Showing 48001 words to 51000 words out of 190762 words

Chapter 17 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

4009

na rawa , na tashin hankali da tsoron da take ciki ta ce" Ina zaka kai Ni?"


Motar ya tsayar ya juyo yana kallon yannayinta, kashe motar yayi da kula sosai irin nasa yace" Gidanmu zan kai ki in boye ki, kin san zasu iya nemanki a ko'ina banda gidanmu baby"

Idannuwanta ta rintse stilll jikinta na rawa ta girgiza kai a tsoracen nan ta ce" Nanma zasu zo nemana, saboda na rubuta takardar kai nake so in dai ba zasu bani kai ba su yi hakuri da Ni"

Ido ya zarro yana kallonta da mamakin wautarta, wannan ai shirme ne a kan me zata wani rubuta musu takarda? wannan yarinyar banza ce Walahi, shi da ya so ya kaita dakinsa a boye ya boyeta su zuba life dinsu asirinsu a rufe shine zata kwafsa masa har haka?, ai kuwa gaskiya gwara ya kaita gidan uwarta dan kuwa ya sani ne haukan Elhaji ya fi na ubansa bale nasa, ba zai janyowa kansa zaman prison ba ana zaman kalau

Tsabar takaici bai iya bata amsa ba ya dauki hanyar gidan mahaifiyarta

Yana karasawa ya tsaya ta kuma kallonsa tana zarro ido ta ce" To ai nan gidan babu inda babanmu ya raina kamarsa, ai in ya tashi in ya sameni a nan har kakata sai ya zane ba mamana ba, ka dai kaini wani wajen dai"

"kin ga , babu inda zan kai ki da ya wuce nan da kuma gidanmu, gashi kin yi wani shirme kin rubuta takardar da babu wanda ya aike ki aikata haka kin bari, ba zai yiwu in kai ki gidanmu ba, dole nan zan kawo ki in kuwa duniya zaki shiga sai in kai ki bakin boda!"
Ya karashe a zafafen da ya saka ta zuba masa ido hankalinta na son karra barin gangar jikinta

Fita ta yi daga motar ta nufi kofar gidan ta shiga bugawa, lokaci daya take jin wani tashin hankali da nadama na son shigar ta...... kuma abin mamaki da takaici bai tsaya ya ga yadda zata kaya ba yayi tafiyarsa ya barta tsaye sai dukan kofar take yi


kakarta ce ta zo da tocila tana haskawa ta kasa tana fadin" Waye da tsakiyar daren nan ke buga mana gida? lafiya? waye?"

Murya na rawa Karima ta ce" Ni ce, karime ce, ki bude min"

Ido kakar ta zarro , tana kokarin mikewa dan ta bude malan Karimar ta karaso ta kama kofar ta bude da sauri tana fadin" Karima, kece da daren nan ko Elhaji ne ya mutu?"

KARIMA ta kalli Mamanta ta girgiza kai ta shige ciki ta karasa kusan shinfidarsu ta zauna tana hade kai da gwuiwa ta saki kukan da take ta rikewa tun a hanya

Uwar ta zo ta zauna bayan ta gama leke lekenta ta gane Karimar ita kadai ce

Da murya sama sama ta ce" Ke, kukan uban meye kike min wai ba zaki fada min abinda yake faruwa ba? waye ya mutu? me ya fitar da ke daga gidanku da wannan daren? me yake faruwa ne? a me kika zo? inace jiya jiyan nan zaki hadu da bakon ki?"

