Showing 33001 words to 36000 words out of 190762 words
Chapter 12 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
shigo ai yanzu nake sanar masa fitowar ka "
"ok, bari in gama da kosan mutuniyar sai mu gaisa" Ya fada yana murmushi, domin yana matukar ba Aba girma a rayuwa irin yadda ya shaku da y'ar yar nan tasa kwalin kwal, yana jin alhairansa a wajen Elhaji, uwa uba irin yadda Elhajin ya shaku da shi shima sai wanda ya gani, shi yasa ake cewa a duniya kowa yana da gwani, du tsaurin halayar mutun ba zai rasa gwani ba ko yayane........................................
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*🇳🇪
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na Goma (10)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
*META FORCE*
*menene meta force*
business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake duniyar network marketing ba’atabayin business din dayake bada kudi sosai kamar meta force ba kuma dollars ne sukebadawa sannan inkinason canja dalarki cikin mintuna qalilan zaki canja dollars dinki zuwa naira hankali kwance kinadaga gida dollars suna sauqamiki hankali kwance yawanci yan nigeria ko ince yan arewa bakuda lbrn wannan business din business ne daya karade duniya akwai qasashe da dama wanda sukafimuma cigaba sunacikin wannan business na meta force
*shidai meta force crypto currency* ne
kuma munsan cewa yanzu babu wani business dayake bada kudade a duniya yanzu irin crypto currency
akwai program dayawa acikin meta force wanda akayi lunching da wadanda ba’ayiba amma za’ayi nan bada jimawaba
yanzu bari mudau programs guda 1muyi dan taqaitaccen bayani akai
*TACTILE*
1 Tactile : matakin farko kenan dole idan zakshiga meta force saikafarayin registration a tactile sannan zakasamu damar shiga kayi joning sauran programs din
tactile yanada levels guda 12 1 to 12 kowani level da kudinshi level 1 5 dollars
level 2 10 dollars
level 3 20 dollars
level 4 40 dollars
level 5 80 dolllars
hakadai
kudin kowani level yake ninka na bayanshi saikzabi wanda zaka iya saikayi shi tactile ananne akasamun abunda muke qira
*Spillover*da*over flow*
wato kanazaune baka kawo kowaba zakaduba wallet kaga ansama mutum har dollars sun sauqama anbiyka kuma bakayi aikin komaiba a wadannan levels din dakasayadin ko wani levels dakasaya idan spillover yatashi fadoma to adadin kudin wannan levels dinne misali level 1 5 dollars to ynada dakuna 6 duk lokacin da kayiwa mutum register kokuma spillover yafadoma zakasamu 5 dollars ne akowani daki 1 amma banda dakuna 2 na farko da daki 1 na qarshe amma daki na 345 dukka sunafadowa biyanka za’ayi kaga 15 dollars kenan dakuna 3 sannan idan dakunan suncika za’aske sharemaka kasake zuba wasu mutane inma kaikanemosu inma spillover kasamu
to haka zakayita samun wannan dollars din a kowani levels dakasaya duk zagaye daya zakasamu adadin kudin daksayi levels dinnan sau 3 kagdai kudin dakasyi levels din sundawo harda riba kuma hak za’ayita sharema dakunan anasa wasu mutane koda mutanen sunkai millions 💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Atakaice kenan sauran bayanin kubiyoni awannan number domin jinkarinbayani
👉0912 262 1080
*Sannan zaku iya zuwa kuyi browsing google youtube*
*zakusamu kowane irin bayani kukeso game da meta force
Aunty Hajja
LABARI
Mai kosai ta fara zubawa kurma dake zaune gefen MAHAIFINTA
Tana amsa ta juya ta shige cikin shagon, hakan ya saka mahaifinta sake Binta da kallo sai kuma ya mike dan ya ga me zata yi ne? an zuba mata da yawa kuwa a plate mai murfi da mai aiki ta biyo su da shi tunda ta ga fitar kurma da babanta ta san wajen mai kosai aka nufa
Yana shigowa da salama ya ringa gaisawa da masu aiki har ya karasa inda Elhaji yake zaune kurma ta zauna saman kujerar da aka bata tata , daf da shi ta bude kosan nan tana masa nunin su ci
Yayi dariya ya ce" Yau ganimar tamu baba ce ga dukkan alamu iyeah"
Murmushi Al Walid yayi ya masa salama
Aba ya mike tsaye yana amsawa, sani ne ba'a yi ba, sau uku yana nufar hanyar fitar dan ya masa oyoyo ama yana danar kansa yana tunawa kansa shine sirikin ya kama girmansa shi ya fi alkhairi
Hannu ya bashi yana fadin" Barka da sauka Elhaji"
Al'walid ya furta" Barka da safiya kakan kurma"
Aba ya yi murmushi yana fadin" Ba kurma bace, bebe ce"
Ai kuwa al Walid yayi murmushi, domin dama Elhaji Hamza ya sanar masa du fadan da zasu yi in yana so ya kula shi sai yacewa baby kurma, nan take yake bada amsar ba kurma bace bebe ce
Bayan sun gaisa ya fita ya koma dan shi yake bayar da sadakar kosan nan da kansa ya bar kurma tare da baba sunna yaran kurame
Minti kadan Elhaji Hamza ya shigo, shima ya dauki kujera ya zauna yana fadin" Allah ga Hamza jiki du ciwo Ni kuma gani yaro danye shirattt"
Aba ya dube shi har ya gama maganar kafin ya gyada kai ya ce" An mora, an fa mora Elhaji, ka yi ka paka dan Allah ya isa hakanan"
Elhaji Hamza ya yi dariya ya ce" Yanzu in na mutu ina aka saka ranka? na tabata bina zaka yi"
Aba ya zarro ido ya ce" Ina? wai lahirar? to in barawa gimbiya wa? baka san marainiya bace wa zai kula da ita?"
