Showing 45001 words to 48000 words out of 190762 words

Chapter 16 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3996

duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force

*shidai meta force crypto currency* ne

kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency

akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba

yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai

*TACTILE*

1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars

hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira

*Spillover*da*over flow*

wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu

to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*

*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja

LABARI



Murya cinkushe KARIMA ta bude muryarta sak, dan a yanzu ta gane ba wanda aka turota wajensa bane ke zaune, kuma yannayin shigar sa ba zai sa ta ga kimarsa ba ko kadan a zuciyarta domin a kaf gidansu ta fi kowa rike akidar mahaifinta dan kuwa Hajia Usaina idan ta saka wa'azin wasu malaman namu masu daraja yan sunna da suke wa'azi da koyarwar fiyayan halitta takan bar wajen a ranta tana ta aibatata da fadin lalle ta tabbata ba sai ta yi yakin shigo da mahaifiyarta gidan nan ba, idan baba ya ji da kansa zai saki Hajia Usaina ya maido mamanta domin ya sani mahaifiyarta har kasa kasa take zuwa yawon ma'uludi.

Murya a cinkushen nan ta ce" Ke Anmy, ina bakon? kuma uban me kike yi a nan?"

Khadija ta dago da sauri ta dubeta, sannan ta dube shi kasa kasa ta ce" Bata ganeka bane, bata iya zagi ba samsam salihatu ce ina zuwa"

Wajen da Karima ke tsaye ta karaso ta kama hannunta ta ja ta kiiiiiiii suka yi wajen coridor din falon kasa kasa ta ce" Ke , ki kama kanki shine fa mutumen na baba"

Ido ta zarro kafin ta dubeta da kyau ta ce" Me kike nufi? kina nufin wannan mai tsangalalen wandon ?"

Khadija ta gyada kai ta ce" Shine walahi, ama inaga saka kayan kawai yayi dan kuwa kin ga ai baba sai yayi bincike zai zaba maki miji ko? kuma kin san ba zai taba zaba maki abinda kike tunani ba, kawai dai zaba maki yayi kuma na tabata rikaken dan addini ne wannan "

KARIMA ta rintse idannuwanta, irin yadda zuciyarta ke dokawa kamar zata ballo daga bakinta ta fito ya fi komai damunta, kwarai damuwa ce mai karfi wace bata tunanin a nan gidan duniya dai a wannan karnin akoy wanda zai yi tsaye a gabanta ya sakata aikata wannan gigitar koda kuwa ubanta da uwarta ne

Rike hannunta da Khadija ta yi tana fadin" Jeki mana kar ki tsayar da shi " ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta afka

Sakinta khadija ta yi ta yi ciki tana tikar dariyar iya shege, nan suka hade da Lubna ta jata suka koma ciki gulma cike da ciki ta ce" Akoy yaki ba karami ba yau a gidan nan"

Lubna hankalinta ya soma tashi dan ta san halin kanwarta sarai, ba tsoron fitina take yi ba, hasalima yana iya zamowa Film a wajenta idan ana sama ana kasa, in dai ba lafiyarta za'a taba ba, dan haka ta hade gira ta ce" Anmy, menene?"

Khadija ta yi murmushi ta ce" Ke mutumen yana falo fa, ama idan kika ga tsayin wandonsa bakinsa nan" Ta nuna iya gwuiwarta tana sakin murmushi

Lubna ta zarro ido ta ce" Ke, kina nufin dan gidan rawa ne?, kin haukace ne?"

"ke, ba gwara dan gidan rawar ba da shi a wajen baba? dan sunna ne sak komai a bayyane yake, magautan baba sun cin masa zai aurawa Karima dan Sunna!" Ta karashe da kalar iya shege ta nufi wajen flask din ta dauka tana karra fadin" Bari dai na koma na idasa kashe kwarkwatar idona ke koma daki ki ce mun kai , Ni kuwa zan je na dauko maki komai sala sala, kai abin mamaki baya karewa Allah ka sa in mun mutu mu kwonta......"

Ta juya hankali kwonce ta koma falon, sai dai tana zuwa shi kadai din dai ta samu

Bayan ta ajiye kayan abincin ta zauna hankali kwonce tana fadin" Amaryar shiga ta yi ta fito?"

