Showing 141001 words to 144000 words out of 190762 words

Chapter 48 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt

21 Apr 2026

3988

shi tana fadin" Barka da zuwa Elhaji, ai zuwa na yi na yi sallar isha'i, gamu da baki masha ALLAH "

Aba yayi murmushi kasa kasa ya ce" Wa bilahilazi duba ki ga abin arziki, kai shi fa mai kashin arziki haka ne, du tsiya sai ya nuna kansa sai abinsa ya bi shi, koda yake a jikin uwar ne, tunda nake ban taba baiwa mace sama da million daya kudin kayan aure ba sai ita, ga Khadeejan larabawa ta bi layi, ina take ne? wai me kike a dakin ne Gimbiya?"

Ya karashe yana nufar dakin Mama ya kama ya bude ya shige

Amarya ta rintse idannuwanta wani abu na sake tokare mata kirji, har yanzu ta kasa sabawa da halayar mijinsu, karya ne yayi magana daya a ta biyun bai yaba matar nan ba, karya ne yayi magana bai sako maganarta a ciki ba, ta rasa me ta fi ta, me ta fi sauran matansa, a da ta kaiwa mahaifiyarta kukan cin fuska ne, sai mahaifiyar Tata ta sanar da ita cewa wasu mazan basu iya kara da danne harshensu wajen yabon matansu ba, hakan ke sakawa a yi ta samun sabani saboda wasu ba zasu taba iya amincewa da haka ba, itama da farko ta so yi masa bore a lokacin da take amarya ya ringa rakata yana nuna mata ai ba abinda take tunani bane wace ma wata gimbiya? sannu a hankali ya daina wannan din yake fitowa kiri kiri yace yau fa za'a yabi gwani, dan bakin ciki ya rintse ido nai. shi yasa take cewa bokan Usaina bashi da imani da tausayi ko kadan, ya kwashe komai ya dora a kan Usaina kadai, kuma dan balaki an kasa karya mata alkadarinsu, har sai tana tunanin an ci riba sun fara dambatuwa kwana biyu sai ta ga sun daidaita!

A hankali ta karasa bakin kofar zata saurara aka bude kofar su Lubna suka fito da dan gudu gudu hakan ya sa suka gwaru da amarya da ta duko kunnenta zata yi sauraro

Aba dake tsaye ya gama cewa wai uban me suke yi sun zo sun likun mata basu san halin da take ciki bane ko bakin ciki za'a masa Allah ya dube shi ne shi bai gane ba, ya nuna musu kofa yace kafin ya irga uku kar ya ga kafar daya a dakin , ya sa suka rukuto a guje suka bude suka gwaru da amarya wace ƙarara suka fara gannin irin yadda ta duko kunnenta da kuma mikewar da ta yi a tsorace

Hannaye Aba ya tafa yana zarro ido ya ce" Lah munafuka, innalilahi wa inna ilaihi raj'une munafuka, labe kika koya? yaushe kika fara labe? innalilahi wa inna ilaihi raj'une dama labe mana kike yi? la ila ha ilalahu Muhammadu rasululahi Sallallahu alaihi Wa Salam, ke hala har a bangarena idan aikin gimbiya ne leke kike mana? kardai aje irinku ne ke daukan vidion abokanan zamansu dan su yada su kashe musu aure? ke ko dai gimbiyar kike so ne Ni wala haula wala kuwata ila bilah yau na shiga uku"

Da sauri Mama dube shi , a tsorace ta kalli inda yan matan suke ta ga tuni suka karrawa bujensu iska saboda ita rayuwa lalabata ake yi, bale da aka fito maka a mutun aka nuna maka hanyar da zaka bi ka tsira da Mutuncinka idan ka tsaya aka motsa maka kwakwaluwa ai ka gama janyowa kanka tsiya

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke ta kai zaune tana fashewa da kuka tana fadin " walahi sai ya lalata min tarbiyyar ya'ya da mugwayen kalaman bakinsa , wayo Allahna wayo na shiga uku"

Shiru yayi yana kallonta kasa kasa ya ce" Kukan gaske ne ko na wasa?"

