Showing 51001 words to 54000 words out of 190762 words

Chapter 18 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3990

masu gadinsa sannan ya nufi dakin Mama yana fadin" Gimbiya, walahi , walahi, idan da yawunki a wannan lamari ba zan daga maki kafa ba, gimbiya kina ji kina gani ake danganta Karima da guduwa? ke kin san karimata kaf ya'yan nan ta fi min biyayya a cikinsu, ama ba komai "

yana shiga ya kuskure bakinsa sannan ya ja sallayarta ya kabbarta sallah

jiki a mace mama ta bi bayansa sallar bayan ya kabbarta

Sunna salamewa Aba ya mike fuuuu da nufin fita

Da sauri Mama ta mike ta sha gabansa tana fadin" Ka dakata mu yi magana kafin ka fita, dan Allah ka fara bin lamarin nan a hankali Aban yara ka ji?""

Idannuwansa da suka gama yin ja ya sauke a kanta, muryarsa a hankali ya ce" Kin fa ji me tace wancen? kuma kina gani fa ba'a ga Karima ba, idan ban yi da gaske ba abinda suke zargi na iya tabbatuwa fa, Ni kuwa in saka kaina ina idan haka ta faru da ahalina? da na ji kunya, da wani ido zan bude in kalleku ku bale na waje? Hajia....." Sai kawai ya ajiye Hajiar muryarsa har tana rawa

A hankali Mama ta riko hannunsa tana dubansa ta ce" Ka zauna dan girman Allah "

Kujerar da ta nuna masa ya kalla ya ki zaman

a tausashe ta ce" ama kai ka san ya'yan yanzu an haife su ne ba'a haifi halayarsu ba ko?, ya dace ka koyi sasautawa kanka duk wata fitina kafin ka dauki mataki Elhaji ko dan lafiyarka, dan Allah ka yi hakuri ka zauna in nuna maka wasu abubuwan da ya dace ka duba kafin ka dauki kowani irin mataki ne"

takardar da mama ta ajiye a gaban gadonta ya karasa ya dauka, a tsaye ya bude ya shiga dubawa kamar wanda zai gane wani abu, sai yayi mamakin gannin da Hausa ne aka rubuta, dan haka sai kawai ya shiga karantawa

Mama na tsaye tana kallon yannayinsa, gumi na tsatsafo masa, hannayensa na rawa

a hankali ta matso murya a raunane ta ce" Abansu"


Aba ya dago ya zuba mata ido, yannayinta sai ya bashi mugun tausayi, girgiza kai ya yi ya juya kawai ya fito, hakan ya sa Mama bin bayansa da sauri tana kiran sunnansa, shi kuwa yana tafe yana kiran sunnan kowa dan baya so ace ya karasa falon nan basu fito ba, bai san cewa sun rigayeshi zuwa ba, sun fi shi shiga wani hali dan sun san yau y'ar uwarsu ta ja musu balakin da ba zai barsu ba, sun shiga uku, sai sun shiga halin da baki ba zai iya furtawa ba

yana fitowa mai gadinsa ya shigo ya duka sosai ya ce" Elhaji ana salama a kofar gida ana neman iso"

Aba ya dube shi rai bace ya ce" ina cikin wannan halin ne zaka kawo min masu Bara da safiyar nan?"

Sake dukawa ya yi yana girgiza kansa ya ce" Elhaji Hamza ne ke Magana Elhaji kuma yace lalle lalle a sanar maka shi ne"

Gaban Aban sai da ya sake faduwa ya tsare mai gadin da kallo kafin ya juya ya rigayeshi fita dan kuwa babu abinda ya zo ransa sai tunanin ko har magana ta jewa Elhaji ne? dan kuwa a kusa kusa bai ga dalilin da zai kawo Elhaji inda yake ba da wannan sanyin safiyar

Zaune mama ta kai tana furta" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ya rab ko menene ya tunkaromu ka yi mana maganinsa"

Amarya dake rabe ta samu kanta da amsa addu'ar Mama a bayane, wanda hakan ya sa khadija kallon amaryar, lokaci daya mangarar da Aba ya yi mata ta dawo idannuwanta, ai kuwa dariya ta so kubce mata da sauri ta mike ta nufi ciki tana fadin " Bari in yi fitsari"

Aba na fita filin gidan ya samu Baba zaune saman kujerar da mai gadi Ya bashi


Karasawa yayi yana kallon yannayinsa shima ya zauna a saman kujerar da mai gadin ya kawo masa yana dubansa ya ce" Kai kuwa tsohon nan lafiya zaka min safiya?"

