Showing 42001 words to 45000 words out of 190762 words
Chapter 15 - Farkon Ganin Idona Book Compelet By Sajida Nijar.txt
tausashe ya ce" Allah ya tashe mu lafiya, Allah ya karra miki lafiya"
Hajia inna ta sakar masa murmushi a tausashe ta ce" Ka yi tunani ka ji? ka tuna du wani mai sonka da alkhairi a bayansa yake, idan har ba cutuwa ka yi masa biyayya "
Kai ya gyada ya juya ya rage hasken dakin da na Ac dan sanyin yayi yawa sannan ya tafi ya rufo mata kofar ya nufi bangaren sa
Har ya gama abinda yake yi zuciyarsa na yawan tambayarsa menene dalilin da yasa Elhaji Hamza baya son ya auri Mufeeda da farko, ko yace ya aureta ta zama matarsa daya jal har karshen rayuwarsa?
Mufeeda tana yi masa son da shi kansa bai san girmansa ba, ya dai san cewa tana sonsa fiye da komai da ta malaka
Yarinyar tana jin maganarsa tana gudun bacin ransa, lokuta da yawa ita zai batawa rai ta dawo tana ta bashi hakuri da rarashi har abin na damunsa yana tunanin wai ita ba zata iya nuna masa fushin ta bane?
Yakan hadu da abubuwa da yawa wa'inda yake gannin ta cencenci ya ajiyeta matsayin iyalinsa, Duda akoy wasu halayan da yake gannin ai ba na mace bane, misali irin yada daidai da ba daidai ba in dai shi ya shafa daidai ne, irin yadda take zuwa zance wajensa dai da sauran su, ta yiwu wannan dalilin yasa Aba cewa ba zai aureta ba, ta yiwu tunani yake yi ko tana wani yawon badalar ko yawon ta zubar irin yadda take zuwa nan ta yi rashe rashe abinta bayan sunnan nan din gidan saurayinta ba na mijinta ba , ba kuma dangin junna ba?
Dan tsaki ya ja bayan ya kwonta yana kallon misss call din da ta masa.....
Wannan halaya nata sunne suka janyo, gayanan ta janyo masa wata fitinar da bai ga alamun tsohon nan zai rarasu ba, bale wace yake jin maganar tata ai ya gama yanke shawara da ita, a yanzu yana kyautata zaton wannan mai shagon da yake wuni wajensa shi kadai ne zai iya tunkara da zancen dan ya masa tsawa ya hanna abin, domin ya kula kamar sosai yana jin maganar kakan kurma.
Da wannan tunanin ya kwanta yana sakawa a ransa gobe in sha Allah zai samu kakan kurma da maganar dan ya dakatar da abin tun kafin yayi nisa, gashi yana ta batun ko baya so a ja maganar? Allah mai iko.
Washe gari, tunda sasafe suka shirya suka nufi kauyen Mirya wajen jana'izar daya daga cikin abokan Aban, wanda ya jima yana jinya Yanzu lokaci yayi , kasantuwar ba a cikin garin bane sai da suka cika motoci da jama'ar gidan suka nufi kauyen, bayan an yi jana'izarma sai da yama ta yi lissss sannan suka dauko hanyar Damagaran, a gajiye sosai suka karaso gida hakan yasa babu wanda ya kula dan uwansa suka shige dakunnansu dan hutawa kafin su fita sallar isha'i
ELHAJI HAMZA bayan an yi sallar isha'i ya yi kiran Baba da kansa a waya ya shaida masa gobe zasu zo wajen yarinyar, yana fatan ya sanarwa yarinyar? Baba ya tabbatar masa ai ya sanar mata ba wata damuwa suka kashe wayar
Sunna kashewa baba ya sanarwa Mama bakon na Karima gobe zai zo dan haka su zauna cikin shiri, nan take ya shiga duba kayan da suke da na tarbar bako , ya gama yin list din abubuwan da za'a kawo gobe da sasafe domin ko ruwan roba ashe babu a gidan sai na piyawata da tarin lemun yara yan goma goma Abin takaici, to hauka ake yi a tarbi Alhaji da piyawata? , su dai daga Mama har amarya sun gama gane bakon nan na mai gidansu ba karamin bako bane, dan haka suka zuba ido sunna kallon ikon Allah, har safiya ta yi aka ringa shigo da ruwan roba da kayan cefane da jus din kwalba masu tsada kai harta falonsu sai da yayi tsaye aka fitar da kujeru aka wanko aka cenza su cafet da komai ya ja musu kashedin du mai son kansa da lafiya kar ya taka cafet ko ya hau kujeru har sai bakon ya tafi......, da haushi haushin hanna shi sauke bakon bangarensa ya dubi gimbiya wace ta hanna din ya ce" Ki dai ji, yau bakon nan zai zo, walahi in y'ayanki suka hau min kujera ko suka bata falon nan naku sai na jinyata yaro da babarsa!, kuma ke zaki yi girkin tarbar bakon na fada maki"
Amarya da mamaki ta ce" Ama ai ka san yau girkina ne ko Baban yara?"
