Showing 138001 words to 141000 words out of 190762 words
Chapter 47 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
ta yin ai
Sai na karshe shawarar da take tunanin ya dace ta dauka....., shin ta amsa ne ko a'a?????
Bude kofar da shigowarsa ya saka su duka duban hanyar da ya shigo din
Da sauri Maman karima ta boye daurin maganin kirjinta na amsawa , saboda bata taba tunanin zuwansa a irin wannan lokacin ba
Shigowa ya idasa yi da kula ya amsa gaisuwar da Maman karima ke yi masa har kamar zata duka daga zaunen da take, sannan ya sake dora dubansa a kan Khadeeja da shigarta ta fi komai fizgarsa.......Ya rab, ko dan ya jima rabonsa da mace a cikin falo wace zai je ya dawo ya tarrdo ta yi kwaliyar tarbarsa ne ya sa ko me yarinyar nan ta saka ke daukan jikinta?, a gaskiya an tafi da shi, ya yaba sosai, kwaliyar ta yi kyau
A tausashe Khadeeja da ta dan dubi fuskarsa ta dan sada kanta kasa kasa ta ce" Barka da warhaka, wannan mamanmu ce , sako ta kawo mana mai mahimmanci shine zata bani"
Da sauri Maman KARIMA ta dubeta jikinta na son daukan rawa
Sarai ya ga yannayin maman Karimar sai dai bai tsaya ya jima ba ya nufi hawa sama bayan ya furta" Masha Allah, mun gode mama Allah ya saka da alkhairi, A huta lafiya "
Irin yadda kirjinta ke luguden kida hakama jikinta ke rawar balaki, zufa kuwa ta keto mata nan da nan
Tana gannin ya haye ta dubi Khadija da kyau ta ce" Ni zaki wulakanta ki nemi tona min asiri?, daga zuwa kawo maki abin alkhairi shine zaki nemi falasani?"
Khadeeja ta yi kamar bata gane ba ta ce" Mama, ki yi hakuri dan Allah, na zata ai idan ya ganima murnar hakan zai yi ya yi maki godiya shi yasa na sanar masa"
"Tafi cen munafuka, wato ni zaki tabatarwa kin tsotsa a jikin mugun iri ko? ba laifi zamu hade ne, ban gama da ke ba!" Ta mike tana fada da zafi zafi sannan ta juya fuuuuuuuuuuuuuu ta yi tafiyarta
Khadeeja ta jima tana kallon hanyar da ta bi, a hankali ta budi bakinta ta furta" La'ila ha illalahu Allahu Akbar, la'ila ha ilalahu wahadahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kullu shai'in kadir, la'ila ha ilalahu wala haula wala kuwata ila bilah" har kafa bakwai A karkashin zuciyarta ta ayana' Ya Allah, Ni baiwarka ce mai rauni, gani a sabuwar rayuwar da ka hukuntani kasantuwa a cikinta, kai ka san me ka boye a ciki, ya Ubangiji ina da niyar yiwa iyayena biyaya,, ina da niyar yiwa mijina biyayya....., ya Allah ka tsare Ni ka dafa min ka sanyaya min dukkan abinda ke cikin kadarar aurena, ya Ubangiji duk wani mai nemana da alkhairi ya rigayeni samu kafin in samu, idan shari yake nemana da shi ya rab ka dorani samansa ka tsare ni, ka sa sai dai idan na juya ya ga bayana'
Wani karfi ta ji ya karra shigarta, a nutse ta dauki wayar dake ajiye daf da karamin table ta danna numbar kicin kamar yadda aunty shareefat ta koya mata , sunna dagawa ta yi musu salama sannan a tausashe ta ce" maman baby a zo a kwashe kayan, sannan yau me kuke girkawa ne? ina nufin na mai gidan??"
Maman baby ta ce" Za'a yi masa samosa da miya ne Hajia"
Khadeeja ta dan yi tsam, a tausashe ta ce" Har kun kwaba?"