Mama ta dube shi hawaye na zubowa ta ce" Kukan wasa ne, nace na wasa ne baban Ishaq, yanzu ba zaka rufawa kanka asiri ka rufa min ba mu hadu mu tatala yan yaran nan har Allah ya rabamu da su lafiya? shine kake budar baki kana inkayi da kalamai ire iren Wadinnan a gaban yaran nan?, yaya kake so ne gobe idan ka ji sun fada suma? yanzu fa mutun ake kiwo ba daba ba , haba dan Allah, ke kuwa....."

Ta nuno amarya da ta yi tsuru tsuru ta ce" Ke ba zaki yiwa kanki wa'azi bane mu zauna lafiya? ke ba ruwanki da hakin mutun, haka kuma ba ruwanki da na Allah? haba dan Allah, kin iya yin abinda zai zo kulun ya hautsina mu ya hadasa mana tashin hankali a cikin gidan nan ya hade daga Ni har ke ya yi fata fata da mu kuma ki dora min da cewa nice ke janyo maki bakya tsoron Allah ne? ki sani duniyar nan ba matabata bace, ki aikata alkhairi ma lalube ne bale ki dage kan lalle sai kin kuntatta min!"

Ta dakatar saboda ji da take kamar zata kifu, ta ɗora da fadin " Me zaki labe ki ji? me kike son ji? me yasa zaka barta a kofa ka rufo kofa ne? du laifinka ne, kai ke janyo min magana, du matsalata kai ne, kai ne ke sakani a damuwa, kai ne ke janyo min ana zagina, Ka zage ni, matarka ta zage ni, yan cikin gari su zage ni, du dan ina aurenka ? na gaji......na gaji.....na gaji........." Ta karashe tana dukewa hadi da fashewa da wani kukan

A hankali Mama Fateema ta shigo bayan ta janyo hannun amarya ta kara kofar dakin ta rufe, ta nufi inda Mama ke duken nan ta duka ta kama hannunta a hankali ta ce" Aunty, haba Aunty, dan Allah dago ki dubeni, innalilahi wa inna ilaihi raj'une me yayi zafi ne har haka? me yake faruwa ne?"

Kamar yarinya karama Mama ta fada jikin Mama Fateema bata bata amsa ba tana kukanta

A hankali Mama Fateema ta kalli Elhaji da jikinsa ya mutu murus kamar an yi masa tsinanen duka, a sanyaye sosai ta ce" Baban ANMY, a taimaka a je a duba bakin nan wasu har sun tafi fa, Hajia Binta da aunty shareefat din ne kawai ke nan ,, kar su gaji da zama"

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya dubi takardar check din da ya shigo da ita, muryarsa kasa kasa sosai ya ce" Dama zuwa na yi in tambayeta nawa ya dace a dora matsayin tukwuicin masu kawo kaya?, ban san me ya faru kafin in shigo ba har ya tunzura min hankalinta haka....., Ki yi hakuri Gimbiya " Ya karashe yana dubanta da kyau, wanda hakan ya karya mata zuciya ainun har ta zuba masa ido a boye tana ji kamar ta mike ta bashi hakuri, sai dai ta ki mikewar , sai Muryar Mama Fateema da ta ce" Ka yi hakuri yaya, in sha Allah ko menene zai wuce, ka yi hakuri dan Allah, a saka abinda Allah Ya hore, Allah ya karra budi"

Kai ya gyada ya juya zai fita ya ga amarya a tsaye tana jijiga

Wani haushinta ya kama masa wuya ya daga hannu zai kwadeta ta yi kusan su Mama da gudu
Rai bace ya nunata da yatsa ya ce" Ke kam wai uban me kike min a gidan nan banda hada husuma? na rasa ya aka yi kike nan har yanzu ko dai zuwa kika yi kika min asirin duk rintsi kar na sau ki?, Ni zaki hada da matata ko? Ni zaki yiwa labe ki hadani rigima da Gimbiya bayan ba Laifina bane?, du masu yiwa gimbiya karyar tana min asiri Allah tsine musu albarka su ji duniya uban kowa ya huta, to idanma asirin take min sai me? ta je ta yi na yafe mata duniya da kiyama, yo a halin nan nawa idan ya zamo du duniya bani da wanda ke taroni ai dan wuta konane zan zama, ke kam tabas yau ba zaki kwana a gidan nan ba, kawai ki je gidanku na....."


