Showing 87001 words to 90000 words out of 190762 words
Chapter 30 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
bai dace dan kawai zai zo gida ta zo ba, bayan iyayenta basa gari, sai ta nuna ai yayi daidai da lokacin hutunta ne, kuma idan ta zo uncle dinta da matarsa na nan, hutu ne kawai suke yi su juya, ya sani bata taษa tafiya in yana gari ba, wani lokacin tare suke juyawa a jirgi sai dai sauran su dawo da mota, ama bai taba Sannin a haka yarjejeniyar abin yake ba, da ta fita daga mota tana magana yana jinta, domin motar a bude ta barta kuma tana magana sama sama kamar tana magana da kanninta ne, domin idan kana da mutunci ko abokin ka ba zaka yiwa magana irin haka ba, shin so hauka ne? wannan so din ne kuwa take yi ko wani abin ne??????????
A nutse ya budi baki ya ce" Mufeeda dama wayar da kika gama kina watsa hannaye a waje da dady kike?"
Mufeeda ta dube shi da wani saurin irin na dazu , a lokacin da ya mata tambayar nan
Yanzu ma da inda inda ta ce" A'a fa, bab ba shi bane ba fa, mai aikinmu ce take bani soko in ji shi, shine nake yi mata fada"
Tissu din dake cikin aljihun rigarsa ya lalubo ya kai wajen fuskarsa yana dan gogewa ya ce" Ok, yayi, ki je ku tafi Niamey yanzu, ku gyara kayan ku direbobin su fitar da motocin su kai a duba su sannan su amshi katin mai su cika a gidan man Litle na bakin hanyar fita daga Damagaran, ku sauka lafiya"
Kallonsa take yi idannuwanta na cikowa da hawaye, kanwar Tata kuwa tana gama jin haka ta juya tana fadin" An gama, tunda ogan ya bada umarni yar rainin hankali kawai!"
Kicibisss suka yi da Jaruke ta fito da gudu gudu da wayarta a hannunta jikinta na rawa
Wayar ta kubce ta fadi, da sauri ta rarumo tana fadin" Innalilahi ke dan ubanki kauce, mun shiga uku,lalle yarinyar nan khalisat take ko wa? ta gidan su honorable y'ar iska ce,kuma walahi kiyayar da take yiwa Mufeeda ba karama bace, ke ji fa abinda ta yi posting a Tiktok, wai daurin auren ELHAJI AL'WALID jibi, yarinyar nan dole mu ci ubanta , mune zamu bata hankali banza wawuya!"
Rikota auta ta yi tana zarro ido ta riko damtsen y'ar uwar tata sama sama ta ce" JARUKE , ashe mahaukaciya ce ke?, aure fa kika ce? ELHAJI AL'WALID din dake cikin mota gayacen? Aure? jibi? shi da wa to? kan ubancen ke lalle wannan yarinyar bata san da su wa take magana ba , what!"
Mufeeda dake masa hawayen ita ba zata je Niamey yau ba ta juyo da sauri, saboda mota dai a bude take, kuma magangannunsu sama sama ne, ba wani a hankali bane, maganar da suke fada kuwa tsaf ta ji, hakan ya sa zuciyarta ta yi wata irin bugawar da ta ji zufa na keto mata a zaune
Bata iya cewa komai ba kawai ta fita ta nufi inda suke,
Tana karasawa bata tsaya wata wata ba ta wankawa JARUKE mari , rai bace, hannayenta har sunna rawa, fuska tamke ta ce"
07/12/2024, 15:05 - samiraharounayacouba: ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*FARKON GANIN IDONA*
๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ๐ธ๐บ
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*๐ณ๐ช
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you ๐*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ฦAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAฦIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi ashirin da biyar(25)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
https://chat.whatsapp.com/KmdHXVV1oUlKAT6ldQEXOf
YAR UWAH SHIN KINADA LABARIN WANNAN BUSINESS MAI SAURIN KAWO KUDI KIKA TSAYA HAR YANXU BAKI SHIGABA TOH BARI KIJI IDAN KINADA BURIKA A ARAYUWAR KI TOH MAZA KI SHIGO META FORCE DOMIN CIKAN BURIN KI DA KIKA DADE KINA SON KI CIKA TA GEFEN KUDI HAJIYATA IDAN KINA META FORCE KI KASHE KUDI BAKOMAI BANE A WURIN KI DAN HK KADA KIBARI KIYI WASA DA WANNAN DAMAR YIMAZA KISHIGO KEMA KI FARA SAMUN KUDI IN DOLLARS WATO MAZAJEN KUDI*๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
๐0912 262 1080
LABARI
Tana karasawa bata tsaya wata wata ba ta wankawa JARUKE mari fuska tamke ta ce " Uban me kike fada ? kina da hankali kuwa?"
