Showing 99001 words to 102000 words out of 190762 words
Chapter 34 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
wa inna ilaihi raj'une gimbiya! An ci amanata, an cin min ina barci, an ga daren farko, gimbiya! gimbiya kina ina"
Mama dake saman salaya tana ta addu'a ta yi wuf ta mike har hijabinta na tadeta kamar zai kidaya m da kasss ta yi sauri ta rike tana haki ta shiga rarumar wurare tana neman ky din dakin nata bayan a daf da ita ta ajiye da zata fara sallah
Da sauri Khadeeja ta mike zaune tana zarro ido, a lokacin da yake kara matsowa ihunsa na tayar da kowa a gidan Domin harta mama Fateema sai da ta zabura zata fito kuma sai ta dakata ta yi tsaye tana sauraro saboda wani tunani da ta yi cewar haka kawai ma matarsa tace yakan tada irin haka wani lokacin cikin dare
yana matsowa suma sauran ya'yan sunna farkawa gaba dayansu a tsorace har gware suke yi sannan suka hade sunna kallon kofar da Mama ke kokarin budewa da ky din nata, cikin ikon Allah ta gaza kamo na dakin tsabar firgita da ta yi
Murya a raunane Lubna ta ce" Mun shiga uku, waye ya tabo Aba?"
Khadeeja ta yi tsuru , dama ba barcin ta yi ba, idannuwanta sun rine sosai, gaba daya daren bai fara Bama ama ganni take yi yayi tsayin gaske, dan ta kasa samun barci kasa kasa ta ce" Koma waye ya tabo mana rigima kuma shi da Allah gaskiya saboda Bama yannayin guje guje!"
Kofar ya dora hannu yayi bugawar farko zai yi ta biyu Mama ta bude ta bayyana a gabansa tana haki ta ce" Lafiya? waye ya mutu? ko auren aka fasa?"
Aba ya zarro ido yana kallonta ya ce" Bakinki ya sari danyen kashi na safe irin bakin nan, auren waye za'a fasa din? to ai ko mutuwa na yi na bar salahu a daura auren nan da kike tsaye kumatu na maki rawa kina janyo min alkaba'i ko kunya bakya ji!"
Mutanen da suka biyo shi sunna tambayar lafiya? kanneen amarya ne su biyu ne suka kalli junna , sai amaryar da ta bude kofarta ta yi tsaye tana kallonsa dan ta san halin abinta, idan ta yarda ta shiga abinda ya shafi gimbiya da shi itace a matsala ba kowa ba
A hankali Mama ta ce" Elhaji gani na yi dare fa ya tsala, kuma ai ka san gidan cike da mutane, dan Allah mu je"
Aba ya girgiza kai ya ce" Ku kuka ga dare, mu a balaki muke, Mu je ina? gimbiya an wulakantani, an wulakanta maki Ni, an zage Ni tasss innalilahi wa inna ilaihi raj'une gimbiya yanzu aka shaƙar maki kwalata"
Mama ta zuba masa ido, sam bata yarda wai an zage shi an kama kwalarsa ba, haka kuma bata so koma meye ya fada a idon bakin mutanen da suke gidan yau, labarinsa suke ji, harta fateema ba zata so ta ji ko ta ganni gannin idannuwanta ba, Allah ya taimaketa ma bata fito ba, ta kuma san ta farka dan kuwa hargagin Elhaji in ya fara ko me kake yi sai ka jiyo shi
A hankali ta ce" Mu je bangaren naka mana Abansu? mu je dan Allah"
Ya girgiza kai ya ce" Karima zaki miko min, ina take? ke dan ubanki mai jan ido ashe kannin d'an iska ne, maganar nan ta daren farko ya gani ko bai ganta ba wace kuke yi a wayar taki ? ita kawai nake son sani!"
Mama ta zarro ido, lokaci daya ta dafe kai, ta rasa abinda zata yi, wata irin kunyar furucinsa ta rufeta, da sauri ta rike hannunsa bata tsaya wata wata ba ta ja shi kiiiiiiii suka dauki coridor din da zai kai su bangarensa yana tirjewa yana faman fadin ta bashi Karima kawai , ita kuwa tana janshi da karfinta sunna karra yin gaba
Amarya na gannin haka da sauri ta biyo bayansu , cikin ikon Allah hakama yan uwanta suka mara musu baya dan kuwa wannan lamari su zasu so ganewa idannuwansu komai, cabdijan lalle ana gwarama a gidan nan
Mama na kokarin bude bangaren nasa da ky din wajenta ya juyo yana duban kannen amarya da mamaki ya ce" To, ku kuwa ina zaku je? Nan din ai dakina ne "
Da sauri amarya ta waiga, da ta ga kannenta sai da cikinta ya juya, innalilahi gidan wa zasu je su kuwa?