"Kin gani ko? walahi idan ka saki matar nan nima na saku" Mama ta fada da karfi tana mikewa tsaye

Da sauri ya saba babar rigarsa ya juya bayan ya harareta ya ce" Aikin banza aikin wofi, wai shishiginma ka rasa wa zaka yiwa sai kishiyar dake sonka da tsiya, sai ki bitan in gani, ke bari ki ji, cikin nan dake saka ki wulakantani sai dai ya ji kunya dan ubansa, yanzu haka namiji ne dan kutumar uba zai nunan kishi tun a ciki, zaka zo ka bani lafiya da matata, du wani mai kin zaman lafiyar gidana kuwa gwarama a yi garkuwa da shi ko a rage mugun iri, sai an jima!"

Ya yi gaba ya mako musu kofar sai da suka zabura su Dukansu

Shiru ne ya wanzu a dakin, mama ta kalli amarya amarya ta kalleta kafin ta juya ta fice ta nufi dakinta kamar zata tashi sama

Mama Fateema ta bi Mama da kallo har ta zauna bakin gadon ta

a nutse ta karasa kusa da ita tana dubanta a tausashe ta ce" Kin kuwa san cewa kina daf da wuce gona da iri? ko da gaske hormone din ne ke fitar da ke a hayacinki?"

Mama ta dubeta ta ce" Ban gane ba"

Mama Fateema ta ce" Aurenki kike son kashewa?"

Mama ta tabe baki ta ce" Idan auren ya mutu ba shikenan ba kowama ya huta?"

Mama Fateema ta yi murmushi ta ce" Uhum, harta yannayin maganarki ta koma irin ta mijinki, ke yanzu a irin wannan zafin zaman da kika koya waye zaki aura ku yi zaman lafiya in ba shi din ba?, bayan wannan ke yanzu gani kike yi kina iya juya baya ki bar mutumen da zaku tashi ku daku da junna rana na yi ki aika masa abincinsa cikin kiyaye saka magi da yaji saboda kar su yi masa ila, ki wuni kina hidimar ya'yansa da suka gama saye maki zuciya kike yin yaji da su, ke yanzu aunty har tunani kike yi cewa zaki kwashi yan ya'yan nan ku kaura gidan Hajiar Larabawa da ranta ku mata me?, aunty kennan da akace yana asibiti fa jikinki haka yake rawa....., to walahi bari ki ji idan me kike tunanin ya zama ko ya mayar da ke ko wani tunaninki na baki cewar kina iya yin rayuwa nesa da shi ki farka, ya riga ya mayar da zaren kalar ɗinkin, ya riga ya mayar da ke mahadin rayuwarsa, gwara ki gyara takunki ki yi rayuwa da shi cikin kiyaye shiga hakin wasu matan nasa, domin idan kika biyewa baban su Anmy tsaf zaku shige inda ba'a so saboda shi ba ruwansa abinda yake tunani yake fada!"

Ta saurara ta sake dubanta ta ce" Aunty, cikin harkar farin cikin nan da ake ciki ne zaki bari har ta bata maki rai haka? aya a tunanina a yanzu ko shine yake neman daga maki hankali sai ki ba iska ajiyarsa ki yi abin arzikinki ki gama, aunty Anmy fa kika aurar, tana dakinta, tana gidanta aunty, shikenan sai ki bijiro da rigimar da baki yi ba a da?, kece ke cewa hakuri shine maganin komai, ke kike ce min babu abinda hakuri baya yi, shin a da ba ciki ba ko mutuwa kike yi kina farfadowa yana duban wani fushinki ne?"