Sai da ya juyo ya kalleta daga kafa har kai kafin ya girgiza kai ya ce" Ai ba zan yi saken da sanadiyar dandanon miyarki zai ce bai ga abin aure ba, Ni dai da aka cuta an gama da Ni, ki tabbatar baki rabi tukunyar gimbiya ba in ba haka ba rai zai ɓaci matuƙa!"
Ya yi ficewarsa ya bar Mama da tarin takaici, ta dubi Amarya ta ce" Kin ga, ki dauki abinda ya shafi namu da nasa ki girka, Ni iya na bakon zan yi, babu wanda zai sa in kone a kan shiga hakin mutun ba, .......in banda gidan nan ina aka taba yiwa saurayi irin wannan sarautar? haka kawai, ko mijinta ne ma yi wannan abin bale saurayin da zai zo ganninta yau kawai? Allah ya kyauta , an kwashi yaya an kai min su gidan gyaran kai an dawo da su an hanna su fitowa ko falo wai kar rana ta taɓa su? ina jiran gannin wannan sarkin da Elhaji ke yiwa wannan fadar!"
Amarya na kallon Mama da tarin bacin rai ta ce" Hakane, du wani abu kin bi kin kange kin tare, ke komai ke komai ke, ko tsoron haduwarki da Allah bakya ji? Ni dai du idan aka shiga hakina ba zan taba yafewa ba !"
Ta yi gaba rai bace dan walahi ko nashin ba zata girka ba yau sai dai a yi abinda za'a yi, wannan mulkin mallakar ya isheta, a kan me zai ringa fada mata magana a gaban kishiyarta? girki ne bata iya ba ko tarin wulakanci irin na Elhaji? koda yake ba laifinsa bane, asiri babu abinda ya bari, idan aka gama da kai ko sunnanka mantawa kake yi bale , da sauki ma da har yanzu yake gane cewa ita dinma matarsa ce, dan mahaifiyarta bata zauna ba, kulun tana nema musu maganin mugun asiri da kuma fuskar Elhajin summa, ama ai da abin yayi yawa.
