Showing 78001 words to 81000 words out of 190762 words
Chapter 27 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
gidan inna tsohuwa mai bada dabarun zaman gidan miji nake, Ni har yanzu abin ya kasa sakina wai ko dai bai gane ba?"
KARIMA ta zarro ido tana kallonta ta ce" Innalilahi, ban gane ba Anmy "
Khadija ta ce" Karimeme, walahi idona idon matarsa tace masa daga cen nake, ta kuma nada min bulala ya kwaceni, karshema dakinsa ya kaini, kin ji warin man zafi ? to nasa ne, ya kuma tabatar min in an jima zan ci kaza, ya karasa da fadin du wanda ya nemi taba min zaman lafiya da shi yake maganar, ke in ba dafawa ta mala'ikan mutuwa ba me kike gannin zai fitar da shi a hayacinsa haka?"
Lubna ta girgiza kai ta ce" Babu, innalilahi wa inna ilaihi raj'une "
Ummi da ta fito daga karkashin gado ta budi baki zata yi magana aka budo dakin nasu da karfi
A zabure du suka mike sunna kokarin dake junna su gudu
Mama ta dafe goshi tana harararsu ta ce" Allah ya shirya, ko barewa ta baku lafiya, sai ku fito ku kama aiki ai kun san bakwa yi min zaman daki, ga ayyuka cen an kawo masu yawan gaske, ku uku maza ku je ku shiga aikin hatsin cen, ku biyu kuwa ku shiga gyaran kayan miya saboda baki"
Da mamaki du suka kalli junna, Khadija ta ce" Mama baki? me ake yi a gidan namu?"
Mama ta gala mata harara ta nunota da yatsa ta ce" Ki yarda in sake damkar ki, marar kunyar banza da wofi, kuma ban gama ba sai kin fada min abinda kike yi a gidan inna yau!"
Mama ta ja kofar garam ta rufo musu
Da sauri suka shiga daukan hijabansu, Khadija ta rataya nata a kafada ta ce" Yanzu gidan nan abu ƙalilan in ka yi itama matar tasa sai ta dau fushi ta ringa neman karya ka, Allah dai ya sa shi ya dore a neman kwato mana hakin dan in dai suka zama horor biyu in sha Allah gidan takwarraty zan kaura mu ringa shan hantsi muna yi da makotanmu, gwara wannan da zama kusa da su gaskiya kennan"
Ita dai Lubna bata ce mata komai ba, sai Ummu da ta fitar da numfashi, Karima kuwa dama yanzu bata da sakewa in ba a dakinta take ba, sunna fitowa ta ringa rabe rabe karfi da yaji ta mayar da kanta mujiya a cikin yan uwanta saboda kin jinta
Badariya mai aiki ce ta ringa wani nan nan da su tana furta" ga amarenmu kai Allah ka nuna mana, Allah ka kai mu babar ranar"
Kasantuwar su a sanninsu auren Karima ake hada hada sai kawai suka buge da murna sunna fadin kennan ba'a fasa ba? ita din da kanta sai ta shiga tunanin yaya kennan? ba'a fasa aura mata mutumen ba ko kuwa an daidaita da Mudansir ne?, gashi a yanzu ita ta san ko tana hauka ba zata je ta tambayi kowa kan maganar ba, gwarama ta nemi waje ta rike kafarta ta zubawa sarautar Allah ido.......
.......( wannan kennan ).
___________________________________
Barcin da ya yi bai fi na awa uku ba ya farka cike da zumudin wannan lamari a zuciyarsa, haka kuma jikinsa da dan kuzari saboda ya samu ya yi barci, dama shi akoy kokarin tafiyar kasa shi yasa du irin yadda shekarun nan suka ja yana da dan kuzarinsa harma ya fi wani mai kananun shekarun kokari
Bangarensa ya wuce dan Bama zai nemi AL'WALID warhaka ba ya san baya bangaren, ta yiwu ya fita ko yana cen wajen su Hajia inna
Shiryawa yayi ya fito ya je wajen su Hajia inna ya sameta a jingine , kurma na tsaye kusa da ita tana goge mata bakinta da tissu , kunnu ta gama bata shine take gyara mata bakin, tana iya shan kunnun da kanta fa, kawai dai rigimar kurma ne bata yarda ta barta ta sha wahala komai kankantarta
Kujera ya janyo a hankali ya zauna yana amsa gaisuwar kurma da nuni da hannayensa sannan ya dubi Hajia a tausashe ya furta" Barka da warhaka, shikenan bakya nemana yau baki ganni ba tunda asubahi?"