Ta dan dakatar tana kallon Mama, a sanyaye ta ce" Kin san cewa ba wai dan ya yiwa Anmy miji mai arziki bane yake gudun bacin ranki, kin fi kowa Sannin cewa Dukiyar ka ba itace zata saka Elhaji Ya'u ya dubeka ba, kin sani cewa addu'ar ki, hakurinki, jurriyarki ne suka kawo ki wannan lokacin da mijinki har a yau aka wayi gari Allah ya saka masa gudun bacin ranki, shikenan kuma sai ki nemi lalatawa? aunty ni'imar Allah fa kina ciki, Allah ya horar da Yaren nan yi maki biyaya, ya saka musu kaunar ki a zukatansu, ya haɗa kanki da su, daga mazan har matan, a gidanki baki rasa ci, sha , ko sutura ba, to kuma ai dole idan aka taba dadin da yawama an jarabci bawa ko?, haba Aunty "

Mama ta lumshe idannuwanta, a hankali ta furta" ya Salam, Fateema walahi bana Sannin inda hankalina yake zuwa da zarar na hasala a wannan dan tsanin, Fateema labe fa matar nan ke min, kuma shi kuwa shine ya bude baki a gaban Yaren nan yake sakin zancen da ko iya mu ne ya dace ace ya kiyaye saboda kar ya bamu kafar da zamu koyi ire irin abubuwan nan"


Mama Fateema ta fuskanceta da kyau ta ce" kin fa san halin mijinki, bai ci ace ya baki wahala ba ke kam, kin fa san shi sarai"

Bubuga kofar da ake yi ya saka su dakatawa mama ta bada damar a shigo

Shigowa Aba yayi yana dan tsayawa ya yi murmushi ya ce" Sannu FATEEMA, sannu, dama madara ce na saka habubacar ya karbo mata mai sanyi dan na san ba abincin take iya ci ba yanzu"

Mama Fateema ta mike tana fadin" Masha Allah baban su Anmy, nima tafiya zan yi dare na yi, sai gobe in sha Allah sai mu zo a cire na kaiwa din, a kai mata na bukata tunda bai fi kala shida da aka tafin mata da su na kwaliya ba, sauran du na zaman gida ne kawai muka zuba mata"

Aba ya gyada kai ya ce" Hakane madallah Allah dai yayi albarka Fateema sannu da aikin lada, kema ga taki takardar nan Allah ya bada ladan zumunci"

Mama Fateema ta noke tana fadin" Haba dai yaya, a Barka da hidimar Nanma kadai ta isa ai, masha ALLAH ana ta kokari ai, kuma fa kyautar nan kashi kashi mun samu harda ta mamaki, a'a gaskiya"

Aba ya hade fuska ya ce" Kya karba ko sai raina ya bace?, idan gimbiya ta baki zaki wani tsaya jayayya ne?"

Mama dake cike da jin nauyin fushin da ta nuna dazu yayi yawa ta ce" Sannu da kokari Elhaji, ki amsa kawai Fateema Allah ya karra budi, ki gaishe da malan in sha Allah zan shigo nima jibi idan na sauko daga asibiti"

Aba ya saki murmushi yana zaunawa ya mikawa Fateema ta amsa sannan ya ciro madarar yana ajiyewa Mama ya ce" Madallah gimbiya kin saku Allah ya karra sanyaya mana fushin nan ya raba lafiya"

Murmushi kawai ta yi ta amshi madarar suka shiga shawarar inda zasu ajiye kayan nan da yadda za'a yi a kai mata abinta dan cewa yayi komai za'a kai mata na dinkawar da za'a diba a kai dinki kadai za'a cire.

..........................................................