Hajiar ce da kanta ta yi girkin, kuma bata wani taso ya'yan ba dan gudun kar su shiga lamarin falon da yake nasu su bata a shiga uku, sai dai bata sani ba tana kicin din tana aikin Khadijah ta sadada ta yi ficewarta a gidan domin tana gamawa magariba na gabatowa Elhaji ya kuma rikitata a kan lalle lalle ta je ta yi tsaye a kan Karima ta shirya sosai da sosai, ta tabatar da tana fitar da kanshi mai dadi, kai abin har tsoro ya fara bata irin yadda Elhaji ke irin rawar jikin nan
"Khadijah , ki daina kukan mana, haba Anmy" Abdul karim ya fada a sanyaye bayan ya yi ya yi ta daina kukan ta ki dainawa
Ajiyar zuciya ta sauke a karron da babu adadi ta ce" Sai da nace ka daina shiga shirgina, idan soyaya kake yi da ita ai ba wani damuwa, shine zaka tsayar da Ni gashi na yi dare daga gidan inna, gashi ka tsayar da Ni har an fito daga masallaci, tabas yau sai Aba ya kasheni a gidan cen, bari in je, idan ya kasheni ka sani zan je lahira da kai a raina yaya Abdul "
Daga nan ta dauki hanya tamkar barauniya ta nufi gidan, tana tafe tana tsintar kannanun duwatsu a hannunta sai da ta tsinci kwaya shida sannan ta karaso daf da kofar gidan ta shiga a hankali ta dakata ba tare da ta waiga bayanta ba a hankali ta shiga addu'ar da ban san a inda ta koyeta ba, da duwatsun nan du idan ta yi sai ta jefa, gabas da yama, kudu da Arewa, ta wurgar daidaya, ta wurga daya sama ta duke da sauri tana tarewa da hannayenta dan kar dutsen ya fado mata saman kai , a lokacin ne kuma ta dauki dayan zata y'ar a kasa kunnayenta suka ji motsi a bayanta
A zabure ta juyo , lokaci daya cikinta na neman murdawa dan tsabar tsoro da firgicin kar aje wanda ta gama yiwa addu'ar Allah ya sa kar ya yi mata komai din ne a bayanta sai idannuwanta suka sauka a kan wani ustazzz
Eh, zata iya kiransa da ustaz dan jalabiyar dake jikinsa da kuma dogon gemun dake fuskarsa baki sidik, daga nan bata iya gane komai ba saboda tsoro ne ya kamata na irin tsayinsa da kuma hasken fatarsa, bata san lokacin da ta yar da dayan dutsen kasa ba, ta kifta ido ta sake dubansa kamar yadda idannuwansa ke kanta bayan ya dan rintse idon abinda ya sauka a kansa
A hankali ta furta" Sorry"
Sannan ta shige gidan da dan gudu gudu
Dutsen da ya dawo ya dakun masa ya duka ya dauka a hankali yana dubansa , sai kuma ya saka shi a aljihunsa ba tare da ya gane abinda hakan yake nufi ba
Kicibisss din da suka yi da Aba ya sakata direwa kasa ido na neman cikawa da kwala
Aba ya dubeta shekeke kafin ya gyada kai, a ransa ya ayana' wato gimbiya ta yi niyar sai ta neme Ni da balaki ko? yaya zan ce a je a tarbi bako ta tura khadija tarbarsa ko shirin da nace ƴaƴanta su yi su yi wanka su saka sababin kaya ita khadijar bata yi ba?, ba laifi
Cikin ikon mai sama Sarkin sarakai sai khadija ta ga adu'arta ta ci Aba bai gane daga waje take ba
a zabure ta mike daga kasan ta yi ciki da gudun tsiya ta nufi dakin Mama tana kyautata zaton samun mafaka a cen
Tana shiga ta samu yan matan gaba daya a nan ga Karima cikin shiga ta alfarma sai zuba kanshi take yi
ido ta ringa zarrowa ta zauna tana sauraron irin nasihar da Maman ke yi bayan ta dago ta yi mata kallon daga ina kike ta mayar da dubanta kan Karimar sannan ta sake duban su Khadija a tausashe ta ce" Idan ta fita suka gaisa, ku biyu zaku kai kayan tarbar bako, kunna kaiwa ku gaishe da bakon ku juyo, daga nan kar in ji kun zauna kun saka su a gaba kun ji ko?"