Baba yayi murmushi kafin ya dube shi da yannayin serius sosai ya ce" Me ka yi kennan? me yake faruwa a gidan nan?"

Aba ya yi shiru zuciyarsa na bugawa, a hankali ya ce" Me na yi Ni kuma?"

Baba ya nuna masa yatsa ya ce" Ka ga ka kiyayeni, dama yarinyar nan bata son auren kake son yi mata dole? domin Ni dai na tabata maganar auren da muka zo nema ne jiya dan baka fada min zaka yiwa wata aure a cikin ya'yan gidan nan ba sai wace nace a bani aka bani, ita uwar yarinyar da yarinyar basu san Elhaji bane za'a ba auren da basu nufe Ni da zancen basa so ba sai dai su fadawa wani , kennan kuwa da sun sani da ina zasu je neman agaji? kulun ina maka fadan zafin nan naka bashi da anfani ama ba zaka rage ba, ai d'an yau ba'a yi masa dole, da ka fada min bata so da ba za'a dauko maganar Bama bale a direta a wannan katobarar, to ka ga, ka kula, sun sameni da mahaifiyarta sun nuna zaka yi mata auren dole ne ita kuma bata so , Ni kuma ban nuna masu na san zancen Bama bale har in nuna musu Nine mai neman auren wa Elhaji karami, dan haka ka bar maganar kawai kuma ka yafewa yarinya ta zo ta yi zamanta asirinmu a rufe"

Har ga Allah sai da Aba ya ji kamar zai kifa daga saman kujera, eh lalle ko ba komai d'an yau ya gigitashi da salonsa mai zafin gaske, ashe ya'yan yanzu baka isa ka ci alwashi a kansu ba? ashe har haka tabarbarewar zamani ta kai? an kai wajen da za'a yiwa d'an yau zabin miji ya sa kafa ya shure? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ashe dama Karima haka take? ashe ya haifi ɗan da zai hada shi da bugawar zuciya irin haka bai sani ba? yanzu tsabar hauka su rasa inda zasu kai maganar nan sai wajen Elhaji?

Da kula Baba ya ce" Ka dai ji abinda na fada maka, bari su shigo ka fada a gabana ka yafe mata ta yi shigewarta ka ji?"

Sam baba bai gane Aba baya tare da shi ba , dan shi ganni yake du yana fahimtarsa, bai san a irin wannan lokacin Aba tuni ya gama tsara dukan abinda zai gyara shi a zuciyarsa da kuma irin abinda zai faru a nan a yanzu ba, sai da su Karima suka shigo da mahaifiyarta suka duka a gaban Aba, baba ya umarci Karima ta ba Aba hakuri

Murya na rawa kamar yadda jikinta ke rawa ta budi baki ta ce" Babanmu dan girman Allah ka yi hakuri, dan Allah dan annabi ka yi hakuri, babanmu mutumen nan fa yaudarar ka ya zo yi dan kuwa irin yan sunna din nan ne masu mugun rikon akida mai tsaurin gaske, babanmu walahi kana ganninsa ka ga kasurgumin dan....."

"Tashi ki shiga ciki" Ya katseta da Muryar da ta saka zabura da sauri ta nufi cikin tana waiwaye kamar zata kifa tsabar tsoro da shiga uku, kamar ta juya ta bi duniya dan tashin hankali, domin bata san abinda zata tarda a ciki ba, shi kuwa a ransa ayanawa yake' Ka ga mahaukaciya irin uwarta sak, wai dan sunna ne , to da dan ubanki zan aura maki? KARIMA ban san yaya zamu karke da ke ba, Ni da kaina ban sani ba, ashe soyaya kike yi? innalilahi'

Aba ya dubi baba da kula ya ce" Elhaji, kana kan batun ka ko wace na zaba maka zaka amsar masa ko kuwa lalacewar tarbiyyar gidana ta baka tsoro ka janye?"