Da sauri ta ja su suka koma ranta bace tana fadin " Ina zaku je? kunna gannin an tabo shi ne, ita kuwa so take yi ta tare shi ta rarashe shi ita kadai kamar yadda ta saba, Ni dai ina gannin tashi tsaye a wajen matar nan, kunna gannin abinda nake fada muku? gida a hannunta karfi da yaji nake rayuwa da su, dan na nuna musu nima na iya ne!"
Kanwarta ta ce" Lalle mun ga katt, ki ga fa matar nan yadda take tare shi kar yayi magana a gabanki, walahi sai kin karra tashi tsaye in ba haka ba kina ji kina gani zata maido ki gidan lungu "
amarya ta cije lebe a ranta tana ayana' sai dai mu kashe junna dan walahi ba zan bar gidan nan ba!'
Mama na budewa ta sake danko hannun Aba ta sako shi ciki sannan ta rufe wajen ta juyo tana kallonsa Da tarin takaicin furucin cen da yayi
Shima ita din yake kallo kafin ya tabe baki ya ratsa ta gefenta yana budewa ya ce" Aikin banza da an tabo ya'yan cen ki wani hayayakowa mutun , dadin abin y'ayana ne, ai na zata kina sakonni nan din wanka min mari zaki yi ai dan in gane tabataciya ce ke gimbiya, eh ajiye tarihi wanka min mari, shikenan ke da kin samu wani abin sai ki koma jarababiya Allah dai ya baki lafiya!"
Mama ta dafe kai ta karasa wajen kujera ta zauna tana dubansa ta ce" Yanzu fisabililahi wannan furucin da ka yi a kan Karima ka kyauta? yau koda ace haka take meye anfanin kai da bakinka ka daga murya kana fadin haka? bale inada yakinin Allah ba zai bari ta ci amanarmu ba? haba dan Allah haba Elhaji haba, kawai dan dai ka sa in biye maka mu yi ta barin abin kallo har a wajen yayanmu? dan Allah ka rufa min asiri ka sasauta wannan abin!"
Aba ya dubeta da kyau ya ce" Shikenan gimbiya, nace shikenan, in gama fada maki an ci kwalata, in fada maki an ce yayan yaron ya haifar da wata yarinya, kuma fa uban na zaune yake fada min hankali kwonce har yana fada min sau biyu aka yi abin, ke dai ga dukkan alamu shi wannan ba damuwarsa bace, tunda da suka fito ma yace shawara zai yi da ya'yan, ya'yan da ya san yan iska ne zai yi shawara da su? innalilahi an ci amanata"
Mama ta ce" Walahi ka daina kiran ya'yan wasu da yan iska, kuma ka daina kiran naka hakanan, saboda shi fa d'an iska idan Allah ya haɗaka da shi sai ka raina kanka, kuma Elhaji da kake maganar ya haifar da yarinyar mutane ne d'an iska kuma kake mamaki dan babansa yace zai yi shawara da shi bayan laifin da ya masa ai ba damuwa bane, kaine kawai kake muzanta y'ayanka kake wulakantawa, in ba wannan ba yarinya ce ta yi laifi an hukuntata sai a bata lafiya a ci gaba da yi mata addu'a, ama sai abu kake yi kamar wayonka ne ya ankarar da kai ba Allah ba, da Allah yayi niya sai lokacin da yayi niyar a sani zai tona a lokacin da tafiya ta yi nisa da me muka isa mu yi? ama rufin asiri na huwan rahamanu ya taimaka ga y'armu nan a tare da mu a daki tana cikin nutsuwarta shikenan sai ka ringa neman tayar da fitina? Ni fa bana so ka aura masa ita, saboda wulakanci sai ya biyo baya tunda ta yarda suke neman shanshantar da junna ta nuna masa ta raina mu, nawa ake musu auren handin su je gidan mijin su ci gaba da soyaya da wanda suke soyayar kafin a musu mijin? nawa ake yi musu auren su kashe mijin? nawa ake musu su gudu su shiga duniya? nawa ake musu kafin a daura su kawo cikin da dole za'a amsa? ka cika neman fitina, ka mayar da ni wata iri ya zamo har yayanmu na tunanin da bashi da kyau a kanmu wai Ni zan ja da kai, Ni din me, ka ga Ni dai ka yi hakuri, ko menene ka yi hakuri ama Ni kam ka ringa kiyaye idannuwan mutane da na y'ayanmu!"
