Showing 129001 words to 132000 words out of 190762 words
Chapter 44 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
ta ce" Wai me na muku na kiyaya ne a gidan nan baba?, babana yace ka hanna zamana a nan idan na zauna din me zan yi da zai cutar da wani a gidan ne?, dan me yasa kana yiwa kowa uzuri banda Ni? ka tambayi ra'ayinsa mana kafin ka dauki mataki Baba"
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, da ta san waye AL'WALID da bata yi tsaye a gabansa ta dagawa baba murya haka ba, domin hannayensa har rawa suke yi ya mike tsaye da hannunsa ya nuna mata hanyar fita ya ce" Mu je waje"
Baba yayi gagawar fadin" a'a fa, kana ji Elhaji karami zauna zauna, "
Mufeeda cike da dacin zuciya da bakin cikin halayar tsohon nan ta dauke kanta ta juya din ta nufi wajen saboda yace su je ne, idan kuwa su je ne haka din take so itama, dan tana son magana da shi, dama sai da ta fadawa babanta ya kyaleta da rigimar nan ita zata shawo kan abinta da kanta ama ya kiya, ta so yayi tafiyarsa , ta ci gaba da zuwa da komawa kamar yadda ta saba a da, domin a haka ne zata cimma matsaya ta kuma amshi AL'WALID dinta, sai ya nuna ya fi so ace tana cikin gidan, gayanan mahaukacin brother din nan nasa da dan iskan dansa sun zo sun musu shirme a nan, ama ba komai ko kasheta AL'WALID zai yi a shirye take ya dawo mata irin na da, so ai ba karya bane, ita fa Bama ta kawo maganar wata a zuciyarta, ta riga ta ajiye haka matsayin yayi ne dan ya horata, har akoy yarinyar da zata kaita wani abu ko ta fita matsayi a wajensa ne? shekara nawa suke tare ko ita ba dukkan abinda take so ta samu a wajensa ba, bale bakuwar yau yau? su zuba su gani.
Dan murmushi kawai ya yiwa Baba Hamza ya juya ya bi bayanta
Bai tsayar da ita ba sai da suka yi nisa kadan da bangaren su Hajia inna , a lokacin ne kuma Khadeeja da kurma suka fito daga bangarensa , khadeeja na rike da hannun kurma wace suka gama tsara zasu je su kwaso kayanta a dakinta su dawo da shi nan, domin tun dazu firarsu ne suke sha, harta docter da ta zo ta dubata ta tafi sai da suka birgeta, aunty shareefat kuwa wani farin ciki take ji a ranta da yarda cewar in sha Allah kurma ta yi uwa, haka kuma da Khadeeja tafe su je haka kawai ta ji a ranta eh barima ta barta su je din ko Mufeeda ta ganta, dan ta tabata idan ta ganta ko y'ar faduwar gaba ce sai ta yi, saboda zata ga cewa ita Tata tsarin halittar ba komai bane a gaban ANMY!, kuma zata ga abinda suka gani gaba dayansu cewa ANMY fa zata samu abinda ke ba wasu matan wahala cikin ruwan sanyi, koda yake dama ance idan ka ga ana gardamar kokowa babu kasa ne a wurin (โน๏ธ Allah ya sa haka karin maganar take)
"BAB" Mufeeda ta fada bayan ta langwabar da kanta hawaye na bale mata
Idannuwansa da suka yi ja ya dora a saman fuskarta, lokaci daya yana jimke hannunsa ya dan dago mamakinta ya ce" A gabana?, Baba kike dagawa murya? ashe baki da tarbiya?"
Da irin abun kukan nan mai tafe da yannayin rarashi wanda ya ba su Khadeeja damar jiyo muryarta ita, domin tunda suka gansu Kurma ta yi tsayuwar jin tsoron Mufeeda, ita kuwa Khadeeja ta samu kanta da zuba musu ido , Bama kamar mutumen da dazu ya fito daga dakinta, ta shaki numfashinsa ya shaki nata, ya hadasa kusancin da a yanzu a duniya idan bata da lafiya muguwar rashin lafiya ne kawai Mama, da yan uwanta yan mata ke kawo fuskarsu daf da Tata dan su ji abinda take fada, hakan ke sakawa har idan numfashinta ya fito ya shige hancinsu, itama kuma har ta shaki nasu, ama shi a yau , ido bude kai sake cikin hayacinsa ya bata wannan abin , ya saka wannan baban kusancin da ya soki kirjinta har ya barta da wani irin tunani mai girman gaske, suturar dake jikinsa ta matukar haska shi ta yadda a yanzu ma ya karra haska idannuwanta, a hankali ta bi kusancin dake tsakaninsu da ido kafin ta sake zuba masa idon shi, dan haka kawai wani baki da munin macen da suke tare yaa rufe mata ido., Mufeeda ta ce" Bab, ai ba zaginsa na yi ba, ba kuma magana na......."