Baba ya dube shi, yannayinsa shi da kansa ya tabbatar masa yana wani hali mai girman gaske da bai taba ganninsa a cikinsa ba, ya so ace ya masa bayanin wannan ba wata damuwa bace, idan an fasa din ba wani matsala a bar yaran su zabi zabinsu duba da shima na wajen nasa har yanzu daukan maganar yake yi wata shatakai dan ya gane shi ya gane yannayinsa sosai ya kuma shirya masa surprise din da zata bashi mamaki matuka in dai aka daura masa auren nan, ama kuma ba zai so ace yarinyar ma an yi mata dole ba, dan haka a tausashe ya ce" In dai har yarinya ta amince, ina maraba da hakan, na fi kowa Sannin waye kai, lamarin yaran zamani kuwa wannan sai a bi su da addu'a kawai"

Gaba daya mahaifiyar Karima sai kanta ya so cushewa, tsoro ya kamata, tashin hankali ya shige ta, shin waye Elhaji baba ya nemawa auren nan har suka kiya! ta san dai da shi Elhaji babban ne ke neman auren da Karima ba zata gaza gane shi ba, ta yiwu wani a cikin yaran gidansa ne? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ai kuwa da Karima ta tafka kuskureb da ba zata taba gyarawa ba, dan kuwa koda baran gidansa ne mai kudin masu kudin anguwanninmu ne, innalilahi Karima wace irin shegiyar yarinya ce ne?????

Tana cikin wannan tunanin tuni Aba ya raka baba ya dawo, wucewarsa ciki ya sakata mikewa tana rabe rabe ta bi bayansa gabanta na faduwa tana ta addu'ar da bata san cewa ta iyata ba ita da kanta dan kuwa adu'o'in babu abinda bata kamowa tana shafawa da hannayenta, ko sallar asubahi fa bata yi ba ta nuna bata yi da baba ya nuna su yi sallah su karya sai su je, kawai ta nuna su je din ya fi a ranta kuwa ta kudurce sallah ce ta rama daga baya.


Sunna shiga ta budi baki murya a rarrabe ta ce" ELHAJI, Ina son in yi maka bayanin abinda yake..........."

Kau , karar dauke fuskarta da yayi da mari ya sa ta rike gefen kuncin lokaci daya ta daka tsalle tana sakin ihu fitsari na son kubce mata sannan ta saka ihun da ya sa kaf mutanen falon mikewa

Amarya sake boyewa ta yi da sauri, Mama kuwa ta mike da sauri tana zaro ido da karfin hali ta nufota tana fadin"
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺


*LABARI DA RUBUTAWA*

*SAJIDA NIJAR*🇳🇪

*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*

LITATTAFAN MARUBUCIYAR

DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na sha Biyar (15)*


*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
*META FORCE*

*menene meta force*

business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja









LABARI



A rikice Mama ta ce" Elhaji ya da mari? haba Elhaji subahanallah"

Da sauri mahaifiyar Karima ta Tare ta tana fadin" Ina ruwanki a nan? babu abinda ya shafe ki dan Elhaji ya dake Ni, ko ba komai Elhaji yayana ne, kuma uban y'ata sai dai maki gani ya mutu, du ba kece ke ziga min yarinya ba? du aikinki ne kuma in sha Allah sai kin ji kunya, yarinya sai ta yiwa ubanta biyayya, ta anshi aure ta gama koda mahaukaci ya haɗata zata je ta zauna in dai ina raye"

Mamaki ya kashe Mama a tsaye, hakama Karima wace ta dago a zabure tana kallon uwar tata da mugun mamakin furucinta

Aba kuwa karasawa yayi ya zauna yana girgiza kai ya kalli Mama tamkar kwai ya fashe mata a ciki ya ce" Sai ki zo ki zauna yar bani na iya, tace ba ruwanki gimbiya sai ki dawo ki nemi wani dalilin nemana da rigimar ba dai dan na mari wannan marar mutuncin ba!"