KARIMA ta dago kanta, murya a birkice ta ce"
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Sha huɗu (14)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*





*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja




LABARI




KARIMA ta dago kanta murya a birkice ta ce" Bako? kin san wani irin bako ne kuwa? kin ga yannayinsa? a jigace tufafin jikinsa suke, jikinsa kuwa sai shunin dati yake yi, kina ganninsa kin san bai ajiye sisi ba bai ba wani ajiya ba, Mama....., sannan dan izala ne, dan kuwa daga yannayin shigarsa zaki gane, irin mijin da zai kaini ya buga min azaba a gidansa, ban taba Sannin a cikin ya'yan babanmu Ni ya fi tsana ba sai yau, walahi ba zan auri mutumin nan ba koda yanka namana babanmu zai yi ya soya ya cinye sai dai ya yanka, ba zan aure shi ba, sai dai in shiga duniya!"
Ta karashe tana fashewa da wani kukan

Kakarta ce ta kai zaune tana sallalalami ido waje sosai, ta ce" Ke, kina nufin guduwa kika yi kika nufo gidan nan? to walahi tashi ki koma, ko uwarki ta hadaki ku karra gaba hala kawai ki ja min masifa da ubanki marar mutunci? ba zan iya ba ki tashi ku tattara ku karra gaba ke da uwarki , dan kuwa Ni dai ba zan iya fitinar ubanki ba tun kafin ya zo ya karyani a gidan nan!"

Mamanta dake rike da haba ta kalli tsohuwar ta ce" Baba ki yi shiru mana mu ji abinda yake faruwa sai a san abin yi ama kin san nan ai gidana ne babu inda y'ata zata je ko?, ki yi shiru mu san mafita kawai dare ne fa sai daga murya kike yi, ke KARIMA yanzu gidanku ne yayi lalacewar da kika fito ba'a sani ba?, inace ta kofar gaba kofa biyu ce ? yaya aka yi kika fito? a me kika zo? shi baban naku bai neme ki ba jiyan ne ko me?"

KARIMA ta ja hanci, sannan ta shiga fayacewa mahaifiyarta abinda ya faru sala sala wanda hakan ya daga hankalin uwar ainun, ita da kanta ta san sun cira bata nuna ba, lokaci daya ta shiga kai kawo tana neman mafita, dan kuwa idan har ta yarda safiya ta musu a gidan nan daga ita har y'arta sai sun dandana kudarsu

Wayarta ta dauko ta shiga neman layin wani bazawarinta polise , tana bugawa tana fatan Allah ya sa baya gidansa dan kuwa a kaf tunaninta wannan itace kadai hanyar da zata bi a zauna a yi masalaha, domin idan gidan sarki tace zata kai shi a kirayeshi a masa magana kafin ta samu gannin Sarkin shi ya halakata, idan cewa ta yi ta je da yarinyar a zauna a yi magana hade su zai yi ya musu dukan mutuwa, a bayane dai ta riga ta gane Karimar ta saka su a masifa da tsakiyar daren nan, kuma ba laifin y'arta take gani ba, a'a, ta fi gannin na uban, domin da ace mutumen kirki ya zabawa y'ar da yanzu wani batun ake yi ba wannan ba

Sai daga baya ta gane bata da kati ne, dan haka ta ce da Karimar ta Bata wayarta ta buga

Sai a lokacin Karima ta gane baban tashin hankalin da take ciki harda na rashin wayarta a tare da ita, wayar da ba zata so ko mahaifiyar Tata ta san abinda ta kunsa ba bale wani ɗan Adam a kaf duniyar nan, wayar da idan har sirrin cikinta ya bayyana ta riga ta shiga uku kennan, wayar da bata san ita da kanta irin girman iya shegen dake cikinta ba , nan take ta ji juwa ta sake zubar da ita kasa a zaunen da take, sai kawai ta saka kukan da ya fi kusa kusa a tarin abinda take iya yi dan neman mafita