JARUKE ta rike kuncinta, rai bace ta ture Mufeeda tana fadin" Shine zaki mareni? , kali abinda na gani a Tiktok a page din khalisat din nan ta gidan su honorable, shine zan gwada maki, kalli fa wai cheri zai yi aure wai!"
Ido ta rintse ta sake daga hannu ta tsinkawa JARUKE marin da ya sa JARUKE daka tsalle ta yi wurgi da wayarta kasa wayar ta fashe, da ihu ta ce" Innalilahi ke kina da hankali kuwa?"
Bude gefen da yake ya yi ya fito daga motar, saboda har sun fara tarawa kansu mutane, ya nufo inda suke a lokacin Mufeeda ta nunawa JARUKE yatsa ta ce" Walahi, walahi idan bakinki ya kuma danganta mijina da wannan maganar sai na shake ki, walahi kar ki ja in yi sanadiyar barinki duniya , ki kula, ki kiyaye!"
Tsayawa ya yi a bayanta, a kausashe ya ce" Kina cikin hayacinki kuwa? me kike fada?"
JARUKE da ta fara tsorata da yannayin yayar Tata ta dube shi da sauri a tsorace" Big brother walahi babu abinda na yi mata, wai khalisat din gidanku ne ta ษora wata magana a Tiktok shine abin ya daga min hankali na taho in kawo mata ta gani shine take marina"
Da sauri autar ta karษe maganar tana fadin" Kema me yasa baki bari ta ga abinta da kanta ba, tunda ta san sun tsaneta sai ta iya da su, ama kin san ai babu abinda ta fi tsana irin maganar da kika fada a rayuwarta ko?"
Mufeeda kuwa tunda yayi maganar nan da sauri ta dauko wayar JARUKE ta shiga, duda screen din ya fashe haka ta shafata cikin dabara ta shiga ta dana kan abin ta fara kalla sannan ta kawo masa, hannayenta har sunna rawa ta miko masa , kirjinta kuwa yana sama da kasa tarin bacin rai da tashin hankali ta ce" Ka gani? da nake fada maka su suke tsokanata su suke jana da fitina ka gani ko? wai zaka yi aure, wai jibi zaka yi aure tana gayatar ilahirin mutanen Nijar da ketare, duba ka ga a cmmnt section ana ta tambayarta ba'a gane ba aure? da wa? bata ba kowa amsa ba sai wannan da yace ashe gari zai yi tumbatsar mamaki auren honorable da Mufeeda kalli amarta, kalli abinda ta rubuta, wai ba da Ni bane...., ka ga abinda take yi min ko? walahi yarinyar nan ba zan taba yafe mata ba, du abinda take min sai na rama, in ita tana yin haka ne dan ta bata min rai bata san baban abu take tabowa ba? ba damuwa, zata ga abinda zan yi mata!"
Gaba daya Mufeeda ba a hayacinta take ba, irin yadda take magana sama sama ido waje jikinta har yana rawa kawai yake kallo daga shi har kannenta
Kai ya girgiza ya juya zai yi tafiyarsa, danma yama ta yi a inda suke tsayen innuwa ta karaso da sun sha dukan rana da noncence din Mufeeda
Ya kama marfin motarsa zai shiga ta yi gagawar riko hannunsa tana fadin" Bab yanzun ma laifin nawa zaka gani ko?, yanzunma gani zaka yi nice mai laifi ko? ka duba fa ka gani irin abinda take min"
"MUFEEDA!, CIKA NI!" Ya fada a mugun kausashen da ya sakata sakin hannun nasa Tana duban fuskarsa
Rai bace ya dago hannunsa da ky din dake ciki ya nunata ya ce" Gaba daya baki da nutsuwa? gaba daya baki da linzami a harshen ki? Ni zaku mayar shashasha ke da kannenki? Ni zaku fito kunna ihu a gabana kunna wulakanta junna da ahalina? ok, dan khalisat ta ษora haka a Tiktok shine wannan daga Muryar? i said shine na furucin zaki halaka y'ar uwarki? da matata kike a yau a gidana yaya zaki yi kennan in hakan ta fito maki?"
Kanta ke sarawa, babu abinda ke jijiga nutsuwarta irin fadansa a duniya, sai kuma furucinsa masu tsauri ne sosai yau a kunnayenta
Da sauri ta shiga murza goshinta tana kallonsa, sai kuma ta girgiza kanta tana furta " No, no No, ta san abin nan da ta yi baban abu ne da zai fidani a hayacina, ta sani sarai ta yi, su burinsu su ga bayana ne kawai , burinsu kennan fa! bab yaya zaka ce da matarka nake, dama Ni ba matarka bace? kuma ko matar taka nake ai ba wannan maganar, aure fa take nufi, kai ka yi aure da wata macen ina duniya? hahahahhaa lalle khalisat!"