Sororo mahaifiyar Karima ta yi tana kallonsa, hakama duk wani dake falon

Aba ya girgiza kai da takaici ya ce" Ni zaki fitowa a baibai? a halayarki ai babu wanda ban sani ba, ba ni kike son wulakantawa ba? a tabani sannan a hanna ni magana ko? ba damuwa y'arki Karima gaki ga ita nan , ta yi gagawar fitar da miji tun kafin ranku yayi mummunar ɓaci, ki ji da kyau ba zan kyale Karima ba sai ta fada min gidan ubanda ta samu waya, kuma sai na zauna na bincike wayar nan tassss, sannan sai ta fada min hanyar da ta bi ta fita daga gidan nan ko in yanka shegiya in binne!"

Ya ajiye maganar yana cije lebensa ya sake bin ya'yan nasa mata da kallo, nan da nan kowace ta sada kanta dan sun san hali , yanzu shafi zata shafe su

Ya sake girgiza kai ya ce" Ke fa Allah ne ya toni asirinki na so hadaki auren nan da mutumen kirki kika kiya, shegiya du kin fi yarana muni a haka wai kema har gudun wani kike, na godema Allah da ba ke kadai na haifa ba , da na yi kukan bakin ciki a gidan nan"

Mikewa yayi bayan ya gama maganar ya kama hanyar coridor din dakin matansa ya kuma dakata ya dube su ya ce" In sha Allah, KHADIJA ba zata watsa min kasa a ido ba, itace ta dace da wannan mutumen, darajar ta ce ta dace da shi, in sha Allah nan da yan kwanaki zan daura mata aure da shi zan kaita dakinta da kaina, a nan zaki gane kin tafka asara KARIMA dan sarai na gane dalilin da ya sa kika gudu,, ki sameni dakina dan ki bani amsoshin da na tambayeki nan da yama kafin nan na gama bincikar wayar taki!"

Mama dake tsaye kan hanyar da zai wuce idannuwan da ta ruko ta ɗora a kansa har ya shige ta gefenta ya wuce ciki

Da sauri ta bi bayanta tana fadin" Wace Khadija ce zaka yiwa auren nan da kwanaki?"

Aba ya dakata yana dubanta a hankali ya ce" Wata khadija gareni banda Anmy?"

Mama ta dube shi da mamaki tana yatsina bakinta ta ce" A'a, ban yarda ba gaskiya"

Aba ya tsareta da ido sai kuma ya juya ya ci gaba da tafiya

Mama rai bace ta ce" Walahi ka ji na rantse ba zai yiwu ba, ba zaka daukar min yarinya karama ka yi mata auren dole ba, Allah na tuba auren soyayar ma da ya aka kare bale wani auren hadinka cen da ka samo, walahi ba zai yiwu ba"

Dakatawa yayi, sannan ya juyo ya sake dubanta, A kausashe ya ce" Dama kina da karfin ikon hanna Ni yadda na so da y'ata?"

Mama ta dube shi cikin ido itama ta ce" Kana da tantama ne ko kana wasi wasi? gwara ka karbi tayin uwar wace ta fi yi maka biyaya, ba zan yarda ba, koda kuwa hakan na nufin karshen zamana da kai kennan a duniya!"

Hannunsa na rawa ya dago yana nunata ya ce" Ni kike gayawa wannan maganar Usaina? Ni kike son wulakantawa a kan y'ar da na haifa da cikina Usaina?, to bari ki ji, ko Karima da na kyale dan na gane zalamar abin duniya ce ta saka ta bijire min, shi yasa zan bata nata zabin ta je ta ga meye rayuwar auren, ama kin ga ke da Khadija na isa da ku, walahi na isa da ku, da Khadija zan daura auren nan koda tana mutuwa ne, sai ki kashe naki auren

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login