Ya dubeta bayan ya dan dage girarsa saboda bakin man nan da Elhaji Hamza ya shafa masa yana damunsa sosai da sosai, so yake yi ya tafi kamar a kaya yake haka yake ji, ga zafi ya ishe shi sosai Duda pankoki biyu dake kunne da kuma humudifier da aka kunna, ama ji yake kamar a cikin ruwa mai dumi yake zaune

A tausashe ya ce" To ai bata zo ba"

Khadija ta zarro ido tana dubansa a hankali ta ce" Kuttttt, yarinyar nan kar fa ta ja mana tashin hankali, gwara ta zo bari in leka dakinta"

Tana mikewa a tausashe ya ce" Zauna "

Khadija ta juyo ta dube shi, ita walahi dariya yake bata, wai zauna dinma na zai fadi irin ta mutane sak ba, sai yayi magana da makogwaro, gashi rusheshe a zaune dan kuwa duk da jalabiya ce ya saka a bayyane yake wannan ba karamin jiki ne da shi ba, Duda bata ga tumbi ba ama dai ta ga kafadu da damatsunan hannu, kuma wannan ta yiwu matansa uku zai SANKAMA karimeme ta hudu, Allah sarki su Karima a haka za'a kare? Allah kennan mai zancen karshe , Allah Ni dai khadija jikar ta gidan Larabawa a bani Safa Safa kar a bani irin wannan na manya ne, a RUFAN asiri a bani Abdul mu sha soyaya dan har cikin kuluna shine ZABINA.
ta idashe tana zama ta sake fuskantarsa, dan bata son manta komai a labarin da zata kai wajen yan uwanta dake jira a ciki

Da kula sosai ya ce" ama, ke din Wacece?"

Khadija ta dube shi, a ranta ta ayana' ina ruwanka da ni kuma?'

A bayane kuwa sai tace" Ni Anmy ce, ama ita matar taka sunnanta KARIMA yayanmu"

Murmushi yayi yana jin kamar yannayin takurar da yake ciki na son barinsa, dan kuwa a bayane yake karantar iya shegen da take yi masa, kuma cikin ikon Allah abin nishadi yake bashi, shi da kansa da aka gama shirya shi sai da yayi dariya kuma ya fadawa baba tsoho cewar koda yarinya ta kiya ba zai ga laifinta ba, to zamanin nan waye yake son namijin da ba dan gayu ba?

Da yannayin kalkaltar nan yace" Ina fata baki da ra'ayin dogon karatu a rayuwa?"

Khadija ta gyara zama bayan ta fitar da hannunta da kyau ta ce" Cabdijan, to ai Ni din nan da kake gani sai inda mai ya kare, karatu ko? na bokon nan dai ko? ai sonsa nake yi sosai"

Murmushi yayi a boye, a bayane kuwa yace" Ni kuwa bani da ra'ayinsa gaskiya, to mace ta zauna ta kula da ya'ya ai ya fi"

Khadija ta dafe haba cike da alhini ta ce" Allah kuwa na gode masa da ba nice Karima ba"

sai kuma ta shiga muimui da baki a ranta tana ayana', Allah ya saka katangar karfe da Ni da kai"

ta ɗora da fadin" Ama kuwa yayanmu ai wannan sai a cuci Karima ko?"

Sosai ya ji dariya na son kama shi, ra'ayinta na son karatu kuwa sai yake ji a ransa Allah ya sa wace aka bashin ma haka take, dan kuwa zai fi kowa murna ace tana son karatu koda ba wani zama zai yi da ita ba, dan yana son yaro mai karatu zai raineta ne har ta girma sai ya san abin yi , hakan zai sa ta kula da kanta ta yi ilimi mai kyau harma ta sakawa kurma ra'ayin hakan koda zuwa gaba bata da shi

A bayane ya wani kame ya ce" Lalalala, ba wani takura ai, meye a karatun bokon banda wahala? zata yi na addini a gida shima"

Khadija sai ta ji hankalinta zai tashi, ba zata taba so y'ar uwarta ta shiga irin wannan halin ba, su sun taso da son karatu a zukatansu sosai, ko dan shine kadai wajen da suke fita su sha shagalinsu hankali kwonce? domin du takurar da ake fadin ana yi a makarantar su, su basu gani ba dan kuwa su dadinta suke ji, nan ne wajen da suke abubuwansu kai tsaye, kuma a haka sunne salihan makarantar

A hankali ta mike jiki a mace ta ce" Bari dai in kirawota, ama dan Allah ka bar maganar nan, karatu y'ar uwata zata yi in sha Allah "

Ta yi gaba tana mita kasa kasa, wanda hakan ya saka shi dan girgiza kai ya mike yana ayana' yarinta kennan, mi dadi, idan ta wuce shikenan sai dai ka ringa tunawa kana murmushin shirmen da ka tafka"

Yana karasawa wajen motar ya samu Elhaji Hamza da Elhaji sunna fira a jingine jikin motar

hannu ya sake basu, a nutse ya karasa ya shiga motar ya zauna

Kasa kasa baba ya ce" To ba zai fada mana yadda suka yi ba hala?"

