Showing 36001 words to 39000 words out of 190762 words
Chapter 13 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
a yau
Basu ji tsayuwar motarsa ba, basu ma san da ya zo gidan ba domin bangarensa yana nesa da bangaren motoci, uwa uba idan aka shige dakinsa ba lalle a ji hayaniyyar waje ba sai in mai karfi ce, tsayuwar mota ba za'a jita ba in dai ba katarpila ba
Kicin din ya bude yana kama haba, Amarya na lekowa ta bayansa tana zarro ido da mamaki kamar zai kasheta a lokacin da Khadijah ta gama zuba kayan jus din da zata markada ta juyo zata yi magana idannuwanta suka sauka a kansa, A bayane da dan karfi ta ce" Innalilahi Ba.........."
Ai kafin ta rufe bakinta sauran suka kusa fadawa cikin wutar
A zabure ya ce" Du yar kaniyar da ta fada ta kone jikinta idasata kawai zan yi in huta da bakin ciki, dan ubanku dodo kuka gani? Gimbiya y'ayanki basu da tarbiya, dan ubansu dodo suka gani? Walahi Karima idan kika yarda kwarzane ya samu wannan shegiyar fatar ta uwarki sai na idasaki na huta, yau Ni na ga jaraba daga lekowa dan in ce muku sannu da aiki shikenan sai ku nemi fadawa wuta? mtsssssssss aikin banza aikin wofi kina kallo y'ayanki na wulakantani ko Gimbiya? ya miki kyau " Daga nan ya juya ya nufi dakinsa sai fadan za'a masheshi shashasha yake yi a cikin gidansa
Mama ta yi boyayen murmushi a ranta ta ayana' lalle Elhaji ' A fili kuwa ta dubi ya'yan da suka yi zuru zuru a tausashe ta ce" Meye haka kuke yi? aljanni kuka gani?"
KARIMA da jikinta ke rawa ta girgiza kai ta ce" A'a mama, dukanmu zai yi shi yasa"
Mama ta girgiza kai tana dubansu ta ce" Ku ringa kiyaye duk wani abu da zai sa ya taba lafiyar jikinku, idan har kunna kiyaye wa ba zai doke ku ba, komin abinsa ai sai an masa laifi zai yi dukkan ko?"
Khadijah ta sada kai tana hadiye dariyar yannayin Lubna a ranta kuwa ta ayana' wai baban? ta dai raya masa ya yi dukkan tsaf zai daki mutun koda kuwa kallonsa yayi, ai shi ba sai an masa laifi ba yake hukunci, hukuncinsa na biyowa ta kan wanda tsautsayi ya fadawa ne"
Sunna jin fitarsa sallar isha'i a lokacin sun gama haɗa komai sun zuba sun kai nasa wajen da yake ci, sun kai nasu, dama sunna yin aikin sunna wanke wanke ne sharewa kawai suka karra yi suka goge komai sannan ta yi tsaye suka duba sun kashe komai da suka yi anfani da shi sannan suka tafi bangarensu
Baba na dawowa daga masallaci ya zo kusa da gidansa ya ga Abubakar tsaye da Mudansir sunna magana
Karasowa yayi a lokacin da Mudansir ke fadin " Dan Allah ka min wannan kokarin"
Kai tsaye baba ya ce" Na me fa?, wani kokari?"
Cikin Abubakar sai da ya juya, da sauri ya dubi baba, kafin yayi magana Mudansir har ya yi gaba bayan ya yiwa baba gaisuwar gagawa Baima tsaya ya amsa ba
Baba ya kure Abubakar da kallon idan baka fada min ba komai na iya faruwa
Jikin Abubakar ya kwashi rawa, muryarsa da gargada ya ce" Dama ba komai bane dan ajinmu ne, sakon karatu muke tataunaw......."