"Ke har kin isa ki zage shi ne?, " Ya fada a kausashen da ya sakata dan ja baya tana rintse ido saboda fargaba, sai kuma ta bude idannuwanta tana fashe masa da kuka da sauri ta miko hannayenta zata kama nasa, ya janye yana sake yi mata wani kakausan kallo ya ce" Na fada maki, dabi'ar taba jikina itace babar dabi'ar da na tsana a tsakanina da ke saboda ina kokarin kiyaye hakkin adinina, Mufeeda bana son abinda zai sakani a yannayin bacin ran da zaki yi mamakina ama kina Kai ni wajen da zaki ga haka, kina ji.......ki tafi gida , idan kin je ki wuce tare da su dady Niamey, zan neme ki."
Daga haka ya juyo da nufin yin tafiyarsa ne idannuwansa suka sauka a cikin na Khadeeja dake tsaye a inda take idannuwanta tsai cikin nasa
Idannuwan nata ta lumshe a hankali ta cire daga cikin nasa ta kama hannun kurma a hankali ta ce" Mu je mu dauko kar yama ta yi litle am"
Kurma ta juyo dan ta ji Khadeeja ta dan matse hannunta ne ta dubi Khadeejar sai ta ga ba magana take yi ba dan haka ta sake juyawa inda babanta ke kallonsu, Duda ba wai kallon kafewa da idon nan bane, ama ya dan kalle su ne, ya juya ya sake kallon su din nan
Mufeeda tunda ta ga irin kallon da yake musu, da kuma yannayin shigar Khadeeja, da kurma dake hannunta, da kuma alamun daga ษangaren da suka fito hankalinta yayi mugun tashi
Kallon Khadeeja take yi irin kallon nan na neman makusa a yan sekwani, kuma ta gani kam, kwarai ta ga makusar, haka kuma lokaci daya idannuwanta suka gama rufewa, kishi? kishi balaki ne, kuma idan ana so babu abinda ke yin iyaka da abin so din nan sai kulawarsa , .....kwarai Mufeeda na cikin baban tashin hankali saboda abin yayi mata yawa ne da ya hadu da rashin mafada da kwaba, a irin wannan lokacin babu abinda ta fi buฦata irin rarashin uwa da kwaba da nuna gaskiya a bayane, shi kuwa uba ya zamo karma ya bada fuskar jin wannan lamari , domin idan har abu ya kai inda yake to kuwa a duniyar mu ta hausawa, idan kuwa ya kai inda yake tabas hukunci ne zai dauka mai tsananin da sai hankalin kowa ya tashi sai dai son zuciya da kwadayin abin duniya ya saka ita uwar ta manta cewa Mufeeda fa sunnanta yarinya a duniyarsu, kuma koda akoy buri na son mallakar baban mutun da dukiyarsa da kyansa din nan, akoy soyaya mai tsananin gaske dake rike zuciya da dukkan wani tunani, basu sani cewa ba a halin da take ciki tunda har ta iya duban idannuwansu su iyayenta ta sanar musu cewar eh fa so din take yi mai tsanani ya dace su dawo hayacinsu su nemi mafitar tsira da mutuncinsu da na y'arsu ba, sai suka ga ai babar hujja ce da zasu tayata yakin samun abinda take so, sai suka sake turata cikin ramin domin ai abinda take so din nan ba wai ita kadai ce ke so din ba, a'a, su din sun fita bukatar a yi abin saboda datin duniya mai hada uwa da uba fada ya riga ya lashi harshensu.
A hargitse ta dawo gabansa ta bangaren da yake kallon su Khadeeja zuciyarsa cike da tunanin ina zasu je suka fito? me yasa suka tsaya suke kallonsu? lafiya?, me yake faruwa? me yasa da ta yi musu kallo daya ta dauke dubanta? me yasa bata tsayar da idannuwanta a kansa ya zamo du motsinsa sai ya ga shi take kallo ba? me yasa bata fashe da kuka dan ta ganshi da wata ba? me yasa hankalinta bai tashi ba? eh ya san Yaushema aka hada su, ya san basu ma san junna ba da har haka zai iya faruwa ba, ama darajar aure ai ta isa ta sa a nuna an damu da shi harma a yi masa kuka dan an ganshi da wata ko? ya dace a nuna masa mahaukaciyar damuwa da haka din saboda shi dai a iya haka da ta fito da mayafi filin gidan nan bayan hijab yace ta saka da zai fito sai ya ji wani abu a cen cikin ransa irin na kare hakkin addininsa ya dane masa kahon zuka
"Itace?" Mufeeda ta tambaye shi a hankali tana nuno inda su Khadeeja suke
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, shi kam yau ya ga jaraba, wai da bata tafi ba?, .....shine kallon da ya sauke a kanta da wani mamakin nata da tunanin wannan anya ba sai ya aikata mata halin da mata ke kiran an wulakantansu ba kuwa ko ta bashi lafiya?