Lubna ce kawai ta amsa, Khadija kuwa tuni ta nufi wajen da aka jera kayan tana murmushi a ranta tana ayana' shikenan za'a yi biki a gidanmu da wayonmu muma? ai kuwa walahi dole Elhaji ya bari mu wataya mu dauko mai kalangu a buga, tabasss sai mun rakashe a auren gidan mu, bari dai in fara kaiwa dan fatana Allah ya sa dan duniya ne mijin ya mana diner a high classss mu faso muma'
Jug din da aka saka jus mai shegen kyau ta dauka, a nutse ta kama hanya ta nufi falo tana karra zance a ranta har ta bayyana a falon
turus ta yi a karro na biyu idannuwanta cikin nasa, haka kuma abinda ya faru da ita a dazu ya faru da ita a yanzu, wanda ta tabbata irin kashedin da babansu ke masu kwanakin nan a kan zuwan bakon nan ne ya saka yanzu ta ji faduwar gaba, na dazun kuwa ta ajiye haka a matsayin ta yi tunanin baba ne ya sameta a lokacin da take adu'o'in da suka dace da shi
Mamaki ne ya kamata, ta sake kallon mutumen daga kasa har sama ta kuma tabatarwa kanta eh abinda take gani kennan,, wato dan izala ne a zaune a falon baba, wannan wace irin muguwar kadara ce ta sako bawan Allahn nan gidan nan? innalilahi wa inna ilaihi raj'une, shin bai san kiyayar dake tsakanin baba da su bane?
Ba wai zagin addinin kowa suke yi ba, hasalima su a islamiyya an nuna musu cewar hakan ba kyau, babu wani dan izala ko dan kabalu da sauransu a wajen Allah, a gobe kiyama wanda ya riki Allah daya ya shaida Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wa Salam ma'aikinsa ne, ya guji aikata sabo, ya yi ibadar da aka haliceshi domin ta ne zai tsira, ba wai wani rigima ta yan kabalu da yan izala da meye meye ba, sai dai abinda ba zaku gane ba shine, shi fa baba da kuka ganshi an sha dakuwa da shi da malaman addini da suke wa'azi yake cewa yan izala, yakan ja rantsuwa tsakaninsa da masu tsangalalen wando da dogon gemu sai dai jifa, yakan ce shi ya fi karfin ko bangon gidansa suna izala ya raba, bale a tarihi masana suka ce a lokacin da ya nemi auren gimbiya an so kasa shi Allah ne ya taimake shi, to a lokacinma ya ce tabas ya gane yan izala na nemansa da balaki, to kuwa sun samu, ai shi da shi da duk wani abinda ya rabe shi ba shi ba su, ya sha sakin mace d'an izala ya aura yakan ce sai dai su saka tsohon takamminsa, shi dai ya riki akidar nan da zafi sosai, idan watan ma'uludi ya tsaya sosai ake hidima a gidansa, har ranar ma'uludin gidansa, sai ga wani bakon sababi idannuwanta na gane mata abu a zahiri ba mafarki ba
Alamun motsi ya saka ta karasawa tana sake kallon kaffafuwansa dake cikin safa, hakan ya bata haushi ainun har ta ajiye jug din ta dago kanta da nufin sake yi masa kallo irin na kwam ko dan idan ta rantsuwa ta kamata a daki ta ja ta kirta kai tsaye
"AMA, KIN SAN KALLON SHARA'A GUDA DAYA NE KO?" Ya fada a tausashe, yana dan kawar da dubansa daga cikin idannuwanta, lokaci daya kuma ya dan sake gyara rufar kansa
Ido ta zarro, ta dora hannu a saman bakinta a bayane ta furta" Lah!"
Sai ta dan dirirce ta ce" To wai Ni du na rikice, shin wanene kai din ne?"
Shima ya zuma mata ido a hankali ya furta" Ni ne bakon yau"
Ido ta kwalalo waje, sai ta tafa hannu a hankali ta zauna A ranta ta idasa da 'walahi talahi d'an sunna ne, ta yiwu baban malami ne, ama babanmu bai sani ba kau? kutttt kar aje ya sani ya daki banza a gidan nan mu shiga uku'
Juyowa yayi a karro na uku kennan ya zuba mata ido ganni ya yi kafafuwansa take kallo, kuma kamar zancen zuci take yi, a tausashe bayan ya ja hiramin nan baya ya kuma boye kafafusansa ya ce" Yaya zaki yi da goshina?"
