Showing 90001 words to 93000 words out of 190762 words
Chapter 31 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
zuciya, abu da d'an uwa ta karaso murya a sanyaye ta ce" Mofi, plz Mofi mu je ciki"
Mufeeda ta juyo tana kallonsu, ta juya ta kalli wannan ta kalli wannan, muryarta mai zafi yau ta nema ta rasa, murya na yi mata gargada a hankali ta ce" Kun ji me yace? wai aure zai yi jibi? kun ji kuwa? wai ko dole zai amshi bukatar danginsa? dan Allah wai dan ya daga min hankali ne ya fada ko da gaske ne?"
Gaba dayansu sai suka gaza magana , dan auta tuni jikinta ke rawa
Mufeeda ta sake dubansu ta ce" Bai san irin darajar da yake da ita a rayuwata bane, da ba zai taba hada min kansa da wata halittar ba, kun ga Baima gane irin kishina a kansa bane ko? bab bai sani bane, ama dan Allah kirawo direba su zo mu bi bayanshi, fushi ne kawai yayi , na tabbata da zarar ya huce shikenan zai daina maganar nan, dan mun yi fada da su ne fa yayi fushin nan, kun san yana da shakuwa da su sosai baya so a taba masa dangi, plz baby yi kiran Cross mu bi bayansa plz"
Baby ta gyada kai ta amshi wayar Mufeedan dake hannun JARUKE ta shiga neman layin, JARUKE kuwa tana tsaye
Mufeeda na kai kawo, hawayen nan bai tsaya mata ba ta ce" Bai san irin addu'ar da nake yi bane du ranar da zan yi sallah ko? bai san cewa ina addu'ar da wata ta rabe shi gwara gawarsa a gabana ko? bai san ina cema Allah bana so ba? hum, lalle, bab kennan, ......"
Sai kuma ta yi turus tana duban su JARUKE ta ce" JARUKE, yi min kiran Dady, dan Allah yi min kiransa, wannan nacin da yayi kan mu taso yanzu yanzu in ji na menene..... innalilahi JARUKE kirjina zafi yake yi, kar aje maganar nan gaskiya ce....?"
Sai kawai ta cire abayar dan ta fara rike mata numfashi, ta barbaza gashin kanta ta ce" Kan baban bur'''''''''''''''', JARUKE bani shi bani, wayo Allahna zan mutu, wayo zuciyata wayo na mutu na lalace, wayo Allahna zan mutu, zan mutu, hello, walahi inaga da gaske yake, hello, hello dady, aure bab zai yi da gaske? shi yasa kace mu taho ko? dady kana jina kuwa.....? walahi ko Wacece sai na halaka..................................................................wayo kirjina numfashhhhhhhhhhhh......."
Ta saki wayar KASSSSS , ta rike kirji tana wani irin numfashi
Ihu yan uwan nata suke yi, hakama mahaifinta da mahaifiyarta a wayar ihun suke yi, domin uban ya daga ne ta warci wayar
"MUFEEDA, Mufeeda, Mofi! ta mutu, ta mutu!" Auta ke fada da karfi tana sakin ihun kuka
Da karfi JARUKE ta kamata tana jijigawa itama tana ihun ta mutun, masu gadi da abokansa ne suka karaso da gudu suka shiga tataba Mufeeda a yannayin da take ciki na rashin wadataciyar sutura , nan suka tabbatar musu da bata mutu ba, a lokacin ne kuma wayar mai gadin ta kwashi ringin, croossss da ihu ya sanar masa ya bude masa kofa dan sunna waje
A guje ya je ya bude suka shigo da gudu da motocinsu , nan suka cicibeta suka yi mota da ita, sunna waya da Elhaji Maiga kamar zai fado ta cikin wayar yana sanar musu gayanan, su GAGAUTA kaita babar asibiti gayanan zuwa
Asibitin suka nufa da ita, da kannenta rungume da ita, ba wai iya Mufeeda ba, harta JARUKE dake da makamancin halayar Mufeedan zuciyarta tafasa take yi, alwashin dake ranta kuwa mai tsananin gaske ne, ta daukarwa ranta cewa idan har da gaske aure AL'WALID zai yi sai ta jigata matar nan ko y'ar uban waye!
