Showing 180001 words to 183000 words out of 190762 words
Chapter 61 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
nata, sannan mun nemi layinta , yanzu haka kai nake jira in ji idan a tura a dauko ta ko a kyale ta"
AL'WALED ya dan dubi wajen da su aba suke a tausashe ya ce" A amshi wayarta, sannan a tuhumeta idan da wanda ta turawa......, sai a goge kawai....koda yake lamarin social media ai baya wani goguwa, a dai sanar da mahaifinta sai a basu dama idan sun gyara fine, in basu gyara ba kuma sai in je da kaina"
"Okay sir " ya fada da girmamawa , sannan AL'WALED ya katse kiran yana dan juya wayar a hannunsa tunaninsa gaba daya a kanta da tunanin irin rashin kunyar kannun mufeeda...., wai harda rubuta in sha Allah angulu sai ta koma gidanta na tsamiya?....., to ai shi ba shashasha bane da zai tashi yana ji yana gani ya kai kansa wannan waje......., Allah ya rufa asiri....... Wato abin har ya kai a nemi taba kimarsa da darajarsa a duniya? Koda yake duniyar nan ta yanzu abin ya zama abin tsoro, sai adu'a kawai , domin hatta malamai ba'a bari ba.
Bayan sun fito daga masallaci nan aka taru aka gabatar da daurin auren, cikin lokaci kankani aka ringa watsewa ya zamo sai na gida kawai da sirikan Aba dake faman salamar baki suma
Aba na kada kafa ya ce" Allahu akbar shikenan na mika musu yayana kaf, ka san Allah tsohon nan idan suka saki suka yiwa yayana kishiya zuwa zan in dauko abina dan babu wanda zai dagawa yayana hankali !"
AL'WALED ya dubi Aba, hakama Baba, baba ya nuno Aba da yatsa ya ce" injin dai ba hudubar da kake yi musu ba kenan?, ina fata ba abinda kake kitsa musu ba kenan?"
Aba ya turo baki yana dauke kai, AL'WALED yayi murmushi a hankali ya sake duba hoton nan yana ayyana abu kamar haka' Allah ya sa ta iya yafe min.......bani da hujjar kare kaina....tunda har ga hoto nan.... Allah ya sa kar ta min tunanin zina , ya rab ka sassauta min fushinta'
Su dai suke ta ihun murna, shi , shi kadai ya san halin da yake ciki har aka watse ya rage su kawai, domin hatta mijin yayarsu sun wuce shi da matarsa da ƴaƴansu, baba Hamza kuwa ko dare baya dubawa bale ya tuna amare yake tare da su fisabililahi???
Sai kusan karfe tara baba Hamza ya mike bayan Aba ya shige dan kirawo Anmy
Ba'a jima ba ta fito tana turo baki gaba , ita daya dinta dan har Yan uwan zasu rakota Mama tace yanzu fa kuma fita sai sun samu izini zasu ringa yi , a dole ta taho da gudu saboda ashariyar da Aba ya tafka gannin ta ki mayar da hankali ta fita bayan mijinta na jira dare yayi ai kau?, shine dalilin turo bakinta a lokacin da ta fito tana sake jan mayafinta ta lulube jikinta da kyau da shi, shi kuwa Aba ya ɗan dakata ana zuba kunnun baba Hamza
Baba Hamza a gaba yake zaune, direba a gefen direba, su biyu kuma ne zasu shiga baya, inda AL'WALED ke tsaye idannuwansa kyam a kan fuskarta har ta karaso ya sauke ajiyar zuciya ya bude mata motar yana ta kallon fuskarta , a lokacin Aba ya fito da abin kunnun nan ya yi turus yana kallon ikon Allah, AL'WALED na kallonta har ta gama cire ciren kanta sannan ta shiga inda ya bude matan fuska na dada daukan ja dan wallahi sai ta ji kewar Yan uwanta da mahaifiyarta kai harda Aba sun rike mata kirji, shi kuwa du sai yake tunanin fushin hoton ne har yanzu shi yasa idannuwansa a kan fuskarta , yana sassauta tasa fuskar sosai dan so yake yi Tata dinma ta sassautu irin haka Ama ta Kiya ta daureta, ga idannuwanta dake ta cika da hawaye.....