Ai kuwa suka saka dariya, Elhaji Hamza ya ce" Kana tunanin mace na maraicin miji ne? ka dai yarda ka rakani tsaf zata samu wani mai rikon marainiyar ya riketa da kyau"
Aba ya yi shiru yana kallonsa kafin ya ce" Ya haka tsoho? Ni zaka haudawa jini?"
Elhaji Hamza tabe baki yana hangen Al Walid ya gama bayar da sadakar ya nufi gida almajiran sun bi shi ya maido dubansa kan Aba a tausashe ya ce" Yaya maganar mu? ina fata ka sanarwa yarinyar?"
Aba ya yi murmushi yana gyada kai ya ce" Na sanar musu har mamansu, Allah ya tabatar mana da alkhairi, yaushe ne zai je gidan?"
Elhaji Hamza ya dan sauke numfashi, shi da ko zancen bai masa ba? yana tunanin ta inda zai hau shi, ama zai barshi ya huta yanzu, zuwa dare sa zauna, su fuskanci junna sosai su tsayar da maganar nan, dan baya so ya yi tafiyar kai tsaye basu gama magana ba
Da kula ya ce" In sha Allah idan ya gama hutawa zan sanar maka"
Aba ya gyada kansa ya ci gaba da ayyukan gabansa, a ransa kuwa abu dayan nan da ya tsaye masa yana son tambaya ama baya so Elhaji Hamza ya ga ko wani abin ne, wato yarinyar nan mai tafe da masu tsaronta da kowa ya gama Sannin budurwar Elhaji Al Walid din ce, gatanan yanzu haka a cikin gidan ta zo ta wuce ciki, yaya ita tsakanin nasu? Wane ake ciki ne? shin duka biyun zai aura rana daya ko yayane? shi dai yana son ji ama zai yi jira ya gani
Sai da kurma ta gama ya kama hannunta suka nufi gidan yana yi mata nunin yanzu malamin islamiyarta zai zo, dan haka su je ta dauki litatafanta ta yi bita
Mufeeda kuwa tana dakin Hajia inna lokaci zuwa lokaci sai ta duba agogon dakin sannan ta duba kofar shigowa, sai dai tun tana sa ran ganninsa har ta cire ranta
Zuciyarta na kunna kwarai da gaske, a zaunen nan da take ita kadai ta san halin da take ciki , ta kai dubanta kan Hajia inna da barci ya dan figeta ya fi a irga, babu irin abinda bata sakawa zuciyarta ba har ta gama yarda cewar du inda yake warhaka lokacin barcinsa ya gama yi, yana bangarensa ne
Manya manyan kulayen da aka shake da girki na alfarma kawai take kallo, tun daga baban garin kasar Nijar Mahaifiyarsu ta hado su da manyan kuku da zasu ringa yi musu dahuwa da kuma abincin da zata ringa kaiwa Al Walid, kafin ta yarda ta dauki mai aikin sai da ta tabbatar da sun iya duk wani launin abincin da yake so sannan aka dauke su,
A yau tun karfe biyar na asubahi suke kicin din gidan da suka sauka, sun yi girki mai rai da lafiya ko su da suka dandana sai da suka yaba, gashi ta kawowa wanda aka yi domin sa ko kallo girkin bai ishe shi ba bale ya yaba din
Mikewa ta yi ta bar komai a nan ta fita ta karasa cikin motarta ta shiga ta zauna a lokacin ta ringa sauke wani irin numfashi a jere a jere na bacin rai
Ihu ta yi ta daki sitiyarin motar, lokaci daya kuma ta cusa hannayenta cikin kanta ta rintse ido tana fitar da numfashi a hankali a hankali tana fadin" Ki nutsu Mufeeda, ki nutsu, ki kwontar da hankalinki Mufeeda, kin sani sarai ba da irin haka kika kawo matsayin da kike a gabansa a yanzu ba, kin sani sarai ba da wannan halin har kika tako matsayin da kika tako ba, kuma kin san kin take umarninsa, ke dai zaki yi hakuri ki nutsu, in kika yi haka zaki ci ribar tafiyar Mufeeda....."