(Wannan kennan)
Tuki AL'WALID yayi gaba daya zuciyarsa a cinkushe
Ba dan komai sai dan irin lokacin da ya bata yana kallon ikon Allah da tarin surprise na halayarta, furucin bakinta kuwa tamkar ba wace ya sani mai hakuri da biyaya ga umarninsa ma ba wai na iyayenta ba, a tunaninsa Mufeeda ko wuta iyayenta suka hura suka ce ta fada zata fada ne tsabar biyaya, ashe haka take magana da iyayenta? kuma tsabar raini ta dube shi tace da mai aiki take magana, to ko mai aikin ce wace ta zama a tsakaninta da mahaifinta ai ba karama bace, kuma shakuwa akoy tsakani , koda mai aikin ce ai ba baiwarta bace da zata yi mata magana a haka, idan da tarbiya kuwa Bama zata yi haka din ba,
sai furucinta a kan maganar auren nan, a tunaninsa idan ya sanar mata eh zata iya daga hankali, ama in har ya nuna mata abin nan ya zo ne kai tsaye maganarta na nan, zata bar maganar a wuce wajen ko? sai gashi cikin ikon Allah magangannu da yannayinta kamar na wace bata cikin hayacinta....., hum Mufeeda kennan, ita da zarar ranta ya ษaci ko hankalinta ya tashi sai ta ringa furuci irin haka kennan? , Tabas ya san yana kaunar yarinyar saboda tunda ya hadu da ita cikin kyautata masa da y'arsa take, in anguwa ta je sai ta yiwa litle kyautar wani abin, kulun cikin yiwa litle siyaya da nuna soyaya take, dole zai so ta, saboda tana kula da dukkan abinda yake so tana kuma taya shi so, a wannan zuwan ne ya fuskanci abubuwan nan, sai ya ji du ta sire masa! hummmmmm
Tunda ya tunkaro gidan ya hangi babar kofa a bude, kuma abin mamaki mutane na dan kai kawo kamar ana yin wani abin
Sojawan dake tsaron kofar sunna gannin motar suka sara masa, ya tsayar da motar a lokacin da daya ya zo ya sake sara masa sannan ya gaishe shi
da kula ya amsa, a nutse ya ce" me yake faruwa a gidan ne?"
Sojan nan ya ce" Baki ne ke zuwa, ance a bude gida a kuma bar kowa shiga na shirye shiryen auren naka ne sir"
Ido ya dan zarro, kafin a ransa ya ayana' toh fa' Sai kuma ya zubawa gidan ido, kafin ya daga birkin ya dan shafa accelerator ya gangara ciki a hankali yana yi yana gaisawa da masu aiki da masu gadi da direbobi dai da sauransu
Tun bai bude motar ya fito ba ya ringa jin rurin kurma da gudunta, dan haka ya bude motar ya zuba mata ido
Da gudu ta karaso , ta sha kitso harda kunshi a hannayenta, ta shiga nuna masa tana dariya sannan ta masa alamun tambayar wai aure zai yi jibi? ta nuna da yan yatsunta kafin ta kafe shi da ido
Dariyar da take, da farin cikin da take kawai ya zubawa ido, a hankali abinda ya faru da shi da Mufeeda ya ringa wankewa, har ya bi kyawawan hakoran kurma dake waje da ido kafin ya samu kansa da sakin murmushi yana dubanta ya dan rage tsayinsa ya dan bude murya da kuma hannayensa ya ce" Farin cikin ki yau ya saka Ni farin ciki litle, waye ya maki kitso?"
Dariya ta yi tana son sake yi masa tambayar wai aure zai yi? sai dai da ya bangarar da maganar a dole ta yi shiru dan mahaifinta ya yi mata horon da idan ta dauko magana in bai bi ta kai ba to fa baya so su yi maganar, hakan ya sa tana dariya ta nuna masa baban falon kakanin nasa ta duka da sauri ta rubuta" Baki sun zo, ta ko'ina sunna zuwa, tunda ka fita da safe aka fara baki, papa harda auntyn Maradi ta zo da yaranta duka"
Dogon rubutun ya bi da kallo, sai yayi murmushi kawai ya kama hannunta ya yi mata nunin ta je zai je masallaci, domin an fara kiraye kirayen sallar magariba, a ransa yana tunanin ko ina ta bar ipad dinta da take rubutu a ciki ta nunawa mutun? lalle yau tana cikin farin ciki da har ta iya fitowa babu ipad din nan, farin cikin nan nata ya saka shi a madaukakin farin ciki har ya manta abinda ya baro na takaici.