Kafin ya rufe bakinsa Baba ya daga ky din shagonsa da yake yawo da shi du inda zai je ya maka masa a gefen kunne, ky din dauke da kys da yawa ya zuba masa shi da karfin gaske
Da farko kamar za'a zare ransa zai ce ya ji ko menene? shi dai wata azaba da bai taba Sannin akoyta a duniya bace ta ziyarce shi,, daga baya kuwa sai ya ji kamar zai summa kafin zafin ya shige shi sosai
Du girman saurayin nan sai da ya ji kamar fitsari zai sako masa, a guje ya nufi gida, babansa kuwa ya daga kafa ya bi shi, Duda shi nasa gudun ba mai girman na Abubakar din bane, dan kafin ya isa tuni Abubakar ya nufi dakin Hajia yana ihu yana fadin" Innalilahi wayo Allahna Mama Mama ya kasheni"
Mama ta bude humurarta zata shafa, Khadija na zaune ta ja turaran wutar da ta gama turara tufafinta itama ta rufa tana turarawar ta mike zurbat, Maman kuwa ta saki ƙatuwar kwalbar turaren ta tartsatse a kasa lokaci guda tana tare Abubakar da ya rukunkumeta sai ihu yake ga kuka, ga jini ya gama wanke masa duka kafff jikinsa
A rikice ta riko kan tana kallon wajen da jinnin ke zuba daidai baba ya shigo yana fadin" Dan ubanka Ni zaka yiwa karya? in tambayeka uban waye shi kace min dan makarantar ku? wannan mai askin yan daudun? a makarantar taku harta aski ba a cen ake maku ba du bayan mako biyu? ko sun zama yan iska ban sani ba? zaka yi bayani ko sai na wulakantaka?"
Da sauri Mama ta ture hannunsa da yake son sake shako Abubakar Rai bace ta ce" Walahi walahi idan ka yarda ka yi kisa in ba sai an rataye ka ba idona idonka kace ba jinnin larabawa ke yawo a jikina ba, kullll, ka yarda ka kashe sai an kasheka Elhaji "
Baba ya zarro ido yana kallonta ya ce" Yanzu kina tsaye kina kallo zai kasheni Ni da raina? kin ga yaron ne? dan daudu sak wa bilahilazi, gimbiya da yayi daudu gwara na rage mugun iri a hademu a kashe, bani shi in gwada Mai wando yake sakawa dan ubansa!"
"Walahi walahi ba daudu nake yi ba, shima ba dan daudu bane, Karima yake nema, shine yace in duba masa ita walahi daga wannan Ni babu abinda ya hadani da shi baba!" Abubakar ya fada da ihu yana sake rushewa da kuka
Lokaci daya Khadija ta dora hannu a kai tana fadin" Lah shikenan, Habu ka kashe y'ar uwarka"
Baba kuwa kamar bai ji da kyau ba sai da ya sake duban Abubakar sannan ya dubi Mama dake huci ya ce" Yau in kububuwa zaki zama sai na ji abinda ya haɗa Karima da yaron nan, Gimbiya a kan wannan komai na iya faruwa na rantse maki....Karima....ke Karima....Karima!"
Ya fita kamar zai tashi sama
A rikice Mama ta dubi Abubakar dake kuka ta zaunar da shi a bakin gadonta ta dubi Khadija da fada fada ta ce"
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*🇳🇪
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Sha ɗaya (11)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
*META FORCE*
*menene meta force*
business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force
*shidai meta force crypto currency* ne
kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency
akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba
yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai
*TACTILE*
1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars
hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira
*Spillover*da*over flow*
wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu
to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*
*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja
LABARI
Ta ce" Ke likitace Anmy, ama kina ganni irin yadda yake zubar da jinni me kike jira da ba zaki wanke masa ba? mtsssssssss"
Ta sakar mata shi ta fita da gudu gudu sauri sauri ta nufi Dakin Karima domin ihun yaran a nan ya fi karfi, hakan ya tabbatar mata babansu yana ciki
Da gudu ta je ta bayansa ta kama kokowa da shi dan ba zata iya ta gaba da gaba ba, domin ya dirtse Karima ya rike mata wuya tafff kuma fadi yake sai ta fada masa abinda ya haɗata da dan Daudu dan uban babanta!