Hajia ta yi murmushi itama muryarta a hankali da yannayin jinya da take fama ta ce" Baban anmata ya sanar min cen ka samu gado kake barci ai, shine nace a Barka ka huta"
Yayi yar dariya yana sake duban kaffafuwanta ya ce" Allah ya baki lafiya"
Hajia ta yi murmushi kawai, domin addu'ar nan idan an yi mata ita yanzu murmushin kawai take yi, dan har cikin ranta takan ji addu'ar ana yi ne dai, koda yake sauki kowane na Allah ana so, ta yiwu a bar duniyar shine sauƙin wata wahalar, Allah ya bamu sauki mai sauki.
A tausashe ya ce" Maganar daurin auren baban kurma ne, in sha Allah jibi nake so a daura, yanzu haka zan fita ne mu je a bada sanarwar a duk inda ya dace, yaya kike gani?"
Hajia ta zuba masa ido na yan dakiku sannan ta ce" Du abinda ka yanke, na san alkhairi ne, domin kana fara Bama Allah zabi a dukkan lamuranka "
Ta dan dakata dan bata cika yin doguwar magana ba tare da tana shasheka ba
A hankali ta ce" Shi din me yace?"
Baba Hamza ya ce" Mun gama magana da shi, yace ba damuwa du yadda na yanke"
Hajia ta dan lumshe idannuwanta a hankali ta ce" Allah ya tabbatar da alkhairi...., ama dan Allah a tabbatar da an yi du abinda ya dace dan a ba yarinyar kariya daga dukkan abinda yake na cutarwa...."
Ta dan dakata ta ɗora da fadin" Saboda kace yarinya ce, bayan wannan ba'a san me d'an yau ke iya aikatawa ba, ka samu mahaifin yarinyar nan ku yi magana ta fahimta, bana son abinda zai zamo fitina ELHAJI "..
Baba Hamza ya ce" In sha Allah, fitar nan da zan yi, harda maganar mahaifin nata, zan samu yayansa mu yi magana shi sai ya sanar masa....., ban ki jinnin su ba, ama ina son shinfida mai kyau tun da sauran numfashina"
Hajia ta gyada kai tana addu'ar alkhairi, sannan ya mike ya tafi
Kurma ta dawo dakin bayan ya fito, Duda ba sosai take ji ba, ama in ta ga sunna magana takan fita ta basu waje sai sun gama take dawowa
Baba Hamza ne a zuwa falo ya samu Hajia Binta da masu aiki sunna ta maganar abinda za'a girka
Gaisawa suka yi da girmamawa suka mike suka tafi, Baba ya zauna yana dubanta da murmushi ya ce" Ina yan uwan naki? yi min kiransu akoy maganar da zamu yi"
Hajia Binta ta mike ta nufi bangaren kowace tana sanar mata kiran Elhajin, saboda koda kuwa a yanzu tsakaninsu da Elhaji zaman auren ne ake yi mai sunnan kawai babu wani amfanuwa ta fannin auren shi da kansa sai sauran ibadun da ake kiyayewa, sunna matukar girmama shi kuma sunna kiyaye duk wani abin da zai iya zamowa fitina a tsakaninsu da shi
Babu wace ta jima dan amsa kiran suka zo gaba dayansu falon suka zazauna sunna gaisar da junna daya bayan daya
Murmushi yake yi yana dubansu, a cikinsu Hajia Binta ce kawai mai shekaru sittin da uku, sauran basu rufe hamsin Bama, kuma dama Hajia Binta ta girmi Hajia Inna, ciwo ne kawai ya Kwontar da ita ba dan shekaru sun kai a yi kwonciyar ba
A tausashe ya ce" Dama dan in sanar muku maganar daurin auren jikanku ne jibi idan Allah ya aminta"
Har ga Allah a cikinsu babu wace bata ji hankalinta na neman tashi ba, kuma kowace a zuciyarta take son kamo sunnan wani jikan daban ba shi ba, bayan zuciyar tasu ta fi yarda cewar shi din dai ne ake nufi, domin sauran ba zai taba yiwuwa ba ace har jibi auren daya basu sani ba
Shiru ne ya wanzu a wajen, babu wace ta iya budar baki ta yi magana, hakan har ya bashi mamaki matuka, yana dubansu ya ce" Baku ji abinda na fada bane?"
Hajia Binta ta share gumin dake goshinta a hankali ta furta" Mun ji Elhaji, masha ALLAH, Allah ya tabbatar da alkhairi, ama yaushe har aka kai kayan Niamey din har aka saka rana bamu sani ba? inace mune zamu yi duka wannan hidimar ko shi ya bata komai?"