Tunda suke bai taba kai hannunsa shi AL'WALID da kansa a jikinta ba sai yau, a yau dinma dan ya dawo da ita hayacinta ne ko menene? gaba daya rainin wayonta nema yake yi ya wuce misali, abinda ba zai taba dauka ba, Shi bai taba duban budurwa da nufin zai zauna da ita, ita kadai ba a duniya, karya ne, kuma ko macen aure wace suka zauna har Allah ya raba basu taba yin magana makamaciiyar wannan ba, to a kan mema zata nemi ษorawa kanta ciwon da bashi da magani? ciwo ne, baban ciwo ne marar Tabas, domin shi da kansa bai taba tunanin za'a kawo masa magana irin wannan a rayuwarsa ba, har yanzu matar da akace za'a aura masa din fa bai tantanceta ba, ta yiwu ta leko ta koma za'a yi saboda daga inda ta tsaya ta hararesu ta juya baya tunanin tana da wadataciyar tarbiyyar da zai yi zaman aure da ita, shi kuwa ba zai dauki raini da wulakanci ba! kwarai zai je ya samu moma karama kan abinda ta yi, bai dace ba, ta yi neman fitina, Duda bai san girman abinda ke tsakaninsu ba, ama bai kamata ta ษora abin nan a Tiktok ba, kai subahanallah bai san me suka dauki social media ba, ace kai jira kake yi komai ka kai ka watsa duniya? kai baka da sirri ne a rayuwa? komai sai ka kai ka watsawa duniya? mtsssssss
Habarta ya dago ya saka idannuwansa cikin nata, ga kannen nata kuwa yuuuuuuu a gefensu a tsaye,
A kausashe ya ce" Na taba yi maki alkawarin koda Allah ya sa mun yi aure daga ke ba kari?"
Mufeeda kallon cikin idannuwansa kawai take yi
Ya dora da fadin" Ki yiwa kanki adalci, ki kiyayi furucin bakinki, idan har kina cikin hayacinki kin san cewa ko alkawarin aure ban taba yi maki ba, saboda Allah keda komai ba Ni ba, du yadda zan so zama da ke sai ya aminta, kin sha son na yi alkawarin nan na fada maki bana alkawarin abinda ba Ni nake da shi ba, kina tune? i mn kina cikin hayacinki kina tune?"
Mufeeda ta lumshe idannuwanta, a kausashe yake yin maganar, ya dan duko da tsayinsa daidai ita, ya kare tsakaninsu da kannenta, sai dai a kausashen kuma kasa kasa sosai ta yadda duk wanda ya ji abinda suke fada balakin son jin gulmarsa ba kadan bace, hakan ya sa gaba daya tsigar jikinta ke tashi, kanshin turarensa ya idasa hade jikinta,
A hankali ta rike damatsunan hannayensa, a lokacin ne kuma JARUKE ta kashe musu hoto , domin su ji suke sasantawa ake yi harma ana daf da shan minti
A nutse ya dora da fadin" Ban taba saka maki sasari na, ina cikin manema aurenki ne nah?, ko a yanzu bata cenza zani ba, sai dai yannayinki na yau ya sa ba zan je da bukatar a hade bukatar gidanmu da tawa ba, dole zan karbi bukatar gidanmu kafin in gama gane tawa bukatar, domin kwarai ta yaro kyau take bata karko!......., Mufeeda ba karya khalisat ta ษora ba, jibi zan daura aure, ba yana nufin na rabu da ke bane, ki nutsu ki je ku shirya ku tafi , kin fahimta?"