A gidan Aba
07/12/2024, 15:11 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na ashirin da shida (26)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐0912 262 1080
LABARI
A gidan Aba
Wuni aka yi aka ta shirye shirye da kai kawon da ya'yan suka gaza fahimtar ko na menene,
Da yama ta yi gidan sai ya dinke da ya'yan gidan Hajiar Larabawa da duk wasu wa'inda suka shafi Mama, hakan ya sa yan matan suka ringa yiwa kansu tambayoyin to wai me ya sa suka fi yawa bayan ance auren karimeme ne kuma ita babu dangin mahaifiyarta ko kadan? , karshe dai Lubna ce ta dube su a matsayinta na wace ta fi su fahimtar abinda yake faruwa ta ce" Ku kuwa, kun ga Mama baba itace mamanmu gaba dayanmu, kuma kun ga baba da maman karima basa shiri, sun yi fada, Karima tace zanetama ya yi ko?, to kuwa kun ga dole a rasa danginta, kuma mutanen gidan Hajiar Larabawa kuwa dole ai su cika gidan nan, in baku manta ba shi baban namu da kansa ya sha cewa koda Mama bata gidansa Hajiar ai mamansa ce, hakan na nufin ko baa akoy zumuncinsu shi da Hajia da gidan nan, to kuwa dole ya'yan gidan su cika gidan!"
Khadija dake zaune ta rafka tagumi a cikinsu ta cire kai, gaba daya bayanan Lubna bai wani shige ta ba, bale da ta ga yau samarin gidan tunda safe an tafi da su wajen mai dinki wai, su kuwa dama ba kasafai ake daukan awonsu ba, yawanci ma mai musu ษinkin tana da awonsu idan ka rame kadan , ko ka karra kiba kadan ne kake sanar mata shikenan kuwa in ta yi maka dinki dasss da shi, domin da ta ki fara yi musu ษinkin zamani nema suka so sakata a wani hali , dan so suka yi su daina bata ษinkin, sai Mama ta sa y'arta ke musu, itama yan mata ce mai tafe da zamani, ake kamanta musu na zamanin ama kuma ba'a mugun dame sun nan , shi yasa Khadija ta fi ganewa a yi mata bubu ta kashe dauri, cewa take yi gwara ta san su ta jibga a kayanta dinkunna ne classss masu hawa kowani kamar jiki kuma ba baba ba yaro du wanda yake so idan ya dinka zasu yi masa kyau, da ta saka buhunnan sket din da ake yi musu hawan jinni ya kamata
Shekeke ta kalli Lubna ta ce" Ke, kin ga wace ta zo? cousine sister din Hajiar Larabawa, kin san a ina take ai ko? ba sai na fada maki ba, kuma kin san ai basa shan innuwa daya da Abanmu, ke dai kin ga bari in karra leko Maman ko bata da lafiya ne? kuma abin mamakin bata da lafiya za'a ringa cenja su kujeru? ke wai kin ga falon kamar ba na gidan nan ba fa, Ni kam sam ban son abin nan wollah!"
Lubna ta rafka tagumin itama, Karima ta ce" Tashi ki gano mana manan, du kun karra birkita min lisafi, na rasa ta inda zan kama walahi "
Khadija ta mike ta dauki hijabinta ta zumbula a saman farar rigar dake jikinta, rigar damamiya ce a jikin nata sosai, kuma harta shap din pant dinta da breziya ana gani, haka take sakata ta lafta hijabi, idan sun zauna daga su sai su a dakin dayarsu sai ta cire......, ita kam haka Allah ya haliceta, tana son saka yan iskan kaya kamar yadda Mama ta yiwa kayan nata sunna, dan kuwa karfi da yaji ake basu dama su je su dan zazago kayan sakawa da cikin gida, dan ba rayuwa zasu yi dawamamiya da atampa ko lesh ko shada ba, dole an saka na shan iska, idan fa suka zaba aka gama an gama dauki ba dadi da ita, domin kalar kayan da take daukowa ba irin na ya'yan Elhaji bane gaskiya.
Lubna ta girgiza kai ta ce" Ji wata shegiyar riga, Allah sai na cira rigar nan idan kika cireta!"
Khadija ta gyatsina kunci ta yi gaba tana fadin" Sai in cira taki nima Malama ku ji kai neman balaki ina zaman zamana, mu ji da abinda ke damun mu ma kunna son saka mu a uku!"
A lokacin da ta nufo baban falo, a lokacin Hajia iya ta nufo coridor din da abin turaran wuta suka hade da Khadija
Da sauri khadija ta riko hannun iyar, tana buษe hijabinta turaran na shigarta kasa kasa ta ce" To, ikon Allah, abin alkhairi dumu Dumu haka, iya harda ke a gidan namu ko dai yah baba zai yiwa Hajia amarya ne bamu da labari ne Ni Dije?"