Aba kallonta yake yi, lokaci daya ya karra yarda cewar du inda aka je aka dawo gimbiya nada wata kama, domin idan tana da wata kama bata tsoron uban kowa, bata gudun a yi abinda bai dace ba! in ba wannan ba ai sai in shaye shaye ta yi zata yi fito na fito da shi, ko kuwa bata gane me yake nufi ba? bari dai ya karra kwatanta mata
A hankali ya ce" Gimbiya, daga gidan su Mudansir fa muke, kuma kin ji abinda ubansa ya fada"
Nan ya kwashe komai ya fada mata
Mama ta zuba masa ido ranta ya ringa bacewa matuƙa, hankalinta itama ya tashi ta ce" Shi har yana da bakin fadin haka kennan shi uban nasa? Ok, ya kai karar, nan zai gane bashi da wayo!, ya kai karar, wato mun zo masa da laluma shine zai mana tsiya? dan an tambayi d'ansa ya fadi abinda ake son ji zai nuna mana ya fi mu son d'ansa? idan bai kai karar mu ba nice zan kai tasa, in sha Allah gobe da sasafe zan kai kararsa in shi matsiyaci ne!"
Ai kuwa Mama ta ringa sababi , har dira take tana karawa, du idan ta daka kaffafuwanta sai Aba ya dan zaunar da ita ya bi cikin da kallo a ransa yana ayana' na shiga uku, ji wata jarabar dama na san bata gane me nake nufi ba, ita dai in tana da wata kama du rikicewa take yi, an tabani ta fini fada, kamar ba ita ke fadan na yi fada ba, da da ita na je ta yiwu yanzu haka ana cen ana dakuwa da Gimbiya, Ni kam na auri masifafiya!'
, fada take yi kamar an aikota, har sai da Aba ya gyara zama ya ce" Yi hakuri mana ke kuwa, jibi fa daurin auren Anmy, in muka kai karar gobe ai kin ga ba zamu samu nutsuwar bikin Anmy ba"
Mama ta sake tabe baki ta ce" Ba ruwana da wannan, a daura aure mu wuce polise station din!"
Aba ya girgiza kai ya ce" A'a, kin ga dai mijin Anmy baban mutun ne, a gama bashi tasa sai mu je a yi wace za'a yi da d'an dan iskan....., au da shi marar jin"
Mama a ranta ta ayana' na shiga uku, yanzu da ban masa haka ba da yana nan yana fuzgewa ina riko shi, Allah ka kara haska min hanyoyin da zan bi dan in karra koyar zama da wannan bawa naka
A bayane ta ce" Ba laifi ai akoy gata, aikin banza bari in je in duba maka ita, idan har abinda ake tunani hakane ban san irin dukan da zan yiwa Karima ba!"
Ta mike tana huci, Aba ya rikota ya maidota ya zaunar ya ce" A'a, kyaleta, Ni gaba dayama wani tausayinki nake ji baiwar Allah, kin ci abinci kuwa? sannu gimbiya in sha Allah Karima da uwarta ba zasu kashe min ke ba, yi kwonciyarki a nan, Allah ya baki lafiya barta a gama taron nan sai mu ci uwata"
Jikinta ne ya dauki wani irin nauyi , lokaci daya tunanin da take yi a kan hailarta ya dawo mata, haka kuma yannayinsa ya tabbatar mata, domin tunda Allah ya bata ƙaruwar Anmy shine ya fara sanar mata, haka wanda ya zube din nan shine ya sanar mata, kuma ta irin haka ne yake sanar mata, ya ringa fadin zauna ki huta, Allah ya baki lafiya kennan
Wani irin nauyi da fargaba suka darsun mata, tunani take yi yaya haka? mutumen da take faman gannin rabuwarta da shi kuma shine a yanzu da shekarunta suka kai arba'in da hudu tana daf da rasa damar daukan wani cikin , wani abin ya samu? innalilahi ciki kuma? ita ai ta barwa matansa, ina ita ina ciki fisabililahi?....... innalilahi yanzu yaya zata yi kennan? kai gwara da za'a yiwa Anmy aure, da dan sauki, ta yi tafiyarta cen dakinta ita kuwa ta boye koma meye a yi shi a daka!
Madarar da ya dauko mata ya bude ya mika mata sannan ya kwabe babar rigarsa ya ce" Gimbiya, yau y'ayanki sun bani mamaki, ashe yaran nan ba zasu bari a taba darajata su kyale ba? sun birgeni, cewa suka yi sai sun rama abinda aka yiwa Karimar ma ai"
Dan tsai ta yi tana dubansa ta ce" Na'am? sai sun rama a kan wa? kai kuwa me kace?"
Aba ya yi dariya ya ce" Ni ai daga yanzu na gane sunna iya zuwa shago su kula da dukiyarmu , bale kin ga Anmy fa ba zan iya barinta ita kadai a gidan nan ba, sai na saka ido sosai kar a salwantar min da yarina, kawai motoci zan siyawa kowane daidaya sannan in sakar musu kudi su je su rama, mu za'a nunawa kudi? aikin banza da ban siya musu ba dan kar su lalace ne ai!"