Gannin ta yi ta yi ta kasa kwatar Karima , ya ki ya saketa, sai ta samu dantsensa ta dartsa masa cizon da ya kusa summar da shi
A rikice ya hangazata sai da ta daku da amarya dake bayansu tana tsaye tana kallo
amaryar ta je baya ta fadi a kasa ta daku itama da karfin da sai da ta fasa ihu dan walahi bayan ya daketa da karfi gashi Hajia ba kadan ba kuma ta nausata a kasa
Da ihun fada ya ce " Ba nace maki a kan haka sai in sake ki ba? ke dai bakya gudun bacin raina ko?, ba zaki bari ta fada min da ubanwa take tare ba? ba zaki bari ta fada min abinda ya haɗata da dan Daudu ba? Ke, ke Karima kin san waye Ni? Ni zan miki miji jiya jiyan nan in sanar maki cewa na maki miji, yau sai in ga wani dan daudu ya zo nemanki? Ni zaki watsawa kasa a ido? uban me ya hadaki da shi ido ya masa jajir ? kwaya yake sha ko? innalilahi ga kwaya da daudu? uban me ya haɗa ki da shi nace?"
Mama ta kama ta tashi da kyar, a tausashe ta nufe shi tana fadin" Yi hakuri, saurara ka ji, yi hakuri, kar ka rike mata wuya idan ka rike mata wuya yaya zata yi maka bayani?, Ni fa na sanshi yaron da kake magana a kai, dan nan bayan gidanmu ne fa, cewa yayi yana sonta na dakawa abin birki dan Bama zaka yarda ba, ka san dan yau da naci shine ya dawo , ka yi hakuri ka ji abinda yake faruwa mana"
A hargitse ya dubeta ya ce" Kin san shi? yana sonta? dan ubansa ya rasa lokacin nacin sai yanzu da na mata miji? miji da na yiwa Karimar"
Mama zata yi magana ya damki hannunta ya fice da ita rai bace ya nufi bangarensa da ita
Sai da ya je bangarensa da ita ya saketa ya ce" Zo nan mu yi magana saboda yan sa ido dan ban yarda da wancen matar ba tana iya zuwa ta fadawa mai neman auren Karimar , Gimbiya Kin san da maganar? Usaina kin kuwa san waye wannan mutumen? ko labari makamancin wannan ya ji ba zai taba hada jinni da ita ba fa, kin kuwa san abinda hakan yake nufi a wajena?"
Mama a tausashenta, dan ta riga ta gane ya hau wajen da komai na iya lalacewa ta dube shi ta ce" Ka yi hakuri mana baban yan albarka, Yanzu Elhaji, saboda wannan kake daga jijiyoyin wuyanka har haka? kai kake da macen fa, mune zamu yi iko a kansa fa, haba Elhaji du takamarsa ya kai ka ne? aman Duda haka layin manema aurena nawa ka bi? Elhaji ina takamar mace ba masoya? ko waye shi ya san tana da masoyanma ai ya fi dan ya riketa da kyau"
Kai baban ya dafe ya zauna yayi shiru kamar da gaske sai kuma ya dago da karfi yana fadin" Ni din banza , na fada maki Ni din banza, mu layi muke zuwa mu bi, su layin ake musu fa!, Ya Allah ba zaki gane ba, da ace zaki gane abinda nake nuna maki da ke da kanki sai kin ji zaki summa a kan wannan maganar, Gimbiya kasheni kike so ki yi? walahi zuciyata zafi take yi sosai kamar wanda ake tsikara min allura, abu daya nake son ji, wannan yaron babu komai tsakanin y'ata da shi? idan babu shikenan zan neme shi in saka masa warning , ba shi ba y'ata na yi mata miji, idan akoy ki fada min tunda wuri Gimbiya dan walahi in na ga laifinta kema zan ga naki"
Mama ta ringa sauke ajiyar zuciya, dan kuwa yannayin magangannunsa sun nuna koda bai sauko gaba daya ba ya saukan
A tausashe tace" Na cire maka halin d'an yau, bayan wannan inada yakini a kan tarbiyyar ya'yan nan, koda akoy maganar soyaya iya nan ta tsaya, ka yi hakuri ita dinma an soke, ba ita ba shi, ba sai ka neme shi ba, Ni zan yi mata magana kuma ka dauka cewar an gama, dan Allah ka yi hakuri"
Baba ya yi shiru a zaunen nan har mama ta fita dan so take yi ta koma wajen su Abubakar ta ga yaya yake
Tana fita baba ya mike ya shiga kai kawo , zuciyarsa fal da tunanin abinda zai yi dan ya yiwa tufkar hanci, ba zai taba lamunta ba, ya'yansa basu da samari, tarbiyyar gidansa ta sa ake son hada zuri'a da shi, idan har samari masu irin wannan askin suka fara yi masa salama ai ya kafe, gwara ya san shi da kansa ya kwashi ya'yan ya kai ƙauye ya haɗa su aure da gardawan kauye da a yi masa sakiyar da ba ruwa
Mama kam da ta koma direct dakinta ta je, ta samu Khadija da Abubakar aiki ya kankama tamkar zata yi masa tiyata, harda su hular likitoci ta kuma ta wani saka glassss rike da sizosss tana aikinta ka'in da na'in
Da sauri ta karaso tana fadin" Subahanallah, ANMY, sosai ne ciwon?"