Maman baby ta sanar mata cewa a'a, dan haka ta ce" Ok ba damuwa kar ku kwaba, duba da dare ne idan ya samu abinda ba na fulawa ba zai fi, saboda harkar kwonciya barci, ina zuwa bari in ji me zai ci sai in sauko mu girka ko in sanar maki maman baby"
Maman baby cike da farin ciki da girmamawa ta ce" In sha Allah Hajia sai kin sauko Allah ya sauko mana da ke lafiya ya tsare"
Murmushi KHADEEJA ta yi ta ajiye kiran , a nutse ta mike ta sake kallon falon ta ga bashi da wani dati, haka kuma kanshin turarensa na nan, sai kawai ta juya ta shiga haurawa sama tana jin tuni an fara kiran sallar magariba sai ta nufi nata dakin da dan hanzari dan ta yi wanka ta yi sallah kafin ta je inda yake din saboda sallar ta shigo ba za'a yi komai ba sai an yita
MAMAN KARIMA kuwa na fita ta nemi Hajia Z bata gani ba ta fito ta nufi bangarenta kamar zata kifa har yanzu jikinta na rawa
Da ta shiga ta samu Hajia Z din na falonta tana duban hanya hankalinta du ba a jikinta ba domin da ita ya fara haduwa , ta sanar masa maman su Khadeeja ce ta rako Duda bata da lafiya shine zata koma bangarenta, jikinta sai rawa yake yi dan tsoron kar aje ya shiga ya samu wata barakar da zasu shiga uku gaba dayansu.
Maman KARIMA bata zame ko'ina ba sai kasa tana rike ciki ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Kaka Z gaba daya ta rakito itama, wannan karron cikin nata na juyawar gasken gaske ta ce" Na shiga uku, me yake faruwa?, me ya sameki kina mata? shikenan zaki kashe min aure ki sakani a uku"
Maman karima ta ce" Zainaba ba zaki gane ba, balaki ne ya shigo maku gidan nan, yarinyar nan har ta dame uwarta ta shanye, zainabu kin kuwa san ce masa ta yi sako na kawo musu shi da ita? innalilahi wa inna ilaihi raj'une Ni zata saka a uku? Wannan yarinyar sai ta fi uwarta balaki, tun bata tafasa Bama har zata kone?, "
Hajia Z ta ce" mene? ki ce ya amshi abin? wai meye kika kullo a ledar? to walahi ba ruwana ko me kika kawo babu hannuna a ciki, walahi ba ruwana"
Maman karima ta ce" me fa ya amsa? ban bashi ba , ki daina irin haka kina karra tsoratani dan Ni tsorona daya kar ta fada masa abinda na fada mata ya sa a kamoni a gidan nan"
kaka Z ta mike tana zarro ido ta ce" Shine kika nufo nan? tashi tashi ki kama hanya dan du inda suke ma yanzu sun kusa karasowa Ni ba baki jaza min ba wata fitinar, ma yi magana ta waya"
Haka tana ji tana ganni kawarta ta koreta dan kar ta sakata a matsala, ta fito zuciyarta cike da daci ta kama hanya a kafa tana ayana' shikenan, zan je in samu Karimar in fada mata bata da miji sai wannan balaraben mai kudin, zamu hada kai mu yako abinda ya dace, zaki yi bayani ne zainab!'