Iya tsohuwa ta janye abin turaran wutar tana zarro ido ta ce" Na ga Manzo idan na yi hali na gari, ke ki RUFAN asiri kar rabon a yi ya kawo Ni gidan nan, ban fa rike kaskon nan da kyau ba, a kanki kuwa a yanzu dai Elhaji sai ya kar da tsohuwa rami, wuce mu je kawali an fara kiraye kirayen sallah maza mu je "
Khadija bata gane komai ba iya ta tunkudarta dakinta ta rufe daga ciki ta zauna ta ce maza ta shige bayi ta yi wanka sosai ta hado da alwallah
Mamakin abin ya kama mara zuciya, dan ba zata tuna lokacin da ta ga iya a dakunnansu ba, bata taba gani ba, iya mutun ce mai matukar kamewa da rikekaffafuwanta inda Allah ya ajiyeta, tana zumunci da su sosai ama idan ta zo bakin baban falon, wani lokacin nan dinma bata shiga take juyawa, cewa take yi babu abinda zata shiga dakin yara ta yi, ita uwa ce ba zata shiga dakunan iyayensu ba, babu ruwanta da wannan katsalandan din, Sai gashi yau har a dakinta, ta kuma sakota gaba ta yi wanka? to dai ta san tarin tsaftar iya, dan a wajenta ta dauko dabi'ar yin wanka sau uku bayan ba matar aure take ba, har ga Allah a gidansu idan ka samu ka yi na safen nan sai na dare da mamansu ta koya musu karfi da yaji, ama da take zuwa gidan iya ta dauko sirfar wanka na uku a saman na biyun nan dan a cike gayun a bayyane
A nutse ta darji jikinta ta dauro tawul ta fito bayan ta dauro alwallah
Tana fitowa iya tsohuwa ta ce" Ina suturarki?, dauko abaya bak'a ki saka maza y'ar albarka
Karasawa ta yi ta dauko abayar, ta ciro pant da breziya ta juya ta koma bayin ta rufo sannan ta saka ta dawo tana duban iya ta ce" Iya wai me ake yi a gidan nan?"
Iya ta dafe haba ta ce" Kya barni da tambaye tambaye y'ar nan ? maza yi sallar , mu du mun yi kunna daka kunna kirba wani balaki? yi maza , yi ki gabatar abokiyar taya fira a kabari"
Khadijah na duban iya ta zumbula hijabinta ta karasa saman dardumarta, ta karra kallon iya ta ga ta dage kai sai kawai ta kabbarta sallar ta nutsu ta shiga gabatar da sallar magariba
Murmushi iya ta yi ta sake dubanta kafin ta gyada kai ta ciro turaran da mama ta bada a yi mata ta gyara zama
Khadija na gamawa iya ta karasa ta zuba turaran a wuta ta saka mata a cikin hijabinta tana kallonta ta ce" Zauna da kyau ya bige ki"
Zuwa wannan lokacin tsoro ya fara shigarta, bata gama tantance komai ba aka kwonkwasa kofar
Iya ta je ta bude tana amsawa kafin ta bada hanya
Mama Fatima ce ta shigo tare da auntyn asibiti, suka karaso fuskokinsu washe da fara'a
Mama Fatima ta kama khadija dake kallonsu ta cire mata hijabin dake kanta , auntyn asibiti ta ware sabuwar atampa baba suka rufa mata
Tsoro ya dirar mata, lokaci daya gigita ta nemi zautar da ita
A tsorace ta damki hannun Mama Fatima, wace ta rungumota jikinga a hankali ta ce" Anmy, ki taka sawayena samu kai ki falo ne"
Tsoro ya sake darsun mata,, murya na rawa ta ce" Mama Fatima me za'a min a falon?"
Mama Fatima ta yi murmushi ta ki bata amsa suka karasa da ita falon, a lokacin yan uwanta kaf sunna falon da duk wani d'an uwa na jini da abokan arziki, uwa uba harda Hajiar Larabawa wace bata jima da karasowa ba, gefenta lalle ne jike, da turare da atampa sabuwa ta saka amarya a lalle
Sai da suka kaita gaban Hajiar Larabawa suka gurfanar da ita, Mama Fatima ta zauna ta riketa da kyau kasa kasa ta ce " Kar in ga kin bude fuskar ki, ki nutsu, ki yi shiru da bakinki, a gaban iyyayenki da kakaninki kike, kar in ji wata firirita Anmy "
Khadija zufa take yi kamar an