Yanzu kam talabe haba ta yi, wato idan yayi kalkaltun nan wata dariya ke neman kasheta in ta hango yah baba a tsaye, innalilahi dole a yi balaki yau a gidan nan,, dole yah baba ya san wa ya zabawa y'arsa a yi tashin hankali sosai a gidan nan, dan haka ta yi murmushin da ya saka shi kallon kasan idannuwanta da kyau da mamaki, yana mamakin dimple a kusan ido har biyu sun wani lotsa abinsu, ta ce" Ama, ana shara'a da keya ne ban san kana bayana ba bakon yau"
Maganarta ta yanzu itama a hankali ta yi, kuma ta so kwaikwayonsa wanda a bayane hakan ya bayyana sakamakon kalkaltun da ta yi bayan a dazu ya kusa minti uku tsaye a bayanta tana adu'o'in da ba zai so ace su sauka kansa ba bale waninsa saboda domin Allah harda su idan hannun wanda zai daketa ya zo dukan nata ya kyandare ya zama kuturu, ta yi gaggawar fadin a'a idan ya zama kuturu babu abinda zai hanna shi yi mata kwondar kutare wace ta tabbata zafinta mai karfin gaske ne, gwara dai ya karye kowama ya huta?...... tabas a yau ya fara ganninta, sai dai me zai ce? *FARKON GANNIN IDANNUWANSA* da ita ya ga abin mamaki mai girman gaske.
Zai bata amsa karar takalmi da shigowa ya saka su dagowa su duka biyun suka kalli inda KARIMA ta shigo, murya a kurya sosai an makale cike da iya yi dan kuwa duka kaf abinda mama ta koya mata ba shi ta dauka ba, nata salon ta yi aiki da shi, domin ko a lokacin da mama ke ce mata ta zama mai kunya a gabansa dan kunya itace adon mace a ranta ta ayana' kunya fa? sai kace dai wata y'ar kauye? a'a dole zan ja ra'ayinsa dan ya gigice yace yana so na'
Tsayawar ta yi itama tana kallon Khadija dake duke daf da table din da aka ajiye dan a tarbi bakon, lokaci daya idannuwanta suka koma kan bakon wanda sai da ta ruko ido da mahaukacin mamaki tana dubansa kai har ta ji sabon hijabin nan zai rike mata wuya ta ja shi da karfi baya ta sake duban tashin hankalin da take gani murya a cinkushe ta ce"
07/12/2024, 14:53 - samiraharounayacouba: 🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*FARKON GANIN IDONA*
🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺🌸🌺
*LABARI DA RUBUTAWA*
*SAJIDA NIJAR*🇳🇪
*PAID BOOK*
*Y'AN NIJAR ZAKU TURO KATIN AIRTEL KO TA SAHELCOM TA DARI A WANNAN NUMBAR 93811618 SAI A SAKA KU A GRUP, YAN NAGERIA ZAKU YI TRENSFER NE NA 500 TA WANNAN ACCOUNT NUMBER 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai a bani shedar ta numbana kamar haka 93811618 , Sajida Nijar thank you 😍*
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
DUK KARYAR KADA
Y'AR MAHAUKACIYA
NEMAN NA KAINA
BANI DA ZABI
DAGA TAFIYA ƊAUKAR SOJA
BAK'A CE
KUTKALE
DUK NISAN JIFA
MAGE
IDAN KA RAINA INDA KAKE
DUTSE
NI ZAN LADABI
ZAKIN SARAKAI
WATA KOKOWAR
DA CIWO A ZUCIYATA
AURE YAƘIN MATA
AZAL
WATA TAFIYAR
*Shafi na sha uku (13)*
*TALLAH, TALLAH, TALLAH*
*META FORCE*
*menene meta force*
business ne ingantacce business ne mekyau business ne daizaibaki kudi 💯
tunda ake