Aba ya yi zuru kafin yace" Ga dukan alamu ba zai ce komai ba, ama bari in je cikin ko na ji yaya suka kare da shi a wajen ita yarinyar"

Baba ya yi murmushi suka yi salama ya shige mota Aba na tsaye har suka bar wajen

Sunna cikin tafiya a mota yana ta anfani da tissu yana faman goge jikinsa bayan ya cire karin gemun da suka yi masa , Baba tsoho na kallonsa bai ce komai ba har mota ta tsaya a filin gida ya cire jalabiyar nan da Safa ya sauka daga motar , burinsa ya ganshi a bangarensa dan yayi wanka sosai da sosai

A tausashe baba tsoho ya ce" me ya samu goshin nan naka ne? ko bugawa ka yi da wani abin?"

Sai a lokacin ya tuna goshinsa, a nutse ya karra shafawa, sai kuma ya dage kafadu ya nufi ciki bai bashi amsa ba, dan kuwa so yake yi ya gane da gasken gaske ransa a bace yake da shi, haka kawai fin karfi? shi zai saka a wannan ha'ula'in ya nuna in bai yi ba bai isa da shi bane? ba damuwa zai yin, ama kuma sai dai ya zauna da ita dan kuwa ana gama daurawa idan ya bar kasar sai ya shekare bai shigo ba

Murmushi kawai baba yayi ya nufi bangaren Hajia shima,, gannin dare tuni yayi yau basu zanta da aminiyarsa ba.


A gidan Aba kuwa da ya shigo gidan shiru kamar yadda ya saba in dai yana gidan

kayan abincin da Hajia ke tatarewa ya duba ya ga komai ba'a taba ba, a tausashe ya ce" Ikon Allah, bakon na y'arki bai ci komai ba gimbiya?"

Mama ta dan tabe baki ciki ciki ta ce" Um"

Ya sake dubanta, fushin nan da take yi ya fi komai damunsa, sai dai a yau babu abinda zai ci da fushin ta, ta jima bata fashe ba kwarewar fushi a kan wannan maganar

Zama yayi yana fadin" A kirawo min Karimar in ji yaya suka kare, ina fata ta yi biyaya wa umarnina ta yi masa biyaya yadda ya kamata?"
Mama ta dakata tana kallonsa, a tausashe ta ce" Elhaji, wai baka kula da irin rawar kan da kake yi a kan wannan maganar ba? ya dace fa ka kama kanka saboda ba'a yiwa namiji haka, kai ke da macen, shine namijin, ka barshi yayi rawar kansa , a hakan zai fi Sannin darajar yarinyar nan Ni dai ina fada maka"

Shekeke ya kalleta sai kuma ya mike yana sakin dan karamin tsaki ya ce" Ke kam baki cika cin ribar rayuwa ba, ke fa Tun FARKON GANIN IDONA da ke na san da zaki yi taurin kai, kadarar haihuwar ANMI ne ya hada mu, Sannin darajar banza Sannin darajar wofi, to ai shikenan zan gani idan ya dawo gobe zan zauna a coridor in ga komai in ga ubanda zai hannani, ana baka kana roko, ana nuna maki kina rintse ido? sai an jima kar ki saki ki zo bangarena dan tataka mutun zan yi a banza a wofi, yarinya kuma y'ata ce sai na aurar da ita ga wannan kamilin mutumen babu wanda ya isa ta hanna!"

ya idasa yana jan wani uban tsaki sannan ya wucewarsa hankali kwonce

Da ido ta raka shi kafin ta kifta idannuwan ta girgiza kai ta nufi dakinta itama zuciyarta a cinkushe, dan kuwa wani irin nauyi zuciyar tata ta yi mata har zazabi ya nemi rufeta, koda yake kwanakin nan ta cika zazzabin dare sosai