Mayafinta ya duka ya gyara da kyau ya sake kallon fuskarta dan ta rufe idannuwan tunda ta shiga motar, karshema sai kawai ta ɗora kai a saman cinya ta shiga shashekar kukan iya shege
Aba ya daga kafa da sauri ya karaso yana lekowa da kyau ya ga AL'WALED ya shiga motar shima yana kokarin dagota a tausashe ya furta" Anmy......"
Sai a lokacin baba Hamza ya jiyo shashekar kukan ya juyo yana fadin" Subahanalah Y'ar baba kuka? Waye ya taba min ke"
Har ga Allah bata san cewa baba Hamza na motar Ba, sai ta ji nauyi na son lulubeta da kunya, shi kuwa Aba kawai sai ya shiga salalami ya mika kansa da hannunsa ya zungureta yana fadin" Anmy? Ubanki, to uban me Aka maki da zaki mana kukan iskanci? Ke ba zaki daina kukan godiyar Allah ba ko?, innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, fito in ci ubanki dan mun kwana biyu ban gagaure ki ba? Kina kallo baban mutun ya bude maki mota anmy? Kina kallo Anmy kike dauke masa kai? To uban me Aka maki nenene Ni Anmy ?, lah'ilah ha ilalahu elhaji ƙaramin zaki yiwa fitsara ?????"
Elhaji karami da ya tare zungurar da aka yiwa matarsa kafin ya dubeta ya ga da sauri tana kokarin kama kanta sai zarro ido take ya ji wata dariya na son kubce masa Ama ya dane ya dubi baba Hamza ya ce" Baba gaskiya Ni dai ka Hanna d'anka irin haka, Ni na yi mata laifi fa, Ni dai bana son irin haka fisabililahi ya haka"
Baba Hamza ya girgiza kai ya ce" ai in fada maka gaskiyar magana ko? Yaron nan baya jin magana ko kadan, kuma bashi da hakuri ko diz, in ba neman fitina ba matar mutane zaka RINGA ta fito ka abinnanan ashariyarta? Ba laifi ai gaka ga ita nan, ka tabata in har ka taba lafiyar y'ar nan zaka gane hukuma a aljihun elhaji karami take, dan kuwa sai hukuma ta karar da mu baki daya tasssss sai mu ga ta tsiya, ta yiwu ma yarinya kukan rabuwa da yan uwanta take yi a wani fasarata, to bude moto ai dole ya bude mata mota kai baka ga irin yadda larabawa ke yiwa matansu bane? Iyi?"
Aba ya gyada kai yana fadin" Direba bude in bata kunnun nan ta rike in koma gida , dan Ni kam ban kalli yama ba, a kan me to ? Gwara in bar muku wajen kafin ku hadani da tashin hankali!, Anmy ko dubeni nan......"
Ya fada yana kai hannunsa dunkule wajen hancinsa , ita kuma ta Dube shi a sace tana sake dan matsawa kusan AL'WALED
Da hannunsa ya mata nunin sai ya fasa mata hanci kafin ya mika mata kunnun yana fadin" Yar kaniya, wa bilahilazi ki yiwa mijinki biyaya ko in zaune ki, fuska uwa kosan gwana "
AL'WALED ya amshi kunnun yana sake turo baki shima dan shi kam kakan kurma ya gama fin karfin sa, gashi suruki bale ya ja masa warning a kan matarsa, fisabililahi haka za'a RINGA cin zalinsu ana saka musu shiga halin firgita?????, ai ba'a kyauta ba gaskiya.
Direba ya ja su suka wuce , sunna tafe baba Hamza na mita da rarashin khadeeja, AL'WALED kuma na rike da hannunta guda kadan kadan sai ya furta" Sorry Anmy......." Wato tunda ya ji sunnan sai ya ringa fada yana dan kallon fuskarta har suka karaso gida
Direct bangaren mahaifiyarsa suka wuce, Khadeeja sai toshe hanci take yi saboda kunnun nan da ta rungumo gaba daya yau karninsa take ji, sunna zuwa ta ba aunty SHAREEFA shi wace ke nan har yanzu tare da mama Khadeeja da kurma tana fadin" Wayo mama dan Allah a zubar da abin nan, yau ban san me aka cika yayi mugun karnin nan ba, wallahi gana daya gidan Aba yau saboda karnin nan falo baya zaunuwa, ban san me aka saka a ciki haka ba, bayan daga madara sai gero da gyada ake yinsa"
Tana mika mata tana maganar ne tana nufar wajen da kurma ke kwonta ta yi barci, sannan ta ce" mama ina Maman take? Ko ta yi barci?"