A hankali ta ringa fitar da huci daga bakinta dan ta karra samawa kanta nutsuwa
A nutse ta shafa fuskarta bayan ta janyo madubin motar.....
Gaba daya ta dame kwaliyar, gaba daya ta hade komai
Dan kwalin dolen da ta dauro ta lalubo ta dauko sannan ta kunna motar ta yiwa yan rakiyarta alamu suka taso , dan tunda ta shige motar hankalinsu ke kanta
fita ta yi ta koma baya suka dauki hanyar gidan da ta sauka sai sake dantse lebenta take yi , bukatarta ɗaya ce jal, ta samu wajen da zata sauke fushin ta ko zata iya shaƙar numfashi mai dadi
Kamar kanwarta ta san a rina, tunda ta tafi take zaune ta ki komawa barcin gajiya tana jira ta ga ko ta kwana
Ai kuwa sai gata ta shigo a fujajen ,a yannayin da bashi da dadi, uwa uba irin yadda yayarta ke kuka idan har abu ya shafi wannan bawan Allahn
gannin ta ki daina kukan ta yi mata kiran Mahaifiyarsu ta saka a handsfree sannan ta mike ta bata waje dan kuwa maganar mamansu kadai zata ji a irin wannan lokacin
Itama mahaifiyar tasu hankalinta ya tashi da jin kukan y'ar Tata
Dama a cikin fada suke ita da mahaifin Mufeeda, ya fada musu ba'a yiwa namiji irin haka, bale Al Walid ba yaro bane, da girmansa da kuma girma irin na aljihu, idan har Mufeeda na gannin nuna masa soyaya ne take yi gwara ta kama kanta, dan babu namijin dake son mace kamar macen titi sai gararamba da rawar kai kamar me, idan har sonta yake yi ba sai ta wahalar da kanta ba, zai dauki abinsa ne a mutunce da dukan tsarabe tsaraben da zai fuskanta, sun dai san ba matsalar kudi ta hanna shi auren nan ba ko? to yayi.....wadinan magangannun su suke daga mata hankali, ita ba yarinya karama bace, kuma ta san gaskiya mijinta ke fada, sai dai ta kasa tsayawa waje daya bale ta fuskanci y'arta su daidaita kansu tun kafin a zo bigirin da kunne ba zai ji rarashi ba
A tausashe ta ce" Ya isa haka kukan nan Mufeeda, dukan ki ya yi?"
Mufeeda ta tsagaita kukanta, duka? kai, a'a, ai zata iya cewa gaskiya Yaren duka ba yarensa bane........, domin Allah ta san ba zata taba nuna inda ta ga ya daki wani Bama bale ita
Sai dai zata iya rantsewa gwara ya daketa da irin horon nan da yake yi mata idan ta bata masa, yana iya share ta yayi banza da ita fa...., ita kuwa wannan abin ya fi komai kasarata, ya fi komai lalata mata nutsuwa da farin ciki
Murya a hargitse ta sanarwa mahaifiyarta abinda ya faru
Ajiyar zuciya uwar ta sauke a tausashenta dan so take yi y'ar ta bar kukan hakanan , ta ce" Mufeeda, ki daina kukan nan, to ai kin ga laifinki ne, kuma kulun fada maki nake yi tunda kika ce kin ji kin gani a haka zaku yi tafiyar dole dai ke zaki yi ta hakuri, ba fa shi zai yi ta rarashi ba, bale ba duka maza suke rarashi ba Mufeeda, ki kwontar da hankalinki ki daina kukan hakanan, idan ya huce sai ki bashi hakuri shikenan kin ji?.."
Da wannan ta yi ta rarashinta har ta yi hakuri , sai dai gaba daya wunin ASABAR yau din an gama lalata mata farin cikinta.