A bangaren su Khadija kuwa sun ci dariya kamar ba gobe, sun yi sun yi Karima ta bude dakinta dan su samu su zolayeta sosai ama ta kiya, karshe sai a dakin Lubna suka tare khadija na basu bayani sala sala sunna kwasar dariya abinsu, domin su sheda ne irin yadda Karima ta tsani masu sufar malaman, ita tana son soyaya ne a rayuwarta, tana matukar son soyaya da gayu da kece raini, idan khadija tace da su Safar ƙafarsa yellow ce sai Lubna ta tuntsura dan dariya, haka suka gama shakiyancinsu suka yi dakunnansu dan yau ba karatun dare malamin nasu baya nan babansu kuwa yace kar su je yau , su da kansu basu san dalili ba ama kuma hakan ya musu dadi

Amarya da ta shirya ta nufi bangarensa tana zuwa ya nemi sauke mata kwondo kwondon balaki ba shiri ta gudu, domin ta sani idan ya riketa babu wani sassauci a tsakaninsu , ba zata taba iya kwatar kanta ba, gwara da ta gudu tun tana iya gane mutane kafin ya haɗa mata kwakwaluwa da jinni.


Dare ya tsala , sawu ya dauke, diffff babu motsin komai da na kowa a gidan kowa ya kwonta banda Karima dake lungun gadonta boye da waya kange a kunnenta

Bayan tarin msg din da suka yi da saurayinta ta gama fada masa dalilin shirunta cewa mahaifinta ne zai yi mata auren dole, sai kuma ta ɗora da fadin idan bai ceceta a yau yau ba tabas za'a yi mata auren nan shikenan sun rabu, ita kuwa ba zata iya rayuwa babu shi ba, wannan abu ya sa yayi kiranta ta sake buya ta fashe masa da kuka tana sake yi masa bayanin abinda ta tsara, wanda ya gama yarda cewar idan fa bai je din ba komai na iya faruwa, dan haka ya umarceta da ta dauki abinda zata iya zai zo ya dauketa ta bayan gidansu zasu taimaka mata ta dira sai ya kaita ya boyeta

Tsabar kanta ya cushe ta gama yarda cewar wannan ce kadai hanyar da zata bi ta ceci kanta daga wannan tashin hankalin dake nufota, wato auren dole da mutun irin wanda mahaifinta ya zaba mata, gaba daya a yau ta gama yarda cewar tsana mai sunnan tsana babu wanda mahaifinta ya tsana kamarta a kaf cikin ya'yansa, kuma in sha Allah zata gudu, zata yi nesa da shi da gidansa, domin babu abinda zata tsaya nema a gidan wanda ke son halakata......wai itace za'a ba miji irin wanann? ai da ta shiga uku a duniya da kuma gidan su, dan kuwa dariyar da yan uwanta suke yi mata a yanzu somin tabi ne, sai an mayar da ita gyadi gyadi a anguwa da makaranta.

Ta yi kai kawo ya fi a irga ta gama gane cewar kwarai wannan shawarar itace shawarar da ta dace da ita, dan haka ta dauki jakar makarantar ta ta juye komai nan saman bed dinta sannan ta cika jakar da kayan bukatarta

Jikinta na mugun rawa ta saka silifasss tana sake duba agogon dakinta ta ga eh lalle dare fa ya tsala, ta zauna bakin gadon ta daga kiran da yake ta yi mata ba kakautawa ta amsa shi murya a kurya ita dinma suka sake yin magana cewar yana ta bayan gidan hanyar da zata iya takawa ta dira

Jikinta ya sake kwasar rawa ta mike a rikice har ta ajiye wayar a nan ba tare da ta ankara ba, harta jakar da ta cika da kayan ba ita ta dauka ba sai kawai ta wawuri wata jakar ta bude dakinta a hankali zufa na son keto mata ta nufi hanyar bude kofar jikinta na mugun rawa kamar zata summa tsabar tsoro, ta kama ta bude ta maido kofar ta rufe sannan ta nufi hanyar sai waige take yi hankalinta a mugun tashe ta je ta inda ta ga ya ziro wata igiya ja ta fara jefa jakar sannan ta kama garun kamar da wasa ta dane shi du tsayinsa ya taimaka mata ta dira suka nufi motarsa da gudu ta shige ya tashi motar ya dauki hanyar gidansu da ita


Murya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login