Uwar ta jima tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko duk wani tanadinta na kudi ta fito a shirye ta sa ta mike suka fice bata cewa mahaifiyarta komai ba dan abubuwan dake kwakwaluwarta ba zasu bata damar yin wani yunkurin ba, Abu daya ta sani Karima ita daya ta malaka a duniya, ba zata taba yin saken Elhaji yayi mata auren wulakanci ba, haka kuma ba zata yarda yarinyar ta rayu a nesa da gidan ubanta ba, dan kuwa ita Burinta a nan duniya ta koma gidan Elhaji ne, du tsautsauran halinsa bata tunanin a kusa kusan nan a irin yadda rayuwa ta yi zafi akoy namiji mai rikon gida irinsa, za'a ci mai dadi, a sha mai dadi, a daura zani mai kyau, a hau mota a yi yawo, shi dai akoy masifa da tashin hankali, wannan kuwa ai lafiya lau yayi abinsa, bale ita da ta san waye shi tsaf zata ringa nokewa yana fatatakar ya'yan da matan nasa ita kuwa ta zama ta cikin zuciyarsa wace ba zai iya yi mata komai ba...................................
Direct gidan aminiyarta ta nufa suka samu waje suka zauna sunna jira asubahi ta yi su shiga gidan, domin mijin aminiyar Tata abokin Elhaji ne kuma mutumen da yake taka shi idan ya so ne a kowani lokaci, domin babu wanda bai san waye Elhaji Hamza a duniyar Elhaji ba, tana kyautata zaton zai shige mata gaba su je wajen Elhajin dan a kashe wannan fitinar , kasantuwar haske ne ko'ina sosai da sosai da masu gadi suka musu magana ta nuna kanta sai suka barsu a nan din har safiya ta yi saboda ba zasu buɗe musu get a wannan lokacin ba, Ita Karima a nan ta yi kwonciyarta jikin Mamanta bayan ta kare yiwa katon get din nan kallo da ginin garun tana tunanin to yaya cikin gidan yake?, uwarta kuwa sai ta zubawa shagon Elhaji ido da fitilu suka zagaye shi tana kallo tana ayana abubuwa a ranta, tabassss bata da miji sama da Elhaji, zata koma dakinta ne ko ana ha maza ha mata
(To fa, ana wata ga wata)



A gidan Elhaji


Kasancewar Mama zazzabin nan rufeta yayi sosai da dare , ko da asubahi ta yi Baba ya kirayi dakinta gannin shiru bata wulga ba, ta sanar masa bata da lafiya ne sai ya fito da kansa da ky dinsa ya zo ya sameta a dakin nata tana lulube cikin abin rufa

Du irin tsauraran halinsa shi ya kamata ta mike ya balo mata maganin zazzaɓi ya bata , ta sha yana tsaye har ta shige bayi dan ta yi wanka ta kuma dauro alwallah sannan ya fice ya nufi dakin amarya yayi kwoking sannan ya dakata yana sauraro

Minti kadan ta bude dakin nata idannuwanta sun yi jajir na barci barcin da ta farka a shi

Kallo ya bita da shi tun daga kafarta har zuwa kanta kafin ya girgiza kai ya ce" Kennan ba ke kika bude bangaren naku ba na same shi a bude?"

Amarya ta bude idannuwanta da kyau tana karra sakin hama ta ce" Ni fa yanzu na farka, ta yiwu ko Hajia ce tunda ita ke kwana tana kai kawo"

Aba ya sake yi mata wani duban sannan ya girgiza kansa ya ce" Ai da lafiyarta kalau da bani da damuwa dama na san hankalinta a kan amanar da na bata na yayana, ama wai har fadi kike ita ke kai kawo, ita ta damu da yayana ai wannan nima na sani, sai ki tashi ki yi sallah in kin ga zaki iya, mace sam ba Sannin ciwon kai, kin ga bata fito ba ke ai sai ko fito ko duba, bayan wannan ai girkinki ne yau, a wuyan ki kula da komai kafin ki kwonta ba a wuyanta ba, ke kam inaga asara kawai na yi ta kudina na auro ki, sai na sauki na huta!"