Mama ta dafe haba ta ce" Wai su rama me? Allah ya kiyaye ba dai y'ayana ba, ka siya musu motar mun gode Allah ya karra arziki, ama bari in je mu zanta, ina zuwa ba zasu rama komai ba, su barawa Allah shine wanda ya san hanyar da zai shiryar da shi da ya'yansa, mu da muke da wasu ya'yan a gabanmu? fatan mu Allah ya raba mu lafiya da su, idan muka tsiro da haka ai mun yi garaje !"
Tana mikewa ya sake mayar da ita ya ce" Dan Allah zauna min, ke sai neman balaki, to ai kya bari gobe ki musu fadan yanzu dai zauna ki huta"
Ta rintse ido, du in yace ta zauna ta huta din nan sai kanta ya sara, yanzu abinda ta aikata kennan? kuma ga dukkan alamu abin nan ya dauki wata biyu, saboda watan da ya wuce bata ga jinni ba ga wani ya wuce, ita da farko ta zata tuni har ta shige monopose din ne, sai dai ta yi ta sauraron signe din monopose din bata ga daya ba, sai kuma ta fara haduwa da yannayin da take samu idan tana da junna biyu, lahauli ciki? innalilahi
Aba ya nufi ciki yana fadin" Kakabe min shinfidar gimbiya bari in yi wanka mu gama maganar kayan dakin na Anmy, Ni fa sai na mata kuma na fadawa tsohon cen, hakama sai na yi Gara, ba ruwana sai na yi!, kayan yanka kuwa gobe da sasafe in sha Allah za'a kawo shanuwoyin, bari in fito mu yi shawara, ni har Elhaji Umar ya gwada min shawara da iyali? Gimbiya bari in fito a kirawo kowa da kowa mu yi shawarar nan muma!"
Da sauri ta mike yana shigewa ta je ta gyara masa shinfidar sannan ta haye ta yi addu'a ta kwonta ta rintse ido, dan kuwa ba da ita ba, shawara? shi da wa? wai shawara , ya samu na makewa dai ya make ya saki na saki, a dai tado wata fitinar da ta fi karfinta, ba da ita ba walahi.
Jim kadan Aba ya fito ya samu Mama ta yi barci, ya dafe haba kasa kasa ya ce" Gimbiya dai Allah ya baki lafiya, yanzu kuma na shiga uku da barcin nan sai ta samu lafiya, ke da ake so a yi shawara kuma kya yi barci? salon a ji ace ban saba shawara da ku ba? akoy gobe ai, bari dai in sake leko shadar da zan saka ta uban amarya, kai Allah kennan mai wanke zuciya, da Karima kadai na haifa da na mutu da bakin cikinta!"
Mama na jinsa ya nufi dakin da kayansa suke , tun tana barcin gangan har na gaske ya yi awon gaba da ita
A dakinta kuwa tana yin gaba da Mama Karima ta furta", innalilahi wa inna ilaihi raj'une me Mudansir ya janyo min kuma? walahi walahi kun ji na rantse tunda nake ban taba yarda mun wuce ka'ida da Mudansir ba"
Khadija ta dubeta ta ce" Karima, ki yi kokari ki yi ta rokon Allah kar Allah ya sa a aura maki Mudansir, idan har kin ga aba ya huce ki same shi ki roke shi ya aura maki wanda ya zaba maki, idan ba haka ba Karima kin san in dai Aba ya aura maki Mudansir ba ke ba zuwa gidan nan da kowace irin fuska, Karima wuce ka'ida ya wuce ki ba saurayi dama ya ringa tarda ke makaranta? KARIMA school fa kike fashi kina binsa, ki yi fatan Allah ya wanke ki shine kawai sannan ki je ki amshi wanda Aba ya zaba maki shi zai sama maki kwonciyar hankali da Aba "
Daga haka ta yi kwonciyarta zuciyarta na tuna mata nata abin son itama, Su Lubna kuwa babu wanda yace da ita ufan domin gaskiyar kennan, basu sakota a gaba bane dan tana ta nuna abin tausayi ce ita, ba dan wannan ba da sun jima da fitinarta, ta yi abin mamaki mai girman gaske ta yi abinda basu taba tunanin zata aikata ba, kuma ba wani zagaye zagaye a kan d'a namiji ne!.
washe gari kusan karfe goma da rabi mahaifin Mufeeda ya sauka a garin Damagaran tare da direbansa da mahaifiyarta
Direct asibitin da y'arsa take ya je, sun same su zaune karkashin runfar da ake zama ɗan a huta
JARUKE na tsaye a gafensu mahaifinsu na tambayar abinda likitoci suka ce da kuma jikin Mufeeda
Auta ta ce" Dady, allurar barci suka yi mata, saboda jiya har karfe uku na dare ana fama da ita, sun ce jininta ya hau kuma ta ki sauraron kowa, karshe dai suka sakata a