Auta ta zabura ta matsa ido waje ta ษora hannaye saman kanta kirjinta na bugawa
wato lokuta da yawa idan sunna nuna mata AL'WALID na basu tausayi in suka tuna halayarta da kuma aurensu shi da ita, du sunna nufin zata wahalar da shi zata saka shi a wani hali na abin tausayi sai tace da su basu san waye AL'WALID ba, da suke ganninsa nan shiru shiru ya fi kowa iya rigima, kuma baya tsoron uban kowa idan abin yayi ya tashi kansa tsaye yake yi sai dai du abinda zaka ji ka ji, gani suke yi a wai ne, domin su dai wani lokacin har ya zo kasar ya bar kasar maganar kirki bata hada su, dan sai su ga ko kallonsu baya yi bale yace da su sannunku su kuwa dama ba gaisar da mutun suka iya ba gaskiya ko waye kai in ba kai ka fara ce musu sannu ba sai dai ku ringa kallon junna da su, haka suke, du basa yarda gani suke yi wai ne sai yanzu da yake tsaye kikam a gaban YAYARSU da suke tsoro kamar me,domin Mufeeda irin yaran nan ne yan balaki, ko a cikin kawaye ta adabi kawaye ba maza ba mata bale a cikin gida, ko a gidansu ita ake yiwa biyayya kuma in abu ne in ta yi tsaye tace ba zata yi ba ba fa zata yin ba sai dai mahaifinsu yace zai lalabata daga baya ta yarda a yi, babu mai shigar mata daki ko mamansu, babu mai taba kayanta , bale da Allah ya haษa soyayarsu da AL'WALID gaba daya abin sai ya idasa rikicewa girman kai,, isa, fada , kala kala, ko a cikin gari an santa yawanci kawayenta mrs AL'WALID suke kiranta da shi, dan kuwa babu wanda bai santa da haka ba, sai gashi idonta idonsa bayan yanzu yanzu ta gama alwashin yar gidansu ta ษora ne dan ta daga mata hankali dan ta tsokaneta , ya dubeta, ido cikin ido ya rike habarta a tsaye a gabanta ya sanar mata? su kam yau ai sunne suka shiga uku ba kowa ba
"A........Au......Aure dai aure? Mufeeda ta fada bayan ta dantsa faratunanta a cikin damatsunan hannayensa, tana jan numfashi da kyar sannan ta sake matse dan space din da ya rage musu ta hade jikinta da nasa dan bata jinsa da kyau , kuma tana da bukatar jin nasa da kyau din
Idannuwansa ya dauke daga fuskarta ya ja baya, ama cikin ikon Allah da wata bakuwar masifar kamar an mana musu gam, sai ta sake matsowa ta matse shi
Du yadda yake gudun nuna mata bacin rai a yau so take yi sai ya nuna mata, gaba daya jikinta kuwa rawa yake yi kamar an jona mata chkng
A hankali ya ce" Ki ja baya"
kai take girgizawa tana kallonsa ta ce" Dan jiya mun yi fada da yan gidanku ne zaka ce zaka yi aure? dan ka daga min hankali ko? idan ka yi aure bab ai ka san zaka sakani a uku ko? bab me na yi da zafi haka? dan kawai ka rikitani ne zaka ce zaka yi aure? wani irin aurenma wai...na gaske ko na wasa......................? bab dubeni dan Allah dubeni dubi fuskana da kyau mu yi magana du bana ganewa , ban ganewa bab.....bab......., aure? walahi idan zaka horani ka guji irin wannan horon, in wasa kake min ka daina, zaka kasheni ne, kana iya kasheni ne, dubi kirjina, taba kirjina ka ji, bab du laifin da zan yi maka gwara ka zane min jiki da ka haษa kanka da wata macen ko Wacece , bab kana tunanin a duniya akoy wata mace da zaka haษa kanka da ita? ko wace ta shani kafin ni dan bata duniya walahi da sai na yi mata abinda zai gigitata!, bab du yarinyar da zata rabeka ta rabarwa kanta masifa da balaki, domin walahi walahi sai na gigita farin cikinta, sai na wulakantata, sai na sakata ta shiga uku........ ka ga ka bari dan Allah, ka cire belt dinka ka zane min jiki in haka zai sa ka huce da wannan maganar ka ji????"
Ta karashe tana son ษora kanta a kirjinsa bayan ta yi dage, sannan ta ษora hannun nata a wajen belt din dake kugunsa hawaye na zuba a fuskarta tamkar an kunna pampo, tunda take bai taba fadin abin da ta ji ta gigice irin na yau ba, bai taba fadin abin da ya nemi sakata a wani hali irin na yau ba
AL'WALID ya rike hannunta da wani irin saurin da bai taba Sannin yana da shi a jikinsa ba, da sauri ya zuba mata kausasun idannuwansa da matsanancin mamakinta, ina zata kai hannunta? innalilahi wa inna ilaihi raj'une....... Allah ya tuba tunda marigayiya ta rasu ai babu macen da ta kara matse masa waje irin haka sai yau, lalle badalar yarinyar nan yawa ne da ita in aka ษauki kalaman bakinta kuwa kamar ba addinin musulunci a tare da ita
Matsar da ita yayi da kyau ya shige motarsa ya rufe da karfin da ya sa ta rintse ido sannan ya kunna motar ya figeta ya fice a gidan, dan kuwa shi dai bai taso ya ga ana dukan macen da ake yiwa kallon wace za'a iya hada gado da ita a gidansu ba, da ace ya ga haka tabas da yau jikin Mufeeda sai ya gaya mata na wulakancin da ta yi masa da raini!
Kofar da mai gadi ke maidowa zai rufe take kallo bayan ya fita, lokaci daya numfashinta na neman gagarar kofar hancinta
JARUKE ta kasa yin