Khadeeja
Ta gabatar da sallar ta cikin nutsuwa ta zauna tana dan jan carbinta ta ji an bude kofar dakinta
A hankali ta dago ta dubu mai shigowar
Yanzunma wata shigar ce a jikinsa mai nutsuwa da shiga zuciyar mai kallo, haka kuma da wata fantsamemiyar waya a hannunsa , dayar kuwa a kunnansa ne a hankali ya furta" Maman AL'WALID gani ai zan nuna mata"
Ya dan yi shiru , a lokacin ne kuma ta mike daga saman salayar ta ninke ta sake dubansa ta ji ya furta" To shikenan"
Kiran ya katse , idannuwansa a kanta, a yanzu hijab ne ruwan madara a jikinta ,, daga kasan hijab din doguwar riga ce ja irin mai dogon hannun nan, irin riga da hijab din nan da ake yi ne, sai Safa mai ruwan madara a kafarta..........., elle est juste magnique ( kawai a hade take ), kallonta kadai ya isa ya sanyayar da zuciya
Karasowa yayi inda take a nutse ya kama hannunta sannan ya nufi wajen kujerar dake dakin ya fara nuna mata wajen zama, ta zauna din, sannan ya zauna dan daf da ita wanda hakan ya sa ta ji nauyi sosai da kunya, harma ta sada kanta tana dan kallonsa ta kasan ido
Kasantuwar wify ne a gidan gaba daya sai kawai ya kamo ya bude vidion da aunty shareefat tace ta yi ta turo a nuna mata ya kunna mata ya mika mata ya zuba mata ido , domin vidion na fara haskawa ta zubawa vidion ido lokaci daya yannayin fuskarta na ta'allaka da yannayin wa'inda vidion ke haskowa har aka kai kan su Lubna dake baban falo da Mama
A hankali ta zuba musu ido, girarakinta na dan yamutsewa hadi da fara'a a fuskarta......, lokaci daya tana sake kallonsu har aka wuce su, da dan sauri ta dago tana mika masa ta ce" Papah litle Please, dawo min da su Please" tana fada din hawaye na sauka daga idannuwanta hakan ya sa ya fuskanceta da kyau a hankali ya amshi wayar ya ajiye ya ce" To menene na kukan?"
Khadeeja ta sada kanta, sai kawai ta shiga shashakar kuka ta ce" Ina missing dinsu sosai........., rabona da jin muryarsu tun da aka daura aure, ita kuma Mama tunda ta min....., tunda ta min nasiha........"
Ido ya dan zarro a hankali ya ce" Why? baki da kudi a waya ne?"
Kanta ta dago ta dube shi, a hankali ta ce" Wayar ce bani da ita ai"
Fuskarta yake kallo, a lokacin da ta sake dago idannuwanta dan kallon tasa sai ya dauke nasa idannuwan sannan ya lalubo wayar tasa ya shiga numbar aunty shareefat whatsup ya danna mata video call
Aunty shareefat ta daga tana fita daga cikin mutane , ganninsu zaune ya sakata sakin murmushi ta ce " Big Son???"
A tausashe ya ce" Maman AL'WALID, kun fito ne?"
Aunty shareefat ta girgiza kai tace" Walahi sun ki yarda mu juyo wai kakan kurma yace sai ya zo, yana hanya shi din dai muke jira, ba zan iya rigimar kakan kurma ba idan muka taho din a kaina zata kare"
Ya dan dage girarsa yana son tambayar to me zai musu idan ya zo din? sai ya share kawai a hankali yace" wai kuka take yi tana son gannin Mama da sisters dinta...., ko in kawota ne?"
Aunty shareefat ta dan zarro ido a hankali ta ce" Yanzu? a'a bari in kai wayar ki gansu ta vidio call Daughter kin ji? in yaso daga baya sai ki zo kin ji?"
Khadeeja da ta dan raba kusancinta da shi bata san lokacin da ta matso tana murmushi hadi da gyada kai ba, shi kuwa sai kawai yake kallon wannan kasan idannuwan nata yana sake mamakin dimple a kasan ido jama'a?
Zuwa ta yi ta shige ta karasa har inda su Mama suke ta yi salama sannan ta shiga a lokacin Mama na tufke gashin Lubna, lubnar na fadin" Mama Allah zan je kitson goben in sha Allah zan je"
Mama ta ce" Karma ki je Lubna, da hannayena ai sai in maki a gida tunda ba zaki je ki yi mai kyau ba"
Dariya Aunty shareefat ta yi bayan ta shigo ta ce" Mama da ya'yanta kin boye a nan Mama, kai na jima rabona da in ga mutun mai kunya irin taki masha ALLAH, kin ga ga Hajia karama fa a waya tana rigimar Mamanta"
Mama ta dan zabura domin kawai sai gannin mutun biyu ta yi a zaune sunna kallonta, da sauri ta duke tana rufe fuska ta ce" Innalilahi"
Ai kuwa Khadeeja dariya take har tana kwonci a saman jikinsa ta nuna masa ta ce" Walahi an shamaci Mama, Lubibin mama kitson karfi da yaji ake maki? ina karime an mata, je ina yar rainin wayon nan take, wai ya aka yi na ga kwana ษaya tak da bana nan Mama ta karra fari?"