Elhaji Hamza ya girgiza kai a tausashe ya ce" A'a, ba'a kai ba, hasalima ba da ita bane za'a daura yanzun, da yarinyar wajen Elhaji Ya'u kakan kurma ne, ita din sai daga baya idan Allah ya aminta"
Hajia zainabu ta zarro ido tana buɗe murya ta ce" Elhaji yi hakuri ban gane ba, kana nufin auren waye za'a daura wai?"
Alhaji Hamza yayi shiru yana kallonta, Hajia ta yi gagawar fadin" Hajia , Elhaji karami din dai ake nufi ko Elhaji baba?"
Elhaji Hamza ya gyada kai yana fadin" eh shi"
Hajia Amina ta washe baki, hakama Hajia zainabu ta kasa boye murnarta ta rangada guda tana tafa hannayenta, farin cikinsu ya kasa boyewa, Hajia Binta ce kawai ta yi murmushi ta dan girgiza kai Bata ce komai ba, sai dai ita da kanta ta san da wani abin Gara wani, Duda sun san shi dinma uban y'ar da akace za'a kawo musu ba kanwar lasa bane, bale irin yadda ake fadin matarsa daya ta gagareshi ta asirce shi ita kadai take zaune a gidan take mulkarsa din nan, sun san ba y'arta bace za'a kawo musu, to kuwa da sauki dan walahi Mufeedan nan ta zame musu balaki da fitina, nema take yi ta kashe su tun lokacinsu bai yi ba , kuma in har itace zai aura tabas da yawa zasu gudu daga gidan nan da kafaffuwansu sai dai Allah ya ba kowa hakuri, sai ga baban albishir da safiyar nan?
Elhaji Hamza da mamaki ya ce" Ikon Allah ku dai mata bakwa girma? meye na daga Muryar kuma?"
Hajia Amina tana dariya ta ce" Ba zaka gane ba Elhaji ba zaka gane ba baban yara, walahi mu kam alhamdulilah, gaskiya a zo a baje mana haja mu kai harka iya harka, domin koda an kai su kaya da dukkan abubuwan da ake kaiwa na tada sai fa mun je mun yi gaisuwa da maraba kafin babar ranar, wai yaya aka yi bamu ji ba tunda wuri? innalilahi ya dace a zo a fitar mana da anko dan kuwa a yau yau sai teloli sun mana dinkunna na daurin aure, raba aiyukan zamu yi wasu su nufi harkar teloli, wasu su nufi harkar girke girke , wasu su nufi harkar gayyatar jama'a domin Damagaran kaf sai ta dauka, ayiyiyiyiyiyiyirrrrrrr"
Hajia Binta ta yi dariya tana dafe haba ta ce" wanann shagali haka? gaskiya Elhaji daina zarro ido, bari a bugawa yaran nan du su tataro su zo su aurar da d'ansu, kai masha ALLAH"
Baba da ya ga abin nasu ba na karewa bane sai ya mike yana murmushi ya yi gaba , domin shi da kansa wani farin ciki yake ji na lamarin nan har cikin zuciyarsa
Yana fita Hajia Amina ta ce" Abin mamaki, na gaza gane yaushe haka ta faru, jiya ma fa yarinyar nan ta zo ta yi tijara a gidan nan"
Hajia zainabu ta tare da fadin" Ni zan fada maki tijara domin ko a jiya sai da ta tabbatar min lokaci take jira ta amsa kiran matarsa ba mu ba ko shi kakan nasa sai ya gagara ganinsa, ke dai du inda maganar nan ta fito daga wajen Elhaji ne, kennan dai yana hankalce da ita ko? dan na tabbata ko jikinsa duka kunnaye ne ba zai taba daukan magangannunmu in ba gani ya yi ba, Allah mai iko"
Hajia Binta a tausashe ta ce" Na sha fada muku, Elhaji bai kai tsufan da zai shirufce ba, baya ne ya ba duniyar ama komai yana sane kuma yana hankalce, yana yiwa abu uzuri ne idan ya ga da gaske ne yake shiga,, yanzu ba gashi ba? Allah ya sa a fasa natan dan gaskiya ba zamu so wace zata zo ta wulakanta mu ba da yayanmu, kaf dangin nan shine a tsaye a kanmu , idan ya auri muguwar mace ai mun shiga uku"
"Hakane Hajia, kin ga bari in tashi in san na yi, bari in yi kiran iyayen nasa na nesa ma su taso dan abu nasu ne maganin a kwabe su, ba zamu taba yarda a yi auren nan a boye ba, kaf duniya sai ta ji, bari ma ki ga in sa auta ta ɗora a Tiktok" Hajia zainabu ta fada tana mikewa
Hajia Binta ta zarro ido tana fadin" Kin ga, ke zainaba zo fa, kar ki janyo mana rigimar da zamu gaza lashe wutarta a gidan nan, barshi ya sanarwa duniyar kin ga rabu da daukan magana walahi"