Sai dai bai sani ba, bai san har inda mace mai so da kuma ta gaza dane zuciyarta da tsananin kishin abin sonta ke iya zuwa ba, har sai da ya ga Mufeeda ta cire hijabin da ta sako har ake mamakinta da shi ta nufi inda su Khadeeja ke kokarin tafiyarsu dan ta gaza hakurin ci gaba da tsayuwar nan ta juyo kurma ta mata alamun su tafi
fa.........., sai ji ta yi da karfi an.............. fizgo hannunta dake rike da kurma an juyota sannan aka miko hannu da nufin za'a shake mata wuya
Cikin hanzari ya nufo su, dan babu abinda ya ayana sai zata karya y'ar mutane, sai dai yana daf da karasawa inda suke din ya ja ya tsaya yana zaro ido cike da matsanancin mamakin gannin lokaci daya Khadeeja ta tare hannunta ta damki tsintsiyar hannun ta dantse da karfe da faratunanta ta mika dayan hannunta ta riko wuyan Mufeeda, ba wai rigarta ba, a'a wuyanta ta rike taf, hakan ya sa mayafinta itama zamewa, ama bata bi ta kansa ba saima sakin hannun da ta yi ta nemi kai Mufeeda kasss lebenta kuwa a dantse yake, idannuwanta ta zarro mata su sosai kamar zaka yiwa d'anka hukuncin nan dan ya tsorata din nan, a kausashe ta ce" In sha Allah daga yau kin daina kai hannunki jikin wata da nufin neman fada ko Wacece!"
Kakarin Mufeeda ya ankarar da shi daga summan tsayen da yayi, da kuma karasowar babanta da gudu gudu tumbinsa sai motsi yake dan a tsaye yake jikin motarsa yana haangensu yana jiran Mufeedan, ya wuce su da nufin kama Khadeeja ya bambareta daga jikin Mufeeda yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une ke saketa, Mufeeda me ya aike ki fada da y'ar mahaukaci? saketa saketa sakar min y'ata!"
Da sauri AL'WALID ya rike hannunsa yana jan baya da shi hadi da aika masa kallon da tunda suke bai taba yi masa irinsa ba, lokaci daya ya karasa inda suke din ya saka hannayensa biyu ya kama na Khadeeja ya cirata daga ita har hannayen nata ya dawo da ita jikinsa lokaci daya ya dago habarta ya.......๐ฅน๐ฅน๐ฅน๐ฅน๐ฅน๐ฅน
๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ
07/12/2024, 15:16 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na talatin da tara (39)*
*IDAN KINA DA BUKATAR TALLAH KI TUNTUBENI TA LAYINA KAMAR HAKA 93811618*
LABARI
A hankali ya furta" Hajia karamahhhh???"
Khadeeja ta dago idannuwanta da kyar ta saka a cikin nasa, kirjinta zafi yake yi har yanzu abinda ya tsaye mata a wuya bai fada ba, ga maganar nan da ta ji ya fada mata kamar haka " Ki je gida zan neme ki"
A hankali ta ษora hannunta a saman nasa dake rike da habarta ta janye, wani haushinsa na tukota, innalilahi wa inna ilaihi raj'une wannan ai an kasheta, ita daga mai labewa da barira y'ar ajinsu yana cin amanarta yana rantsuwar walahi ba soyaya suke yi ba, sai wanda aka dauka aka yi mata dole ashe yanada wace suke tare?