Yan matan kuwa ina, ihu da kokowa suka karbe wayar tuni suka yi waje da gudu, aunty shareefat kuwa dariya take har tana kama ciki ta ce" Mama dago ai sun tafi da wayar "
Mama ta dago tana dafe haba ta ce" kai auntyunsu fisabililahi ya zaku biyewa yarinyar nan?, na zata ita kadai ce ai"
Aunty shareefat ta ce" A'a Mama, tare take da shi ai , kai walahi Mama kin ban dariya"
Ita dai Mama ta yi murmushi zuciyarta na sakuwa da tunanin a wani hali Khadeeja take? dan kuwa ita du gani take yi Khadeeja na cikin matsi da takura saboda har yanzu kallon jaririyarta take yi mata
Yan matan mama tunda suka fuskanci wanda ke kusa da ita sai suka ringa gaishe shi da girmamawa sannan sai su yi shiru, sun kasa ci gaba da ihun da suka fara da murnar gannin junna, hakan ya saka shi murmushi ya dan mike ya bacewa gaban camerar, sai dai a yanzun sai ita ta kasa motsin kirki domin a kujerar dake facing din Tata ya zauna ya zuba mata ido
Lubna na murmushi ta ce" Innalilahi su iyani a gidan miji, ke hijabin meye wannan kika maka kamar zaki je fatawa, iyeah dage mu ga kwaliyar mana? su Anmy an samu duniya ko tunamu bakya yi ko? dazu da muka cewa Mama muna son zuwa wajenki tace mu je mu fadawa Aba, ke dai mun zata ya saku ne kwana biyu da yake cikin haba haba na dariya, Karima tace da shi Aba muna son zuwa gidan ANMY, wa bilahilazi da ya makota sai da Mama ta wuni tana diga mata maganin ciwon kunne......"
Ai kuwa suka bushe da dariya har Karimar saboda dazu ne fa rabon a yi, ya dawo gida yana fadin a tashi a shiga shirye shiryen tarbar baki, ya sako su Mama a gaba yayi kiran su Mama Fateema ya basu kudi masu yawa yace maza a je a siyo zabi a zo a soye, jus kuwa dama na kwali aka jibge, yana ta haba haba din nan ne suka je zungui zungui suka yi tambayar nan, ai ita da ta yi tambayar da ya makota da su din da suka bale a guje sai wajen babarsu, ya bi su cen din ya dudura ashar dinsa son ransa tana tsaye tana kallon sa, har cewa yake yi mutun ya jawa ya'yansa kunne ko ya'yan kuka su janyowa uwarsu jifa , shi ai yanzu zai saka ido sosai kar a je a rikita masa y'a a gidan mijinta
Du yadda Khadeeja ta so dane dariyarta sai da ta gaza, ta saka dariyar tana rufe bakinta, hakan ya saka shi zarro ido yana sauraron na wayar dake bada dukan da dayarsu ta sha abin mamaki sunna sheka dariya
Kasa jurewa yayi ya amshi wayar ya kalle su, ai kuwa da sauri Lubna ta mikawa Karima, Karima ta sakarwa ameerah, ameerah ta mikawa ummi sunna sunne kai, da sauri ummi ta kife wayar tana zarro ido kasa kasa ta ce" Mun lalace ashe yana nan?"
Ya katse kiran ya karasa inda take ya zauna yana murmushi ya ce" Ikon Allah, ya zaku ringa yi maka dariya?"