Tunda suka gama sallar nan Anmy ke neman fita hayacinta, domin gana daya jikinta ya mutu murus, wani irin tsoro ya kamata saboda yannayin da yake nuna mata a bayane ba na wasa bane

Baban kwanon da aka zuba bankararun kajin ya bude a nutse tare da janyo madarar cikin kwalin ya ajiye ya sake dubanta a ransa yana tunanin Allah ya sa dai ta kai 18, yannayin ginuwar jikinta yana nuna cewar ta girma, sai dai yana tunanin hakan a ransa dan ba zai so ace bata kai ba,

A hankali ya dubi yadda ta kasa cin abincin kasa kasa ya ce" Eat"

Abincin ta kalla, haka kawai ta tuna irin yadda ake bayanin daren farkon nan a gidan iya, wani tsoron ya sake kamata , a nutse ta sake sada kanta ta furta" Bana jin yinwa"

Murmushi yayi ya fito mata da cinya guda yana dubanta ya ce" Hajia karamah......, ha, bude bakin"

Shagwabe fuska ta yi ta sake sunne kai cike da jin kunya, kasa kasa ta ce" Madarar kawai zan sha, bana cin abinci mai nauyi da dare saboda bana son tumbi"

Hannunta da take wasa da shi ya rike, a hankali ya dago habarta ya kai mata naman nan, sai da ta amsa ta cira ta shiga taunawa sannan ya dan saki murmushi ya ci gaba da ciyar da ita, har sai da ta nuna ta koshi ya bude mata madarar sannan ya ce" A nan din nan...." Ya fada yana kai hannunsa wajen cikin nata dake lafe , a tausashe ya dora da fadin" , tumbi zai zauna tabbassss, saboda ajiyar da zan yi mai dalilin zamansa ne"

"Ya Salam " ta furta a hankali sannan ta mike da sauri ta nufi gadonta cike da jin kunya ta haye ta lulube jikinta kirjinta na dokawa tana ta addu'a tana hangensa yana cin abincin shima har barci ya fara fuzgarta

A nutse ya gama cin abincin nan ya rufe komai sannan ya mike ya je yayi brush ya cenza jalabiyar dake jikinsa zuwa kayan barci riga da wando ya sake yiwa kansa wanka da turare sannan ya dan dakata yana ayanawa cewa' Ya rab, ka kareni da alkhairan dake tare da ita, ka sanya albarka a tarayata da ita, ka bani ikon fita hakinta ko wani iri........, ka sa ban fi karfinta ba:''''''

A nutse ya fice ya sake duba ko'ina a saman, dama ya gama da kasa tun kafin ya hayo, sannan ya koma dakinta ya shige ya rufe a nutse ya karasa inda take barci ta bude fuskarta dan bata saba yin dogon barci fuska a rufe cikin abin rufa ba

Murmushi ya yi, irin yadda bata matse masa waje na birge shi, ba kamar Mufeeda ba, ita Mufeeda akoy son taba jikin mutum, da ba dan ya jajirce ya hannata haka ba da ta jima da mayar da wannan laifin ba komai ba a tsakaninsu

A nutse ya daga abin rufar ya shiga bayan ya kashe hasken dakin sannan ya janyota jikinsa

Cikin nutsuwa ya ringa kokarin ganar da ita manufarsa tunda ta farka da ta jita a jikinsa ta so zamewa ya rungumeta ya hannata hakan a hankali ya shiga shafa jikinta murya a kurya sosai ya furta" Ki ban dama Hajia karamah, ki amince min in samu nutsuwa a tare da ke"

Sanyi jikinta yayi ta yi shiru tana sauraronsa jikin nata na rawa domin yare ne da ya fi karfinta yake bata

A nutse AL'WALID ke gigitar da duniyarta, Motsi ne yake aikatawa na kwararre a kan lamari da wanda bai taba gwadawa ba, dukkan wani rikicewarta kuwa na dan koyo da tsoron dake bayyana a kan fuskarta na kayatar da shi..........A hankali ya cika lebenta da ya dauki ja ya tsare fuskarta da kallo cikin nutsuwa ya silala hannunsa cikin rigar barcinta wace dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login