Aunty SHAREEFA da ta bude kunnun har hancinta take dan kaiwa gefe kadan tana ja dan ta ji karnin nan da Khadeeja ke fada Ama cikin ikon Allah ita bata ji komai ba sai ta dubi Khadeeja ta ce" Yanzu ta koma tace zata yi sallah ne, wuni ta yi tana sallah sai tace wai nafila take yi, kin san sai a hankali abubuwan nan zasu daidaita........, Daughter Ama menene ke karnin?"
Khadeeja ta dubi aunty SHAREEFA da mamakin gannin zata zuba kunnun nan, daidai lokacin da su baba Hamza suka karaso saboda sunna tafe sunna dan fira ne a kan abinda kanwar mufeeda ta ɗora a social media, baba Hamza na kwontar masa da hankali yana nuna masa ai rayuwar KENNAN, yanzu ta zama abin tsoro, jira ake yi kawai a hadu da abinda za'a likawa mutun Sharif komai kankantarsa a mayar da shi gagara misali.
Sunna shigowa ya ce" Maman Elhaji karami kunnunki ne?"
Aunty shareefat ta yi dariya tana fadin" Baba sannu da zuwa, baba kunnun nan ya min dadi, sai da na so zuwa in koyo shi a wajen Hajiya, ka ga har zan wuce ban samu na je ba, ji na yi Daughter na cewa wai karni shine zan dandana maka"
Baba ya dubi Khadeeja dake ta gyare gyare a falon, duda ba wani dati ama ta yi nan ta yi nan, ta gyara wannan abin kujerar ta gyara wancen dai ta ki zama ya ce" Yar baba kunnun nawa? A'a gaskiya babu abinda ya haɗa kununa da karni"
Khadeeja da mamaki ta dubi wajen aunty shareefat, ai kuwa kamar an sake shaka mata audugar mai digar jinni ta ji wani irin mugun karni ya rike mata wuya, da sauri ta tare bakinta saboda wani amai da ya zo mata , da dan gudu ta yi waje dan bata san inda zata nufa ba a falon ta duka tana karkarin aman, aman kuwa na zuwa da karfin sa
Su Dukansu sun tsorata da yannayinta, baba Hamza da sauri ya ce" SHAREEFA, kunnun nan wani abu ya shiga ciki ko?"
Aunty shareefat ta ce" A'a baba, wallahi bashi da komai kunnu, Ni kanshin flvr ma nake ji na madara mai sanyin kanshi, Daughter ko baki da lafiya???"
Ta fada tana sake riƙe ta ta zaunar da ita bayan sun dawo falon, AL'WALED hankalinsa na neman barin gangar jikinsa, sai dai kunya da kawaici suka sa ya yi shiru ya sada kai , sai dai ki ga ya dago ya sauke mata raunanun idannuwansa ya dan dauke kan
Khadeeja da sauri ta saka fuskarta a jikin aunty SHAREEFA ta ce" Mama wari kunnun nan, karni sosai mama dan Allah a rufe shi"
Baba Hamza ya je da sauri ya dauke kunnun ya rufe bayan ya duba shima ya kai hancinsa dan kusa kadan bai ji karnin ba, yayi kiran mai aiki ya bata yace ta kai wajen Hajiya Inna ta tabbatar da ta saka a hannun Hajiya innar a ajiye masa , sannan ya dubi aunty SHAREEFA dake ta kallon Khadeeja sai kuma ta saki murmushi ya ce" SHAREEFA ko a yi kiran likita ya dubata? Kar aje zazzaɓi ke damunta..........."