Sangartar da Lubna ta fi tsana a rayuwa da lamarin Khadeeja idan ta yi fada ta gama ta yi ta sheka musu kuka in an raba fadanta da kyar suke rarashinta sai tace wai wani abu a kirjinta bai fada ba , ta yiwu ko sai ta ga abokin fadan nata ya summe zata ji abin ya fada matan ne ta yi, a hankali ta fara shashekar, a lokacin kuwa tuni aunty shareefat ta kirawo matan gidan sun fito hankali tashe
Tana kallon nan nasa tana shashekar nan kawai ta fashe da kuka ta dantse lebenta da karfin tsiya ta dubi wajen da Mufeeda take ta sake dubansa
Aunty shareefat ta rikota da sauri tana sallalami hankali tashe tana duba jikinta,domin su basu ga ainahin abinda ya faru ba, rabiyar fadan ta gani ta auna ta kirawo mutanen gidan dan so take yi sosai Mufeeda ta idasa lalata rawarta da tsale, a rikice take fadin" Ta ji maki rauni ne? mama dan Allah sake kira min likitar nan , kin ga tana kuka ta ji mata rauni"
Khadeeja da takaicin lamarin masu kudin nan ta ce" Aunty dan Allah kar a kirawo likita, aunty ya rabamu , ya rabamu dan Allah a barmu , aunty a barmu"
Su kam kama gane bayanin suka yi sai da Elhaji Maiga rai bace har yana magana yana furzar da yawu ya ce" An ki a hada kun, wato ki jinyatata ko? ba za'a hadakun ba, aikin banza bari ki ji, daga ke har ubanki sai na rufe ku, ba zan yarda ba, sai na kai karar ku, mahaifinki ya dake Ni, ke kin dakar min y'a"
Matan nan kusan a tare suka dauki salati, Mama Binta hannu a baki cike da jin kunya ta dubi AL'WALID dake tsaye yana sake kallon ikon Allah, ga wata dariyar kukan da Khadeeja ke yi da mamakinta na kama shi, domin da farko ya tsorata da kukan ne ko ta soka mata wani abu? yanzu kuwa ya ji dalilin kukan sai kawai ya gyada kai yana kallonta , furucin Elhaji Maiga kuwa ya idasa kashe shi da dariya shi kam ina zai saka ransa ne? ga bana Hamza yana ta salalami, Muhammadu a tsaye yana kallon uncle din nasa da haushi, babansa kuwa a nesa a labe
Mama Binta ta ce" Big Son me yake faruwa ne?"
AL'WALID ya yi murmushi kawai yana sake kallon Elhaji Maiga da ya idasa nuna masa waye shi
Aunty shareefat rai bace ta ce" To ka kai karar mana, dan Allah ka kai karar, ai koda an saurareka a wajen karar kai zaka kule kanka, saboda kakan kurma dai nan gidansu ne ka ga babansa nan, a gidansu ka tardo shi ka zage shi du a gabanmu mune shaida, ita kuma Maman kurma ai a gidanta ta tardota ta fara kai mata duka, wannanma mune shaida sai ka kai karar mu ga waye zai kule kansa da kansa, mu je, daughter mu je daina kukan"
Elhaji Maiga du bambaminsa sai yayi tsit ya raka su sharefa da kallo da tarin mamakin sharin da za'a masa, ah to shari mana wai kuma wancen mahaukacin ne dan gidan nan????
Baba Hamza da dan yannayin fusata ya ce" Ni du ban so abin nan har ya kai nan ba, yaya za'a yi ta magana daya ne? ka ga Elhaji karami kawai ka min maganin abinda ka hadani da shi tunda na yi nasiha, na bada hakuri , na yi rarashin an ki a duba furfurata a ji maganata, saima nema da ake yi a nuna min ban isa ba, to ba zan lamunci haka ba, na so a yi hakurin, kwarai na so a duba maganata aka kiya, bafa zan lamunci a ringa kama yan ya'ya da kokowa ba saboda abubuwan da kunnayena suka ji idan har aka aikata har da kai sai na yi shara'a domin kaine ka sanyo min fitina a cikin gidan nan har ka bada dama ake dauki ba dadin nan, "
AL'WALID ya nufi inda baba yake a tausashe bayan ya rike hannunsa ya ce" Na jima da nuna maka ka fita batun ka bari in yi ka kiya baba, na jima da gane cewa ba kowa ke gane idan ana yi masa uzuri ba, yanzu ka je wajen kakan kurma ku zauna zan zo"
Ai kuwa baba Hamza ya juyawarsa yana kallon kurma dake tsale tana biyar bayan iyayenta da kakaninta sun nufi bangaren KHADEEJA yayi dan murmushi, domin rabonsa da ganninta haka tunda ya fada mata babanta zai yi aure ta yi murna sosai daga baya ta shigo tsoro, sai kuma yanzun nan , karshema sai ya ga ta dankara da gudu ta rigaye su shigewa ya tabbata labari ne cike da cikin ipad za'a dauko dan a bayar da labarin nan sala sala, sai kawai yayi murmushi yayi tafiyarsa
Sai da ya bar wajen AL'WALID ya dan daga murya ya ce" Malan