Wani irin juyawa cikinta yayi, lokaci daya ta shiga kokarin bashi hakuri shi kuwa ya shiga buga ɗakunan yan matan, du wace ya buga dakinta zai daga murya ne yace ta farka lokacin sallah yayi har ya zo kofar Karima, wace yana bugawa kofar ta bude domin ba a rufe take ba

Turus yayi yana kallon kofar , kafin ya shiga ciki yana fadin" Ke KARIMA, ke kam an yi shashasha, sau nawa zan ce maki duk rintsi ki rufe dakinki ne? ji wata masifa yaya zaki kwonta barci daki bude? y'ar nan inaga idan magauta suka cin min ita zasu fara cin ma a gidan nan, ..........."
Yana fada yana kunna fitilar dakin

Da ido suka shiga bin dakin da kallo shi da amarya,
yannayin dakin idan ka gani ko yayane zaka saka wani abin a ranka

Wayar dake ajiye saman bed din ya karasa ya dauka yana jujuyawa, waya ce kirar iphone tamfatsetsiya ,

Da sauri ya dubi amarya wace ta nufi bayin ta tura tana kiran sunnan KARIMA

gannin bayin ba kowa wayam ya saka Elhaji dafe kirjinsa da karfi ya fita yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ina masu gadi, Hajia Hajia, ku fito an shigo gidan nan yau, ku fito an shigo an dauke KARIMA, innalilahi wa inna ilaihi raj'une ina kallon ina na yi sakacin da aka san wanda zan aurawa y'ata na barta ba tsaro bayan magauta da masoyansa cike suke da kasar nan? innalilahi wa inna ilaihi raj'une ga wayar daya daga cikin barayin ya manta, an sace min yarinya Hajia Hajia!"

Lokaci daya falon ya dinke da jama'ar gidan baki daya

Jikin Mama haka yake rawa zufa na neman karyo mata ta ce" Elhaji dan Allah saurara mu yi magana, wani irin shigowa innalilahi wa inna ilaihi raj'une, har a shigo a dauketa bamu ji ba? mun shiga uku"

Da muryarsa sama sama ya mika mata wayar baya ya dakawa masu gadi tsawar su masa shiru ya ce" Ba ga katt ba, bata gidan nan, kuma ga waya nan a saman gadon ta bayan kaf gidan nan daga Ni sai ku keda waya kun sani sarai , bana ba y'ayana waya ko mazan bale ita, Hajia Karima bata nan, sun dauke KARIMA sun tagayarani Hajia!"

Ya karashe yana dora hannayensa biyu saman kansa , ya'yan kuwa yan matan kuka ne suka saka na tsoro domin su tsorata suka yi sosai da lamarin

Hajia na kokarin shiga wayar dan ba cod a samanta amarya ta fito hankali tashe ta ce" ELHAJI, babu wanda ya dauke KARIMA guduwa ta yi, walahi guduwa ta yi"

hannun nasa ya sauke daga saman kai yana zarro ido , da baiban hannu ya maketa ta baya, sai da ta daku da Sidik rai bace ya nunota da yatsa ya ce" Lalle baki da mutunci, Ni zaki wulakanta ? y'ar tawa zaki ce ta gudu? me zai sa Karima ta gudu daga gidan nan? ai kaf y'ayana babu wanda yake jin maganata irin KARIMA, me zai faru da Karima da zata gudu? sai dai idan wani ya mata asiri ama lafiya kalau ai Karima ba zata gudu daga gidana ba, kina cikin masu bakin cikin ci gaban iyalina kennan? yanzu aka yi walkiya na ganki, ashe kema yar bakin cikin y'ayana ce, to kuwa ba zan iya zama da ke ba ki je na..........."


"ELHAJI!" Mama ta fada da karfin da ya saka shi kallota a firgice dan bai taba jin Muryarta sama sama haka ba

Ido cikin ido ta ce" Ka salami masu gadinka ka yi sallah muma ka barmu mu yi sallah sa mu zauna, tabasss yau zaka ga abinda ya fi karfin idannuwanka a gidan naka, idan kana son kanka da lafiya ka bi komai a hankali in ba haka ba nadamarka mai yawa ce!"

Ya bude baki ya fi a irga zai yi magana sai kawai ya sake duban yannayinta, da gaggawar magana ya ce" Uban kowa ya je yayi Sallah ya zo, banda ku"

Ya nuna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login