AL'WALED ya ciro wayarsa yana fadin" Eh, bari in yi kira"
Aunty shareefat ta Dube shi , lokacin da Khadeeja ta yi lamo kasa kasa ta ce" Mama wallahi lafiyata kalau, kunnun ne ba daidai ba yau ban san me suka saka ba, kar a yi kiran likitan nan plz "
Aunty shareefat ta ce" Big son, ka barshi fa, ciwon ba ciwo bane ai"
Ya ɗan dakata yana duban aunty SHAREEFA din, wani irin a barshi ciwon ba ciwo bane? Ya Allah........
Baba Hamza ya ce" SHAREEFA kina gannin aman da ta yi fa, kuma dare ne kar sai an zo kwonciya hankali ya tashi ko?"
Aunty SHAREEFA ta dubi baba, a tausashe ta ce" Baba, in dai bata hadu da madara ba...., hankali ba zai tashi na.........., abin laulayi ne"
Da sauri khadeeja ta dago fuskarta ta kalli aunty SHAREEFA, ba ita ba, hatta AL'WALED da sauri ya kalli maman nasa, sannan ya dubi Khadeeja wace ta mike mursisisi daga langwabewar da take yi, kamar an kamata da wani ta RINGA zarro ido ta mike tsaye tana jan mayafinta da sauri ta wuce bayan ta ɗan sosa kai ta yiwa aunty shareefat kallon za'a yi mata hadin zancen da ba shi KENNAN ba a tona mata asiri....., sai kawai ta wuce har kamar zata kifa da mugun sauri
Baba Hamza me zai yi banda dariya, dan wallahi irin yadda take zarro idon kuma ta yi wufff ta gudu sak babanta, kai jama'a jinni ba ruwa ba......,
AL'WALED har ya mike, mahaifiyarsa ta fito, fitowar kuma da saurin tsiya ta zo ta yi raffff da hannunsa tana sake labewa a bayansa ta ce" Tun dazu nake boye tsoro nake ji in fito baba ya koreni...., ka fada masa ba Ni ba? Ka fada masa? Dan Allah kar ya hadani da yan sanda, dan Allah kar a maida ni kurkuku ba zan kuma ba, Ni Bama zan kuma yiwa kowa magana ba bale in amso magani ko? AL'WALED dina zo in goyeka ka yi barci in je in dawo daga anguwa kafin babanka ya zo, ina AL'WALED yake? Waye ya dauke min jaririna?????"
Da sauri aunty SHAREEFA ta mike ta nufe su ta kama masa ita suka zaunar da ita, a tausashe ta ce" Aunty, ba nace maki idan kin ji tsoro ki yi ta hailala ba? "
Sai kuma ta dubi AL'WALED a tausashe ta ce" Abinda na fahimta idan ta tsorata ne take fara ire Iren haka, ka ga ko yanzu ai tana ta tsoron haduwarta da Baba, ka ga nan da nan ta firgice, haduwar tasu ce"
AL'WALED ya dago saboda baba da ya zo shima daf da su ya zauna ya sauke idannuwansa a kan baba
Baba Hamza cike da tausayawa da tsoron duniya da tuna yannayin Khadeeja a da , mace har mace, ga kyan, ga komai, Ama yanzu ga yadda ta dawo a tausashe bayan ya kama sunanta ta kalle shi a tsorace sosai a hankali ya ce" Ki kwontar da hankalinki, babu wanda zai rufe ki, kin ji? Ni ai babanki ne ko? Ki daina kukan nan sai ya daga min hankali ya kuma dagawa AL'WALED dinki hankali ko?...., Allah ya baki lafiya Khadeeja"
Maganganun sa sun lafa yannayinta sosai, saima ta koma dariya tana faman maimaita baba yace babu mai rufe KHADEEJA, baba yace babu mai rufe KHADEEJA ko AL'WALED
A haka suka ɗan dauki lokaci tare da ita sannan AL'WALED ya Kaita har shinfidarta ya kwontar da ita, ya yi ta yi mata addu'a sannan ya baro dakin nata mai kula da ita ta shige saboda tare da ita take kwana koda jikin na motsawa cikin dare ita ke kula da ita.