Khadeeja ta dago tana kokarin hanna kanta dariyar ama ina, tana nuna masa ta ce" Ka kuwa san yadda Aba ke maka? da baiban hannu yake yi, idan ya kauda maka hannun nan ko waye kai sai ka hantsila, ga KARIMA da tsoron duka, ko yaya aka yi ta yarda suka sakata a gaba wajen wannan jihadin????๐คฃ๐คฃ" ta idashe tana yin wata dariyar har tana dantse lebenta
A hankali yake dauke dubansa a kanta, sai kuma ya maido, dariyarta na saka shi a cikin wani yannayi na shaukin dake son fin karfinsa
A hankali ya kama hannunta guda ya matsota jikinsa sosai, lokaci daya dariyar Tata ta dauke ta kalli fuskarsa ta bude baki murya a dan hargitse ta ce" Au, dama nace me za'a dafa ne?, abinda zaka ci yau. da d.............."
Hade sauran maganar ta yi sakamakon bakon al'amarin da ya ziyarci lebunanta wanda bata taษa kawowa ranta shi ba, lokaci daya kirjinta ba wani irin bugawa sannan ta so janyewa
A hankali ya saka dayan hannunsa ya sake hade jikinta da nasa ba tare da ya saki lebunnan nata ba, idannuwansa kuwa a lumshe suke tamkar ya samu wani gagarumin abin da yake ฦishirwa, hakan ya hanna masa gannin kokarin sumewar da take yi ya ci gaba da shafarinsa har sai da kiran sallar isha'i ya shige kunnayensa sannan ya dakatar da abinda yake yi a hankali idannuwansa lumshe kirjinsa na bugawa da sauri da sauri
Idannuwan nasa ya bude ya sauke dubansa a kan fuskarta dake duke kamar zata nutse, jikinta kuwa rawa yake yi kamar an jona mata chkng
Murmushi ya dan sauke, a nutse ya mike daga saman kujerar dan kar ya rasa sallah domin ya san da sai ya sake dauro alwallah, dan haka ya dan duko inda kanta ke kasa a hankali ya ce" Kar ki shiga kicin plz......., nd abinda zan ci a yau......ai yana tare da ke"
( Innalilahi nan kwate ce ta rubuta๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ๐ถ๐ฟโโ๏ธ)
Kai baka san baba Ya'u ba ko? kaikaikai han, to ai hikenan ba zamu ce maka komai ba ka yarda dai ka aikata, ka yarda!โน๏ธโน๏ธโน๏ธ๐๐๐๐
41
07/12/2024, 15:25 - samiraharounayacouba: Ido ta zarro ta sake sunne kai har sai da ta ji karar rufe kofar ta zabura a tsorace ta yi tsuru tsuru sai kuma ta ringa furta " Innalilahi na shiga uku, wayo me kennan? na Bani me yake nufi? wayo Allahna "
Tana tsugunen nan gaba daya jikinta na rawa rawar nan har aka tada sallar isha'i sannan ta mike kamar an zare mata laka ta nufi bayi saboda yin wanda da dauro wata alwallah , ba dan ta tabbatar hakan ya zame mata wajibi ba, a'a, ko daya, dan dai kawai a cire shaku ne!
A gidan Aba kuwa bai jima ba ya shigo gidan fuskar nan tasa tamkar gonar auduga ya karaso yana sake yin salama, matan na amsawa
Kaka B ce ta ce "Barka da isowa kakan kurma, sannu da karasowa"
Aba ya saki murmushi ya ce" Barka kadai Hajiar tsoho ya hakuri da tsohon cen? , ba fa kurma bace bb ce Hajia"
Aunty shareefat ta ce" Kai yaya yanzu baban naka ne ake hakuri da shi? a'a ai babanmu shine damo Sarkin hakuri"
Aba yayi dariya ya ce" Na rabaki, mutumen nan ina hakuri da shi sosai da sosai, yauwa y'ar albarka bari in ga gimbiya, ina take ne? Gimbiya"
Da sauri ya wuce ciki, aunty amarya dake dakinta tunda aka ringa shigowa da akwatunnan nan ta kasa zama ta yi dakinta ta zauna ta ringa sauke ajiyar zuciya mai zafi ce ta yi wuf jin muryarsa ta fito tana tsane ruwan da ta yi saurin diba a kofi ta shafawa fuskarta ta dube