A gidan baba
kasantuwar yauma ASABAR du yan makarantar gaba da primary sunna zuwa makaranta hakan ce ta faru da ya'yan gidan, kuma shigar da baba ya umarci Karima ta yi ita ta yi, sannan uwa uba ta kashe wayarta bayan sun yi waya da mahaifiyarta ta daina kula wayar saboda Mudansir, domin ba zata so raunin da take da shi a kansa ya hannata cikar Burinta ba, ita fa ko menene tana iya mayarwa gefe in dai a kan ya'yan banki ne kamar yadda mahaifiyarta ta nuna mata sun fi komai mahinmanci a zaman auren, in dai akoy su to fa ko menene za'a iya cinyewa a yi hakuri a zauna, ta riga ta nuna mata duka kaf mazan haka suke, kafin su aureka zasu bautawa soyayarku kamar me, da zarar sun aureka shikenan komai ya wuce ka zama tamkar abokin hamayarsu, du irin kyautatawarka kuwa sai sun wulakantaka, da talakan da mai kudin, shi yasa ta horeta da auren gata ya fi armashi fiye da na kudin
Da suka dawo daga makaranta basu huta ba Mama ta tisa su gaba suka yi kicin su duka yan matan bisa umarnin baba , dan tunda ya je shago ya yi kiran Maman suka yi magana cikin ruwan sanyi ya nuna mata bukatarsa Karima ta karra gogewa a fannin girki da du wani abin da ya kamata na gida, ya riga ya san ta wannan fannin bashi da matsala ama yana so a karra, wannan dalilin yasa ta yi masa list harda ta mamaki ta nade kafa tana sakacen hakori har aka kawo dukkan abinda ta bukata cike da bayan mota guda
Wannan lamari ya sake tabbatar mata lalle akoy abinda mijinta ke shiryawa mai girman gaske, kuma du inda mijin nan da ya yiwa Karima ya fito lalle zabin cikin zuciyarsa ne
Bata yi kasa da gwuiwa ba ta hade kan yan matan gaba daya suka yi bangarensa
Ita kanta tsaye take lamarin ta, su kuwa du a tsorace suke dan tunda suke basu taba shiga kicin din bangaren mahaifinsu ba
Lahauli, kicin irin ta Film,.kicin mai kyan gaske dauke da kayan aiki shake , ama komai a kwalinsa, to wai menene dalilin da yasa babansu ya yi wannan kicin din kuma babu mai shiga? , su dai tunda suka ga Mama kanta tsaye tana fitar da dukan abin bukata sai suka saki jiki sunna bin dukan motsinta
Kafin su fara girka abinda zasu girka sai da Mama ta koya musu mahinmancin gyara kicin kafin a yi girki da kuma tsaftacewa bayan an gama, Duda sun san da wannan ama basu san kicin din nan da irin tasu da aka musu a gargajiyance ba
Cikin nutsuwa da fitar da kayan tsaftace kicin din, sai da suka cire su yanar tautau da komai tunda a rufe take ba aiki ake yi a ciki ba, sannan suka fitar da kwanuka tana tsaye tana sake gyara musu dukan abinda bai yi mata ba na harkar wanke wanken, da goge gogen komai da komai, sai dai Karima gaba daya a gajiye yake yin aikin, dan har cen kasan zuciyarta ita bata ga dalilin da zai. sa a sakata irin wannan aikin ba,, ita fa gidan hutu zata je, gidan da tana zaune za'a yi mata komai, ba wai gidan wahala ba, gaskiya ba zata taba zuwa gidan da zata ringa yin girki da wahalce wahalce irin na gidan babanta ba, Sam, auren hutun da mamanta ke yi mata nunin zata yi to fa lalle lalle sai ya zama na hutun ko kuwa ta dagawa kowa hankali walahi
Sallah kawai ke fitar da su daga kicin, kasantuwar sai da yama ta yi lisss suka shiga kicin din hakan ya sa sallar magariba ta ritsa su a kicin din suka je suka yi suka dawo wannan karron a tsorace dan sun san du inda babansu yake ya kusa dawowa, idan ya zo ya same su a kicin dinsa sunna aiki yaya za'a kwashe? sun riga sun san ko ita maman tasu idan bulala ta biyo ta kanta zane mata jiki zai yi tassss a nufin su yaje duka ta tare musu, bale su kwari
Ita kuwa Hajia, ba wannan yake gabanta ba, ta san idan ya same su a kicin dinsa yana iya kirta rashin mutuncin da zai hadata da hawan jinni, sai dai kuma tana son karra tabbatar da darajar mutumen nan a zuciyar Elhaji, domin ta san mijinta ciki da bai, babu abinda zai yi ya boye mata yarensa, sai dai in bata gani ba
Tana yi tana duba agogo, Gannin lokaci na karra tafiya tana tunanin inda ya makale yauma? kwanaki ukun nan a waje yake yin sallar magariba, bayan ba dabi'arsa bace, du tsiya yakan shigo gida kafin magariba
Sun kusa gamawa saura hade haden jus da ta yi niyar sai sun hada uku ciffffff