Khadija ta dan daga gira a nutse ,, cikin yannayin maganar mama cike da yanga da kuma saukar da harufa a kan yannayin saukar furuci ta ce" Eh, fashewa ne wajen ya yi, ko nace tsagewa so dole muka yi dinki"
Mama ta mika hannu tana fadin" Bani in gani, ya Allah, sorry son"
Khadija ta dan ja baya tana yiwa Mama irin kallon da sukan yiwa iyayen patient idan sunna asibiti koyon aiki ta ce" No Hajia, ba zan baki ba, asalima dole sai polisawa sun shiga lamarin nan, dan kuwa sai an kawo mana wanda yayi abin nan mun rufe, yanzu muna da bukatar space mun kusa gama aikin mu, ama fa ki sani dole mu daukaka karra danma kar ya mutu ne muka taba da ba dan wannan ba da ba zamu taba ba gaskiya"
Mama ta zuba mata ido, da farko da ta ji khadija na kiranta Hajia kuma tana faman fadin su su sai da gabanta ya kece ya rigizo yayi warwasssssssss, dan kuwa tsoro ta ji kar aje wata gingimemiyar jarabawar ce zata kutso rayuwarta mai karfin gaske wato kar aje khadija aljannu take yi, sai dai da ta kalli idannuwan Khadija ta gane idannuwan y'arta ne fakewa zata yi ta kirta ba dadi a fakaice....., hum, wasu lokutan takan ji a ranta tana tunanin yaya khadijah zata yi zaman aure? lalle idan yannayin wayonta da kisarta zata yi anfani da ita, to kuwa tabasss zata ji dadin zaman auren koda kuwa da juyayen miji ta hadu
Fuska ta hade ta ce" Zaki bani ko sai na tsinka maki darajar fuska a bainar nasi?"
Khadija ta dan zarro ido, ta mikawa Mama sannan ta cuno baki ta dan ja baya a ranta tana ayana' ya za'a baka aiki ka bi yadda aka koya maka kuma ace za'a ga laifinka?'
Mama ta duba, tuni ta goge masa ta saka magani, yanzun wahalar da shi ne kawai take
kama hannunsa ta yi ya tashi ta ballo magani ta bashi ya hadiya da ruwa sannan ta umarceshi da yaje ya yi wanka ya kwonta ya huta yau ba za'a je karatun daren a wajen baba ba
Yana dingishi ya fita saboda gudun da ya yi ya dan bugu da kofar shigowa dakin Mama
Yana tafiya Khadija ta shiga gyara dakin Mama tana goge abin jinni jinnin da ya zubu a ko'ina ta cenza abin shinfidar sannan ta tafi da wanda aka bata a lokacin ta shiga wanke shi
Mama kuwa ta nufi dakin KARIMA, sai dai du bugawar da ta yi KARIMA bata bude ba, hakan ya sa ta karra kunnenta a hankali ta ce" Karima idan kina jina, Mama ce, Babanku ya kwonta tuni, ki