Aunty shareefat ta raka su tana sake yi masa nasiha da hakuri da kadara da ci gaba da adu'a da nuna masa ba komai bane wannan zai wuce na dan lokaci ne in dai har an yi kokarin sadata da likitan da ya dace sannan aka bi ka'idojin da suka dace
Shima sai da ya raka baba har dakin Hajiya Inna sannan ya wuce nasa bangaren cike da son zuwa ya ga fuskarta, sai dai sai da yayi wanka da dan gaggawa sannan ya karasa dakin nata cike da zumudin hakan
Saman gadonta ya sameta , barci ya ki zuwa , gaba daya kanshin turaransa, domin fatar jikinsa take burin su Manu da nata da kuma hancinta , sai ya zamo sai juyi take yi tana sake duba kofar dakin har ta ji an bude an shigo sannan ta ji hayowarsa hakan ya sa ta sauke boyayiyar ajiyar zuciya kunya na sakata sake Mane idannuwanta
A hankali ya shige cikin abin rufar nata ya dagota ya dora saman kirjinsa yana bin idannuwanta da kallo ..............,
A hankali ya ce" Ummumumumuummmmmmm.., ashe ashe Anmy an iya amsar sako????, tashi fada min wai hakane? Kwallonmu ya fada raga....tl me bab"
🥹🥹🥹🥹 Wayo soyayya 👣👣👣👣🥹🥹🥹
53p
Sauran mu 2 page in sha Allah 🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
07/12/2024, 17:39 - samiraharounayacouba: Da sauri ta dago tana kallon fuskarsa, a hankali ta ce" Banda komai fa, kunnun nan ne yayi karni yau"
Murmushi yayi yana duban idannuwanta shima a tausashe ya ce" Kunnu bashi da karni, hancin nan ne baya so....., kin kuwa san irin yadda nake mafarkin karin samun baby?....... Litle ta fi Ni zumudin haka....., anmy...........ina so"
Khadeeja ta yi murmushi ta kwontar da kanta saman kirjinsa ta yi shiru cike da tunani a cikin zuciyarta
A hankali yake shafa kanta yana dan jin saukar numfashin ta
A tausashe ya ce" Ba zaki tambayeni abt hoton da kika gani ba"
Khadeeja ta yi tsammmmmmmmm, kafin ta dago tana kallon fuskarsa, zuciyarta cike da son sannin amsar maganar nan, sai dai kuma ta kasa budar baki dan bata san me zata ce masa ba
A hankali ya ce" Babu wani abin tashin hankali a ciki....., banma san dalilin daukar hoton ba saboda a lokacin ina yi mata magana ne dan ta dawo hayacinta daga irin abinda take fada...."
Sai kuma yayi shiru cike da mamakin kansa, kai, yanzu fisabililahi anmy shekarunta nawa?, in ba aure da daraja mai girman gaske ba kato da shi ya bude baki yana fadin abinda ba'a tambaye shi ba har kokari yake yi ya gane idan an fahimce shi kuma an yafe masa?????? Allah mai iko
A hankali ta iya budar bakinta......cen kasa kasa ta ce" Kusancin yayi yawa Aban litle....., ya yi yawa sosai...kuma ita ba matarka ba.... , ka ga ai muna da litle ba zan so ta ga hoton nan ba ko kadan......kuma.....kuma......"
A hankali ya juye da ita yana kallon fuskarta cike da kiyaye ɗora Mata nauyinsa ya furta" Kummmmmmmmma..........???????"
Khadeeja ta Dube shi, da kyau cikin idannuwansa, a hankali ta furta " Kuma, a lokacin da na gani .....sai na ji kamar zan summa dan bacin rai"
Ido ya saka cikin nata yana karra matse fuskokinsu, a tausashe ya ce" Why......? Bakya so ki ga irin haka??????"
Ajiyar zuciya ta sauke mai sanyin gaske kawai ta kasa bashi amsa, saboda zuciyarta dake so ta bude baki ta fallasa halin da take ciki a kansa
A hankali ya ce" Anmy......?"
Khadeeja ta bude idannuwanta sosai tana kallonsa
Kasa kasa sosai ya ce" Ki so Ni plz......"
Khadeeja ta ɗan yamutsa idannuwanta tana kallonsa da yannayin son karfin haske
A hankali ya hade lebensa