Ina tuni ta fice tana ta guda, dama itace karamar su domin bata wuce shekara arba'in da uku ba , yarinyar mace ce, haihuwarta daya da shi daga nan ba'a kuma ba, kuma ta ki barin gidan take zamanta domin duk wata kyautatawa ta rayuwa tana samu a gidan Elhaji Hamza, harta dukiya zata yi abinda ta ga dama ne a lokacin da ta ga dama, y'arta guda da shi khalisat ana kiranta da auta tace Allah ya raya musu abinsu, sannan a tunaninta auren da y'ar aminiyarta ce, domin tana tune da karar da kawar Tata ta kawo shekaran jiya, ta yiwu da ya je yin sulhu dan ya kashe fitinar yace a ba AL'WALID, shine kawar Tata ta boye mata wannan abin arziki? lalle sun tsinta a kasa, sun haye, koda yake ba iya su ba ita da kanta ai daga yanzu hayewarta ta yi kololuwar sama, abin arziki zai ninku domin zata janyo yarinyar a jiki ne sosai ta mora fiye da da
Murmushi kawai Hajia Binta ke yi ta mike ta nufi ciki wajen Hajia Inna saboda su dan zanta kan lamarin sannan ta ji in su yi gayar? saboda ko yayane itace baba ita ke saka duk wasu tsare tsare a gidan, kuma ta rike girmanta domin yawancin lokuta ita ke tsawatar da wasu yan fitintinun, a tsakaninsu ma babu sai abinda ba za'a rasa ba na zaman , a tsakanin yaran ne akoy rigingimu, danma sun aurar da su sai kwaya hudun nan da suka rage, su dinma fitinarsu ba kadan bace, ama kuma sunna tsoron d'an nasu sosai.............
Fitar baba Hamza tare da direba da makocinsa da kuma yaron makocin nasa suka fara tafiya wajen baffan MUFEEDA, a garin Damagaran yake zaune, talaka ne, domin bashi da karfi , wannan dalilin ya sa in ba ta kama ba ba zaka taba Sannin sunna da shi a raye a duniya ba, ama shi baba Hamza ya san shi, dan a lokacin da suke yawan samun matsala da uban ya zo suka hadu da baba Hamza ya zo da d'an uwan nasa ya kawo shi gidan
Basu wani sha wahalar samunsa ba, suka same shi cikin suturarsa da rufin asirin Allah, dan kuwa mutun ne mai nagarta da godiyar ubangijinsa
Bayan sun zauna , baba Hamza da abokinsa sun karra gaisawa baban ya dubi mutumin da shima zai ba shekaru sittin baya, a tausashe ya ce" Malan Abdullahi sai ka ganmu kamar daga sama ba sanarwa ko?"
Malan Abdullahi ya yi murmushi ya ce" A'a ba komai Elhaji, ai ko wani lokaci kofa a bude take in sha Allah, ina fatan komai lafiya"
Baba Hamza ya sauke ajiyar zuciya ya ce"
07/12/2024, 15:03 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*🇳🇪
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da uku(23)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
👉0912 262 1080
LABARI
A tausashe baba Hamza ya ce " Eh to,, lafiya kalau malan Abdullahi, sai dai tafe nake da wata magana wace nake kyautata zaton samun kyakkyawar fahimta a wajenka harma ka sanar da d'an uwanka, ko Elhaji sabitu?"
Elhaji sabitu ya furta" Kwarai Elhaji, in sha Allah"
Baba Hamza ya dora da fadin" Maganar aure ce ta tashi ta yaron nan dake neman yarinyar wajenku, wato Mufeeda,yanzu haka maganar da nake yi maka jibi jibin nan in sha Allah za'a daura auren, malan Abdullahi ka san aurz hukunci ne na Ubangiji, kuma kasantuwarmu datawa ya zama wajibi mu zo mu bada hakuri mu kuma sanar cewa ba ana nufin babu maganar da ita yarinyar nan din bane, a'a, ana nufin za'a yi daga baya idan Allah ya aminta, ina fata zaka yi mana kyakkyawar fahimta"
Malan Abdullahi kansa a kasa har ya gama sauraron magangannun baba Hamza
A hankali ya dago ya dube su gaba dayansu, kwarai ya san su waye su, Sannin da ya musu ba na iya gidan rediyo bane , sani ne na farin sani, ya san cewa ba'a fara dan a yi cuta ba, ya kuma san cewa in dai wani abin ya bulo to fa lokacin abin ne ya yi kawai, sai dai tashin hankalin