALED dama ya fuskanci mahaifiyarsa, shi sai dai Allah ya musu hisabi dan baya jin ko a yanzu ya yafe mata raba shi da gudan jinninsa da ta yi a kan ganganci da son zuciya irin nata.


Aba ya juyo ya kalli Sadik ya fi a irga tunda ya janyo shi cikin gidan yace da shi maza ya shiga ya irga uku a cikin hudun da zaman gidan nan bai zame musu dole ba ya fito masa da su, a sume ko a hayacinsu, ama shine Sadik ke tafe a nutse dan uban babansa kamar yana curt?

Dawowa yayi fuuuuuuuu ya tankada keyarsa sama sama ya ce" Habu ubanka, zaka daga kafa ko sai na ci uwaka gimbiya a gidan nan? Dan ubanka sai sun kashewa anmy aure zaka san balaki ake shirin hada min a ciki? Dan ubansu to kukan da suke tayata na ba zasu fito ba na wani munafurcin ne? Ka sanar da su, su fito ko in shigo na rantse sun san Dukansu a nesa da gimbiya ba karamar azaba zasu sha ba yan kundun uba kai!"

Da gudu yaya Sadik ya shige get din farko yana shasheka, daidai baba Hamza ya zo yana fadin" Duka? Yau da an daure mu daga Ni har kai dan WALAHI kakarsu tace in sanar maka idan ka daki jikokin ta ba zata kyale ka ba, kuma ka dai ga a fusace take"

Aba ya kalle shi shekeke ya ce" kai fa kamar tsoron marar cen kake ji fa ko?, mu je mu dake sun a yi abinda za'a yi"

Baba Hamza ya girgiza kai ya ce" mu dai je mu rarashe su, haka kaima"

Da mamaki ya kame haba ya ce" A yi haka? Ai da kunya in shiga gidan anmy in ji gimbiya "

Baba Hamza ya girgiza kai dan takaici kawai ya nufi ciki yana fadin" Ai sai ka yi"

Aba ya wani wawaiga sai kuma ya shiga bin bayan baba Hamza a ransa yana ayyana ' ai bata nan , idan ta ji kuma ƴaƴanta suka fada mata zai daki hancin yaro ne, shi ba shashasha bane ehe !'

Samun su yaya Sadik yayi sun yi shiru da kukan, kowace kumatunta sun mata ja, sunna zaune kawunansu a kassss, AL'WALED na murmushi saboda amsar da khadeeja ta bashi da ya tambayi ba'asin kukan bayan ya sa sun yi shiru tace Karima ce ke kuka kuma ta ki fada musu abinda aka yi mata

Salama yayi, suka gaisa da AL'WALED da kula saboda sun san junna sosai tun daga ranar daurin aure, sannan ya karasa daf da su ya duka kasa kasa ya ce" kwa ci ubanku ne, zaku yi na kirki kukan ga ɗan larabawa cen shigowa, in ba masifa ba ku ba zaku yi abinku ku kadai ba sai kun sako wani a ciki? Du y'ar da ta ja min duka sai na rama a kanta ne!"



47
07/12/2024, 17:31 - samiraharounayacouba: Da sauri khadeeja ta Dube shi tana zarro ido ta ce" Kana nufin baban mu? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, ke Karima Allah ya isa, banza kawai zaki bude baki ki fadi kukan da kike kafin ya shigo ko sai ya tardomu nan ya karya banza?"

Karima da jikinta ya kwashi rawa a tsorace ta ciro wayar nan da ta boye ta mikawa ƴaƴansu bakin nata na rawa ta ce" Ka ga fa, ka ga fa abinda maman gidan iya ta bani, dama ka ga irin abinda amarya ke fada a kan mamanmu? Kuma maman gidan iya itama ta ce.........."

"Ai ba sai kin fada ba, ku tashi mu je kawai" Lubna ta kasteta da sauri, ba dan komai ba sai dan gudun janyowa kansu abin a dasa ayar tambaya a kan ahalin nasu baki daya, wato tana matukar jin kunyar a ji irin abinda wasu daga cikin mutanen da Allah ya kadarta musu zama na zagin mamansu du irin yadda take zaune da su, tana jin kunyar abin tana jin takaicin abin, tana jin ciwon abin sosai a ranta....................

Khadeeja dake kallonsu bayan Lubna ta mike tana mikar da sauran ta ce" ke lubna ba a nan zaku kwana ba?, ga fa aba nan za'a bude masa shi da baba innalilahi"

Da sauri ta rarafa ta karasa daf da AL'WALED tana jin zufa na cike hannayenta saboda tsoron kar aba ya wujijiga rayuwarsu a nan

AL'WALED ne ya bita da kallo, sai ya saki murmushin yadda take masa alamun ya fa ceceta, sannan ya kalli kakan kurma da ya tsaya daga bayan babansa sosai yana leke ya ce" ku tashi mu je ai yama ta yi kar gimbiya ta mana fada"

Murmushi ya kwace masa , a tausashe ya ce" Kakan kurma me zai hanna a bar mana su su kwana a nan din?"

Aba ya dan zarro ido yana girgiza kai ya ce" kai haba dai , kai kuwa ai an kwana biyu koda sa zo su saka maku ido, yanzu dai ban ma tambayi haka a wajen gimbiyar ba, idan mun je abinda tace sai a yi ko baban bebe?"

AL'WALED ya yi murmushi yana kallon yadda suke zagayawa sunna ficewa da gudu har Sadik din , sai ya mike a tausashe ya nufi wajen aba yana fadin" Bari in raka su, Aba ga amanata"
Ya fadi kasa kasa sosai sannan ya fice saboda baya so su tafi bai kwontar musu da hankali ba, duda bai fahimci komai ba ama zai saka su kwontar da hankalinsu babu abinda zai faru

Sunna fita khadeeja ta duka kanta a kasa tana gaisar da su baba da tambayar jikinsa

Ya amsa da kula sosai sannan ya yi mata fatan alkhairi

Aba dake sakin murmushi ya wani kawar da kai ya ce" Masha Allah uwata, Allah ya maki albarka ke kam, a yi ta biyaya Allah ya muku albarka"

Khadeeja ta sake sada kai tana mamakin bata samu ashar ba????, a'a , wai da gaske???? Mamaki.....................

Sunna gamawa suka fice daga falon sai kawai ta mike ta haye sama dan kunce kunshin nan , danma mai lalle ta sanar mata da zarar yayi awa biyu ta cire lalle ne mai kyau kuma an masa hadin da ya dace, gashi yanzu har ya fi awa hudu, tsoron ta daya kar aje ya kwabe....., kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login